← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 96

Sashe 38

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowa tayi chest ɗinta ɗaure da towel White color, sama sama ta shafa lotion saboda yanayin garin sannan ta shirya cikin kayan shan iska, riga fara mai hannun vest sai wando crazy jeans ash color, sannan ta ɗauko Ribbons white color nd ash color guda biyu, ta tufke doguwar suman kanta, ya zubo har gadon bayanta, wani siririn gyalle ash color ta ɗauka sannan ɗaura akanta tayi kyau ba ƙarya. Ta fito sak RAASHI KHANNA, gaban dress mirror ta ƙarisa ko powder bata tsaya shafawa ba, ta ɗauki man baki ta saka a siraran laɓɓanta jajaye dasu.

𝑳𝒐𝒗𝒆💘𝑮𝒍𝒂𝒎𝒐𝒖𝒓💋𝑫𝒆𝒔𝒕𝒊𝒏𝒚😼𝑻𝒐𝒍𝒆𝒓𝒂𝒏𝒄𝒆😥𝑹𝒐𝒎𝒂𝒏𝒊𝒛𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏_𝒉𝒊𝒈𝒉𝒍𝒚🌹𝑫𝒆𝒂𝒕𝒉😭𝑴𝒂𝒔𝒕𝒆𝒓_𝒅𝒆𝒗𝒊𝒍👹𝑪𝒉𝒂𝒎𝒑𝒊𝒐𝒏𝒔𝒉𝒊𝒑👑𝑪𝒉𝒆𝒂𝒕𝒆𝒅🤕𝐁𝐞𝐚𝐮𝐭𝐢𝐟𝐢𝒄𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💅𝑳𝒂𝒖𝒈𝒉𝒆𝒅😆𝒂𝒏𝒅_𝒑𝒆𝒓𝒇𝒆𝒄𝒕_𝒄𝒐𝒖𝒑𝒍𝒆𝒔_𝒓𝒆𝒍𝒂𝒔𝒉𝒊𝒐𝒏😇__𝑨𝒍𝒍_𝒊𝒏__S̟A̟R̟A̟U̟N̟I̟Y̟A̟R̟ K̟Y̟A̟U̟__T⋆a⋆k⋆u⋆n⋆_F⋆a⋆r⋆k⋆o⋆

*💋💋S̑̈Ȃ̈Ȓ̈Ȃ̈Ȗ̈N̑̈Ȋ̈Y̑̈Ȃ̈Ȓ̈ K̑̈Y̑̈Ȃ̈Ȗ̈💋💋*

*💥𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛💥*

Đ₳₲₳ ₳Ⱡ₭₳Ⱡ₳₥ł₦

*💘𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖'𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ💘*

*☆𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝐾𝑑☆*

*page 33&34*

Fitowa tayi Drawing-Room ta shiga ta É—auko wani board wanda akeyin zane akanshi da kuma Drawing-paper da sauran kayan zane.
Sannan ta fito palo daga can gefe ta shirya kayan zanen da ta É—auko, komawa tayi ta É—auko wata royal chair ta zauna akai yadda zataji daÉ—in yin zanen yadda ya kamata.
Sudai su Nainarh sun zuba ma ta ido suna kallon ikon Allah, yau kuma Haleesat ce da zane, aikuwa akwai kallo, ita kuwa tanayi tana É—an tsayawa tunani.

Lailah, Afeefah, Deejarh sune suka shigo palon bakin su É—auke da sallama, duk suka amsa musu Nailah na faÉ—in "har andawo daga garden É—in kenan?,"

Afeefah ne kawai ta iya bata amsa, domin Lailah da Deejarh hankalin su yana kan Haleesat da ta taƙarƙare tana zanenta ba abin da ya dameta.

Da sauri Deejarh ta aje Books É—in dake hannunta a saman center table sannan ta nufi wajen da Haleesat take, faÉ—i take

"Auntie Haleesat zane kikeyi kenan?,"

Juyowa Haleesat tayi tana goge uban gumin da ta haÉ—a da wani handkerchief ash color, tana murmushi ta ce "you know kinsan abin da zan zana ne."

Deejarh ta ce "a'a zandai sani idan kika gama zanawar,"

"Okay, saka ido kiga ikon Allah," dariya Deejarh tayi sannan ta zauna a saman carpet tana faÉ—in "to Auntie Haleesat É—inmu,"

Tanayi Suna taɓa fira sama sama da mutanen palon da duka suka zubo ido suna jira ta kammala suga abin da ta zana.

Lailah ta ce "da alama wannan zanen is very very special tunda har naga an ɓata lokaci ba'a gama ba,"

Zaynerb ta amshe da faÉ—in kika sani ko Brother In law É—in mune?,"

"Kudai kawai ku zuba ido kusha kallo, koma waye ai dai zata gama, kuma zamu gani."
Cewar Nailah da duk tabi ta ƙosa Haleesat ɗin ta kammala zanen suga ko wani kala ne.

