← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 37

Sashe 23

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Saurin dafe kanta haɗi da dawowa daga duniyar tunanin data yafi mameey'n tayi jin numfashinta na ƙoƙarin fara seizing. Tuno wasu abubuwan da suka riga suka shuɗe datay. Wanda kuma take jin har a yanzun bawai ta saduda bane se dan ma tanajin har a yanzun tana kan bakarta bawai ta gajiya bane. Cikin iya taku da kuma yaudarar data saba tamkar koda yaushe tana komawa cikin room ɗin.
{Anan ina son haska mana wata ƴar hanya ce ta cewar. Ba kowa bane ze nuna maka soyayya a fili kuma har a zuciyarsa ta kasance hakan ba, haka kuma ba kowa bane ze nuna tsanarka a fili ya kasance kuma har cikin zuciyarshi haka ɗin abun yake ba. Kuma karka yadda zuciyan ka haka kawai taka rudarka akan haka kawai kaji ka tsani wancan ko kaji seka mulki wannan haka nan. Don haka karka yadda ka taɓa judging mutum by cover ba tare da ka tsaya ka gama karantar ya yanayin sa yake ba. Kuma kun ga anan ALLAH nason nuna mana cewan Meesherh yarinya ce kafin Allah, ba don Allah na tare da ita ba da yanzu ba wannan zancen ake ba}
✯
Alhamdulillah yau kwanaki uku kenan ciff da yima Meesherh aiki. A kuma yau ɗin ne kowa ke sanya rai da farfaɗowanta, dan haka tun sha biyu na daren yau ɗin kowa da kowa zuciyarsa take a cikin zullimi da kuma fargaban abinda ka iya zuwa yaje. Ƙarfe shida na safiyar ranar dayay daidai da Ranar juma'a Meesherh ta farka, Gaba ɗaya dactor's ɗin da suka mata aikin ne zagaye da ita suna fatan ta farka a gaban su ba tare da wota matsala ko damuwa game da aikin nasu ba, Se kuwa paah da Maah da suke cikin room ɗin suma, domin suma suna son ganin farkawan Shalelen nasu akan idonsu. Shi kaɗai ne ya lura da ɗan motsawan da yatsarta ƙwara ɗaya yay.hakan ya sanya shi kafe yatsar cak da kyawawan idanunsa akan yatsun ƙafarta nata dake motsawa, haka har zuwa hannayenta biyu da suma ke motsin. A hankali kuma gashin idanunta suma ke motsawarn kafin a hankali numfashin ta ke sauya salon fita daga na duniyar sumewa zuwa na wadda take a cikin duniyar rayayyu.
      Da farko bata iya ganin komai ba se taci gaba da motsa idanun sannu a hankali har ta fara ganin jama'ar dake kewaye da dakin dishi dishi. Idanun ta maida ta rufe tana ɗan matse fuska tare da daƙuneta, jin yadda Gefen ciki da kuma kanta suka mata wani kalan kummmmm,
Ahankali ta shiga ƙoƙarin ɗaga hannunta dake ɗaure da canular tana son dafe kai da kuma cikin nata. Se a sannan kowa dake room ɗin ya lura da farkawan nata. Tana kuma sake jarraba bude idon nata wanda kai tsaye ganinta akan Dr John Amaan ya fara sauƙa. tayi kusan sakan sha biyar tana kallonsa kafin ta janye kanta a hankali zuwa ga na kusa da ita.Kai tsaye basu faɗa ko ina ba se cikin Idanuwan Sheikh juraij lumshe idon tayi ta sake buɗesu akan Sheikh juraij ɗin still. Yanda take kallonsa haka shima yake kallonta cike da fargaban ALLAH yasa tana a taytayinta ne, Tafi tsayin 10 minutes tana masa kallon ƙurullah da duk ya ba kowa dake room ɗin tsoro, dan tamkar tana masa kallo ne me kama da rashin sanin nan. Ɗauke kanta dake ɗan jujjaya mata tai tana maidawa ga Maah. Gaban Maah ne yay wani kalan bugawa ganin yacce itama ta ƙureta da idon tamkar ya ce ta ƙure Sheikh juraij da Dr John Amaan. Kan papiey ta sake maida kallonta sema kawai ta meda idanunta tana kullesu don tamkar wacce ake mata kiɗa da ihu haka takeji a cikin kanta.
