← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 96

Sashe 22

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lailah ta ce "akwai wanda kike hakurin jira ne, Afeefah ta amsa da "a'a."
Lailah ta ce "ae na É—auka sabbir kike jira,"
"Wanene sabbir kuma?," Zaynerb da Haleesat suka haÉ—a baki wajen tambaya, da sauri Afeefah ta ce "ah shiÉ—in saurayin Lailah ne."
"Saurayin Lailah kuma?, Nainarh ta tambaya da É—an mamaki sai kuma tayi murmushi ta kalla Afeefah ta ce "bamu ruwan labari mutsa Æ´ar uwa," Afeefah ta gyara kwanciyar ta a saman two sieter da take sannan ta fara magana.....
"a birthday partyn wata Zahrah c.m É—inmu muka haÉ—u dashi shi kuma yaga Lailah ya faÉ—a kogi,"

"Amma Afeefah kina ruwa wallahi," cewar Lailah jin ƙaryar da Afeefah ta zubo.
"kusada breaker ma kuwa🤣"
Afeefah ta bata amsa hadda mata gwalo, Lailah tayi murmushi, "aikuwa da gaske ne tunda kukaga tana murmushi cewar Nailah, da sauri Lailah ta ɓata fuska ta ce "Allah kuwa, bada gaske bane."
"ba wani nan kedai kawai kin faÉ—a gaskiya," Haleesat ta faÉ—a, shiru kawai Lailah tayi dan tasan koda ta faÉ—a musu gaskiya ba yadda zasuyi ba tunda Afeefah ta riga da ta mata sharri, haka suka cigaba da fira abin gunin ban sha'awa suna haÉ—awa da flirting.

🅺🅰🅽🅾

*

𝑊𝑢𝑟𝑎𝑟𝑒𝑛 𝑘𝑎𝑟𝑓𝑒 𝑏𝑖𝑦𝑎𝑟 𝑛𝑎 𝑚𝑎𝑟𝑒𝑐𝑒

Zaune take a bakin swimming pool, yayinda kyawawan ƙafafunta duka biyun suke cikin ruwa, tana lilawa a hankali da alama yanayin da ake ciki yana mata daɗi, kamar ko yaushe sanye take cikin ƙananan kaya Riga top white color, mai zanen stairs c.green sai wando shima crazy jeans c.green, sai hular vani ita ma white color saman hular anyi rubutu da zare c.green an rubuta '𝐺𝑙𝑎𝑚' da ƙananan baƙi, wayarta ne a hannunta na dama tana tsalawa.

Can gefe kuwa Bilki sai faman safa da marwa takeyi takai mari takai goho, doguwar rigar atamfa ce a jikinta mai dogon hannu gaban rigar kuwa anyi ado da flowers masu kyau wa'inda suka ƙarawa ɗinkin kyau, sai kuma ɗan kwalin rigar datayi ɗaurin ture kaga tsiya.

Da ta gaji da safa da marwan saita ƙarisa gurin da Jieddarh, take ita ma ta sama guri ta zauna sannan ta kalla Jieddarh ta fara magana a hankali kuma cikin damuwa.

"Jieddarh na kasa nafa kasa, Jieddarh Yasi na kasa," haka kawai Bilki take ta faman faɗa tana ƙarawa kamar mai bitan karatu.

Kallon ta Jieddarh tayi da ta isheta ta ce "malama kinfa isheni da surutu, waima miye kika kasa É—inne?,"
Ajiyar zuciya Bilki ta sauke sannan ta ce "nakasa shawo kanshi, mana," dariya Jieddarh tayi ta ce "au ni sai yanzu ma na fahimci abinda kike nufi, ae kece bakiyi yadda zai kulaki ba, kuma ai nace ki dena kallon shi idan yana guri, amma kinƙi ji, Bilki taja ajiyar heart sannan ta ce "wallahi Jieddarh ba zaki fahimci yadda nakeji bane amma kamar kullum yauma na miki uzuri saboda bakisan Menene Love bah💘

"Toki faÉ—amin Menene Love É—in mana," cewar Jieddarh, Bilki ta ce "nidai ba take nake ba, yanzu nasan ya kusa dawowa daga office kuma inaso na ganshi amma ba dama,"

Jieddarh ta ce "akwai dama mana kala kala ma saidai idan kece bazaki iya amfani dashi ba," Bilki ta ce "kamar yaya bazan iya amfani dashi ba, ki faɗamin nikuma zanyi iya bakin ƙoƙarina, don naga nayi amfani dashi."