"Yes yasin ta kammala wallahi ta kammala."

Deejarh ta faÉ—a hakan cike da farin ciki, da sauri su duka suka taso banda Nainarh.

"Kun gani yasin yayi kyau sosai sosai fa."

Deejarh ta kuma faÉ—a tana juyi a gurin, dukansu dariya sukayi ganin abin da Deejarh takeyi.

"To a bamu mu gani, mana a nata ja mana rai fa," Lailah tayi ƙorafin tana kuma cusa kanta danta hango zanen, yayinda Haleesat taƙi bari kowa ya gani.

Ganin zasu iya qwata ta ƙarfi tunda sun fita yawa ne, yasa da sauri ta aje zanen a saman center table na tsakiyar palon.

"Kinyiwa kanki gata da kika aje." Zaynerb ta faɗa tana ƙarewa zanen kallon ƙurilla, kamar yadda suma su Afeefah sukayi suna kallon zanen.

Wani haɗaɗɗen cute guy ne, dogo sanye cikin trouser jeans da t-shirt, fuskar shi rufe take da wata haɗaɗɗiyar face mask. Ba'a iya ganin komai a fuskar shi, sai manyan idanun shi farare kyawawa dasu, sai kuma dogon hancin shi da face mask ɗin bai gama rufewa ba, kanshi kuwa p_cap ce wacca ta kusa rufe mishi fuska, yasa hannun shi ɗaya cikin trouser pocket ɗinshi yayinda ya riƙo saman p-cap ɗinshi da ɗayan hannuna shi, kafafun shi sanye cikin back-shoe irinna jami'ai.

Ajiyar zuciya ko wanen su ya sauke bayan sun kammala ƙarewa mutumin da Haleesat ta zana kallo, kafin suka dawo da kallon su akan Haleesat da sai faman sakin murmushi take kamar wata zautacciya.

"Shin zaku iya cinka ko waye wannan É—in?,"
Haleesat ta tambayesu dan tasan tambayoyin dake a bakunansu kenan, shiyasa ta riga su.

Qara kallon zanen ɗin Afeefah tayi da kyau tana nazari. "a tunanina yanayin falsafar tsayuwar shi, ya nuna kamar detective ne shi, especially idan ku ka lura da yadda ya zura right hand ɗinshi cikin trouser pocket, zai iya yuwuwa bindiga zai ciro, sannan kuma ku duba da kyau, yanayin yadda ya rufe fuskar shi, da face mask da kuma yadda yasa hannun shi yana kuma janyo p-cap ɗin, sannan kuma da alama wani yake nema, ko kuma yake shirin bi, sannan kuma ku ƙara duba yanayin shigar shi, yafi yanayi da shigan jami'ai, jami'an ma na sirri."

Ganin yadda suka zubo ma ta ido suna kallo ne, yasa tayi saurin faÉ—in, "amma fa, hasashe ne bawai nasani bane, kawai dai yadda zuciyata ta hasasomin ne."

Ajiyar zuciya dukansu suka sauke sannan suka juya Suna kallon Haleesat da tayi shiru kamar mai tunani, tabbas idan bata manta ba, kamar wani taga yake bi a lokacin.

Deejarh ta ce "to har yanzu dai ba'a faÉ—amana ko wanene ba," Zaynerb ta amshe da faÉ—in "nidai nasan Brother In law ne, kawai tana kunyar faÉ—ane."
Harararta Haleesat tayi tana faÉ—in duk cikin ku, banga wacca zanji kunyar ta ba."

Lailah ta ce "to idan abin haka ne, faɗamana ko wanene tunda dai ba haka kawai zaki zauna ki ƙera drawing wannan handsome guy ɗin ba."

Lumshe kyawawan idanunta tayi, sannan ta buÉ—e a hankali ta wani juyasu in styling, ta kallesu su duka ta ce.

"MY SOUV£NIR."

Kwashewa sukayi da dariya su duka Afeefah ta ce "aha kice shiyasa naga ake wani jin kunyar mu, ashe our Brother In law ne."

Duka Haleesat ta kai mata da sauri ta matsa gefe tana dariya, Lailah ta ce "ah lallai Auntie Haleesat, kin kamu da yawa, irin wannan special handsome haka, wai damma a zane muka gani ina ga ace a fili ne, ai dole ma kiyi nisa."

Nainarh ta ca fe da faÉ—in "ah banga laifinta ba, soyayya daÉ—i bakuji ana faÉ—in, Love is sweet like a lollipop ba?."

"Yanzu dai our sister, finally she's fall in love, dan haka dole mu haÉ—a shagali, ko ba haka ba sister's?."

