← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 96

Sashe 45

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Afeefah tayi sannan ta ce "Ina godiya sosai nima Deejarh tawa Allah ya bar ƙauna mara adadi tsakanin mu."

Mister Mai Kyau ya ce cike da zolaya "Yanzu dai a barmin Shalele taje ta shiga mota driver yaja mu tafi gida, sannan ayi taya murnar a gida can ina ga zaifi. Dariya sukayi sannan babu musu suka É—un guma cikin motocin su cike da farin ciki sai gida.

KANO

HUMAIRA

Humaira zaune suke a ƙaton wajen gunadanar da gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jahar Kano, wanda ya sama hallatar manyan mutane maza da mata da ƙananan yara hadda ma Larabawa da Turawa da kowa da mutane, gurin ya haɗu sosai sosai. Especially ma saman floor ɗin gaba ɗaya launin komai na gurin sky blue and White color ne, jama'a ƴan kallo gaba ɗaya an nutsu ana jira a fara gunadar da Gasa. Daga gefe gasu Photographers nan birjik, ga ƴan gidan T.V nan, ƴan jarida ne da sauransu ana sai ta camerori ana jira lokaci ya cika da.

Daga ɗayan gefan kuwa Alƙalan Gasar ne kamar yadda aka saba mutane huɗu Baƙaƙen fata biyu, sai Baturiya ɗaya sai kuma wata Kyakyawar Balarabiya suna zaune saman wasu haɗaɗɗun kujeru irinna zaman manyan mata masu jida kansu, ga wasu uban littafai da papers a gaban kowannensu, mutane an cika gurin ba masa tsinke gurin yayi tsit ana jira lokaci ya cika a fara kafta Gasa.

MISALIN ƘARF£ GOMA SHA ƊAYA DAI DAI...

Humaira suna zaune a first chairs na gurin ita da Ni'ima dake a gefanta na hagu sai kuma Auntie Mrs Komai Naka, daga gefan dama, sai su Auntie Nafeesa da su Na'ima.

Gaba É—ayansu sun bada hankulansu suna jira suga kyakyawar da zata fara fitowa. ah domin kuwa taron na kyawawa ne.

TOHM

Ta wani dogon korido wata haÉ—aÉ—É—iya kuma kyakyawar budurwa ta fito tana takun gayu, tana sanye cikin shigarta na Gasar tayi kyau harta gaji da yin kyau É—in, duk taku É—aya da zatayi sai ta tsaya masu É—aukar hoto sunyi ma ta sannan...

Da sauri Humaira ta ciro tsadaddiyar wayarta a jakarta, ta fara É—aukar Video ana gudanar da Gasar, ita kuma tana É—aukar duk wacca tazo sai ta ma ta Video idan ta koma kafin wata tazo sai tayi saving É—in Videon a wayarta, idan wata ta fito ita ma ta ma ta nata É—aukar daban.

TOFAH

Gasa ta fara É—aukar É—umi fa, a domin kuwa Æ´an matan Gasar biyar har sun fito saura biyar kenan.

Gaba ɗaya gurin ya kuma yin shiru ana jira budurwa ta shida ta fito. domin ganin nata salon kyawun😘

WOW

Daga ganin irin shigar Princely Dresses É—in da take ciki sai ka rantse Æ´ar sarkin ETHIOPIA ce, saboda tsananin kyau irin kyawun da tayi.
Tayi irin kyan nan na bugawa a kowani irin takarda da kuma bayyanawa game da nunawa a gidan talabijin na duk duniya.
Irin kyawun nan wanda samari suke poster su dinga liqawa a unguwa unguwa fa, tayi kyau as Diamond.

So Casual and Perfect take cikin wata arniyar Gown sky Blue irinna ƴa ƴan sarauta. Har ƙasa rigar ta sauka ma ta.
Pastel twist hair ɗinta lulluɓe da wata kalar mayafi sky Blue mai adon stones, fuskarta tasha make-up abin sai wanda ya gani, hannayenta cikin wasu handgloves sky Blue irinna Princely Princess, hannunta na dama riƙe da wata ƴar siririyar sanda mai launin sky Blue and purple color, shima dai irinna na yaran sarauta, kai idan nace zan tsaya lissafo kalar kyan da tayi sai a kwana ba'a kai ko rabi ba, saboda haka just kuyi imagine kawai guys 🥳

Kyawawan ƙafafunta kuwa cikin wani haɗaɗɗen Crystal Princess Heels mai shaining, launin shi white and blue color, ga kyawawan idanunta masu launin Ash color cikin wani arnen glass no respect mai launin sky Blue.

