← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 96

Sashe 93

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Toh Balarabiyar India na gode highly da kulawarki a gareni."

Murmushi Afeefah tayi sai dai bata ce komai ba, ta buɗe ƙofar bedroom ɗin ta fita.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma cikin bathroom É—in.

"Yane feefah bai dai zo ma ta da ciro bah koh?."

Hameeda dake tsaye bakin ƙofar ta tambaya.
Afeefah ta ce "Eh bai zo ma ta da komai ba an goda Allah."

Komawa suka yi Palo sannan suka zauna, Hameeda saman 3sieter Yayin da Afeefah ta zauna saman 2, tana faÉ—in.

"Auntie Hameeda jiya fa, naga É—aukar firan da kika yi da wannan budurwa da tayi rashin nasara wajen gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jahar Kano na shekaran jiya."

Murmushi Hameeda tayi ta ce

"Oho Juwairiya Jabir Bici, ae ina faɗa miki Afeefah Yarinyar ba ƙaramin tausayi ta bani ba, shiyasa ma saida Nasan Yadda nayi Dad yamin Hanya Nayi fira da ita cikin asibitin."

"Aikuwa abin dai akwai tausayi domin saida na kusa ma ta kuka a lokacin da naji labarin ta fa."

Cewar Afeefah, Hameeda ta ce "Ae shi ne ma Babban dalilin da yasa nayi fira da ita, domin ƙara wayar da kan mutane, yanzu kamar ita Juwairiya kaf Gidan su fa, wai YaYanta ne kawai yake mara ma ta Baya, ni banga amfanin mahaifiyar su ba Wallahi, menene amfanin uwan da ba za ta tsaya taji matsalar Yaranta ba, ae babu yanzu da Abin yazo da tsautsayi fa, duk da ba fata ake ba, ace ita Juwairiya ɗin wannan faɗin da tayi ta sama cardiology ko kuma wani ƙaton ciwon fah?.
Da sai dai uwan tayi kukan nadama only."

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke tana faÉ—in
"Please Auntie Hameeda idan kin san Gidan su, please Gobe zaki rakani, domin kuwa Haka kawai naji ina so naga Yarinyar face to face."

Murmushi Hameeda Tayi sannan ta amsa ma ta da cewa

"Sosai ma nasan Gidan su, dama nima gobe ina shirin zuwa duba ta, saboda Yanayin aikina bai bari naje duba ta ba kinga sai muje tare."

Hmmm wannan Aiki naki ma, ae kina ƙoƙari highly highly domin kuwa idan ni ce, wallah Bana iyawa."

Cewar Afeefah cikin kyaɓe fuska

"Kin ji ki feefah da wani zance, ae gwara aikin jarida akan wannan aikin da kike karanta na likitanci amma fa ganina?."

Cewar Hameeda.

"Duk da haka aikin jarida kamar zai fi wahala fa."
Afeefah ta kuma faɗa, taɓe baki Hameeda tayi
"Kyaji dashi dai don nidai duk da haka nafi son aikina domin kuwa yana bani nishaÉ—i obaaa."

"Wani lokacin kuma ya na sakaki kuka ko?."

Afeefah ta kuma maganar.

"Ke feefah rabu dani haka kinji domin kuwa aikine a gabana, na tsaya fira dake zuwa anjima zan fita nida wata Abokiyar aikina Humaira, za muje wani company ne, da ake zargi ana safaran mata da ƙananan Yara a ciki."

Waro Manyan idanunta tayi tana kallon Hameeda da tayi maganar hankali kwance, buÉ—e baki tayi zatayi magana, sai ga Deejarh ta fito daga bedroom É—in da take ciki.

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke bata ce komai ba, saima kallon Deejarh da tayi cikin murmushi ta ce

"My Deejarh kin gama ke nan?."

"Eh Balarabiyar India, na kammala."

"Okay yanzu ni wurin Amma zani zaki rakani ne, ko kuwa na tafi nika É—ai ke zaki tsaya anan?."

Afeefah ta Tambaya Deejarh É—in tana kallon ta.

"Eh zan rakaki wurin Amma É—in kawai."

Deejarh ta bata amsa. Miƙewa Afeefah tayi sannan ta kalla Hameeda tana cewa

"Auntie Hameeda bari muyi wajen Amma wata ƙila ma karki fita ba zaki gammu mun dawo ba."

