← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 37

Sashe 35

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren su Aysha kuwa tare da Rumaisa me napep ɗin nan na sauƙe su sukai cikin gidan su Rumaisa ɗin kai tsaye. Da aunty'n Rumaisa suka fara cin karo se kuma baby'n Nuwaira. Cike da murmushin jin daɗi suke kallon Aunty ɗin tamkar yacce baby'n Nuwaira ke kallonsa da murmushin itama. "ALLAH yayi aure da mara kobo dai Aunty Amaryar mu🤗 fine dai Diamond Meesherh Jedaans ta amshe mu da hannu bibbiyu ba tare da duba da yanayi ko suturar dake jikku nan muba,ganan ma harda ƙarin tsaraba" Aysha ta faɗi take dama ba'a kasheta a zance a kwana ƙalau bare ayi tunanin zaunawa lafiya. Woyoyin hannuwan nasu dake bi da kallo da kuma uban kuɗin da ya kusa tashin kanta. "Bara ki kalla Aunty gudun kokonta" Rumaisa ta faɗi kai tsaye tana buɗe wayanta tare da shiga cikin Mx pleyar nata dake pisc da video's ɗin da Meesherh tayi tare da sune kaɗai ya sanya bama tasha woni wohalan nema ba da pisc ta fara tun a na farkon Aunty Amaryar ta wani kalan zaro ido woje tana toshe bakinta da hannuwanta alamaun mamaki me girman gaske na ratsata. Haka ta ci gaba nunnunamata har zuwa kan video's ɗin da duk ta musu. Wani ihun tsalla baby'n Nuwaira ta saki tana furta "Yes wllh taci sunanta wato *SPECIAL* _TA DABAN_ kenan kalla nima a yau na zama shaidar hakan don kuwa ganau ce ba jiyau baaa...." Daga haka ta falla ana kare zuwa gidan su Aysha ɗin tun kafin ta isa.
Nan ma da ihun murnan ta isa Umman Aysha ɗin wacce ke alwulan ƙiran magriba da taji an fara yi a wosu masallatan dake kusa. Miƙewanta daidai da loƙacin da Aysha da Rumaisan na shigowa, itama nuna mata sukai wanda hakan ya wanzar da murmushi kwance saman fuskarta me taushi. "Ubangiji ALLAH ya bata abinda take nema duniya da kuma lahirarta! Ya kuma saka mata da gidan ALLAH mafi tsada ya kauda ita daga duk wani sharri dake shirin tunkarota ko wanda suke tare da ita badan ALLAH ba, Ubangiji ya biyata da mafificin Alkhairinsa tamkar yacce itama take Alkhairan wa mutane" duk da amenn suka amsa suna jin ƙaunar Meesherh ɗin na sake kanainaye ko ina na cikin jikinsu. Alwalan itama Rumaisa ta kama ita kuwa Aysha dake fashin Sallah ƙasan bishiyan dake tsakar gidan ta nema tana zama. Deta nata ta kunna kai tsaye tana buɗe Gmail address tare da shiga cikin pley store nata, kai tsaye app's ta shige sauƙewa wtsp lite se Tiktok da dai sauran app's masu muhimmanci. Tiktok ta fara bude da nem account nata inda ta buɗe da *ƳAR LELEN MEESHERH JEDAANS* haka ta ringa buɗe app's da sunayen ƴar lelen Meesherh ɗin har zuwa kan wtsp nata. A kuma duka dp profile nata pisc nata tare da Meesherh'n take sanyawa. Se bayan data gama seta komai tayo send's na duka abubuwan ta zuwa new Phone nata samsum galaxy me shegiyar camera kamar me. Ɗora duk wasu pisc da videa na Meesherh ta fara ta ringa post har zuwa kan wanda sukayi tare. Wanda hakan ya ɗauke ta ɗan lokaci me sawo. Cikin ƙanƙanin lokaci Aysha ta sama mabiya sama da dubu biyu da wani abu, wai ma hakan iyaka yau kenan seya school Meta nata wanda a da suke discount nata nata following nata ciki kuwa harda masu ƙarfin halin mata magana.
