← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 96

Sashe 31

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin tsantsan kyau da kamala daɗin daɗawa, ga wani uban kwarjini da ya ma ta, wannan bawan Allah dake a tsaye gabanta, sanye cikin Expensively GUCCI higher Dress, tun daga kan p-cap brown color, dake nutse cikin sumar kanshi wacca jelar ta, tsaban tsayin da take dashi, ta leƙo ta waje.

Har izuwa Cost shoes ɗin dake special kyawawan ƙafafun shi, komai na companyn 'GUCCI' ne, hatta tsadadden watch ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannun shi.

Ta sani kuma tasan sannan tanaji ana faɗin tanada kyau na nunawa a television kyau irin highly ɗinnan, amma yau kuma a yanzu sannan a wannnan taƙin, taga wanda ya damata a kyau nesa ba kusa ba, ya shanye.

Tsayawa tayi da kallon ƙurillan da take mishi, saida ta saita nutsuwar ta sannan ta kuma kallon shi ta ce "please bawan Allah, ka barmin wannan perfume ɗin, ka nemi wani."

Tun kafin ta ƙarisa mishi maganar ya jefo ma ta tambaya da faɗin.

"Because of what reason"

Yayi ma ta tambayar a gajarce, É—an jim tayi sannan ta ce "saboda ina sonshi sosai fa, kuma dani yafi dacewa, bawai dakai ba." Ta bashi amsar a É—an tsiwace.

Gyara tsayuwar shi yayi yana lumshe kyawawan idanun shi, sannan ya ce "amma kuma, na ga maza ne ko, And naga ke macece, So bakya buƙatar amfani da abin da, ba naki ba."

Kallon shi tayi jin abin da yace, sai kuma tayi murmushin rainin wayo ta bashi amsa.

"E, na sani akwai wanda nakeso naba ne shiyasa, sorry dan Allah ka bani, ka nemi wani, rayuwata zan ba, kuma kasan rayuwa yadda take ko?,"

Yi yayi kamar zai bata, sai kuma ya fasa ya jefa cikin kwandon dake gaban shi nasa kayan siyayyar, har zai tafi, sai kuma ya juyo ya kalleta sannan yace.

"ki nemi wani fa, wannan ya zama nawa."

Yana faÉ—in haka yayi gaba abinshi ya barta da bin bayan shi da kallo tana cizan yatsa.

Jin an taɓota ne yasa tayi saurin juyawa tana kallon wacca ta taɓeta.
Deejarh ce tana murmushi ta ce "Auntie Afeefah ina kikaje ne, inata neman ki, amma banganki ba, sai yanzu?,"

share maganar Afeefah tayi Sannan ta kamo hannun Deejarh É—in.
"zo mu tafi gida angama siyyayar, na yau,"

Bin bayan Afeefah Deejarh tayi, suka nufa wajen dasu Nainarh suke, saida suka jira su, Nailah suka kammala sannan suka ɗunguma suka fito a tare ma'aikatan gurin suka biyosu da niƙi niƙin shopping thing's ɗin da sukayi suka saka a wata mota na Mall ɗin, zata kai musu gida.

Kamar ance Afeefah ta juya, aikuwa tana juyawa ta hangoshi cikin abokanshi suna tsaye daga gefan kwalta, da alama wani suke jira, ɗan taɓo Lailah tayi, sannan ta ma ta nuni da shi, a daidai lokacin shima ya juyo....

Murmushi Lailah tayi domin ta ganeshi, 'SABBIR SALIS MAI NAIRA'.

cikin sauri ya ƙariso gurin da suke a tsaye, kallon Afeefah yayi sannan ya mayar da kallon shi akan Lailah, ya fa ruɗe ya kasa gane wacece ma Lailah a cikin su saboda yanayin shigar dake jikin su kala ɗaya ne, baya da hakan kuma Afeefah da Lailah suna ɗan kama, normally irin wanda ake samu tsakanin ƴan uwa da suka haɗa uba ɗaya😍

Ganin haka yasa Lailah tayi murmushi sannan ta ce "barkanka dai, aboki ya kake?,"

In rushing ya juyo yana kallon ta, sai kuma yayi murmushi yana amsawa da.
"Yauwa barkanki dai, Ƙawata, amma fa, ina cikin ruɗu na kasa gane wacece Lailah Mai Kyau ac ikin ku biyun?,"

Har Lailah ta buÉ—e baki, zata bashi amsa, Afeefah ta rigata da faÉ—in "Allah sarki, ae ga Lailah Mai Kyau nan, a gabanka, ko dai, baka gane ta bane?,"

Da sauri Sabbir yace "E' ita fa."

