← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 96

Sashe 8

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aikuwa kwaÉ—on dafaffen zogale da quli yaji kayan hadi tayi sannan ta zuba a kula Æ´ar daidai taba Zaynerb dake kallonta tana murmushi ta ce "gashi an kammala" Amsa Zaynerb tayi tana yima Auntie sa'adah godiya sannan ta fita daga kitchen É—in.
Auntie sa'adah ta bita da kallon tausayi dan kuwa sosai take tausawa Rayuwar Yarinyar ita da Æ´ar uwanta Afeefah basu da wata matsala saina Rashin uwa ga mahaifin su shiba mazauni ba gashi sun haÉ—u da kishiyar uwa mace mai son kanta da Yawa, kai kurum ta girgiza sannan ta ci gaba da aikin ta tana mai musu addu'ar samun ingantaciyar Rayuwa cikin zuciyar ta.

{𝔗𝔬𝔣𝔞𝔥 𝔍𝔞𝔪𝔞'𝔞 𝔐𝔢𝔫𝔢𝔫𝔢 𝔄𝔟𝔦𝔫𝔡𝔞 𝔐𝔞𝔥𝔞𝔦𝔣𝔦𝔶𝔞𝔯 𝔰𝔲 𝔄𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥 𝔱𝔞𝔶𝔦𝔴𝔞 𝔪𝔬𝔪𝔶 ℜ𝔞𝔣𝔦`𝔞𝔱 𝔫𝔢 𝔡𝔞 𝔷𝔞𝔣𝔦 𝔥𝔞𝔨𝔞, 𝔡𝔞 𝔱𝔞 𝔡𝔞𝔲𝔨𝔦 𝔞𝔩𝔴𝔞𝔰𝔥𝔦 𝔪𝔞𝔦 𝔤𝔦𝔯𝔪𝔞 𝔥𝔞𝔨𝔞 𝔞𝔨𝔞𝔫𝔰𝔲 𝔷𝔞𝔶𝔫𝔢𝔯𝔟 𝔡𝔞 𝔄𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥, 𝔄𝔫𝔶𝔞 𝔨𝔲𝔴𝔞 𝔨𝔲𝔫𝔞 𝔱𝔲𝔫𝔞𝔫𝔦𝔫 𝔴𝔞𝔫𝔦 𝔞𝔟𝔲,𝔨𝔲𝔴𝔞 𝔨𝔬𝔡𝔞𝔦 𝔫𝔞 𝔟𝔞𝔨𝔦𝔫 ℌ𝔞𝔩𝔢𝔢𝔰𝔞𝔱 𝔡𝔦𝔫𝔫𝔢,𝔐𝔬𝔪𝔶 ℜ𝔞𝔣𝔦`𝔞𝔱 𝔱𝔞𝔫𝔞 𝔡𝔞 𝔰𝔞 𝔥𝔞𝔫𝔫𝔲 𝔞 𝔰𝔥𝔞𝔶𝔞𝔰𝔥𝔞𝔶𝔢𝔫 𝔡𝔞 𝔷𝔞𝔶𝔫𝔢𝔯𝔟 𝔱𝔞 𝔱𝔰𝔦𝔫𝔠𝔦 𝔨𝔞𝔫𝔱𝔞 𝔠𝔦𝔨𝔦 𝔨𝔲𝔪𝔞 𝔱𝔞𝔨𝔢𝔶𝔦 𝔱𝔬 𝔨𝔬 𝔪𝔦𝔶𝔢 𝔞𝔪𝔰𝔞𝔯 𝔡𝔲𝔨𝔞 𝔴𝔞𝔡𝔞𝔫𝔫𝔞𝔫 𝔗𝔞𝔪𝔟𝔞𝔶𝔬𝔶𝔦𝔫 𝔰𝔲𝔫𝔞 𝔠𝔦𝔨𝔦𝔫 𝔴𝔞𝔫𝔫𝔞𝔫 𝔡𝔞𝔡𝔡𝔞𝔡𝔞𝔫 𝔏𝔞𝔟𝔞𝔯𝔦 𝔪𝔞𝔦 𝔰𝔲𝔫𝔞 🅢🅐🅡🅐🅤🅝🅘🅨🅐🅡♥︎🅚🅨🅐🅤 𝔨𝔲 𝔟𝔦𝔶𝔬 𝔞𝔩𝔨𝔞𝔩𝔞𝔪𝔦𝔫 𝕋𝕙𝕖 ℕ𝕒𝕚𝕟𝕒𝕣𝕙 𝕂𝕕 𝔡𝔞𝔫𝔧𝔦𝔫 𝔴𝔞𝔫𝔧 𝔦𝔯𝔦𝔫 𝔡𝔞𝔯𝔞𝔰𝔦 𝔩𝔞𝔟𝔞𝔯𝔦𝔫 𝔶𝔞𝔷𝔬 𝔡𝔞𝔰𝔥𝔦, 🄺🄷🄰🄳🄴🄴🄹🄰🅁🅃🄷 🅂🄰🄱🄸`🅄 🅈🄰🄷🅈🄰🄷, { 𝕋𝕙𝕖 ℕ𝕒𝕚𝕟𝕒𝕣𝕙 𝕜𝕕 ✍️👑👸📲 }♥︎💖💝 }