Jieddarh ta ce "da gaske kikeyi, Bilki ta ce "of course kuwa," Jieddarh ta miƙe ita ma Bilkin miƙewa tayi.
Saida Jieddarh tasa flat shoes ɗinta sannan ta riƙo hannun Bilki tayi gaba ita ma Bilkin tabi bayanta kamar raƙumi da akala....

Cikin palon gidan ta nufa da ita saida ta tsaya ta canza shoes É—inta da na shiga palon, a gurin da aka tanadar domin ajewa kafin a shiga palon sannan suka shiga cikin main palon ba kowa saida suka tsaya a tsakiyar palon sannan Jieddarh ta saki hannun Bilkin.
Ita dai Bilki tana kallon ikon Allah daga cewa a bada shawara.....

White curtains ɗin Window's na palon Jieddarh ta yaye ta hango motar Heesham Benz Ash color ana parking ɗinta a parking lot, da alama shine ya dawo daga office, da sauri ta saki curtains ɗin ta koma wajen da ake aje mopper ta ɗauko ta miƙawa Bilki ta ce
"riƙe na faɗa miki kalar dramar da za'a shirya," karɓar mopper ɗin Bilki tayi, da sauri Jieddarh ta raɗa mata abin da zatayi a kunne, murmushi Bilki tayi takai ma Jieddarh duka tana murmushi Ita ma Jieddarh murmushi takeyi ta kauje da sauri ta koma wani korido ta tsaya sannan ta lalubo wayarta ta shiga camera.
.

Ita kuma Bilki ta fara mopping tana raira waƙa kamar da gaske😅

A daidai lokacin kuma Heesham ya turo ƙofar palon ya shigo bakin shi ɗauke da sallama, da sauri Bilki ta amsa ta tsuguna zata gaisheshi daidai lokacin kuma wutar lantarki na palon ta ɗauke, ihu Bilki ta kurma ta ɗafale a ƙirjin Heesham Like a little baby dai dai lokacin da wutar ta dawo ita kuma Jieddarh ta fara zuba musu pictures kala kala saida tayi wajen kala biyar sannan ta tsaya.

Ita kuwa Bilki ƙara ɗafale Heesham tayi ta rumshe idanun ta tana faɗin.
"wayyo duhu yaya heesham ka taimakeni duhu banason duhu zan mutu." Haka kawai take faɗa tana ƙarawa-Shikuwa bawan Allah Heesham gabaɗaya jikin shi ya mutu ƴar gajiyar daya kwaso sayya nemeta ya rasa, ga Bilki ta ɗafale mishi a ƙirji gabaɗaya sayya tsinci kanshi cikin wani hali wanda ba'a faɗa.
A hankali yake ɗan shafa bayanta alamar rarrashi kamar yana lallaɓa karamar yarinya cikin kunen ta ya raɗa mata.
"ki buɗe idonki wutan ta dawo kinji?," yanayin yadda ya mata maganar ba ita ba hatta Jieddarh dake laɓe ta korido tana leqen su saida tsigar jikinta ya miƙe, ai ba shiri Bilki ta sauka ƙasa tana sunkayar da kai da gudu ta ɗauka mopper ɗin ta bar gurin a three sixty 360😃

Murmushi yayi yana shafa sumar kanshi sannan ya É—auka briefcase É—inshi da ta faÉ—i tun lokacin da Bilki tayi hugging É—inshi, kana ya fara taka staircase's in twin's ya nufa part É—inshi..

Saida ya ƙule sannan Jieddarh ta fito daga muɓoyarta, ɗaura hannu biyu ƙugu tayi tana bin staircase's ɗin da kallo kamar mai neman wani abu.
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta fita daga palon swimming pool ta nufa dan tasan acan zata sama Bilki.
Ilai kuwa tana ƙarisawa taji an rungumo ta baya da sauri ta juya sai taga Bilki bakin nan kamar gonar auduga saboda fara'a, dariya kawai Bilki takeyi tana faɗin Jieddarh "nagode nagode sosai, highly obaaa."

Tureta Jieddarh tayi tana faɗin "zaki ɓallani fa," dariya Bilki ta kuma yi ta ce "kece Jieddarh akwai basira yasin,"
Ɗan murmushi Jieddarh tayi tana miƙama Bilki wayarta ta ce "ai ina faɗamiki daga yau kisa ido kawai zakiga canji," karɓar wayar Bilki tayi tana faɗin "Menene zanyi da wannan wayar da kike bani", ai bata rufe baki ba ta daka tsalle ganin pictures ɗinsu ita da masoyinta Heesham kala kala ƙara hugging ɗin Jieddarh tayi tana faɗin wayyo Jieddarh "na nagode miki sosai, kai gaskiya kinyi a rayuwa."
Murmushi Jiedarh tayi ta ce "kedai Bilki wannan duk a cikin soyayyar ne?," ta tambaya a lokacin da ta koma ta zauna akan É—aya daga cikin resting chairs dake a gurin...