Tafiya take a dogon koridon Hall na Gasar har ta ƙariso tsakiyar floor ɗin. So Casual and Perfect Jiddarh ta gama haɗuwa tako ina abin dai hmm hummm sai mai iya imagine, gata kyawun ta Natural ne babu ƙarin na kanti ko kaɗan fa.

Fuskar ta cike da fara'a take kuma taku mai cike da salo na musamman, tunda Jiddarh ta fito gurin ya ɗauki ihun murna anga kyau kamar a wanke hannu sannan a taɓa.

Daga ɗayan ɓangaren kuwa gaba ɗaya Photographer's sun tattare hankulansu guri ɗaya suna ɗaukar hoton Jiddarh domin takai a ɗauketa hoton, harta wuce matsayin tuni.
Sai da tayi mintuna biyar dai dai sannan ta koma ciki, wata ta fito haka abin ya dingi tafiya har akazo kan ta goma kuma ta ƙarshe wacca daga ita shikenan Bye Bye Gasa😊

Ita ma dai ta haɗu babu ƙarya sam z tsarin, sai da ta goma tayi five minutes kamar sauran ta koma, bayan mintuna goma ansamu dai gurin yayi tsit sannan...

Miƙewa ɗaya daga cikin Alƙalan Gasar tayi tana magana cikin harshen Turanci magana take akan yadda su duka suka nuna farin cikin su akan hallatar Gasar da mutane sukayi sannan suka bada gudun mawa wajen ganin Gasar ya tafi yadda ya kamata, kana ta gangaro da maganar nata akan ƴan matan Gasa, ta ɗanyi bayani a taikace sannan ta bada dama duka ƴan matan Gasar su goma suka hallara a tsakiyar gurin Gasar.

Madam Miracle ta ci gaba da cewa "A halin yanzu zamu ji kuma mugani sannan musan wacca ta sama nasarar lashe wannan Gasar ma'ana dai tazo ta É—aya."

Tayi maganar tana duba wata white paper doguwa dake a hannunta na dama tayi murmushi sannan!.

Ta ci gaba da faɗin "Ya kamata mu taya Malama Jiddarth Komai Naka, murnar lashe wannan Gasar na SARAUNIYAR KYAU matakin jaha...Dan haka cikin girmamawa muna gayyatar Malama Jiddarth izuwa saman floor domin ta karɓa gift ɗinta na musamman da ta cancanci samu."

Ta ƙarishe maganar a yayinda take kallon kyakyawar Diamond Lady ɗin da sunanta yake a matsayin Jiddarth har cikin zuciyarta ta yaba da kyawu da komai na Jiddarh, don ita Jiddarh ake kira one in Dollars bama
million ba eheee . 🤗😁

🎀J££DD@RH🎀

Fuskarta kawai idan mutum ya kalla zai fahimci tana cikin farin ciki ba ɗan ƙarami ba, farin ciki irin wanda mutum baimasan taya zai bayyana shi ba.
Tafiya take cikin nutsuwa a yayinda zata ƙarisa ta karɓa gift a matsayinta na wacca ta lashe Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha. A garin Kano Najeriya.

Sannu a hankali take tafiyar yayinda duk taku ɗaya da zatayi sai kaji ƙarar Crystal Princess heels ɗin dake a kyawawan ƙafafunta.

ÆŠoss, ÆŠoÉ—É—os, ÆŠas, ÆŠas.

Haka sautin yake bayarwa, gaba É—aya gurin yayi tsit hankulan mutanen gurin gaba É—aya yana akanta.

Qarisawa tayi saman floor ɗin sannan taja ta tsaya a gaban Madam Miracle, murmushi Madam Miracle tayi sannan ta ɗauko wani haɗaɗɗen box Blue color an nanɗeshi da wasu kyawawan igiyoyi Yellow color and other's ta miƙa ma ta tana faɗi cikin ƙasa da murya.

