← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 37

Sashe 37

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwanci tashi akace asaran me rai haka Ahmed xm ya dinga bibiyan Meesherh har seda ta fara kulashi, wanda cikin ƙanƙanin lokaci wata soyayya me zafi ta shiga tsakaninsu su. Amma yasha fama tabbas ba laifi don wai duk dan ya guje mata har Matsalan ta da In banda su Family'n babu wanda ya sani seda ta faɗin meshi cewan barata taɓa haihuwa ba. Amma amsan daya bata shi ne dalilin daya sanya kai tsaye ita kuma ta buɗe masa zuciyan ta. "Meesherh be wai haihuwanki ko rashin haihuwan ki nake SO ba ke zatinki nake SO har cikin zuciya da ruhina kuma na yarda in aure ki a hakan in yasa mu mutu hakan ba tare da tunanin samun haihuwa ba Cwty..."
Wannan maganan nashi dama wanda yakan faÉ—in mata makamantansu sune suka rinjayeta a kansa. Wanda yakai a yanzu har gidama amsan da maganar Ahmed xm É—in.
An kuma saki Film nata a duniya wanda yaja wani irin ƙura a duniya don kuwa duk inda ka gilma maganar Film ɗin ake wanda ya fita da wani irin zafi na garari. A wannan karon kamm har gida Jedaans Aysha suka zo suka kawoma Babbar Role model nasu ziyara. Inda suma suka zama manyan yara sosai wanda a yanzu suke yawan ganin Meesherh ɗin akai akai. Suma kansu sunan su wani irin fice yay a duniyar gajimare. Wanda suke nasu video's ɗin suna ɗaurawa amma ba wanda zeja magana ba masu nutsuwa suke yi cikin aji. Kowa yana da salon nashi masoyan wanda idan ka leƙa shafin Aysha se kaga kamar tafi Rushuna person sunan, itan ma da ka shiga shafin Rushuna person ɗin saka kalla tamkar ma tafi Aysha ɗin suna. Wannan abu ma daɗa Hargitsa masoya mabiyansa.

Kasancewar shirye shiryen azuma ya gabato ya sanya uncle El-muaz da Uncle jamaal Jedaans dawowa Nigeria wanda duk shekararn duniya haka suke a gida suke azumi da kuma sallah. Inda dawowan nasu shi ne ya zama mabuɗin komai cikin sauri amma ba irin na garajeba. Dan kai tsaye a cikin ƴan tsakanin Awwb El-muaz Jedaans ya bayyana soyayyar sa ga Meesherh wanda dama sosai yake sonta amma ganin kamar da wota alaƙarn soyayya tsakanin ta da Sheikh juraij ne ya sanya shi kin bayyana mata love nashi. Amma da suka zo wannan zuwan se kawai ya buɗe mata zuciyan sa wanda ita kuma a lokacin da riga ta kamu da love ɗin Ahmed xm. Amma da akace jininka duk inda yake jinin kane se cikin ƙanƙanin lokaci ya rinjayeta akan soyayyar sa me tsafta da yake mata. Wanda tama iyayen dadi dan kuwa dama kowannensu auren Meesherh ɗin yake da burin ganin. Se dai wani matsalan da kai tsaye aka samu shi ne mahaifiyan Awwb ɗin Mum Khadija don kai tsaye tace bata yarda ba ba kuma da yawon taba. Da me yasa tun a azziƙi basu bashi auren Meesherh ɗin ba har se data sama matsala akan haihuwa a sannan ne kuma za'a liƙa ma ɗan ta to wllh bata yarda ba.
Shi kuma El-muaz Jedaans Turaki ya ce mazawar ta hana auren Awwb El-muaz Jedaans da Meesherh Sameer Jadeens to taje itama a bakin nata auren. Sosai hankalin mum Khadija yake a tashe wanda take cike da tsabar baƙin ciki da takaicin zuwansun Nigeria'n kasancewan ita ƴer cen Islamabad ɗin ce. Alhamdulillh kuma haka aka shiga watan azumi lafiya cikin salama da buwayer Ubangijin al'arshi. Wanda kuma kai tsaye aka tsaida maganar auren bayan salla da sati ɗaya, ita kanta Maah bawai tana son auren ba har ma se tabi jin kwara Ahmed xm ɗin akan duk Family'n JEDAANS ɗin. ALLAH Sarki shi kuwa bawan Allah yana can bama ya kasar yana cen ƙasar saudia. besan wainan da ake toyawa ba. Dake komai na alaƙansu bawai sauyawa yayiba komai na alaƙansu nanan sedai ta gaza sanar masa da abinda yake faruwa domin wani mugun tausayi taji yana bata.
Haka kwanakin azumin ke tafiya ayi ba ayi ba har kaci karfin watan azumin wanda mafi yawan dake ribanta da irin yadda wannan shahararren malamin Sheikh juraij thabit Jedaans duk wani masoyi bemin fejin nashi dama wanda suke samun tafsr nashi basu son watan azumin ya ƙare. Domin wata irin nutsuwa ne ke zaunar musu da kuma karuwa daga irin yadda yake farke gaskiya akan komai ya kuma dilmiya masoyansa ji da son kasancewan Ina sune shi. Dan kallon ɗan baiwa haihuwan Sa'a kawai suke mai.inda iyaka aikin ladan da yake bazama jama'a kaɗai suke ƙara rikicewa akansa da ƙaunar sa. Banda gidajen marayu gidajen marasa ƙarfi kai dama kowa da kowa. Dan kawai ribata da watan me tarin falala da tarin alkairuka. Kuma har zuwa wannan lokacin babu abinda ya shiga tsakaninsa da Samha wanda a cikin watan azumin har kukansa yakai wa mahaliccin sa akan ya bashi feelings ɗin da zai iya fuskantan matarshi Samha ɗin. Kuma yanzu sosai yake ƙoƙarin ganin ya faranta mata kuma ƙoƙarin janyo ta jikinsa wanda wani bin har kwana sukanyi tare amma ba tare data taɓa kallon ko satin cibiyoyin sa bane bare kuma jikinsa. Ita kanta yanzu duk wani rawan kai nata se ta nema shi ta rasa ga uwarta data sako ta gaba akan lallai tasan duk yacce zatai tayi ta sama ciki ko cikin watan azumin nan ne. Sedai takai ta kawo woyar mahaifiyanta ma ta dena dauka a takaice don wllh ita tama fara gajiyawa. Sema kawai taji auren Sheikh din na fita a kanta. Wanda take jin tana gan da zuwa ta bayyana ma iyayensa cewan shi ɗin ba cikakken namiji bane in yaso komai ze faru ya faru. Se shima sannu a hankali ta fara janye masa wanda koba komi se hakan ya masa daɗi.
Gefe guda kuma har yanzun yana nan akan case na accident É—in Meesherh,wanda ya gama kammala komai akan case É—in bayan sallar yake jira akan ya dokasu a kotu. A ranar da aka kai azumi na ashirin cif a ranar ne Prof Sameer Jedaans ya bama Sheikh juraij waliyyin da zai É—aurama Meesherh Jadeens É—in aure.
Wanda iyaka waliyyin da aka bashi Anniey ta ringa surfa balai da masifan hakan har seda itama daddy ya taka mata birki kana ta shiga hankalinta amma kuma bawai ta haƙura tana ji tana gani a kaƙaba ma danta waliyyin auren Meesherh ɗin bane........

