← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 96

Sashe 53

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Matan kuwa a ƙasa Nigeria sukayi karatun su a wancan lokacin, Yayin da Zuwaira da take Babba ta gaji mahaifiyar su Dr_ Raheemah, tana karatun Likitanci ita ma a Babban University dake Jigawa State na wancan lokacin.

Sai kuma Jawaheer Æ´ar qwalisa ita Fashion and Love affair's take karanta.
Sai Jummai da Sakeenah suna karatun Likitanci suma ɓangaren E.N.T.

A haka rayuwa ta ci gaba da lulawa, har bikin Yunus Babban Yaya da kuma matan gidan duka Zuwaira, Sakeenah, Jawaheer, Jummai ya taso.

_

Yayinda da Yunus zai aura Yaganah ɗiyaga ƙanwar Hajiya Zuwairiya auren soyayya, Zuwaira kuma zata aura wani ɗan unguwan su mai Suna Jamil wanda tsohuwar soyayya ce domin kuwa tun suna yara suke son juna, ita da shi Jamil ɗin ɗa ga Alhaji Jalaludeen Aboki ga AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.

Sai Sakeenah wacca ita kuma wani ɗan Adamawa State zata aura ɗa ga Yayan Hajiya Harirah, Auren muna son junan mu.🥰

Sannan Jawaheer da Jummai suma duka anan Jigawa State mazajen da zasu Aura suke suma duka Auren so da ƙauna ne.

Haka akasha shagulgulan biki aka gama lafiya, daganan kuma aka kai amare É—akunan mazajensu.

Shi kuma Yunus ya ɗauki amaryarsa Yaganah ya wuce da ita ƙasar France inda ya sama aiki a ofishin jakadancin Nigeria dake a ƙasar.

Haka Rayuwar ta ci gaba da tafiya, har Abubakar da Yusuf harda Sameen suka kammala karatun su, ya rage saura Sagir ya kammala.

Wata Ranar Saturday zaratan samarin Ƴaƴan AL_HAJI SAMEER LAMIƊO..! suka sauka a ƙasa Nigeria, anan international airport dake Jigawa State.

Basu faÉ—awa kowa a gida dawowarsu ba, sai dai kawai ganin su akayi gida, a lokacin AL_HAJI SAMEER LAMIÆŠO. An fara tara jikoki ta wajen su Zuwaira bayan haka ma tsufa ya fara zuwa ba laifi.

Haka akasha murnar dawowar su sosai, barin ma dai Hajiya Harirah kamar ta goya twin's É—inta kamar yadda ake faÉ—a Abubakar da Yusuf dan murna kamar me.

___
Satin su Abubakar É—aya da dawowa Nigeria zuwa lokacin Abubakar ya sama aiki a Abuja. Yayin da Sameen ya samu a Lagos.
Yusuf kuma a Mai Duguri ya zaɓa ɗaya daga cikin company na AL_HAJI SAMEER LAMIƊO.
Zai ci gaba da kula dashi acan Mai Dugurin wannan abu ba ƙaramin daɗi Yayiwa Hajiya Zuwairiya ba.

___

Wata Ranar Saturday gaba É—ayansu jama'ar gidan suna zazzaune a palon gidan, hadda su Zuwaira, Sakeenah, Jawaheer, Jummai da suka zo ganin gida da Yaran su.
Yunus ne kawai babu da ya ke yana zaune a France ne, da Iyalanshi.

Ana cikin fira sukaji Door Bell, Sakeenah ce ta miƙe, taje ta buɗe don ganin waye.

Galala ta tsaya tana kallon kyakyawan matashin saurayin dake tsaye gabanta. Yana sakar ma ta murmushi jikin shi sanye cikin t-shirt Red color and trouser jeans Ash color. Ya É—aura rigar sanyi a saman t-shirt na jikin sa, ga sumar kanshi mai tarin yawa a waje baisa hula ba.

Da sauri yayi throw away da trolley É—in dake hannun shi, bai tsaya komai ba ya rungumota yana faÉ—in, "Yayi kewar su baki É—aya,"

Da sauri Sakeenah ta tureshi daga jikinta tana dariya ta ce "Haba Sagir kai baka girma ne wai, ai sai ka shigo daga ciki."