      Gaba ɗaya se duka jikinsu yayi sanyi har likitocin, dan da alama ta manta komai ɗin kenan. Tamkar kuma daga sama a bazata sukaji ta furta.
      "Pa'apahh!!!" Shi kansa dukan kansa ƙiranyan sunan shin datay yayi. Janye fararen idanuwan sa yayi yana lumshe su da kyau a kuma nutse yana lafewa jikin cough ɗin dake room ɗin. Duk da maganar tan da ƙyar ta fita amma duk sunjita kowa da kowa duk da cewan a hankali ne tayi maganan murya cen ƙasa. Rikicewa duk sukai da farin cikin jin har ta iya sheda woni a cikin su, su kansu dr's ɗin sunyi murna sosai. "Pa'apahh nan a ina muke?" Ta sake yin maganan muryanta cen kasan dai. Papiey ne ya bata amsa da cewan "$halele ki daina magana haka muna asibiti ne mun kawo ki baki da lfy" Ɗan maida idanunta tayi ta kulle acan ƙasan ranta tana me furta. {Ohhhh GOD!) Ta furta tana ɗan Runtse idanunta da ƙarfi. Ummeterh tace tayi saurin tashi tana taro kan Meesherh ɗin tana haɗawa da nata wasu zafafan hawaye na kwaranya a cikin idanunta. Sauƙar ruwan hawayen da Meesherh taji na ƴar uwan nata shi ya sanya nata idanun cika da kwallar itama da bata san kota miye ba amma kawai abinda ta sani tana jin kanta tamkar wata sabuwar halitta kodai akwai abubuwan da suka sanja a cikin jikinta. Kuka sosai Ummeterh take na tsananin tausayin Meesherh ɗin duk da kasancewan hasashe ne kawai har yanzun dr's keyi akan matsalan mahaifan Meesherh ɗin. Amma duk da haka da tausayi abun ace Tun kamin yarinya tayi Aure ta fara fuskantan manyan ƙalubale irin wannan. Mohan Sameer ne ya matso kusa dasu tare da sanya hannayensa duka biyun yana zagayesu suma yana ɗora kansa tsaƙiyarsu tare da furta. "Please mu daina kuka domin ba'a yima ƙaddara kuka. A duk loƙacin da Allah ya jarrabi wani bawa nashi da wata ƙaddara to ba kuka ya kamaci ace ya tsaya zaman yiba, Alƙibla ze fuskanta yayima ALLAH godiya domin baya taɓa jarrabar wani baya nashi face a ƙarƙashin ita wannan ƙaddara akwai ɓoyayyen wani abu bayan hakan! Kuma ita wannan ƙaddarar tamkar Inuwa ce domin kowa yana da nashi salon ƙaddarar. A kuma koda yaushe tana bibiye da mune matuƙar kar wai kaga ƙaddarar wani ka masa dariya domin kaima bakasan me gobenka zata haifar maka ba. Kalmar ƙaddara! Kalma ce mai ɗauke da rassa biyu walau ƙaddara mai kyau ko Akasinta. Ƙaddara abokiyar tagwaitakar inuwa ce domin bawa ba ya taɓa shallake ma tarin ƙaddarorinsa, Duk iya gudun ka duk iya saurinka baka isa kujema tarin ƙaddarar da ubangijin ya ƙaddaro taka bace, Dan Rayuwa da ƙaddara a tare suke tafiya tamkar ƴan uwan haka suke, tamkar yadda kowacce Rayuwa take tafe da tarin ƙalubale a cikin. A kullum kwanan duniya sake canjama bawa ajin karatunsa take domin yau ɗin kace kawai zata tabbatar maka da hakan, musamman idan kaga ta banbanta da ƙaddarar jiyanka!. Rayuwa mataki biyu ce Acikin kowacce duniya duk wacce kaddararka ta zabar maka zata kaika ne zuwa makomarta, sabanin shine kawai dace wajen banbance nagartacciya ko gurbatacciya don haka godema ALLAH ya kamata ace munyi Ummeterh, Matsalan da muke tunanin Meesherh tana da bashi ze sanya mu sata gaba muyi ta kuka ba" Ya kare maganan cikin muryan kukan shima, bawai don bayajin ciwo ko daci da raɗaɗin hakan a cikin zuciyarsa ba sedan kawai kwarara ita kanta Meesherh ɗin.