Zaynerb bedroom ɗinta ta koma ta canza hijjab iya gwiwa fari dama doguwar rigar pakistan ne a jikin ta blue black sai wando shima na pakistan Red color mai adon stones blue black, kular ta ɗauka sannan ta fito daga gidan gabaɗaya ta nufa gidan maƙwabciyar su mai suna ⓈⓊⓃⒶⒾⓃⒶⓇⒽ!.

🅛🅐🅘🅛🅐🅗♥︎🅜🅐🅘♥︎🅚🅨🅐🅤

Ɓangaren Lailah kuwa suna zaune a lecture Room suna ɗaukar lecture ita da Afeefah ne bencinsu a gaba sai bencin su zahrah a bayan nasu sai kuma sauran student, nan wayar Lailah Tayi ƙara alamar shigowar kira waƙar mawakiyar korean "J.Fla" na Tashi mai taken { Attention }

Gabaɗaya hankulan mutanen dake cikin lecture Room ɗinne ya dawo kanta hadda lecturer ɗin dake musu lecture gabaɗaya sun zuba mata na mujiya har Afeefah dake gefenta suna kallo, Da sauri tayi checking excuse. Lecturer ɗin ya bata dama sanin wacece ita da kuma mahaifinta badan haka ba a ƙa`idar makarantar ba`a zuwa da phone idan ba aiki da ita bane ya taso,amma sanin waye mahaifinta a ƙasar yasa, ba ko musu bai mata ba,balle kuma kallon banza ya bari ta fita ɗaga kiran, kuɗi kenan😇

Fita daga lecture Room É—in tayi tana sauke ajiyar zuciya tana shirin É—aga wayar kiran ya tsinke tsuka taja Cike da Takaici, To dama da unkown number aka kirata,don batasan ko waye ba,To koma ta sani indai Laila ce,ba bin kiran zatayi bah.

Zata koma wani kiran ya ƙara shigowa wayar sai dai wannan karon momy ne mai kiranta ba wancan ba.
ÆŠaga kiran tayi da sallama.
Daga can Ɓangaren Momy Rafi'at dake zaune saman Royal sofa nata ta kira sunan ɗiyartata "Lailah!", amsawa tayi da "na'am momy da wani abu ne ina class Yanzu please zan kiraki anjima Bye bye, Love you, Bata tsaya jin mai momyn zata ce ba ta katse kiran tana jan tsuka sannan ta kashe wayar gabaɗayanta.
Sannan ta koma Lecture Room É—in basu daÉ—e ba Lecturer É—in ya fita dama daga shi ba wani sai kuma gobe, dan haka fitowa sukayi suka nufo Gida GabaÉ—aya.

A mota Afeefah sai tsokanar Lailah takeyi dan tasan bazai wuce sabbir bane ya kirata😇

Ita dai Lailah bata kulata ba driving ɗinta kawai takeyi tanajin yadda Afeefah ke tsokanar ta taƙi kulata har suka iso Katafaren Gidan nasu Wanda Ya gaji da haɗuwa ta kowani ɓangare securities ne..
Horn tayi gate man ya wangale musu wagameman gate ɗin gidan, sannan Lailah ta cusa hancin motar cikin Katafaren Gidan a parking lot tayi parking sannan suka fito dukansu a gajiye suke, Don Haka koda suka shiga cikin palon bajewa sukayi saman Royal sofa's da aka qawata qaton palon dasu kuma sukayi ƙyau.

