← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 96

Sashe 60

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri gate man ya ƙarisa bakin gate sannan ya wangale gaba ɗaya, sannu a hankali motocin suka shiga gidan, sannan a jere suke tafiya har suka ƙarisa wajen da aka tanadar domin ajiyar motoci, shikuma gate man ya mayar da gate ya rufe.

A hankali ya zuro ƙafarsa waje daga cikin Motar kana ita ma ɗayar ta biyo baya, daga ƙarshe kuma gaba ɗayansa ya fito daga motar, kamar yadda yasa ba sanye cikin Business suit black and White color.

Tafiya ya fara sannu a hankali a yayin da da escort service nasa suke take mishi baya, wasu kuma suka tsaya suna ciro trolleys a boot na Mota.

A dai-dai bakin ƙofar palo escort ɗin suka dakata, shikuma ya shige ciki yayin da waɗanda suka ɗauko jakunku nan na tsaraba suka biyo bayan shi a palo suka jere wuri ɗaya sannan suka fice abun su.

Staircases ya hau yana qwalawa matar sa kira, amma yaji shiru shi dai yasan yana dawowa zai sameta a Palo tana jiransa amma yau tsit kakeji, babu ita babu alamar ta.

Qara É—a ga muryar sa ya yi yana kiran sunan da ya raÉ—a ma ta

"Matar Mai Kyau.!"

"Matar Mai Kyau.!!"

Still shiru dai, da sauri ya tura ƙofar bedroom nata ya shiga tun daga kan mattress bathroom wardrobe babu inda bai duba ba, amma ba Rafi'at ba labarin ta, da sauri ya kuma fitowa wannan karon bedroom nasa ya nufa yana tunanin ko tana can ne bacci ya ɗauketa shi yasa bata fito ba.

Sai dai abin mamaki bedroom É—in nasa ma, ba inda bai duba ba, still dai babu Rafi'at.

Zuwa lokacin fa hankalinsa ya fara tashi danma shi É—in Namiji ne.

Fitowa ya kumayi ya shiga duba gaba É—aya gidan, amma ba Rafi'at ko alamar ta

Zuwa lokacin ya fara gajiya da nemanta domin kuwa shi ba Engine bane.

Dawowa palon ƙasa ya yi ya zauna ya zuba uban tagumi yana kallon tilin kayan wasan yara da ya bada ordered ɗin su aka kawo.
Can gefan zuciyar sa kuwa tunani yake wai shin yaushe ya fara son Rafi'at Rafiq Rayyan ne da zai damu haka da rashin ta?.
Ko dai ya manta ita ɗin Likita ce wata ƙila ma tana can anyi ma ta kiran emergency shi yasa ta fita ba tare da ta faɗa masa ba.
Wani ɓangare na zuciyarsa kuma cewa yake

"To dama kasan da haka shine zaka dama kanka kodai ka fara son matar mai kyau ne?."

Da sauri ya ba kanshi amsa da faÉ—i a fili "A'a ba sonta nake ba, unborn É—ina dake a cikinta nake so, ba ita ba, zuciya ta É—aya ce, kuma na riga na mallakawa wacce ta cancanta da samunta..."

Shiru ya yi daga hakan. Ya daÉ—e zaune a palon yana tunane tunane a cewarsa ba Rafi'at yake jira ba.

A kalla yakai mintuna talatin da biyar a wurin yana jira, can ɗa go kansa da zayyi suka yi ido huɗu da ita, a Yayin da take ƙoƙarin wuce shi, da alama bata lura dashi ba.

Da sauri ya miƙe ya ƙarisa wurin ta yana kiran sunan ta

"Rafi'at.! Rafi'at..!! Lafiyarki kuwa daga ina kike haka?."

Tambayar yake hankali a É—an tashe, ganin kamar ba'a cikin hayyacinta take ba yasa ya É—auketa gaba É—aya bai damu da cikin dake jikinta ba, ya wuce sama da ita.

A ranar Rafi'at gaba ɗaya jikinta kamar a sanyaye yake, saboda haka Abubakar bai takura ta da tambayar inda taje ba, saboda yasan yana yin aikinta daɗi da ƙari kuma ita ɗin mace ce mai ɗauke da juna biyu.
Wata ƙila a can Asibitin da take aiki ne taga abin da ya firgita ta saboda haka ya yanke shawarar ba zata ƙara zuwa wajen aiki ba har sai ta haihu.