Ita ma Rumaisa buɗe komai tayi sedai ita da sunan Rushuna person ta buɗe tare da baza pisc da video na Meesherh. Dan da nan itama se gata a media tana shawagi. Cikin ƙanƙanin lokacin yaran suka yara wasu mahaukatan FAN'S su kansu.
ꨄ
Zaune take kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun dake jere a gaban Railer'n Hotel ɗin ta harɗe ƙafafunta tana ɗan duba ipad nata fuskarta se hasken ipad ɗin ya sake haskaka kyakkyawar Innocent face nata. Cikin takunsa na ƙasaita yake tunkaro inda take zaunen idanunsa lumsassun nan na yawo akanta wanda suke a janye se kuma hakan yamai yanayi da kamar yana jin bacci ne baƙin sajen daya gama sake ƙawata kyakykyawar chocolate fuskarsa kyau yana nan kwance luff-luff haka ma bakinsa da hancinsa  mai kyau wanda ya dace da fuskar sa, sanye yake cikin jeans da riga masu kyan gaske designers,tinda ya tunkaro inda yake ta ɗauke kanta a gareshi, Ta inda ta juya kan nata ya juyo yana ɗan rankofowa gareta kafin a hankali cikin dakakken sautin sa me class yace. "Cwty barka da hutawa!" A fusace Meesherh ta miƙe daga zaunen da take  ta ce
" Wai kai wane irin banza ne mara hankali daƙiƙi mara aji?, Idan kai baka da tunani me kyau ne to inason daga yau kayi gaggawan fita a cikin rayuna all of you. Ko kai a naka daƙiƙin tunanin zaka iya ja da Meesherh Jedaans ne?"
Nose Mask na shi da kusan ya zama shi ne ɗabiansa ya zame jajayen tausasan laɓɓanshi masu wani irin ɗaukan hankalin mace na bayyana haɗe da tsayayyen hancinshi.fararen shanyayyun idanuwanshi ne suka ɗan rine ruwan hawaye na taruwa a cikinsu na ɓacin rai, sedai tsananin SO da ƙaunar da yake mata shi ya gaza bayyana ɓacin ran nasa bayyana. Hakan ya sanya a mugun fusace ya kaima iska naushi cikin tafasarn zuciya yana barin wurin baki ɗaya. Duk ma se taji baki ɗaya garin na fita a ranta iyaka jiya da yau kaɗai. Wanda kuma a yau ne dama za'a haska Film ɗin wanda ya kama da gobe kenan zasu koma gida. Wata nannauyar ajiyar zuciya take sauƙewa sanda ta gama tabbatar da cewan ya bar wurin. Duk wani shiri akan lounch Film ɗin an gama hakan ya sanya ƙarfe 8:15 na cika daidai duk wanda yake a cikin list na lounch Film ɗin bayyana, ciki kuwa harda ita uwar gayyar. Tsit kowa yay baki ɗaya suna maida hankali da nutsuwansu akan Gellary Odyssey screen ɗin dake shafe da bangon wurin. Tunda suka fara kallar Film ɗin wani kalan shauƙi shauƙi ke ɗiban masu kallon. Wani kalan gentle classic life aka shimfiɗa a cikin Film ɗin wanda haɗewa da kyansa har ya gama yin yawa. 12:20 cif cif aka gama kallar Film ɗin inda wanda sukay lounch na Film ɗin suka suka Bama Meesherh kyauta na wasu mahaukatan kuɗaɗe maƙudai na tashin kai, sedai ita a gareta ba komai bane domin ko ita kanta tana iyama mutum kyautan nin kuɗin sau goma ba tare data ko girgiza ba. Tun a daren dama an gama tanaja musu komi na komawa wanda tafiyan nasu ze kama ne se yamma bayan an sake tattauna akan Film ɗin da kuma yacce za'a sake shi kai tsaye a duniya. kwanan su uku a Lagos ɗin suka tattara suna barin Lagos zuwa kd kai tsaye ita daga gida masu shegun bugaggun manyan car's guda uku ne suka zo suka ɗauke ta se gida.