Zaynerb kuwa tana fita Gidan Kai tsaye Gidan wata Neighbor ɗinsu sunainah ta nufa, Da isarta ƙofar wagameman gate na gidan ba tare da ɓata lokaci bah.

Knocking ɗin ƙaramar ƙofar gate ɗin Tayi, sannan mai gadi ya buɗe mata bayan Na`urar tsaro dake jikin gate ɗin ta gama bincikarta, fuskar sa ɗauke da fara'a yake amsa gaisuwar da Zaynerb ke mishi domin kuwa Ya santa highly, ah ae dole yasanta sosai kodan na ce fa ne datake bashi huh🤣😂😅.

Shiga cikin Gidan Tayi sannan ta tura door É—in palon a buÉ—e yake dan haka shiga palon tayi da sallama saidai ba kowa ciki..

A tsakiyar palon ta tsaya tana ƙwaɗawa matar Gidan kira, faɗi Take "Ummyn farhana", "Ummyn farhana!", Da sauri wata ƴar dattijuwar mata wacca ba za ta wuce ƴar aikin gidan bane ta fito daga kitchen. Da sauri ta ƙariso gurin Zaynerb.....
Ganin ta Yasa Zaynerb ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Yawwa Babah dije matar Gidan tana nan kuwa?", Zaynerb ta tambaya Babah dije data fito daga Kitchen na Palon, ,Eh madam ki sama guri ki zauna bari na kira ta inaji Bacci ne ya É—auketa kinsan masu juna biyu sai da hutawa", Babah dije ta faÉ—a tana nufar wani korido dazai sadata da bedroom É—in matar Gidan.

Zama Zaynerb ɗin tayi tana latsa wayar ta kafin matar Gidan ta fito ilai kuwa bata daɗe da zama ba, Babah dije ta fito tana faɗin "gatanan zuwa bacci ne ya ɗauketa, amma fah batayi nisa ba domin kuwa ina magana ɗaya ta farka duk nisan bacci irinna masu ciki," cewar babah dije lokacin data ƙariso gurin da Zaynerb ɗin take, Godiya Zaynerb ta mata da sauri dan ta fahimci tsohuwar shegen surutu ne da ita,dan wannan surutun da tayi ya fahimtar da Zaynerb ɗin haka domin ita ɗin ɗalibai lauyanci ne kuma zaqwaqwura don tasan makamar karatunta shiyasa da zarar ta haɗu mutun mai surutu ko wani abin take fahimta.
Ita kowa babah dije ta koma kitchen ta cigaba da abinda takeyi.

Zaynerb tana zaune can saiga wata ƙyakyawar mata wacca ba za ta wuce shekaru ashirin da bakwai ba, ta fito tana faɗin "ah ah Yau manyan baƙi ne a gidan namu ashe" Ta faɗa tana zama a three sieter, Dariya Zaynerb tayi ta ce "uwan Triple yau kuma mune baƙin kodai cikin ne yasa ba'a gane mutane Yadda Ya kamata?"..
Dariya ita ma tayi sannan ta ce "ras nake gani kece dai kikayi nisa kinfa kai one week baki zo ba wallahi, Afeefah tafi ku kirki dukanku harsu Lailah É—in don tafiku son zuwa nan alamu yana nuni da nan gaba ma saita fiku rike zumunci Yarda ya kamata.

"Okay tuba muke uwan Triple" Zaynerb ta faɗa tana miƙa mata kular hannun ta, Karɓa tayi tana faɗin "harda su tsaraba ne Allah yasa dai na'iya ci," Ta faɗa tana buɗe kular aiko tana arba da kwaɗonnan ta fara suburbuɗawa Zaynerb godiya tana faɗin "dama yau da Wani irin kwaɗayin zogale na tashi gashi Allah ya aikomin ke Zaynerb ɗiyar Albarka dashi.

Ita dai Zaynerb latsa wayar ta take tana dariyar kwaÉ—ayin masu ciki, "Ae kigama min dariya Allah kaimu ranar da zangan ki da ciki zan rama nima," sunainah ta faÉ—a ganin yadda Zaynerb ke mata dariyar kwaÉ—ayi.