Koda ya sameta da maganar bata wani damu ba saima cewa da tayi "Allah yasa hakan shine mafi alkhairi."

Zuwa daren Ranar kuma ta ware kamar ba ita bace jiki sanyaye da rana.

__*GAB@ KWANAKI BIYU*
{_TWO DAYS LATER_}

Suna zaune a palo Rafi'at kwance saman 3sieter Yayin da Abubakar yake zaune gefanta yana karanto mata wani £nglish story.
THE MOST BEAUTIFUL HEART.

Gaba ɗayan su labarin yana ƙayatar dasu yadda ya kamata.

Wayar Rafi'at dake gefe ne ta farayin ƙara alamar shigowar kira.
Da sauri takai hannu ta É—auka, sannan ta tashi zaune da taimakon mijinta, kara wayar tayi a kunne bayan tayi picking.

Shiru tayi tana sauraron abin da ake faɗa ma ta ta ɗayan ɓangaren.

Ko ƙaramin motsi ta gaza yi da alama ta fita daga hayyacinta, ganin kamar bata hayyacinta yasa Abubakar tambayar ta Abin da ke faruwa.
Kallon sa tayi kamar wata zautacciya batasan lokacin da ta saki Wayar hannunta ba, aikuwa ta faɗi a ƙasan tiles ba ta tarwatse.

Da sauri Abubakar ya janyo ta jikinsa yana rarrashi, ganin yanda hawaye yake zuba daga idanunta tamkar an buÉ—e famfo.

Sai da ya tabbatar ta sama nutsuwa sannan ya sake ta yana tambayar abin da yake faruwa.
Cikin shashsheƙar kuka Rafi'at take faɗin

"Haleesat Rashid Rayyan."

"Haleesat....

Haleesat ce wai wai ita ce..."

Sai kuma tayi shiru tana kuma fitar da siraran hawaye.

A mugun tsorace Abubakar yake kallonta sannan cikin tsananin matsanancin tashin hankali da murya wacca bata fitowa sosai saboda rarrabewar da takeyi wajen furta maganar yake faÉ—in

"Haleesat Rashid Rayyan. Kuma to Menene abin da ya sameta, ki faÉ—amin mana kinji Rafi'at Please..."

Ya yi maganar yana jijigata tamkar ta faÉ—a mishi Haleesat É—in rasuwa tayi.

Cikin tsananin kuka Rafi'at ta ci gaba da cewa

"Haleesat ce wai aka sace ta tun kwanaki huÉ—u da suka wuce shine, Sailuba ta kirani tana faÉ—amin...."

Bata ƙarishe maganar ba ta kuma fashewa da matsiyacin kuka kamar zautacciya.

Shi kuwa Abubakar za'a iya cewa suman zaune ya yi jin abin da Rafi'at take faÉ—a Tamkar shock na wutan lantarki haka maganar tazo mishi a ba za ta sannan kuma ta dake shi yadda ya dace.

Sun É—auki tsawon lokaci a haka ba wanda ya iya qwaqwqwaran motsi cikin su.

Sai can Abubakar da yake Namijin gaske ne, ya kalla Rafi'at bayan ya dawo hayyacinsa daga duniyar tunanin da ya lula yana faÉ—in

"Ki kwantar da hankalinki in Allah ya yarda za'a ganta nanda bada ɓata lokaci ba, kinji. bata bashi amsa ba, sai ma faɗawa jikinsa da tayi tana kuma fashewa da kuka.

Da yake a lokacin wuraren ƙarfe shida na yamma ne.

Yasa sai da aka kira sallar isha'i sannan suka shirya suka wuce gidan su Rafi'at.

Can ma dai banda kuka babu abin da Rafi'at take yi gaba É—aya Ahalin Alhaji Rafiq Rayyan sun taru anata faman addu'o'i ana fatan bayyanar Haleesat Rashid Rayyan cikin gaggawa daga hannun wa'innan kidnappers da ake tunanin sune suka sace ta.

Sai can cikin dare wuraren ƙarfe sha ɗaya sannan Abubakar ya ɗauki Rafi'at suka koma gidan su, gaba ɗaya jikin ko wannensu a mugun sanyaye.

