← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 37

Sashe 4

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

# Ⲛᕪᐜ Ⲩᕪᵃʳ'ˢ
# 𖢧ᑋᕪ ᵗᕪᐢˢᑊᐤᐢ ꕯᐢ 𖢧ᑋᑊˢ Sᑦᕪᐢᕪ
# SoulmateVibes
# DeeplyInLove
# TogetherForever
# UnbreakableBond
# Endless Love
# SilentLoveAffair
# HiddenHeart
# ForeverAndAlways
# Ɩ૦𝚅𝞔 Ʀ૦Ꮇ𝔸𝑵ᑕ𝞔 𝗕𝔸𝗕Ⲩ
# ɑ.𝚔.ɑ 𝔸ɱɱҽ𝑦 ʟɑ𝑦ʟҽ𝔯һ
👇
https://t.me/+ISpf1lql0GwyNmJk

Duk me neman AMMEYLAYLERH ganan link nawa na Telegram Wanda kai tsaye idan kabi link É—in ze dinga kaika ga post namu kai tsaye.
👇 https://www.facebook.com/share/1A1gMDViUG/

Sannan kuma ganan na facebook don samun post nawa kai tsaye shima.

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
.... Tun da ta mai da doorhandle ɗin ta koma ta jingina da jikin ƙofan abubuwa da yawo na son dawo mata. tun da ga loƙacin da tafiyar su tasha banban da juna wacce wata shuɗaɗɗiyar Ƙaddara tazo ta ratsa tsakani. Haka kuma idan taso wannan ita dai ƙaddarar itane zata zo ta sake haɗe giɓin data riga da raba shekaru da ɗan dama.A zahirance duk inda Kalmar KADDARA take to kuwa kowa yasan kalma ce dake motsa zuciyar ko wanne bawa domin kuwa tabbas wannan kalmar ta KADDARA kalmace me girma da faɗi wacce ta ƙunshi abubuwa masu yawan gaske. domin kuwa Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwa juna.haka kuma kowacce rayuwa tafe take da nata salon ƙaddarar.
Idan har bawa zeyi haƙuri wajen jure wannan tarin ƙaddarorin da suke jerin gwano a cikin kowanne rai mai numfashi game da duk abinda ALLAH ya riga da ya ƙaddara a cikin rayuwarshi,To kuwa duk ALLAH Ya zaɓa maka shi ne mafi alkhayri agareka.
♡ Wani kalan Runtse rinannun idonta tayi sakamon kanta da taji ya wani kalan mugun sara mata da tsanin ciwo. Zaune takai bakin bed haryanzun hannuwanta riƙe da saman kanta dake jujjaya mata. Alamun zurfi datai a tunani nason haifar mata da wani damuwan. Wani kalan zazzafan numfashi ta fesar tana hana kanta bama damar tunanin. Domin kuwa ita ɗin mutumce me tsananin taurin kai da kuma ƙarfin zuciya. Ba kowanne abu take bama yay crossed mind nata ba, Wanda kai tsaye duk ta koya hakan ne daga garesa kasancewarta renonshi ce ita ɗin. Ƙin bama ko wacce ƙofa dama tayi na zurfi a tunanin dake son bijiro mata. Knocking doorhandle ɗin da akai ne ya katse mata tunani, zuwa loƙacin jikinta har rawa yake a mugun wahalce ta nufi doorhandle ɗin tana buɗe. Mah ce Mah ɗin ta ce dama ta sani tasan itace don kuwa bata iya kwanciya duk daren duniya se tazo taga Meesherh ɗin. Saurin rungumata Mah ɗin tay "Subhanallahi Meeshel ɗin Papiey'nta What wrong? Me ke damun ki?" Duk kuma seta bi ta ruɗe kasancewanta auta kuma ƴa mafi soyuwa a zukatan iyayen nata. Ganin duk yacce Mah ɗin tabi ta ruɗe ne ya sanya Meesherh ɗan janye jikinta ana Mah ɗin tare da ƙaƙaro murmushin dole tana furta.
"Headache ne kawai fa Maayh, Don't worry karki woni damu" ta furta wai duk a sonta na kwantarma Mah ɗin nata hankali. "A ahhh ban Isa ba wllh Meesherh dole ko dactor Asia tazo ta duba min ke" tay maganan ne kuma tana laluben number na dact ɗin, Maganan second sukai ta datse ƙiran. Kai tsaye kuma ta maida akalan ƙiran kan Billionaire Sameer Jadeens. Se dai jin ring na woyar dap da ƙofarn shigowane ya sanyata katse ƙiran, Cikin yanayi na nutsuwa da hutu da wayewa suka gama ratsawa ya sanyo kansa bedroom ɗin.