Da sauri Zaynerb ta ce "tuba nake Ummyn farhana kinsan Waya ne a hannuna, Don Haka ita ce ta bani dariya obaa highly bawae keba."

Sunainah bata kulata ba ta ƙwalawa Babah dije mai aikinta kira, Da sauri dattijuwar tazo tana faɗin gani maman Ferhane!!😝😝.

Dariya Zaynerb tayi ta ce "babah dije ba "Ferhane" ake cewa ba "Farhana" ake cewa."
Dariyar ita ma Babah dije tayi tana faÉ—in "ae wannan suna sai ku Æ´an zamani ni ina zan iya cewa wani ferhane."
Sunainarh tana dariyar maganar Babah ta ce "Babah rabu da Zaynerb kawai, Plate zaki ɗaukomin a kitchen", "To" Babah dije ta ce sannan taje kitchen ta ɗauko special plate ta kawo mata aikuwa ta ansa ta juye kwaɗonnan a plate ɗin nan ta hauci kamar ba gobe, Hannu baka hannu plate, Saida ta cinye tas ta sha Ruwa tana mai miƙa Appreciation to Allah.

Da mamaki Zaynerb ke kallon ta ganin ko minti biyar ba'ayi ba harta cinye, "Lallai "Ummyn farhana" wannan ci haka anya ba Triple bane bamu sani ba," Zaro ido sunainarh tayi ta ce, "Triple kuma Zaynerb na kaisu ina? ɗaya ma ya aka ƙare balle kuma har ƴan uku.

Dariya Zaynerb tayi ta ce "ainaga cikin minti biyar harkin cinye KwaÉ—o cikin plate ba dole nace Æ´an uku bane."
Murmushi sunainarh tayi ta ce "idan ma ƴan ukunne Allah ya bada masu albarka, ae Albarka ake nema ba wani abu ba." Zaynerb ta amsa da ameen, nan dai suka ci gaba da fira irinnasu na ƙawaye.

IN BRIEFLY
Zaynerb dai ba ita ta bar gidan ummyn farhana na ba sai wajen biyar na yamma acan tayi la'asar sai da taga mijin sunainarh É—in ya kusa dawowa sannan ta mata sallama ta nufi gida.

🅆🄰🄲🄴🄲🄴_🅂🅄🄽🄰🄸🄽🄰🅁🄷_?

Sunainarh dai itaÉ—in makwabciyar su Zaynerb ce, Kuma asalinta ta kasance Æ´ar bauchi ce, Aure ne ya kawota Abuja "Sohail" Shine sunan mijinta É—an gidan ministan ilimi ne shiÉ—in, haihuwar ta É—aya sunan Yarinyar FARHANA shekaran ta uku a duniya, Shiyasa Zaynerb take ce mata "Ummyn farhana" suna mutunci obaa highly da Zaynerb harda ma su Afeefah.

🆆🅰🅽🅽🅰🅽 🅺🅴🅽🅰🅽.

💋SARAUNIYAR KYAU💋

💄The Fashion Show💄

*page 11&12*

Tun kafin ta ƙarisa shiga palon take jiyo muryar su Lailah da alama gardama sukeyi ko makamancin haka.

Shiga tayi ciki a palo ta samesu su duka Afeefah, Lailah,da Haleesat saikuma wasu Æ´an mata su biyu da alama É—aya daga cikin su da ita akeyin gardaman, guri ta samu saman one siter ta zauna ba wanda ya lura da shigowar sai Afeefah hannu. Afeefah ta É—aga mata daga inda take zaune a dinning Room tana cin abinci, alamar gaisuwa ita ma Zaynerb É—in ta mayar ma da Afeefah martanin murmushi tana gyara zamanta a kujerar da take tana sauraron firansu Lailah tanason gano inda firar tasu ta dosa.
Abin dariya wai gardama suke akan film Yayinda Lailah take faɗin film ɗin, "TILL THE END OF MOON" yafi kyau ita kuma ɗayar matashiyar budurwar da aka kira da Ameenah take faɗin, ina ae film ɗin "THE LEGEND OF ZU yafi kyau👌
Chapter 8 · 0% Book details