← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 96

Sashe 43

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saiga wata kyakyawar matashiyar budurwar ita ma dai wacca shekarunta ta ba za su haura ashirin da biyu zuwa da uku ba, still ita ma dai cikin shigar kece raini ga gashinta nan yasha gyara ba'a magana.
Ita ma dai sai da tayi minti biyar sannan ta koma sai gata uku ta fito ita ma.

A hankali Zaynerb ta koma ta kwantar da bayanta a jikin kujerar da take zaune. Kallon ta Deejarh tayi dama kujerun su neighbors na junane ta ce "Auntie Zaynerb nifa harna fara gundura har yanzu Balarabiyar India bata fito ba, gashi har biyu sunyi ta uku ma ta fito fa."

Murmushi Zaynerb tayi ta ce "Deejarh kenan kamar yadda kika ƙosa ta fito nima dai na ƙosa, wata ƙilama nafiki ƙoss...!!

Sauran maganar bakinta ne ya tsaya cak kamar yadda tunaninta ya tafi hutun wani lokaci saboda tsananin ruÉ—ewar da tayi na ganin wacca ta fito.
Deejarh ganin tana yima Zaynerb magana ne amma hankalinta baya akanta, yasa ita ma ta mayar da kallonta inda Zaynerb ɗin take kalla, ba shiri ta murza idanunta ta buɗe domin gasgata abin da take gani, wani ihun murna ta saki tana miƙewa tsaye har batasan lokacin da ta fara whistle (fito) ba, da bakinta saboda tsananin farin ciki game da zumuɗi.

❤𝔞𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥❤

Sanye take cikin wata kalar shiga wanda kafin kaga mai irin shigar akalla sai ga cike files dubu a kwanaki dubu lokaci dubu komai dubu😜

Wayyo Allah yau nake ganin kyau (Huh The Fashion Show) masu karatu ina ma kunanan a gurin nan sannan kuma a dai dai wannan lokaci da kunga kyau iya kyau da gaske Afeefah kyakyawace cikin kyawawa ku yarda da hakan💃😍

Sanye take cikin dresses gown wanda kai tsaye da Pink Fairy za'a kira dresses ɗin da take cikin😎

Gown ɗin mai hannun vest doguwa har ƙasa ga wasu butterfly ta bayan masu launin rigar sky purple, haka ma waɗannan butterfly ɗin na baya.

Brown wavy gashinta kuwa wanda ya zubo ma ta har mazaunai an ɗauroshi da wasu flowers sky purple wanda hakan ba ƙaramin kyau da burgewa ya ƙarawa gashin ba👸

Hannayenta cikin wasu kyawawan handgloves sky purple suma, sannan ga kyawawan ƙafafunta cikin wasu arnun tsadaddun takalma Glam Boots sky purple masu tsini ga wani shaining da sukeyi humnm👄💥👄

Ga kuma wasu Beautifuls bracelet (munduwa💍) sky purple a hannayenta duka biyun.

Kyawawan idanunta kuwa cikin wani haɗaɗɗen fancy sunglasses sky purple💞

Hallau ga wata beautiful fashion hand bag (Jakar hannu) a hannunta na dama. Ita ma kanta jakar hannun nata sky purple ne ga wasu stones kyawawa da aka ƙawata ƴar ƙaramar jakar dasu.

Wuyanta (Neck) kuwa wata haɗaɗɗiyar Diamond necklace chain ne, doguwa wacca ta sauko har ƙasan chest ɗin ta, Sarƙar mai launin sky purple.

Haka zalika earrings ɗin dake maƙale a kunneta duka biyun kalar sarƙanne sky purple, daga yatsarta na hannun hagu kuwa wani haɗaɗɗen diamond ring ne, na zamani.

Fuskar ta kuwa wa'iya zubilla kyau kenan Natural beauty fuskarta tasha make up abin ba'a magana hatta blush on na fuskar ta sky purple ne.