A cikin gidan kuwa su Ummeterh ne tare da sauran ƴan matan gidan suka shiga murna da ɗan ƙaramin shagali na dawowan Meesherh Jadeens lafiya gida. Bayan sun gama murnan first abinda ta fara yi shi ne Wonka,daga nan ta fito akayi diner duka daga can part nasu Ama ta nupa kasancewan dama su ba kullum bane suke fitowan. A zaune ta tarar da Ama ɗin ƙafafunta mike turaki na daga gefenta shima kishin giɗe. Tana zuwa ta rungume turaki tare da gaida su cike da tsantsan SO da ƙaunarsu tana kwanciya kan ƙafafun Ama ba yanda zata sakar mata nauyinta ba. Albarka da adda'an dacewa da kuma gamawa da duniya lafiya Ama suka shiga mata tana amsawa da ameen daga nan ta nasu tsaraban da tazo musu dashi. Wani irin rass haka taji ƙirjinta ya buga dan Sosai tayi ƙoƙari wajen mantawa da Sheikh ɗin. Kuma Alhamdulillh sosai se ta manta dashi dama auren nasa baki ɗaya tana mantawa dasu tun a daren ranar data bar kd. Cikin nutsuwa da kuma kwarjinin ya kutso kansa cikin parlour'n cike da wani irin majestic takunsa. Tinda ya tinkarota parlour'n taji numfashinta na fita da sauri bugun zuciyarta na ƙaruwa ahankali idanuwanta na kasa ɗaukewa daga kansa, Wannan nutsatstsen ƙamshin nasa mai sanyin daɗi da kai tsaye yake tabbatar da tsadarsa a shaƙa ɗaya na gwamewa da sanyin ac/n daya taho da ƙamshin nasa kai tsaye yana shige mata hanci yana sauya numfashin main babban palon gaba ɗaya da kamshinsa.
Sake buɗe kyawawan idanuwanta a kanshi tayi tana kallo tin daga fararen yatsun ƙafarsa dasuke wani irin fes kaman baya fita dasu sanye cikin versace shoes. Yana sanye cikin shigar lallausan cashmere fuskansa datake wani irin fresh na sake shining. Hannuwansa dake cikin aljihun cashmere ɗin jikinsa ya zare
Cikin sakewan fuska dake tafe da girmamawa ya furta. "Ama barka da dare" Yana zaunawa bayan yama inda take kwance kallo É—aya yana É—auke idanuwansa akanta, sakamakon raight jeans É—in daya lafe jikinta da white Cardigan É—in dake jikinta masu kauri.
Janye idanunta itama tayi ahankali tana ƙoƙarin danne ganinsan da tay.
Wani numfashi me ɗan nauyi ta haɗiye tareda danne ruɗewanta tana sanya dogayen yatsun hannunta farare tana kare fuskanta. Duk da yacce zuciyan sa ke sake ingiza shi akan sake kallon nata amma samm ya ƙiyama hakan tunda yasan haramcin kallon daya fiye ɗaya tattare da hakan. "Ƴar lelen pa'apahh'nta banji kin gaida pa'apahh ɗin naki ba?" Ama tayi maganan da biyu don son ganin reactions na kowa a cikin su. Shi idanunsa yaja yana lumshewa ita kuma tana saurin barin parlour'n a mugun guje. Wanda hakan ya saka wani Kyakkyawan murmushi kwacema tsoffin biyu dukansu don kuwa duk ɓoye ɓoyen da kowannensu keyi akan kowa an kare suke da hakan. Kuma dama alƙawarin Aure ne tsakanin su sedai duk sanda suka so bayyanar da maganan se woni abu ya faru mara kyau koma suji suna mantawa da zancen amren.
Chapter 35 · 0% Book details