Afeefah ta kuma murmushi ta ce "to gata tsaye a kusada kai," ta faÉ—a hakan tana, kuma nuna mishi Lailah wacca tsaban mamaki yasa, ta saki baki tana kallonsu su duka, daga Sabbir É—in har ita Afeefah É—in da ta shirya komai.

Afeefah ta ci gaba da cewa "idan kuma baka yadda ba, ka kira wayanta, ae kanada number É—inta ko?,"

Aikuwa ba musu Sabbir ya ciro ƙatuwar wayar shi, a trouser pocket ɗinshi, ya lalubo lambar Lailah ya latsa ma ta kira. saigata wayar Lailah dake cikin jakarta tana ƙaran shigowar kira.

Murmushi Afeefah tayi Sannan ta ce "bari na tafi mota, na jira ku, kafin ku kammala."
Ta faÉ—a tana kallon Lailah dake galla ma ta harara ba ta bi takan Lailah ba, tayi gaba abinta.

Shiru ko wannensu yayi, kowa da inda yake kalla, da irin tunanin da yakeyi.

Shafa sumar kanshi irinna fulanin ainihi, yayi yana fuzar da iska, daga bakin shi.

"Ko kinsan kinada wani abu?,"

"Me kenan?," Lailah ta tambaya.

"ko kinsan kinada kyau, irin sosai ɗinnan, nasan ance miki kinada kyau, sai dai nasan ba'a taɓa ce miki kina da kyawawan idanu ba 😂

Kiyi haƙuri fa, rasa abin faɗa ne, yasa na faɗamiki hakan fatan banyi laifi ba, a gurin wannan kyakyawar jinin kyawawa mai kyawawan idanu."

Dariya Lailah tayi, domin kuwa ya bata dariya ba kaÉ—an ba.

"babu matsalar komai,"

Ta bashi amsa, still cikin murmushi.

"kai aikuwa dai kwara da kikayi dariya, don na kusa mantawa da wannan, a gaskiya dariya tana yi miki kyau highly highly😅

ᴀғᴇᴇғᴀʜ

Da barin gurin, direct Motarsu ta shiga, tana hangosu suna taɓa fira can kuma taga Lailah tana dariya, abin ba ƙaramin ɗaure ma ta kai yayi ba, a fili ta ce "ikon Allah Lailah kuma da dariya ga saurayi, Lallai abu ya girmama, haka tana zaune a motar saiga bayan wani lokaci Lailah ta taho bayan sunyi sallama da Sabbir.

Shiga motar Lailah tayi driver yaja suka bar gurin, a hanya Afeefah gaza jurewa tayi, ta kalla Lailah ta ce.

"wai kuwa menene ya faɗa miki, naga kina dariya ne, haka harda ƙyaƙyatawa?,"
ƙin kulata Lailah tayi, saima tambayar da ita ma ta jefo ma ta, ta ce "wai kuwai nace ina Deejarh take, naga banganta ba?,"

Afeefah tayi murmushi tana faɗin, "ah wannan karon motar su Haleesat ta shiga, ba tamu motar ba, domin cewa tayi saita shiga ko waca mota, taji irin ta😝.

Sannan bata ƙyale maganar farko ba, ta kuma cewa "wai me muka tattauna, da shi Sabbir ɗin naga kina fara'a haka?."

Lailah tayi murmushi sannan tana cewa, "shiÉ—in akwai shi, da barkwanci sosai fa, ina faÉ—amiki highly."

Afeefah ta tambaye ta da cewa "iya barkwancin gareshi, ko kuwa da wani abu ƙasa, da bamu sani ba?,"

Ta faÉ—a tana murmushi, "meyasa baki tsaya kinji, da gani ba?

Lailah tana maka ma ta hararar ta bata amsar, Afeefah ta ce "gani nake kamar bai kamata, na tsaya tsakanin masoya ba, shiyasa nayi gaba abina."😯

Da sauri Lailah ta kalleta ta ta ce "wani munafikin ne ya faÉ—amiki soyayya muke?."