💋COME ON GUYS💋

𝔄𝔣𝔢𝔢𝔣𝔞𝔥𝔯𝔪𝔲 𝔣𝔞

Tayi kyau so cute. Tayi kyau so sassy so steady so sexy so mature so chic so perfect so casual nd so normal so so so much over💔❤💔

Ta fito as a Natural beautiful Afeefah Mai kyau ɗinta. Gata Afeefah Mai Kyau, ɗiyar Mai Kyau, Jikar Kyawawa, Jinin Turawa da Larabawa game da kannuri da hausa fulani duka 💄💃💄

Taku take irinna cikakkiyar wayayyar ƴar gayu (The Glamouristlelly 👄💋👄)...... fuskar ta a Washe take tana ɗagawa mutane (Fan's ɗinta) hannu kamar yadda suma suke ma ta bakajin komai a gurin sai ihun murnar da mutane maza da mata sukeyi. Toh ata can gefe kuma ga alƙalan gasa (Championship Leader's👀✨)....Ɗayan gefan kuwa manyan ƴan jarida ne, da masu ɗaukar hoto suke aikin su.

Sai da ta ƙarisa dai dai tsakiyar filin tsayuwar sannan ta tsaya a memakon tayi juyi da rairaye rairaye game da malƙwashe malƙwashe da dai sauran abubuwa, kamar yadda sauran sukayi ita nata salon tayi daban sumba (Kiss💋👄💋) ta watso wa mutane tana dariyar da ta bayyana kyawawan fararen haƙoranta...
Idan akace kyau a farko, tofah ana zuwa kan Afeefah Ɗiyar Mister Mai Kyau, an rufe ƙofa ita ɗin kyakyawa ce na first class, a ko'ina ta gama haɗuwa ni dai (Ɗiyar Mutanen Kd💃) nayi shiru a gefe ina zare ido da kallon zallar kyau.

Wani ƙayataccen abu tayi wanda ya daɗa burge mutane, hannu tasa a cikin ƴar ƙaramar tsadaddiyar jakar dake a hannunta ta ciro tsaleliyar wayarta wacca akalla ba'a kasara ba zatakai Ten million's naira a kuɗin Nigeria, camera ta shiga ta juya ta ɗauka selfie tare da mutanen da suke akan kujeru sannan ta kumayiwa kanta ita kaɗai sai da takai tsawo mintuna biyar ɗinta dai dai, sannan ta juya zata koma aikuwa nan gurin yayi tsit kamar mutuwa ta gifta da alama mutane basu so ta koma a yanzu ba, sai da takai dai dai wajen da zata koma ciki sannan ta juyo ta kuma watso musu sumba sannan ta shige ciki, cike da farin ciki bayan wasu sakanni sai ga wata ma ta fito.

Haka aka din gi yi idan wannan ta zo taci mintuna biyar ɗinta sai ta koma wata ma tazo taci mintuna biyar ɗinta a haka har mutane goma sukayi dama kuma su goma ne chas chass Ƴan Tawagar Gasar na Abuja.

Sai da cikon ta gomar ta koma sannan, Sandra ta dawo ta tsaya a tsakiyar floor ɗin, yanzu ma cikin harshen turanci ta fara magana kamar hakan👇

"Hi Hello Welcome Namaste (Da ya ke ita ɗin haifaffiyar Indiyace shiyasa yaren ta na TELUGU ya zauna a bakinta).. Barkanku dai masu kallo muna fatan wannan gasar na 𝔖𝔞𝔯𝔞𝔲𝔫𝔦𝔶𝔞𝔯 𝔎𝔶𝔞𝔲 𝑚𝑎𝑡𝑎𝑘𝑖𝑛 𝐽𝑎ℎ𝑎, tana burgeku da nishaɗantar da ku yadda ya kamata?."

Mutane gaba ɗaya aka amsa, sannan ta ci gaba da cewa "a halin yanzu duka ƴan matan gasa zasu fiffito a tare, ko waccensu ta tsaya a tsakiyar floor kamar yadda aka saba duk shekara, daganan kuma alƙalan gasa su fidda gwana zaqwaqwura ma'ana dai wacca ta sama nasarar (win) lashe wannan gasar na bana wato SARAUNIYAR KYAU💅

Ihu game da sowa na murnar maganarta mutane suka kuma saki maza da mata abin sai wanda ya gani.
Bayan wani lokaci gurin ya kuma yin tsit kamar ba wata hallita mai motsi a gurin, Sandra ta fara da ''one, two, three.!!"