*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*

*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*

*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*

{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}

💘*𝘓𝘈𝘍𝘈𝘡𝘐 𝘞𝘙𝘐𝘛𝘛𝘌𝘙𝘚 𝘈𝘚𝘚𝘖𝘊𝘐𝘈𝘛𝘐𝘖𝘕*💘🤙

<><><><><><><><><><><><><><<><><><><><><><>><><><><><><

*page 21&22*

...A hankali ta lumshe idanun ta tana faÉ—in "oh Allah ko nima yaushe zan haÉ—u da masoyina na gaskiya ne?."
"Nan bada daÉ—ewa ba Insha Allah, zaki haÉ—u da Yariman ki, Æ´ar uwa,"
Taji muryar Bilki tana faÉ—ar haka, É—an waro ido tayi dan batayi tunanin a fili tayi maganar ba, a hankali Bilki ta dawo kusada Jieddarh ta zauna a É—aya daga cikin kujerun tana faÉ—in.
"Insha Allahu nan bada daÉ—ewa ba inaji a jikina, kema zaki haÉ—u da naki Jarumin bi'iznillah, É—an dariya Jieddarh tayi ta ce "Bilki kenan bazaki fahimta bane kawai," Bilki ta ce "ki fahimtar dani mana?,"
Gyara kwanciyar ta tayi a kujerar sannan ta ce "abar maganar kawai," Bilki tana dariya ta ce "a'a wallahi da dai an ci gaba saboda inajin daÉ—inta,"
Murmushi Jieddarh tayi ta ce "Bilki anya kuwa an taɓa faɗamiki kin zare?," dariya Bilki ta kwashe da shi sannan ta ce "a'a gaskiya ba'a taɓa faɗa ba, amma yau anfaɗa,"
Murmushi Jieddarh ta kuma yi, "Bilki kenen YOU CRAZY IN FALL IN LOVE ❤.

"Kinsan miye kuwa?," Bilki ta tambayi Jieddarh, a hankali Jieddarh ta girgiza mata kai alamar a'a.
Bilki ta ce "yau sai naga kamar ba ƙya cikin special mood fa," "saboda me kika ce haka?," Jieddarh ta tambaya, Bilki ta ce.

"Hausawa sukace maganar zuciya a tambayi fuska, alasa nayi hausar dai dai, kinsan hausan nawa sai aslowly fa, abinki da bafulatana,"
Fashewa Jieddarh tayi da dariya, "wai maganar zuciya a tambayi fuska wannan hausan fa, cewar Jieddarh still cikin dariya.
Ita ma Bilkin dariya tayi dama tayi hakan saboda taga fara'ar Jieddarh ɗin ne kuma tayi winning tunda ga Jieddarh tana dariya harda ƙyaƙyatawa.

Gyara zamanta tayi a kujerar tana fuskan tar Jieddarh ta ce

"kinsan wani abu kuwa?,"

"a'a saikin faÉ—a,"

Bilki ta ce "ina faɗamiki a lokacin da zaki haɗu da yarimar ki zaizo miki yana akan farin doki fuskar shi ɗauke da ƙayataccen murmushi idanun shi ɗauke da kallon ƙauna zuwa gareki, zai ɗaukeki ya ɗauraki saman farin dokin sa, kuyita zagaye fili sirdi, abinku cike da farin ciki kuma.....Da sauri Jieddarh ta dakatar da ita ta hanyar faɗin "wait a minutes tsaya_tsaya yarima kikace fa, please faɗamin a wani film kika kalla, hala dai indian film ne nasan sune suke irin wannan labarin soyayyar........Jieddarh tayi ma Bilki tambayar tana zaro ido haɗe da jiran amsa.

Dariya Bilki tayi tana faÉ—in, "a'a ba'a film na kalla ba, inaji ajikina dake zai faru, haka kawai nakeji a jikina É—an sarki zaki aura dan dashi kika dace, domin keÉ—in matar saraki ce, haka zalika matar manya," wayyo Allah na harna fara hangoki a gidan sarauta kina zuba mulki, kuma zakiyi kyau da zama gimbiya yasin.....
Chapter 22 · 0% Book details