Tayi maganar tana É—aukar trolley É—inshi da ya jefar

Gaba ɗaya mutanen dake zazzaune a palon suka mimmiƙe tsaye, suna kallon Sagir cike da mamaki, shi kuwa ko'a jikin shi sai ma ƙarisawa da ya yi ya ɗauki jaririn Jawaheer yana mishi wasa.

Yusuf da mamaki ya É—an sake shi, ya buÉ—e baki yace

"Kai kuma daga ina haka?."

Juyowa sagir ya yi yana kallon su gaba ɗaya, da sauri ya ƙarisa ya rungume AL_HAJI SAMEER yana faɗin

"Abbhee.! ka gani ko wato Ƴaƴan ka basa ƙaunar Autarta, duka suka gudo Nigeria suka barni.

Shine nima kawai na gudo nan, kaga sai na ƙarishe karatun anan, tunda na kusa kammalawa."

Yayi maganar hankali kwance yana zama a kujera.

Suma komawa sukayi suka zazzauna sai kuma aka shiga gaisawa, bayan komai ya lafa Zuwaira ta kalla Sagir tana cewa

"Uhum munaji sai kuma akai mene, kawai ka ɗauko ƙafa ka dawo gida, yanzu me kakeso ayi maka?."

Kai tsaye ya bata amsa da

"Aure.!"

Gaba É—aya palon suka zubo mishi ido suna kallo, Dr_Raheemah ta kalleshi da kyau, tayi murmushi sai dai bata ce komai ba, dan ita macece mara san hayaniya sosai.

"Kaga naka, nace ungo naga kaji?."

Cewar Sameen yana jefa mishi daƙuwa. Su kuwa Abubakar da Yusuf mamakin ƙanin nasu ya hanasu magana.

Dariya Sagir ya yi yana ciro phone É—inshi a trouser pocket, sai da ya ciro sannan ya lalubo wani picture na wata matashiyar budurwa.

ÆŠaga wayar ya yi a tsakiyar palon yadda kowa da kowa zai gani, sannan Yace
"Ga ta sunanta Suwaiba Ƴar Kano ce, karatu ya kai ta London, shine muka haɗu acan muka fara soyayya fa, nikuma naji ina son Aure shine kawai na yanke shawarar na sameku na faɗa muku, a domin aje Kano a nemomin aurenta."

Yana maganar ne yana kuma musu zooming na picture É—in ta yadda zasu gani yadda ya kamata.

Baki sake wannan karon gaba É—aya suke kallon shi, sunma kasa magana dan mamaki.

Miƙewa Yusuf ya yi ya ƙarisa wurin da yake, ya kamo hannun shi ya nufa ƙofa dashi, bayyima kowa magana ba.
Da sauri Hajiya Harirah ta ce "Ina zaka kaishi ne?."

Juyowa Yusuf ya yi yana kallon duka Ƴan palon kana ya yi murmushi kai tsaye yace
"Naga alamar ya sami mental illness. wannan ne dalilin da yasa zan kaishi psychiatric hospital, kinsan akwai wani friend É—ina acan, sai ya taimaka ya duba mana lafiyar shi, idan akwai mai zuwa a cikin ku falil lahil hamdu sai yazo mu tafi, tun kafin abin nashi ya yi nisa fa."

Yayi maganar yana gimtse dariya.
Miƙewa Jawaheer tayi tana faɗin

"Allah sarki Autar mu. Ashe shiyasa naga yana abu kamar wanda baya a cikin hankalinsa. Ashe kuma imagine da nakeyi ne ya zama gaskiya, aikuwa muyi sauri Yah Yusuf dan kasan yamma ta fara, kar su tashi a hospital ɗin."🤣

Ita ma tayi maganar tana É—aukar handbag É—inta da jaririyarta a hannu. Kamar da gaske.

Ganin dai da gaske suke kallon mahaukaci suke mishi, yasa ba shiri ya qwace hannun shi daga cikinna Yusuf.
Ya ruga wajen AL_HAJI SAMEER ya zauna kusa dashi yana faÉ—in

"Allah Abbhee. waɗannan yaran naka ba sona sukeyu ba, kana dai gani wajen psychiatrist zasu kaini fa." Yayi maganar cike da shagwaɓa.

Su kuwa mutanen palo mai zasuyi idan ba dariya ba, aikuwa nan suka shigayi babu qaqqautawa Happy family 🤪.