Kafin ta rufe baki saiga Æ´an matan su goma rhass sun fito a tare sun tsai tsaya a tsakiyar filin gasar.

Nan fa guri ya kuma tsit mutane ana jira aji hukuncin alƙalan ƙasa.

Akalla an kwashe sama da mintuna goma a haka sannan wata Kyakyawar Baturiya daga cikin alƙalan gasan ta miƙe tsaye cikin shigarta na tsadaddun suit na mata kuma na alƙalan fashion show, da alama ita ce chairlady, sannan ne kuma ɗayar baƙar fatar dake a kusada ita, ita ma ta miƙe tsaye ɗaukar abin magana (Micro Tone) baƙar fatar tayi sannan ta fara magana cikin harshen hausa, yawancin maganar nata akan dai gasan ne sai kuma ɗan flirting (Barkwanci) da take sakawa a zancen nata, daga ƙarshe dai ta rufe da faɗin.

"yanzu dai, bari na barku haka na koma mazaunina domin na bawa. Ƴar uwa Mrs William damar bayyana mana wacece zaqwaqwurar da tayi nasara a gasar SARAUNIYAR KYAU na bana😍

Dariya akayi sannan ta koma ta zauna..
Nan wannan Baturiyar ta É—auki abin maganar sannan ta fara da nuna murnar ta akan gasar da dai sauran su, sannan É—aura da faÉ—in.

"dai dai wannan lokacin zamu bayyana muku zaqwaqwurar wacca taci wannan gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha. Wannan Shahararriyar zaqwaqwurar dai ita ce! ita ce!! ita ce...!!"

Shiru tayi tana kallon mutane fuskar ta cike da murmushi kamar yadda zuciyoyin ƴan matan gasa take bugu da ƙarfi, haka ma zuciyoyin ƴan kallo maza da mata har dama ƙananan yara, zuciyoyin suke bugun wuce ƙima, hatta sauran mutane na duniya daga kan masu kallo a t.v show, da masu wayoyin hannu da dai sauransu, gaba ɗaya jira ake aji ko wacece tayi nasara ta zamo zaqwaqwurar shekara, {☆ nima dai ƚԋҽ Nαιɳαɾԋ ƙԃ da nake gefe nayi tsuru tsuru zuciyata bugu take na wuce ƙima saboda tsoro💔®}

Murmushi Mrs William tayi ta kuma kallon doguwar paper É—in dake a hannunta, sannan ta É—ago kanta, ta kuma kallon duka kyawawan Æ´an matan gasa waÉ—anda duka suma idanunsu yake akanta, amma banda Afeefah da tayi kamar batasan a halin da ake ciki ba, saima magana ta ido da takeyi ita da Zaynerb sai faman murmushi suke sakarwa juna.

Gyaran murya Mrs William tayi sannan ta kuma gyara zaman medical glass É—in dake a fuskarta, sannan ta ce.
"ba kowa bace wacca taji gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha ma'ana tazo ta ɗaya kuma zaqwaqwurarmu fa ce 'MISS F££FAH MAI KYAU..." [dayake shine real name na ta a gasar😘].

Wani irin ihun murna gaba É—aya mutanen gurin suka saka hadda masu fito (whistle) da masu rawa (dance) Deejarh saman kujerar da take kai ta hau tana faÉ—in.

"Kai yasin sai Balarabiyar India, Huh Huh ta zama SARAUNIYAR KYAU ta jaha Allah ya kaimu na ƙasa ma, yaƙini nake dashi akan cewa ita ce zata cinye huh hu oh sai Balarabiyar India😛."

Haka kawai Deejarh take faɗa cike da farin ciki, wayyo masu karatu kuzo kuga murna a wajen su Auntie Nainarh, Auntie Nailah, Haleesat, Zaynerb, Lailah abin ba'a iya cewa komai Mrs Mai Kyau kuwa komai faƙonka baka isa kace ga abin da ke a zuciyarta ba, ta dage tana taya murna😆

💋SARAUNIYA F££FA MAI KYAU💋
Chapter 43 · 0% Book details