Miƙewa tsaye ita ma Hameeda tayi tana faɗin

"Bari nima nabi ku wurin Amma É—in domin kuwa yau kwata kwata bamu gaisa ba, saboda makaran da nayi."

Gaba É—aya É—unguma suka yi suka fita a tare, daga palon kai tsaye suka nufa Hanyar da zata sadasu da part na Amma.

Buɗe ƙofar palon Hameeda tayi sannan suka shiga ciki, aikuwa nan suka Hango ta sanye cikin shiga ta alfarma tana zaune saman tattausar carpet. Yayin da gabanta kuwa Littafai ne kala kala wasu na Addini wasu kuma na Likitoci.
Idanun ta cikin medical glass white color.
Ɗagowa tayi tana amsa sallamar da suka yi, sannan suka ƙariso kusa da ita, gaba ɗaya suma suka zazzauna a ƙasan carpet suna gaisheta, amsawa tayi tana ƙare musu kallo.

Ganin dai kamar yau tsufan nata ya motsa ne, yasa Hameeda faÉ—in
"Amma Afeefah ce fa, kodai baki gane ta bane?."

Murmushi Amma tayi sannan ta ce "Au au ohoo Afeefah ta Wajen Abubakari ke nan. Na gane ta mana sosai ma, sai dai kuma wannan ta kusa da ita." Ta nuna Deejarh "Ita ce ban gane ba."

"Okay wai wannan sunanta Khadeejah fa, ita ma É—iyar Uncle Mai Kyau ce fa, sai dai idan kece baki gane ta ba."

Cewar Hameeda tana kwashewa su Afeefah ido.

"Ke Hameeda ja'irar Yarinya, an faÉ—a miki niÉ—in na makance ne ko kuwa?, wannan kyakyawar Yarinyar da ganinta ba É—iyar Abubakar bace, É—iyar Yarona Mai Kyau ne da gani."

Gaba ɗaya fashewa da dariya suka yi na jin abin da ta faɗa wato ba ɗiyar Abubakar bane, ɗiyar Mai Kyau ce. 🤣😂😅

"Kai Amma idan aka ce kin tsufa, sai kice a'a. Yanzu in banda rikicin tsufa, wanene Abubakar?, sannan kuma wanene Mai Kyau?, ae duk mutum É—aya ko?."

Cewar Hameeda still fuskar ta ƙayataccen murmushi ce saman ta.

"Ae kyaji dashi ja'irar Yarinya ni dai nasan wannan Yarinya É—iyar Yaro na Mai Kyau ce ehe."

Cewar Amma tana ci gaba da duba littafan gabanta.

Dariya Afeefah tayi tana faɗin "Kai Amma wato dai har Yanzu baki manta Baya ba, kina nan da wannan karance karance naki na littafan Addini da na ɓangaren ki ko wato Likitanci, to nima dai bari na gani ko akwai wanda zan iya karantawa a ciki."

Afeefah tayi maganar tana duba tilin littafan dake gaban Amma kamar wata professor.

Murmushi Hameeda tayi sannan ta miƙe tsaye ta nafa saman sofa ta kwanta a saman 3sieter tana faɗin

"Ae sai kiyi karatu da kyau da kyau ni dai nayi nan."🏃

Kallon Deejarh Afeefah tayi ganin kamar ba ita ba, duk ta nutsu, a Hankali ta kira sunan ta.

"Deejarh."

"Na'am Balarabiyar India."

Ita ma ta amsa, Murmushi tayi sannan ta ce
"Karfa kice zaki sakawa kanki damuwa, domin kuwa da haka aka fara gaba É—aya, ba kanki fa rau ba."

Deejarth ta ce "Amma Balarabiyar India lokacin da kika fara yi, ya kikayi sannan kuma ya kikaji ne dan Allah?."

Deejarh tayi ma Afeefah tambayar tana dariya.

Sai da tayi tambayar kuma tayi saurin rufe baki, mana kallon Amma, dariya Afeefah tayi ta ce

"Ae indai Amma ce batama san kinayi ba, saboda haka saki jikin ki mutumiyar."