Yana sanye cikin kamilallar shiga ta blue in jallabiya ta maza se hular nan irin ta kafiye nacin nan. Zama yay a gefe da daman Meesherh ɗin suka sanyata a tsaƙiyansu. "Ꮇҽ𝚔ҽ ᙏα𝓶αɳα ђ𝔞қ𝔞?" Kai tsaye prof 𝙎𝙖𝙢𝙚𝙚𝙧 Jedaans ya tambayi Meesherh daidai yana kai hannunsa saman goshinta. Maganan dayay shirin yine ya tsaya may a maƙoshinsa sakamakon knocking door ɗin da akai. Umarnin shigowa kai tsaye suka bada don sun san Dr Asia jamaal ce ta ƙara so. A natsenta ta shigo har cikin bedroom ɗin, gaidasu tay cike da mutumci da girmamawa take kuma ta shiga duddubata Injection ta mata tare da ajje mata magunguna ganin ba normal damuwa bane ya sanya Dr ɗin duban su Mah tare da furta. "Don't think about it totally don't worry, the only stress paining her Ina ganin da zarar ta ɗan sama natsuwa shikenan zata warware Insha Allahu" daga haka Dr ɗin ta musu sallama ta tafi bayan sun mata godiya.Ring ɗin da woyarta a ɗauka ne ya sanya ta duba me ƙiran. Yayartace Ummetah mebin Mohan Sameer Jedaans se ita kuma data kasance autarsu, "Meesherh kince zaki ƙirani baki ƙirani ba tun ɗazun right?" Cikin muryan da yay low Sosai ta furta. "I'm sick fa Aunt"
"Subhanallahi Meeshel baki da lafiya amma baki sanar min ba?"
"No karki woni damu headache ne kawai da wata ƴar damuwa ya haifar min hakan" daga ta can ɓangaren Aunty'n nata ta furta. "Bara na barki kiyi bacci se zuwa tomorrow morning Insha Allah" daga haka suka yanke woyan tana me sake komawa jikin Mah ta kwanta abinta.Duka da kallo suke binta a loƙacin da suka gama tabbatar ma cewan tayi baccin. "Allah ya inganta min rayuwar ki Meeshel!, Allah ya dafa muku gaba ɗaya daga ke har ƴan uwanki ya kuma raba min ku daga sharrin masharranta cikin gida dana woje" tayi maganar tare da jaho hannun Meeshel ɗin ta haɗe da ƙirjinta ta rungume,prof kuwa sai wani kalan murmushi kawai yake saki. Shima jikin Mah ɗin yaɗan motsa kaɗan yana kwantar da kansa setin shoulder nata. Yana rungumeta Ya jima sosai rungume da Mah ɗin,Nan ya shiga musu addu'a shima Mah ɗin na amsawa da ameen.
Seda suka gama tabbatar ma da kansu cewan baccin yay mata nisa sosai kana suka ja mata duvet suna rufeta kana suka fita bayan Prof Sameer ya sake mata adda'an bacci.
★
The great Billionaire juraij Jedaans ne zaune kan wata ƙerarriyar cough yana snye ne cikin wata rantsatstsiyar lallausan farin yadi wanda yake lafe a farar shiny skin nashi wanda kai tsaye ke bayyanar da asalin hutu da luxurious life ɗin dayake cikinsa. Fuskansa sakaye cikin wani yankakken farin gilashi, System ce a gabansa ya zuba mata fararen idanuwansa wanda a zahirin gaskiya bawai kallon nata yake ba ya tafi ne duniya irin ta tunani.
Wani zazzafan numfashi mara sauti ya fesar jin yanda zuciyarsa ta sake karta masa a karo na ba adadi.Yasan kaff duniya haka kuma kaff rayuwar Sheikh juraij Jedaans babu abinda yake haɗawa da bautama ubangijinsa haka kuma shi kaɗai ne abinda keda tsananin mahimmanci da girgiza dakkakiyar zuciyarsa. Me bi ma hakan baya kuma ita ce Zuciyarsa! Bugun numfashin sa *MEESHERH SAMEER JEDAANS* domin ita ɗin ta kasance tamkar renonsa ce. Duk da cewar Ƙaddara ta riga da ta buɗe tafin hannun kowannensu ta masa zanen rubutacciyar ƙaddararsa, wanda har hakan kai tsaye yay sanadiyar ban bancin ra'ayin su koma yace rabuwar su. Hakan ba shike nuna cewar ze barta har abada ba, kana hakan ba shike bayyana cewar ze barta taci gaba dayin duk kalan abinda taga dama, sosai yaji ransa ya sosu da ganin fitar Moh Saif Ameen a ɗakin nata wanda Allah ne kaɗai yasan yadda ya kwana da wani kalan masifan ɓacin ran hakan a daren jiya. Wani gauron numfashi ya kawo yana sake zubama laptop nashi farare ƙal ɗin idanuwansa.
