← Book details Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 37

Sashe 13

Ta Daban Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Da dai duk sauran adda'o'in da duk suka zo bakinsa, kai tsaye ba zaka taɓa fuskantan tasbihi yake ba sedai ka kalla fatar lips nashi kaɗan tana motsawa. Sammm yama rigada ya manta da abinda ya farun yanzu ko na ce dazu. Ganin loƙacin ƙiran sallah yayi ne ya sanya shi fita, se da ya fara shiga bedroom nashi kana ya fito kai tsaye yana shigewa cikin babban masallacin dake cikin anguwarsu. Shi ne ya ƙira sallar ya kuma ja jami'i cikin wannan daddaɗan sautin nashi da sauraran yanda yake fidda tajweed nashi yake sanya mutane cika masallacin duk kuwa kalan girman da yake da.
Dama shi ka'idan sane baya shigowa se bayan sallar Isha'i sosai shi yasa kowa na gidan ke riga shi kammaluwa a dining room É—in,duk da kasancewar tonight baya zaman dining room É—in amma kuma hakan jiran shigowarn nashi ya zama kamar al'adan kowa.
Iyayensu mata kawai ya gaida kasancewar sun gaisa da iyayensu maza tun a can cikin masjid ɗin.Nan ƙannashi maza da matan suka gaida shi shima,A natsensa ya amsa su yana kallar bakin Meesherh da kuma Moh Ameern Saif da babu su a cikin jadawalin gaisuwar.
Directly balcony ɗin da ya saba zama kai tsaye wuce maids ɗin dake aikin shirya dinner ɗin na binsa da tea plask ɗin dake ɗauke da zazzafan tea wanda duk daren duniya shi ne kawai yake sha. Jere mishi tay daga inda yake idanunsa lumshe yana ambatar sunan ALLAH acan ƙasan ranshi. Se da ya tabbatar ta bar wurin kana ya buɗe idon yana jan tea plask gabansa. A natse yake sipping tea ɗin abinsa daga gefe dashi kuma System nashi ce yake aikin sarrafa ta. Yau be daɗe a wurin ba kamar kullum ya tashi ya tafi don yana da abinda zeyi a daren. Ga yawan bugun da zuciyarsa ke mai akai akai yana jin tamkar wani abu mara daɗi na dab da faruwa dashi, Amma sosai yay ƙoƙarin danne hakan se adda'o'in sa da yaci gaba dayi yana adda'an koma miye zai faru dashi to Ubangiji ya kawo shi cikin sauki ya kuma takai ta ma masa ɗin, da haka yanar wurin yana daura alwula tare da fara jero nafil fili wa mahalicci'nsa...

