← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 37

Sashe 19

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

~012 Alongside films shot~
*G 9 building* 4:22pm
✯
Zaune duka manyan director's dama ƙananun producer's suke cikin keɓan taccen wurin da suke gudanar da wasu manyan meeting nasu iyaka su yasu na. To yauma kamar kullum zaunen suke suna tattaunawa akan lamarin daya faru da ɗaya daga cikin manyan jarumansu wato *DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS* Se anan ne ma wasu ke jin abinda ya farun da itan. Tattaunawa sosai sukai director Abdulazeez Dakata daya kasance shi ne shugaban duka masana'antar shirya fina finan Hausa ne ya fara miƙewa daga nan se Muhsin Aliey Yahya shida Moh Ameern Saif. Mohan dake gabana ya juyo Yana kallon inda muhsin ke tsaye daga bayansa, hannuwansa cikin aljihun bakaken coat ɗin dake jikinsa. Iska se baza gashin kansa take har yana rufe may fuska. "Aikin ka na kyau babban abokin harƙalla" Moh Ameern Saif Jedaans ya faɗi da irin jinjinawar nan.
Dan gyara tsaiwarsa muhsin yay tare da fuskantar Moh Ameern ɗin se kuma ya kwashe da wata mahaukaciyar dariya yana furta, "Ai tun ta gama nuna mana ita ɗin ƴar zafin kaice dole mu sauƙe mata shi right?" Shima dariyar Moh ameen saif ya fashe da ita tare da furta. "Mutumina baka da kyau fa ko kayi wanka!!!" Moh Ameern ya faɗi yana sake kashewa da wata mahaukaciyar dariyan."Jirgi ɗaya ne ya kwaso mu nida kai, kaidai kawai ALLAH yakai damo ga harbawa ko be ciba zeyi birgima" chakk kuma Moh ɗin ya tsaye da dariyan da yake tare da furta,"Se dai ban fahimci wannan hausan ba muhsin?" Don yasan halin Muhsin ɗin tsafff na cin amanar ko waye a masana'antar.(Idan na gama da ita banzar zan dake kanka nake nufi) ya furta a cikin ransa a baɗini kuma yana kama kafadar Moh ɗin suka ci gaba da tafiya, "Daɗi na da Moh tsoro tamkar ba namiji ba, ace kana gafjejen namiji kamar haka 👌 baka san wannan karin maganar ta ALLAH yakai damo ga harbawa ko be ciba zeyi birgima ba na jinjina maka" shima ya faɗi yana zaro wayarsa ƙirar apple tare da faɗin "Inji alert" ɗan hararan keyansa Moh Ameern yay a ransa yana ayyana kaima ka kusa barin duniyar ai.transper ya masa na 1:ml. A take yay hanzarin duba alert na kuɗin da suka shigo masa.
_Debit: 320XXXX397 Amt: NGN1000,000 Date: 03-MAR-2025 19:28:33 Desc: QS894:DT/101300014444937337/234703638033. Bal: NGN5,5000000 Dial *894*11# to get loan_ wani ɗan banzan kallo ya cillama Moh Ameern ɗin yana me furta. "Kasan kuwa abinda ka tura min Moh? One million kawai fa ka tura wanda iyaka kafin alƙalami ma ni tashin farko 2 billion na bama yaran da suka mana wannan aikin, amma kai da ka tashi seka tura min One kawai"
Wani ɗan zame jajayen laɓɓansa Moh yayi tare da furta. "Iyaka haka naga dama kuma iyaka hakan zan bada, ba kuma wai don bana shi ba A ahhh sai don kawai hakan na ga damar baka domin kai kanka kansa koda harafin Bb ba zaka taɓa samu a cikin zuriyar mu har ƙarshen rayuwarmu kuwa" "to kuwa wllh zan tone gaskiyan abinda muka bisne Ashe Moh"
"Idan ka fasa ba ɗan halak uwa da ubanka suka haifa ba, wa ya faɗa na ana wa ire irenmu barazana? Stop your dirty mouth all over again" daga haka ya tafiyarsan yana barin Muhsin da saƙar jaki. Khadijah yobe ce ta ƙara so wurin bayan data gama tabbatar da barin Moh daga masana'antar baki ɗaya. Ta na sanye ne cikin Wando palazzo pink colour da Shirt Navy blue , ta yi Rolling wani veil navy blue a kan ta shi ma, se ƴar karamar bag black Itama dake rataye a kafadarta, hannun kuma ɗauke da wayarta. Skin nata ba Farar nan ce kal ba dark skin gareta kalan Wanda ake yayi ɗin nan. Kana tana da manyan idanu ma su ɗaukar hankali wanda cikinsu yake farare ƙal ba laifi. Ta na da shape irin me ƙirar coca cola ɗin nan wato hips da breast din ta cike su ke bamm.
Ta ɗan ɗauka loƙaci tana nazartan yanayinsa kafin ta saki ƴar siriryar dariya tana dawowa ta gabansa tare da furta. "Da dukkan alamu wannan Moh Ameern ɗin na son kawo ma aikin mu wargi" Fesar da wata zazzafar iska ta bakinsa yayi yana naɗe hannuwansa saman shoulder nashi tare da furta. "Yobe pls I hate this.. a yanzun kawai hutu nake da buƙata ba ƙarin wata damuwar ba" yana faɗin hakan yau tafiyansa yana barin ta wurin tsaye, Miƙewa itama tayi tana rufa masa baya tana me furta "Muhsin can pls I promise me you'll wllh nayi alƙawarin tayaka kawo karshen waɗan can wawayen JEDAANS ɗin can Moh Ameern da kuma Meesherh cikin sauƙi" tayi maganan tanason cimmasa don ganin kamar ba zai tsaya ɗin ba, baki ta buɗe da nufin yin wota maganar ya riga ta ta hanyar furta. "Kin tabbata?"
"Yes I promise I will" ta amsa daidai loƙacin da take cimmasan.
"Thank you Yobe Naaaaa'' ya faɗi tare da kyakykyawan murmushi saman fuskansa. Wata Ajiyar zuciya tasaki loƙacin da yake mata magana kan ta shiga cikin car nashi. Cigarettes ya zaro a cikin gidanta seda ya kunna ta da lighter kana ya tada kan motar yana yin reverse tare da ficewa a wurin baki ɗaya.

*SPAIN*

Flight É—insu yana landing motor Ambulance ta Hospital É—in tazo ta É—aukesu.
Chapter 19 · 0% Book details