Pisc na Meesherh yake kalla a cikin laptop ɗin idanuwansa har kalan bala'i bala'in yaji suke mai na ɓacin ran ganinta cikin wasu shegun riga da wando outpit. Wanda kai tsaye yake tabbatar da cewan a shooting film ne tayi koda ma a cikin Film ɗin ko waƙa. Ya rasa me Meesherh take nema a duniyar ta rasa dahar ta jefa kanta cikin shirin fina finan Hausa. Idan suna take da buƙatar yi ya tabbata Kaff Duniya babu inda sunan *JEDAANS POWER MENTION 💪 PEACE and RESPECT* be gama zagaya da kareɗe wa ba a duniya. Haka kuma Idan kuɗi take da buƙatar ya tabbata ita kanta tana da dukiyar da bata san iyakarta. To amma me take da buƙata a wasan Hausa?
A har kullum kwanan duniyar shine tambayar daya rasa amarya har zuwa yanzun kuwa da yake a zaune gaban System nashi. Idan kuma yay duba da yadda Ubangiji yake juya lamuransa daga kyawawa zuwa munana se ya sake jinjina lamarin ubangijin da babu kamarsa a duniya dan kuwa shine kaɗai wanda ya isa yayi abinda babu wanda ya isa juya hakan. dan yana da tabbacin idan wani na juya ƙaddarar wani da tuni ya jima da juya ƙaddarar Meesherh, A kaf cikin duniyar nan ya tabbata babu abinda ya rasa a rayuwa hakama babu abinda bazai iya zubar wa domin ganin ya dawo da Meesherh kan hanya se dai wannan maganar ta *TUN RAN GINI* da tsarin ƙaddararta ya daɗe da rubuta komai da ze wakana da rayuwar ko wanne bawa nashi. Amma duk da haka bazai gajiya ba wajen kaima Allah kukansa kan ya dawo mai da Meeshel ɗin sa hanyar daidai.
Janye fararen idanuwansa da sukai ja yayi a kan laptop ɗin a sanyaye kuma ya maida ya rufe yana sauƙe numfashi me zafin gaske. Knocking ɗin da aka danna ne ya sanya shi dawowa duka cikakken tunaninsa. "Yes Come In" cikin wannan kamilallar muryan ya bada izinin shigowa. Mohan Sameer Jedaans ne ya shigo hannunsa riƙe da wani kyakkyawan farin yaro mai tsananin kamanni da ubansa,shi kuma uban me irin kamanni ɗaya Meesherh Sameer Jadeens. A natse ya iso har inda yake Sheikh ɗin yake zaune,zama yay natse domin badan ban bancin kamanni ba da babu abinda zai hana ace uwa ɗaya uba ɗaya ne suka haife su ba. Yanayin sanyinsu iri ɗaya da yanayin shiru shiru ɗin su da kamala, wannan kamannin banbanci shi ne kaɗai ze nuna maka cewan ba uwa ɗayan ce ta haifesu ba, sedai duk da haka suna fisgen kamanni na alaƙar jini me ƙarfin da yake gudana a tsakan kaninsu.
soft Fararen hannuwansa ya miƙama yaron daya kasance me sunan shi, domin Mohan Sameer Jedaans kai tsaye sunan Sheikh juraij ɗin ya sakama yaron. Wanda Sheikh kema wani kalan mahaukacin so na tashin hankali,Yes shi kansa yasan yana son yara sedai tayaya me zeyi auren bare har a haifar mishi yaran?
A kullum kwanan duniya shine tambayar dake addaban zuciyarsa. So da Ƙaunarsa a gun mace ɗaya yake baida feelings akan ko wacce irin macece koda kuwa zatay yawo tsirarane a gabansa. Sedai a yanzu yasan wannan ɗin ya zama kamar tarihine don ko kyauta aka bashi baya jin ze ko iya kallonta a matsayin mace, macen ma kuma ta aurensa. tun iyayensa na damuwa da rashin aurensa har suka tattara lamuran suka miƙa buƙatunsu wurin me du ka me kowa me komai wato ALLAH. Ɗan gyaran muryan da Mohan yay a karo na biyu ne ya dawo dashi daidai ɗin sa. Magana ne sukai akan zaman meeting ɗin da yake da shi da ƙarfe 11:30 na yau. Daganan suka ɗan tattauna maganganu akan yadda al'amuran kasuwancin nasu yake tafiya.
Chapter 4 · 0% Book details