♡
A hankali Meesherh ɗin ta ɗago manyan fararen idanunta tare da kallon cikin tsakiyar idanun yayyen nata. Haka nan take jin wani irin abu a cikin jinin jikinta, Ji takeyi tamkar akwai wani abu da yake tafiya ba daidai ba, Numfashi me sanyi ta fesar tare da ƙara lumshe manyan idanunta tana jin yadda zuciyarta ke sake bugawa tana hautsinawa bugunta na sake gudu bayan hannunta ta sanya a sace tana share ruwan hawayen tare da sakin ɓoyayyar ijiyar zuciya tana son tantance a wanne mataki gudun zuciyarta yake?. Don sanin zata iya ɗauka ko fuskanta ko shanye wacce irin ƙaddara ce wannan dake tunkaro cikin rayuwarta. ♡
"Alhamdulillh!!!, Duk da bansan ko wacce irin ƙaddara bace take kewaye dani a yanzun haka? amma ina fata da kuma burin me sauƙi ce a gareni" Meesherh ta furta wasu siraran hawaye na saƙko mata kafin taci gaba da furta. "Ya Rabbi ya zul'arsheem majeed kaci gaba da jiɓantar dukkan lamari Naaaaa!!!. Kaci gaba da bani kwarin zuciyan dazan ci gaba da amsar duka jarabawowinka gareni Alhamdulillah ALLAH na gode da tarin ni'imominka gareni" ta faɗi tana kife kanta saman tafin hannuwanta ruwan hawayen na taruwa a cikin hannuwanta tana sake wanko fuskanta dasu. Da rarrafe Maah da ƙara sa garesu tana zuwa ta haɗesu duka su ukun ita cikon ta haɗu suka sake fashewa da kukan. Kafin a hankali ta shiga tapping gadon bayansu dukansu na sakin ijiyan zuciya. Kowa dake Room din ne jikinsa yay sanyi masu raunin zuciyan cikinsu har wasu na hawaye. Mammey ce ta mike tsammm dare da kara woya a kunnen nata like irin an ƙira tan nan tana son amsa woyan. Kai tsaye nesa can ta cikin asibitin ta fita.  A loƙacin da Mameey ta sama ganin nurse amalya yousouf kuwa rufeta tayi da faɗa tamkar irin uwar tan nan.
         Don hatta gaida tan da nurse ɗin keyi mammey bata bari ta amsa ba ta rufeta da jarabar miyasa sunsan bazasu iya aikinba suka amsa mata cewan zasu iya? Bayan kuma har maƙudan manyan kuɗaɗe ta riga data narka musu.