Afeefah ta bata amsa "ke malama ni ba, wani munafikin da ya faÉ—amin, tunani ne ya faÉ—amin hakan."

Lailah ta ce "akwai ki barkwanci, wani lokacin fa, to wannan karon tunanin ki, bai faÉ—a miki gaskiya ba,"
Afeefah ta ce "da gaske nake, wata rana saikin sameni kina kuka, kina faÉ—in kinason Sabbir fa."

Dariya Lailah tayi irin hakan bazai taɓa yiwuwa ba, for Ever. sannan ta bata amsa, "your challenge is failed Insha Allah,"
Afeefah ta ce "Yarinya kenan, ai ba ke zaki faÉ—a, haka ba lokaci ne zai nuna mana."

Haka dai suka ci gaba da firan, har suka ƙarisa haɗaɗɗen gidan su, driver yayi horn, securities suka wangale gate motocin suka shiga gidan a tare.

Parking driver yayi, a gurin da aka tanada domin yi, suka fito a tare suka shiga ciki.

A palo suka tarar da Momy Rafi'at wacca bata fita asibiti ba, zaune ita da ƙanwar ta Momyn su Fareeda da Fadeela, da ta kawowa ƴar uwar tata ziyara.

Gaisar da ita su Afeefah sukayi kafin kowa ya nufi bedroom É—in shi cike da gajiya, Afeefah É—akin Deejarth ta wuce ta tayata shirya kayan da sukayi shopping a gurin da ya kamata.

"Ina da wata ƴar jan kunne gareki, kar ki ga, kin tsinci kanki cikin gidan Mister Mai Kyau, shahararren Billoniya, kiyi tunanin yin ko aikata wani abu ba daidai ba, zan iya cewa, kyakyawar ƙaddarar ki ce tasa, cikin lokaci ƙanƙani kika haɗe da ahalin Mai Kyau, tamkar dama can tare kuke, ina yi miki wannan ƴar jan kunne ne, badan komai ba, sai dan saboda gaba, wata ƙila zakiga wasu abubuwan da suke ba daidai ba, cikin gidannan, to ina mai jan kunnen ki, da kar kiyi gigin shiga cikin lamarin, ko kuma shiga abin da bai shafeki ba, domin haɗari ne babba ga rayuwarki, fatan zaki kiyaye, sannan akwai form da ake cikewa kafin a ɗauki ko wani ma'aikaci da yake aiki cikin gidannan.

Sai dai ke, ban baki form ɗin, domin ki cike ba, wanda nima bansan dalilin hakan ba, sai dai zan iya cewa saboda tun ganin farko da nayi miki, kika shiga raina highly, kuma na ɗaukeki matsayin ƙanwa gareni.

Khadeejah ina miki fatan nasara a raywarki, sannan barkanki da shigowa Ahalin Mai kyau, kyakyawan Ahali, waÉ—anda ba iyakar kyawun sura dana jiki ko fuska gare su ba, harda kyawun zukata, Ahalin Mai Kyau, Ahali Mai É—auke da sirrika kala kala, daban daban, ma banbanta.

Zan baki form ɗin, zuwa wani lokaci domin kiga yadda tsarukan aiki a gida Mai Kyau yake, da kuma sharaɗin da ake cikawa da alƙawura, sannan badan komai zan baki ba, sai dan ki kasance mai taka tsantsan cikin gidannan, domin kamar yadda na faɗa miki ne, kyakyawar ƙaddarar kice ta kawo ki gidan Mai Kyau.

Fatan kin Fahimci bayanin da nayi miki kuma, zakiyi aiki da wanda ya kamata, malama Khadeejah?,"

Afeefah ta kammala wannan doguwar maganar kuma bayani game da jan kunne, ga Deejarh, daga inda take a tsaye gaban window tana shaƙar fresh air, yayinda kyawawan idanun ta suke kallon, can waje ɓangaren da swimming pool yake.

Ajiyar zuciya Deejarh ta sauke, tana tuna shekaru uku baya, kamar haka aka zaunar da ita ana, faÉ—a ma ta irin waÉ—annan kalaman da Afeefah tayi ma ta yanzu.

"Insha Allah Zanyi Amfani da Jan kunnen ki, gareni Balarabiyar india, sannan nagode tuna tarwarki gareni."

"You are welcome Dear"

Afeefah ta amsa ta.
Chapter 31 · 0% Book details