Zaynerb tayi maganar tana kallon su, gabaÉ—ayan su suka haÉ—a baki, hanyar amsa ma ta da "haka ne Æ´ar uwa."

Ba tare da ɓata lokaci ba, Afeefah ta danna wasu lambobi a telephone ɗin dake a palon tayi ordered na pizza dasu shawarma, burger, cake e.t.c.

Sannan ita da Lailah da Deejarh, sai Zaynerb ko wacce ta ɗaura apron suka shiga kitchen aka fara aiki😃

Cikin ƙanƙanin lokaci suka jere komai a dining table zuwa lokacin, ma'aikacin boutique ya kawo ordered ɗin da Afeefah tayi gabaɗaya suka haɗa suka jere a dining.

Tun daga kan snacks juice kala kala ba kalan da babu.
Gaba É—ayansu suka hallara a dining table, su duka.

Zasu fara kenan sukaji door Bell, tashi Lailah tayi ta nufi ƙofar domin buɗewa, saida ta fara duba ƴar qaramar portable computer dake manne a wall na palon, da sauri ta ɓude ƙofar ɗin ganin mutanen dake tsaye a bakin ƙofar.

Da gudu tayi hug É—in Momy Rafi'at dake tsaye cikin shigar cikakkun manyan likitoci, sai da ta rungumi Momy sannan ta juya kan Daddynsu dake gefe yana murmushi sanye cikin Business suit black, shima rungume shi tayi tana faÉ—in.

"oyoyo Daddy kayi surprised É—inmu sosai, shine baka faÉ—a mana yau zaka dawo ba ko?."

Momy Rafi'at ta ce "tunda dai ya dawo lafiya, ai sai ki bari ya shiga daga ciki, sannan sai kiyi shagwaɓar yadda kikeso." Momy tayi maganar fuskar ta a washe.

ÆŠunguma sukayi suka shiga ciki, hannayen Lailah cikin nasu su duka, Afeefah da taji Lailah shiru ta taso domin ganin abin da ke faruwa, saukayi ido huÉ—u da Daddynsh, ai batasan lokacin da ta taka da gudu ba, ta rungumeshi tana dariya shima Mister Mai Kyau, dariya yakeyi.

"zaki ɓalla mana Daddy fa, wannan abu haka kamar ƙaramar yarinya."
Zaynerb da suka ƙariso gurin ta faɗa hakan, Daddyn yace "abarmin shalelena ta wataya abinta, aini zanso ta karyani ma."

Nainarh tana murmushi ta ce "mu kuma ba zamuji daÉ—i ba, idan aka karya mana Daddynmu."

"Ya naga kamar ana wata qwarya qwaryar party, ba'a gayyacemu ba?."

Mister Mai Kyau, daya hango abubuwan maqulashe a dining, yayi maganar.

Zaynerb ta buÉ—e baki zata bashi amsa, da sauri Haleesat dake kusa da ita ta rufe ma ta baki da hannayenta, ganin haka yasa Lailah faÉ—in.

"ah dama Haleesat ce ta antaya soyayya fa, shine muka shirya wannan ƴar qwarya qwaryar partyn, domin tayata murna ta ƙarishe tana qintse dariya, ganin yadda Haleesat take antayo ma ta harara, tana raba ido kamar baiwar da tayiwa sarki ƙarya😝

"Okay shine ba'a gayyacemu ba, zakuyi ku kaÉ—ai, to qwara da Allah yasa muka dawo yanzu sai ayi damu."

Momy Rafi'at tayi maganar tana ajiye Lab coat da jakar ta saman center table.

KANO

💘JIEDDARH💘

Daga kwancen da take a saman bed ɗinta, ta jiyo knocking sama sama, amma a yanayin gajiyar da takejin kanta, tana tunanin koma waye wannan mai knocking sai dai ya haƙura sai gobe koma miye.
Saboda baccin dake a idanunta sai dai me, jin da tayi mai buga ƙofar yaƙi haƙura, yasa ba shiri ta sauko daga saman gadon tana ya mutsa fuska alamar bacci takeji over.

Palon dake a bedroom ta fito sannan ta nufa ainihin ƙofar ɗakin ta buɗe ƙofar.

Da mamaki take kallon wacca take a bakin ƙofar, tana sakar ma ta murmushi. Ni'ima ce sanye cikin sleeping dress, dogon wando fari sai riga blue color, kanta da hula fara mai haɗe da blue.

Martanin murmushin ita ma Jiddarh ta mayar ma ta sannan ta matsa gefe, domin Ni'imar ta sama damar shigowa, shiga ciki tayi, wannan shine karonta na farko da ta shigo bedroom É—in Jiddarh shiyasa batasan lokacin da ta saki baki tana kallon kyau da tsaruwa irinna na bedroom É—in ba.
Chapter 38 · 0% Book details