🎀🎀ϝιʋҽ ʂƚαɾ'ʂ ɯɾιƚҽɾ'ʂ🎀🎀
💦💦ɯҽ αɾҽ ƚԋҽ ρҽɾϝҽƈƚ ɯɾιƚҽɾ'ʂ💦💦
✍️αʅƙαʅαɱι ყαϝι ƚαƙσϝι🤙

_https://chat.whatsapp.com/DP2UrllaLb34m7nsvgeNEd

__*💋 SARAUNIYAR KYAU💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Page *59&60*

__*

Rayuwa ta ci-gaba da tafiya kwanaki suna ja yayin da gaba É—aya hankulan Ahalin Alhaji Rafiq Rayyan yake a tashe na Rashin Haleesat Rashid Rayyan babu ita babu labarin ta.

To abin ma haka ne ta ɓangaren Rafi'at Rafiq Rayyan da mijinta Abubakar Mai Kyau gaba ɗaya sun ɗauki damuwar duniya sun ɗaurawa kansu.

Har takai ta kawo ma Rafi'at bata iya cin abinci sai dai idan Abubakar yana gidan ne, to shine yake takurawa sai taci kodan unborn ɗin su, wani lokacin sai dai ta saka masa kuka tana bashi labarin kyawawan halaye irin na Haleesat Rashid Rayyan gata da haƙuri ga son mutane.

Kwanaki sun ci gaba da tafiya har ya kasance an ɗauki tsawon sati biyu da sace Haleesat Rashid Rayyan amma har yau waɗannan masu kidnapping basu kira sun faɗi abin da suke buƙata ba, zuwa lokacin jikin kowa ya kuma yin sanyi lakwas, wasu ma sun fara tunanin kashe ta aka yi yayin da har zuwa lokacin wasu basu cire rai ba, domin kuwa INDA RAI DA RABO.

____

Zaune yake a tsakiyar palon, saman tattausar carpet sanye cikin jallabiya fara ga hula ita ma fara akan shi hannunsa riƙe da alqur'ani mai girma yana karantawa, daga gefansa kuma Rafi'at ce ita ma zaune saman lallausar carpet ita ma sanye cikin Arabian gown white color ga mayafi fari shima tayi rolling kanta dashi, hannunta riƙe da alqur'ani mai girma ita ma tana karantawa.

Sun É—auki tsawon lokaci a haka sannan a tare suka kai aya, kana suka rufe alqur'anan dake a hannun su.

Wanda hakan Ya yi dai dai da shigowar kira a Wayar Abubakar dake gefansa cikin nutsuwa irin nashi yakai hannun daman sa ya ɗauki wayar kana ya yi picking, a tunaninsa wata magana ce akan ɓatar Haleesat Rashid Rayyan da yasa ana binkcike na musamman, shiyasa bayyi tunanin komai ba ya saka Wayar a free sannan ya a je gefe ta yanda zasu ji abin da mai kiran zai faɗa.

Sallama suka ji mai kiran ya farayi, amsa masa Abubakar ya yi sannan Wanda ya yi kiran cikin girmamawa yake cewa

"Mister Mai Kyau wannan budurwa mai suna Haleesat Rashid Rayyan da aka bamu report na ɓatar ta ita ce aka samu can cikin forest {gandun daji} yayin binkcike, a halin yanzu an ɗauke ta izuwa Asibitin..."

Tun kafin ya ƙarisa cikin sauri Abubakar da Rafi'at har suna haɗa baki wajen tambayar sa wani Asibitin?.

FaÉ—a musu sunan Asibitin ya yi sannan Abubakar ya kashe Wayar basu tsaya jiran ko escort ba, ya É—auki Rafi'at a mota ita kanta bata damu da tsohon cikin dake jikinta ba, suka bar gidan sai a hanya ne ma Abubakar ya samu damar kiran su Alhaji Rafiq a waya ya musu bayanin abin da ke faruwa, sannan ya basu Address na asibitin da aka kwantar da Haleesat Rashid Rayyan.

**

A tare Motar su Abubakar dana su Alhaji Rafiq Rayyan suka ƙari sa Asibitin da aka kwantar da Haleesat ɗin, saboda tsananin tashin hankalin da suke ciki yasa basu tsaya gaisawa ba, gaba ɗaya suka ɗunguma ciki.
Chapter 60 · 0% Book details