"Malama Jiddarth ina tayaki murnar lashe wannan Gasar ina fatan zamu haɗu a gasar SARAUNIYAR KYAU matakin ƙasa?."

Washe fuska Jiddarh tayi sannan ta ce.

"In Allah ya yarda."

Ta faɗa hakan a lokacin da Madam Miracle ta miƙa ma ta box ɗin, harta juya zata koma, Madam Miracle ta ce

"Baki ji ba,"

Juyowa Jiddarh tayi tana kallon ta, murmushi Madam Miracle ta kumayi sannan ta miƙawa Jiddarh wani haɗaɗɗen Diamond Ring ta ce "Wannan dagani ne, na baki kyauta saboda kyanki kawai." 😃

Ihun mutane da sowa gurin ya kuma É—auka kamar kamar mene.
Dariya kawai Jiddarh takeyi a lokacin da Madam Miracle ta kammala zura ma ta Diamond ring a yatsarta na Ƙarshen hannun damar ta, godiya tayiwa Madam sannan ta juya tana nunawa mutane gift ɗinta da kuma tsadadden Diamond ring ɗin bayan komai ya lafa ta koma ta tsaya a gurin ta.

Haka aka ci gaba da kiran sunayen Æ´an matan Gasa har aka zo kan ta uku, aka bata kyautarta sannan ta dawo kusa dasu Jiddarh da budurwar da tayi ta biyu ta tsaya.

Madam Miracle ta ci gaba da jawabi cike da qwarewa da sanin takan abin, ana cikin haka ana shirin tufe taron kenan wata kyakyawar matashiyar budurwa daga cikin sauran Æ´an matan Gasan bakwai ta zube a gurin a sume.

Da sauri wata kyakyawar budurwa daga cikin ƴan kallo ta hau saman gurin tana kiran sunan budurwar da ta suma da alama budurwar Ƴar uwanta ce, duk yadda akaso wannan budurwa ta farka daga suman da tayi abu ya cutura, haka aka kwasheta ranga ranga zuwa asibiti.
Daga haka kuma taron dai ya tashi jikin kowa yayi sanyi laqwas.

Da gudu Jiddarh ta ƙarisa wajen su Humaira da suke tsaye curko curko a harabar Hall ɗin taron, bata damu da tarin mutanen dake kallonta da ɗaukar Video da kuma hotunan ta ba.

Rungumo Humaira da Auntie tayi a tare tana dariya.
"Oh Allah wai ke Jiddarh bakya girma ne?, ai wannan sai ki karyani fa." Cewar Auntie tana dariya.

Dariya Jiddarh takeyi ta ce "Auntie na ina farin ciki da murna yau, kawai dan ma abin da ya faru yanzu ya É—an sanyaya min jiki ne, don da alama yarinyar ta gaza jure rashin nasara ne shiyasa harta suma ko?."

Humaira ta ce "E, gaskiya abin akwai taɓa zuciya wata ƙila tayiwa Gasar dogon buri ne, sai kuma Allah yasa ba ita zata sama Nasara ba, sai ita kuma ta saka jure hakan ta sume."

"Koma miye matsalar ta can taje taji dashi ba damuwar ku bane, kuji da abin da yake a gaban ku yarana."

Cewar Auntie tana ya mutsa fuska. Da tsananin mamaki su biyun suke kallon ta jin abin da ta ce Jiddarh mamaki ya hanata magana, sai Humaira ce tayi ƙarfin halin cewa.

"Auntie wai mane naji kina faÉ—ane?, mutum ce fa ita, kuma mace dole zataji babu daÉ—i kinsan zuciyoyin mu ma ta akwai rauni."

Ɗan dafe goshi Auntie tayi tana cizan harshenta ganin tayi sakin layi a gabansu.😳

"Auntie dake fa nakeyi, kin min shiru?." Humaira ta faɗa a hasale tana fitar da numfar fashin ɓacin rai.

Gane yanayin da Humaira ta shiga ne yasa Auntie saurin kamo hannunta tana faÉ—in.
"Am so sorry my Dear, it's all my fault, na yadda bai kamata nayi wannan maganar ba. Amma ki yafeni kuskuren baki ne."
Chapter 45 · 0% Book details