          Nurse amalya dai kallon mammey kawai takeyi sai waige waigen kar wani ya gansu take yi, don kunsan ance mara gaskiya ko a ruwa gumi yake. Ga kuma tsoron garƙame Dr Maheer da akai hakan ya sanya cikin son ta raba tafiyan sun tare da ɗan ja baya tana me kafe mammey'n da ido tare da soma faɗin. "Ni de yanzu ma na lura da cewan tamkar ƙwalwarki bata aiki da ƙyau Hajiya. Wannan ƙasar da kike gani ba irin africa ɗinku bace da kuka saba aikata ɓarna irin haka da kuma ɗaukar ran mutum ba abakin komai ba!. Sannan mutanen mu ba wawaye bane irinku da suke abu da ka babu wata ƙa'ida ko sanya idon wani akan ka. Duk da aikine mai haɗarin gaske amma a hakan abokin aikina yay ƙoƙarin gwada sa'ar sa sedai sa'ar bata je ko ina ba don a yanzu haka zancen da nake miki Dr Maheer na tsare a hannun hukuma, domin ƙirir ƙiri aka kama shi da ƙoƙarin kisan kai wa patiend namu. Ni ma ALLAH ne ya rufa min bargon asiri dan bansan cewan a ranar bane bama za'a ma ita patiend ɗin namu shi wannan aikin ba, SO dan haka ma ni ina gida bansan wainar da ake toyawaba, Ashe ni hakan ma taimkone a gareni domin kaff duniyar babu wanda besan su waye *peace and respect* wato _JEDAANS Power_ wai tunda kika shigo cikin asibitin nan baki ga yacce yake bala'i bala'in duka families ɗin naku ba?. dan mutane ne masu matuƙar mutunci karamci da kuma mutunci haɗi da ƙarfin iko a kowace duniya ba iyaka a wannan asibitin ba. So Please inason kiyi wani tunani akan kisan yarinyar data kasance jinin JEDAANS"
         A rikice Mameey ta furta "Ban gane duka maganganun ki Amalya kuna nufin kunci kuɗaɗena a banza kenan?"
       "A wofi ma kuwa Madame Fateemah Usman Sannan kuma shawaran da zan baki shi ne karki yadda kiyi ko gangancin saka wani wannan aikin domin kuwa tsaff asirinki zai tonu. Abu na ƙarshe dazan sanar miki kuma shi ne zagaye patient ɗin take da securitys ta ko ta ina bisa karrama wa Ahalin JEDAANS dama Me JEDAANS ɗin baki ɗaya wato SHEIKH JURAIJ THABIT JADEENS. Dan tunda kowa ya fahimci wannan patient ɗin tana da haɗi da mutum me girma irinsa kowa na cikin Hospital din suke wani kalan sake bata kariya da kuma sake ninka kulawarsu fiye data farko a gareta. Kana ita kanta yarinyan a ƙasashe'n ketaren ma ƙasa kaɗan ce basu san ko wacece DIAMOND MEESHERH SAMEER JEDAANS ba. Don haka I DON'T CARE YOUR MANNERS na barki lafiya" ta kare maganar da wani kaɗa ma mameey'n yatsun hannunta guda biyu tare da kashe ido mata idonta ɗaya cikin wani shegen murmushi. Tayi taku ɗaya ana biyu chakk ta tsaya sakamakon tsinkayar muryan Mameey'n da tay tana na furta. "Yaro duk inda yake akace yaro ne!A lallai ruɗin Kuruciya tana kararrawa a kanki amalya yousouf ji da kay kuma yana fusganki shekarunki ƙananune shi yasa ba zaki fahimta a irin ramin damisar da kike shirin jefa kanki ba amalya"
        Kallon ɗaya ta mata tana ci gaba da tafiyanta domin dai tasan tabbas data buga wasa da ƴar prof Sameer Jedaans Turaki kara ta buga da Fateemah Usman ɗin wacce ta kasance ita mata ce kawai a Jedaans ɗin. Wacce a koda yaushe tana iya tafiya itakuwa fa jinin gidan ake magana, bare uwa uba taga wannan Billionaire's ɗin wato SHEIKH JURAIJ THABIT JADEENS.
Chapter 23 · 0% Book details