← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 96

Sashe 17

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read

Shiga gidan sukayi ita dai Dije sai ƙarema gidan kallo takeyi ga hasken lantarki da expensive lights ya haske ko'ina da ina na gidan, ga kuma shuke shuke gashi gidan ƙato gaske "ae yasin gobe da safe saina fito na ƙarewa gidan kallo, kai ina zan bari kallon daular aljannar duniya ya wuce ni, Dije ta ƙarishe maganar nata, a dai dai lokacin da suka ƙarisa bakin ƙofar palon katafaren gidan, don ita ma kanta ƙofar palon na glassa ne, kuma glass ba wai irin normal glass ba, a'a glass ne irin highly expensive glass ɗinnan wanda ba'a ko'ina ake samun kalar shi ba,sai gurin da naira ta zauna aci asha sannan aka tada kai da ita abar da take juya duniyar wato ita 𝑁𝐴𝐼𝑅𝐴💸💲💰

Dije a zuciyarta ta ce ita kanta ƙofar ma abin kallo ne harda Wani Glass, ga kuma gurin danna lambobin sirri, oh ni Dije ta ƙauye yau dai ina ganin ikon Allah da abin mamaki a birni,kuma a gidan shugaban ƙasa. Dije ita duk a tunaninta fah gidan president take,don tun lokacin da ta ga waɗannan jibga jibgan jami'an tsaron dake tsaron gidan ta sadaƙar da cewa nan fa gidan shugaban ƙasa ne, gwaggo ta kawota.

Kallon gwaggo dake knocking ɗin ƙofar palon tayi saboda ta gaza riƙe abinda ke ranta ta ce "gwaggo hala wannan gidan shugaban ƙasa ne ko?," dariya tambayar Dijen yaba gwaggo tayi sannan ta ce "a'a me kika gani?," Dije ta saki baki da hanci ta ce "lah wai dama nan ba gidan shugaban ƙasa bane, to gidan waye?," gwaggo ta ce "ko kaɗan ba gidan shugaban ƙasa bane," Dije ta ce "tabɗijan aikuwa dai...Dije tana shirin yin wata maganar taga alamar ana buɗe ƙofar palon, nutsuwa tayi a zuciyarta kuma cewa tayi bari na natsu saboda aji daɗin sakani a makaranta da wuri.
Wata haɗaɗɗiyar ƴar Gayu ce ta buɗe musu ƙofar, Dije tana shirin gaisheta taga ta juya ta koma bayan ta bisu da kallon banza, baki sake Dije tabi ta da kallo ganin gwaggo na shirin shiga ciki ta barta ne yasa tabi bayan gwaggon da saurinta.

Ae Dije baki,hanci, kunne,ido, ba abinda bata saki ba ganin irin haɗuwar palon na fitar sense ƙarewa palon kallo ta shiga yi kamar wata sakarya komai na palon sky purple ne and white color gashi ƙaton gaske 100by100.

Jin murya ana magana ne yasa ta dawo hayyacin ta tana bin Æ´an palon da kallo kamar yadda suma suke kallon ta.
Muryar gwaggonta ta tsinkayo tana gaishesu, baki ta kuma saki jin wai gwaggo ne take gaishesu su kuma ba kunya sun amsa a zuciyarta ta ce "bala'i Yasin ba shegiyar da zan gaisar tunda ba'a haifeni ba caɓɗijan, gyara tsayuwar ta tayi tana kuma bin mutanen palon da kallo a zuciyarta ta ce wa'innan suba turawa suba larabawa sannan kuma ba chanistawa bah🤣😂😅.

Afeefah dake saukowa downstairs ta hango mutane tsaye a palo kamar masu jiran kota kwana ga wasu abubuwa hannunsu kamar tsummokara🤣.
Ita batama gane su ba saida ta kusa saukowa sannan ta gane kosu waye cike farin ciki ta ce "laha'ila Auntie sa'adah kece?," da ɗan saurinta ta ƙarisa saukowa sannan ta ƙariso gurin su tana faɗin "Auntie sa'adah yaushe kika dawo ne?, yana ganki a tsaye ki zauna mana please, kallon Dije tayi wacca ta zuba mata ido kamar zasu zubo ƙasa saboda kallo.
"Lah Auntie sa'adah wannan fah?, ta tambaya bayan su Dije sun zauna a two sieter ita kuma ta zauna a one sieter. murmushi Auntie sa'adah tayi sannan ta ce "wannan Æ´ar yaya tace nazo da ita zata dinga tayani girki da wasu ayyukan. tayi maganar a gajarce.
Murmushi Afeefah tayi Sannan ta ƙara kallon ƴar kyakyawar baƙauyiyar yarinyar dake kallon ta har yanzu kamar ta sama television, ta ce "barkanki dai please may i know your name?,"

"Sunana die dee deejarth, eh deejarh." Dije ta faÉ—a cikin inda inda, game da daburcewa na ganin tsantsan kyau irinna wannan kyakyawar halitta dake gabanta.
"Hala dai kina inn inane" Afeefah ta tambaya.
Da sauri Dije ta ce "a'a banayi 'Balarabiyar india'.
Murmushi Afeefah tayi ta ce "Wacece kuma 'Balarabiyar indiyar?." Dije ta ce "ke mana ae kece 'Balarabiyar india' don naga kinfi wa'incan kyau, ne sa ba kusa ba Yasin. Ta faɗa tana nuna mutanen palon da suke harkar gabansu kamar basusan da wata hallitar a gurin ba inma sun sani to basu damu dasu bah🙄.