Washe baki Deejarh tayi jin abin da Afeefah ta ce sannan ta kuma cewa

"Ya kikaji ke a lokacin kuma kina ina ne?."

Wani murmushin tuno baya Afeefah tayi tana lumshe ido ta ce

"A Lokacin wai. Eh toh a Lokacin muna ƙasar Jamus ne, ni da Zaynerb da kuma Daddyn.
Ae deejarth ina faɗa miki bazan taɓa mantawa da lokacin ba, tsawon rayuwata, wato dai abin da ya faru shi ne.

Wata Ranar Monday na dawo daga school goye da Backpack ɗita, na fito daga cikin Bus na makarantar mu, wacca ta saukeni a ƙofar gate na gidan mu.
Kamar ance na kalla ƙasa, a lokacin kawai na tsinci kaina da durƙusawa ina kallon white socks dake ƙafafuna, aikuwa me zan gani?.👺
Nan fah naga wani abu kamar jini, kamar manja yana ɗigowa duk yabi ya ɓatamin safa ta, ina faɗa miki bansan Lokacin dana rintima a guje ba, ko tsayawa kula Baturen mai gadi, banyi ba, tunda Allah ya bani sa'a na shiga cikin gidan na dangana da Palo, aikuwa anan na sama Daddy yana duba wasu bayanai cikin laptop. Yayin da Zaynerb take daga can gefe tana Assignment cikin littafan ta na school.
Ae Tunda na shigo palon a guje ban tsaya komai ba. Nayi fatali da wannan laptop wacca Daddy yake aiki ciki. Ban tsaya bah, nanfa nan na shiga birgima ina faɗin shikenan kwanana ya ƙare zan mutu nima wajen Haihuwa tunda Jini yana fito min, shikenan nayi ciki a taimake ni.🙈
A lokacin Zaynerb da ta fahimci komai, in banda dariya babu abin da take min. Yayin da shi kuma Daddy kallona kawai Ya tsayi yi, saida kyar aka samu nayi shiru da kyar da ban baki, sannan ne fa, Daddy da Zaynerb suka min bayanin komai, domin kuwa violence highly highly da nake ciki bai bari na fahimci komai ba, duk da dai lokacin ba wani yawau ne dani ba sosai..."🤣

Tunda Afeefah ta fara zuba zance babu abin da Deejarh da Hameeda dake saman 3sieter suke yi banda dariya, Deejarh harda Birgima a ƙasa tana riƙe ciki saboda mugun dariya. Yayin da Hameeda kuwa sai da ta faɗo daga saman 3sieter da take kwance tsaban dariyar ƙeta.

Shiru Afeefah tayi tana kallon yadda suke dariya babu ƙaƙƙautawa, ita ma kawai saita fara dariyar cike da Nishaɗi.😅🤣😂

Su na cikin Haka sai ga Lailah, Zaynerb, Haleesat, Nainarh, Nailah, da gaba É—aya Yaran Uncle Yusuf da kuma Haseeya da Mah'eesha Yaran Uncle sagir suma sun shishshigo gaba É—ayan su, gaisar da granny tasu suka fara yi.

Gaba ɗaya tsayawa suka yi suna kallon yadda su Hameeda suke ɓaɓɓaka dariya cike da kamar zararru, yayin da Amma ta zuba musu ido tana kallon ikon Allah.

"Ikon Allah sai Look, toh mu dugu ko kuwa mu tsaya?, domin naga kamar Babu Lafiya anan fa."
Cewar Yasira tana zare idanu.

Ido cike taf da qwalla saboda tsaban dariya Hameeda ta kalle su cikin É—an dariya take faÉ—in

"Please ku tsaya, ku zazzauna."

"Ah taya ya zamu zauna bayan kuma kuna dariya sai kace waɗanda suka sama taɓin kwakwalwa. Ni tafiya ma zanyi dama nazo nayi ma Amma sallama ne." cewar Nailah tana shirin fita.

Ganin Haka Yasa duk suka yi tsit Afeefah ta ce
"Please Auntie Nailah zoki zauna, ae mun gama dariyar, jin Haka yasa gaba ɗaya Ƴan matan suka zazzauna a tsakiyar palon, gaba ɗaya suka gagaisa da Amma ɗin tasu sannan.
Chapter 93 · 0% Book details