_ALHAMDULILLAH,ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH 🙏 🙏!!! Anan zamu dakata a book One na wannan littafi mai suna TA DABAN sai kuma Allah ya haɗamu da masu rabo a book two_

★Tofa masu karatu yaya take ne?.

Ni dai AMMEY LAYLERH nace lallei akwai kallo gaba_

_don tabbas Sheikh juraij zubama kowa ido yay ya gama tsalle tsallensa ya aiwatar da shirinsa da ya jima da kullawa_

_to ku a ganinku meke shirin faruwa ne wai......?_

_Shin ya kuke tunanin zata kaya tsakanin Anniey da kuma Sheikh juraij,gefe guda kuma ga Diamond Meesherh É—in mu?_

_Mike shirin faruwa?, Shin wanda tsalle tsalle ne Sheikh juraij ya barmu mu gama ya aiwatar da shirin?_

_★Magana fa ake ta aure sora befi 3 weeks ba Amma kuma hhhhhh Meta fharu Bara dai nai shiru?_

_★Hhhhh masu karatu akwaifa gurmi. Gurmi gagarumi ma kuwa na musamman. Dan littafin nan ɗauke yake da nasa salon shima. Hargitsi da cakwakiyar dake cikinsa kuwa ai ba'a magana wanda a da naso labarin ya kasance dogo kamar MIKIYA amma kuwa wasu abubuwa dana hango ya sanya ni yanke labarin yadda zefe shigar masu karatu, don wani lokacin ma yawan dogon rubutun kan gundira Reader's koba haka ba?_

_★Kai kar dai na cikaku da surutu ku shirya kawai tsaff domin warware muku zare da abawar dake cakude cikin wannan littafin_

_Duk zamu samu amsoshin wad'annan tambaya idan mun shiga book 2 da yardar Allah. Nan muka kawo k'arshen BOOK 1 NA SPECIAL Ta daban Wanda basu biya ba su hanzarta don kar ayi tafiyar babu su littafin TA DABAN Naira 500 ne kacal babu yawa_

_Ga duk mai son biya zai tuntuɓeni a wannan number_

👇
08104493215

Wanda suke sun biya zasu turo kuÉ—in su cikin wannan asusun bankin

👇

3206656358
Maryam Nasiru
First Bank

A turo shedar biya ta wannan number

08107880451

*_Kardai ku manta this one ma is not for free zaku Antayo darinku biyar ta Asusun banki na 3206656358 Maryam Nasiru first Bank ko katin mtn ta wannan number 08104493215 vip suma is 700 kamar yanda kuka sani masoya I no kuna bani goyon baya fiye da yanda nake tunani don haka ina ma kowa fatan Alkhairi don haka kar ku tsaya jiran ayi posting a sato muku na BABA NA BATI ku Antayo kuɗin ku karanta Cikin farin ciki da salama yanda kuke so sai najiku masoya karku sake ayi tafiyar PART 2 na SPECIAL BA TARE DAKE BA HAJIYATA by AMMEY'N LAYLERH'NKU me ƘAUNAR KU FAKA FAKA_*

_wanda a da naso littafin ya kasance ne akan 1k amma ganin na rage labarin ne ya sanya ni barinsa a 500 kacal_

*Byeeeeeeeee my Re@l f@ns sai mun sake haduwa a cikin PART 2 gamai Rabo. Dan koda kuÉ—inka Saida rabonka littafin TA DABAN ba hhhhhhhhhhh To ai shikenan sai a gimtse koooo?_

_A gimtse kawai baaaaa._

_
Chapter 37 · 0% Book details