Kallon su duka Afeefah tayi yaran ƙanwar Momy Rafi'at ne Hajiya Sailiba, su biyu fareeda da fadeela twins ne sai kuma Lailah dake kwance a Three sieter da alama karatu take bacci ya ɗauketa sai kuma can dinning table Nainarh da Nailah ne suke cin dinner ɗinsu.

"To Ke ma miye sunanki" Dije ta tambaya.
"Sunana Afeefah Abubakar Mai ƙyau", "wow nice name" cewar Dije hadda haɗawa da ɗan turancinta da ta kowa a makarantar ƙauyensu. Ta kuma cewa "i'm very pleasure to meet you.
A wannan karon ba iya Afeefah ba hatta su fadeela, fareeda,su Nainarh da Nailah dake dinning room saida suka juyo suna kallon Dije da tayi maganar dan kuwa basuyi tunanin tanajin turanci ba, tun daga yanayin shigar dake jikin ta, huh to akan mema zasuyi tunanin tana jin turanci bayan kallon irin shigar jikinta,duk wanda ya kalleta lokacin kai tsaye da Villager girl zai kirata.
Dije tayi murmushi dan kuwa da gangar tayi turanci dan ta kankarowa kanta daraja, a zuciyarta ta ce jisu sun ɗauka kowama dusa ne taja qwafa🤓.

Afeefah ta ce "wow you are so cute and adorable."

Nanfa ɗaya Dije ta fara zarar ido tana rabawa dan bataji abinda Afeefah ta faɗa a ƙarshen maganar ta ba, turancin ma da tayi yanzu da yaya ta haɗasu, da kyar ta iya cewa "na gode," amma a ranta ta riƙe kalmar "adorable" ƙam saita bari daga ita sai Afeefah ɗin, zata tambaye ta fasarar kalmar.

Afeefah ce tayi magana, Dare fah nayi ta kallesu ta ce "Aunty bari da safe ma ƙarisa maganar yanzu kije ki kwanta kawai," sannan ta kalla Dije ta ce "follow me na rakaki ɗakin da zaki zauna," tashi sukayi dukansu Auntie sa'adah ta wuce ɓangaren su na ƴan aiki ita kuma Afeefah ta nuna ma Dije wani bedroom dake kusada kitchen, tana murmushi ta ce "bedroom ɗinkine shigo nanuna miki ciki," binta ciki Dije tayi hannun ta riƙe da jakar kayan ta, ɗakin yanada girma sosai ba lefi komai na ɗakin milk and Brown color ne.
Yanayin komai na ɗakin yayima Dije kyau sai faman washe baki takeyi ɗakin tsaf da alama kullum ana gyarashi bathroom suka shiga Afeefah ta nuna mata yadda ake amfani da wasu abubuwan dake ciki wasu kuma ta ce sai gobe, sai da Afeefah ta tabbatar da ta nuna ma Dije yadda ake amfani da komai sannan ta fita ta rufo mata ƙofar.

Afeefah na fita Dije ta daka tsalle ta haye saman gado a fili ta ce "huh saini Dije ta ƙauye a birni kuwa deejarh nake Yasin.
Tashi tayi tana kuma ƙara bin ɗakin da kallo iya yinta saida tayi iyayinta sannan ta cire yamu shashshe hijjab ɗin jikinta wanda yaga jiya yaga yau.

Toilet ta shiga jin ana kiran sallan isha'i alwala ta ɗauro as a muslim girl, bata tsaya ƙarewa toilet ɗin kallo ba ta fito, jakar kayanta ta buɗe ta ciro sallaya da hijjab sabo.
Gurin da taga an tanadar domin sallah taje tayi, bayan ta idar da sallan ta cire hijjab É—in, jakar kayanta ta É—auka ta fito da kayan ciki duka waje tayo dasu, saboda tsaban iyayi irinna Dije a wardrobe ta jeresu tas bayan tayi musu ninki irinna guga.
Sannan ta tashi toilet ta koma tana kuma bin ko'ina da kallo yayi kyau sosai gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta saman mirror ta kalla taga abubuwan wanke kala kala sai wanda mutum ya zaɓa.
Ae ba shiri Dije ta zaro ido ganin abubuwa na Æ´an gayu iri iri ba'a magana, kayanta ta cire, ta É—aura towel É—in da taga anyi hanging É—inshi in toilet wall.
Ɗaya daga cikin abin wanke kai ta ɗauka taga an rubuta "shampoo" buɗewa tayi tatso a saman hannunta sannan ta murza zuba saman gashin kanta saida ta gama sawa Sannan ta kunna famfo tasa ruwa ta wanke tas, wani ta kuma ɗauka taga an rubuta "All hair conditioner" ba tunanin komai shima ta wanke kanta dashi bayanta gama wanke sumar kanta da shampoo's ɗinne, tayi wanka ta fito ɗaure da towel fari ga wani a hannunta tana tsane sumar kanta dashi hand Drier ta gani da sauri ta jona a charge sannan ta fara bushar da gashinnata bayan ta kammala ko shafa lotion batayi ba ta je wardrobe ɗin data jere kayanta riga doguwa na material ta ɗauka duk taji duniya ta saka bayan ta gama komai ta haye saman bed sai bacci. {Dije anya kuwa wannan daga ƙauye take?, E mana gani nayi ae ta iya komai daya danganci bathroom sai kace wacca dama can ta saba shiga🤔}.

NKD ✍️ ✊

Khadeejarth Nainarh Kd.

𝐴𝑓𝑒𝑒𝑓𝑎ℎ 𝑚𝑎𝑖𝑘𝑦𝑎𝑢
Chapter 17 · 0% Book details