☆ Meesherh kuwa koda ta koma bedroom nata wanka tayo ta shirya kanta cikin singlet ta mata da wando. Army green da farar singlet inda tayi stocking singlet ɗin cikin wandon ta ɗaure da beld. Sai light green ɗin top wadda ta ɓalle duka maɓallanta ta barta a buɗe, Iskar da ake kaɗawa a gurin na diban rigar nata tana kamar zata cire,gaba ɗaya rigar tabar jikinta sai singlet ɗin kawai, tsaye take daga jikin window na bedroom ɗin ta tayi crossing ƙafafunta suna a harɗe. Sosae iskar dake shigowa ta cikin window'n ɗakin ke mata daɗin shaƙa tare da ƙamshin flowering dake ata bayan window nan suke sake bata nishaɗi da jin cikakkiyar nutsuwa, saima taji ta nema ciwon kan data shigo dashi ta ne meshi ta rasa.♡ Shi yasa most especially Idan tana cikin yanayi mara daɗi idan bata son fita balcony takan tsaya a wurin ne ta yaye duka labulayen wurin nan take samun cikakken nishaɗi sosai.
☆
Lumshe fararen idanuwanta tayi tare da faɗawa wata duniyar ta daban, tunani take akan baya idan tace baya tana tunanin Baya cann da dadewa kafin rugujewar komi. A cikin idanunta dake lumshe komai daya faru yake dawo mata daki daki tamkar komai daya faru ne a waɗan can loƙutan haka komai ya Shiga zeroying mind nata. Saurin dawowa hayyacinta tayi sakamon zuciyan ta da taji tana son maido mata da hannun agogo baya, Bayan nan da har gaban abada bata fata da burin dawowarta cikin rayuwarta koda a matsayin mahaifin ne a gareta. Domin mahaifiyarsa ta rigada ta gama ɓata komi tun a wancen loƙacin. A yadda ta tashi ta tashi ne ta buɗe Ido da shi, Shi ne mutum na farko data fara ƙira da pa'apahh...........
Akan shi ta fara koyan magana tana yima kowa ƙyuwwa amma banda shi ciki kuwa har da Maamah'nta. Domin matukar Meesherh tana wurin juraij bata yarda da kowa bata kuma zuwa wurin kowa se pa'apahh'nta juraij. Ta kai ta kawo ko bacci zatay se da shi a gefenta, shi ke maga wanka ya wanke mata fufu idan tayi, ya goye ta a gadon bayansa da zani irin yanda uwa kewa ɗan ta, a loƙacin shi yana da shekaru sha bakwai a duniya ita kuma tana da 1 year's a cikin duniyar, Shi ne ya Renata yaci kashinta yaci fitsarinta har zuwa sanda ta shekara biyar a duniya, A kuma daidai loƙacinne abubuwa suka soma Sanja kansu, suka kuma soma samun saɓani wanda shi ne farkon jinin tubalin da har ya kai su ga irin wannan matakin da suke kai a yanzu. ♡
Duk wasu ɗabi'iu kalan nashi take yi masu kyau a da can baya kai takai ta kawo ko cima bata cin abinda baya ci, iyaka abinda pa'apahh'nta yake ci itama shi take ci. Saɓanin farko da suka fara samu a cikin rayuwarsu shi ne tun da ta ɗan ƙara wasu shekaru a cikin shida zuwa tara/goma ya fuskanta ita ɗin mayyar jin kiɗe-kiɗe da waƙe waƙe ce, ga shegen son kallon tsiya a wurin ta kamar me, duk yacce zeyi don ganin ya cire mata hakan abin yaci tu ra. Har yakai ga ya dena shiga lamuranta na wasu ƴan loƙuta haka zata zo ta shige jikinsa tayi ta masa koke koken banza har se ya dawo ya kula ta, Amma hakan bazai hana gobe ta sake kunna casunta ba, haka zata sa ata sawo mata irin kayan indiyawa sune kayan sawanta. Ya tattare ya ƙone amma haka Maama zata sake sawo mata wasu. Kai har takai ta kawo Meesherh ta dena shiga cikin duk wasu lamura na Juraij ta dena tsoronsa ta dena ƙiransa da sunan data bashi na pa'apahh wanda a da yayyenta shi kuma ƙannensa koda mutum ne yay kuskuren ƙiran sunan shi da sunan da ita kaɗai take son take ƙiransa da abinda to kuwa ranan wunin rigima zata wuni tana yi. Amma se gashi sannu a hankali komi nasu na sake samun saɓanin ra'ayi.
Se kuma a karo na biyu loƙacin da ya fahimta Film ta karanta, wannan shi ne tushen komi...
Shi ne tubalin dayay sanadiyyar rugujewa da watsewar komi don a nan ne Mahaifansu suka samu babban saɓani na farko kowa ya nuna nashi na shi ne. Daga nan komi ya tsaya musu cakkkk kowa ya fita a rayuwar kowa fita wacce suke jin fita ce ta har gaban abada abadan.
☆
★Wani gauron numfashi ta kawo me kyau lokacin data tuno kaɗan daga cikin wani sashi na rayuwar da suka shuɗe na baya. Tsaye ta miƙa daga zaunen data kai gefen bed nata zuciyarta na wani kalan bugu very slowly ta miƙe. Waƙar (pareshanura ) ta cikin film ɗin Dhruva na jarumi _Ram Charan_ Wacce sukai da _Rakul preet_ ta kunna tana ƙure volume ɗin. Waƙar na sata shiga wani yanayi mai wuyar fassara tare da ɗebe wan can tunanin nata tana ta rawa tana juyi abinta. Ita ta bari on repeat tayi ta kuma dawowa daga nan ta koma waƙar *BAD BOY* ta cikin film ɗin _Saaho_ wacce jarumi _Prabhas_ tare da _Jacqueline fernandez_ kai da kaga yacce take rawan zaka tabbatar da cewan ehhhhhh lallai wannan dole a ƙira ta da TA DABAN ɗin, don kai tsaye kai baka isa cewan ba ita ne ta hau waƙoƙin ba kai tsaye bare kai duba da kalan shigar dake jikinta. Shigowan Maamah'nta shi ne ya katse ta don loƙacin 11:30 na dare harya gota. Kwantar da ita Maamah tayi bayan ta tofeta da adda'an bacci,seda ta ƙara kamar 15 minute kana ta fita a daƙin a tunaninta bacci Meesherh'n ta samu, sedai bata sani ba idonta biyu tana fita ta tashi zaune wani abu na mata suka a cikin zuciyarta. Wanda take yawan jin hakan a da a yanzu ma shike ƙoƙarin gaza control nata.

☆Around 11:30.
Chapter 13 · 0% Book details