Bayan sunyi shiru aka ci gaba da fira Abubakar ya kalla Sagir yace "Au yanzu haka zaka zauna ba za ka shiga ɓangarenka ka huta ba?."

Dariya Sagir ya yi sannan ya dawo ƙasa ya zauna, yana kallonsu gaba ɗaya kana yace

"Kun san wani abu kuwa?."

Duk a tunanin su wani abun kirki zai faÉ—a.
Saboda haka duk suka haÉ—a baki wajen cewa
"A'a sai ka faÉ—a."

Jummai ta gyara zama tana faɗin "A'a ƙaninmu sai ka faɗa, sannan zamu sa ni.'

Murmushi ya yi sannan yace "Da gaske nake fa, Allah Aure nakeso, wannan ne ma Babban dalilin da ya sa na dawo."

Sakeenah ta ce "Kai Sagir yanzu a gaban su Hajiya da Abbhee kake wannan maganar, bakajin kunya, daɗin daɗawa ga yaranka a wurin fa."😅

Tayi maganar tana mishi nuni da ƙananan yara dake palon, ƴan dugui dugui dasu, su na wasannin su.

Murmushi ya kumayi yace "Aha to ai wannan dalilin ne ma yasa nake maganar a gurin, saboda naga suna wurin, kawai dan bakuga Suwaiba ta ba ce, da sai kun fini ƙosawa na Aureta kafin wani yamin snatching ɗin ta."😎

Ko kunya babu yake maganar yana kuma nuna musu pictures kala kala na Suwaiba, zai kuma magana kenan.

Sameen ya É—auki cushion na sofa ya jefa mishi yana faÉ—in

"Yi mana shiru É—an nema baka da kunya ko kaÉ—an, gashi kaje London ka kuma koyowa salo salo."

Dariya kawai Sagir ya ke yi yana faÉ—in "Wallahi Yah Sameen kai ma kasan yadda London É—in nan take, gaba É—aya sun mayar da bawan Allah kamana kullum sai dai nayita É—aukar azumi fa kuma....!"

"Au badai zakayi shirun ba ko, ka ci gaba ne ko?."

Cewar Sameen yana dariyar "Tu no wani drama da ya taɓa faruwa tsakanin Sagir da wata Baturiyar London 😍.

Sagir ya kalla duka mutanen palon yana faÉ—in

"Kunga ni ko tunda kukaga yana dariya shima Auren yakeso, saboda haka kawai a haÉ—amu dasu Yah Yusuf ayi lokaci guda."

Tashi Sameen ya yi daga zaunen da yake ya nufa Sagir zai kama ya naÉ—a.

Ai da sauri Sagir ya miƙe tsaye yana faɗin "Yah Sameen na fa taimaka maka ne, tunda naga kanajin kunyar faɗa fa."

Ya yi maganar yayin da suke zagaye palon shi da Sameen yana binshi zai kamo ya daka, shi kuma yaƙi bari hakan ta kasance, sai faman zagaye ƙaton palon suke cike da farin ciki kamar wasu ƙananan yara ko dama ba wasu shekaru na azo a gani bane a tsakanin su.

Saminu ganin Sagir wahalar dashi kawai yake ba tsayawa zayyi ba, yasa shi ya koma ya zauna yana faÉ—in

"Tunda haka ne sai na faÉ—a, kowa ya sa ni."

Sagir dake can gefa tsaye yana sauke haki yace

"Ka faÉ—amana so what.?"

Sameen yana dariyar mugunta Yace "Kai kyakyawar African Nigeria ka ce na faÉ—a komai ko?."

Jin abin da Sameen yake cewa ai Sagir bai san lokacin da ya yi wata super ba, sai gashi a gaban Saminu ya rufe mishi baki da duka hannayen shi, faÉ—i yake

"Haba my Yah Sameen ba kace ba zaka faÉ—awa kowa ba, indai ni ne na dena maganar Aure indai ba zakayi wannan maganar ba, to daga yauma zan dinga kiranka da YaYah Sameen shikenan, daga Yau haka zan dinga kiranka kaji ko my Yah Sameen?."

Gaba ɗaya Sagir Yana maganar ne a ruɗe tsoron shi Allah kar Sameen ya faɗawa su Abbhee dasu Yah Yusuf abin da ya taɓa faruwa a tsakanin shi da wata Baturiyar London.🤣
Chapter 53 · 0% Book details