← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 96

Sashe 64

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abubakar ya daɗe ciki bai fito ba sai da ya kammala duka abin da ya kamata dan ma shiɗin sananne ne daɗi da ƙari ga Naira shiyasa ba tare da wani ja'inja ko ɓata lokaci ba likitocin suka karɓa budurwar, sai da ya tabbatar da an shiga da ita ɗakin hutu bayan likitoci sun gama bata taimakon da ya kamata sannan ya fito da niyyar zuwa anjima idan ta farfaɗo sai su dawo ganin ta da yake lokacin dare ya fara kawo kai.

Tana zaune harta fara gyan-gyaɗi ta hangoshi Yana nufo motar, ajiyar zuciya ta sauke ta ƙirga a dadin lokacin da ya ɗi ba a ciki kusan awanni biyu.

Gyara wa Nailah kwanciya tayi a saman jinyarta sannan Ita ma ta sai ta zaman ta kana ta rufe idanunta kamar mai bacci.

BuÉ—e motar Ya yi sannan ya shiga bayan ya kammala abin da ya kamata ya tayar da Motar suka bar emergency É—in sannan ya É—auki hanyar gidan sa.

A hanya jin shiru taba yi masa magana ba, yasa ya É—an juyo da fararen idanun shi yana kallonta duk a tunanin sa tayi bacci ne.

Ya yi murmushi a fili Yace

"Mata iyayen kishi."

Tana jin sa tayi muluqwiii kamar mai bacci.

Har suka ƙariso gida Ya daidaita faker motar a wurin da aka tanadar domin yi bayan gate man ya wangale masa gate.

Bata koyi motsi ba, hakan yasa Abubakar É—an bugun kafaÉ—unta yana kiran sunan ta.

Ƙin motsi tayi shi kuma yaƙi denawa haka ba yadda ta iya, ta buɗe idanun ta tana hamma ta Kalle sa cike da ƙissa ta ce

"Oh My Lawful am sorry har mun ƙariso gida ban samu na tayaka fira ba bacci ya yi gaba dani."

Murmushi Abubakar ya yi ma ta sannan yace

"Aah karki damu kinji, matar mai kyau, nasan akwai gajiya fa sosai."

Fitowa suka yi gaba É—aya shiya taimaka ma ta wajen kwashe Yaran suka shiga ciki.
Shi Maleek aka kai shi É—akinshi Yayin da suma sauran ta wuce dasu nata bedroom É—in, shima Abubakar ya wuce nasa dukanin su a gajiye suke over.

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*___________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

Page *65&66*

*WASH£ GARI*

Tana tsaye a kitchen sanye cikin kayan shan iska ta É—aura apron saman kayan tana haÉ—a musu Breakfast cikin nutsuwa take komai abinta.

Alamar taku da ta jine yasa ta tsaya da abin da take yi sannan ta juyo.

Da tsananin mamaki take kallon mijinta dake tsaye gabanta sanye cikin doguwar jallabiya Brown tunani take shin ko ya yi makuwa ne ko me, amma in banda haka mai zai kawo shi kitchen bayan tunda suka yi Aure shekaru wajen nawa ko tunanin shiga baya yi, ko irin yace zai taya ta girki, a'a sai dai wani ba Abubakar sai dai ta girka yaci ba godiya balle 🥰....

A je tunanin tayi a gefe sannan cikin murmushi ta ce

"Barka da safiya My Lawful Fatan dai ba neman wani abu bane ya kawo Babban mutum kamar ka kitchen, kai da kanka baka nema wannan servant naka ba a domin ka bata umarni ba."

Murmushi Abubakar Mai Kyau Ya yi sarai ya fahimci abin da take nufi wato dai gatse tayi masa ko ba damuwa, gyara tsayuwar sa ya yi kana Yace

"Ko É—aya dama nazo ne na faÉ—a miki ki girka abinci daban saboda..."

Da sauri ta katse shi da faÉ—in

"Baƙi zamuyi hala, ai karka damu Yanzu zan kammala sai na saka a kuloli, kaje kayi shirin office kawai oga."

Tayi maganar tana juyowa ta ci-gaba da aikin da take yi, bai kuma cewa komai ba ya fice shima daga madafar.

__*

Wuraren ƙarfe Takwas da Rabi a Ranar tana zaune saman mattress bayan sun kammala breakfast ne tayi wanka tayi shirin zuwa asibiti, shi ne ta zauna a gefan mattress tana jiran shigowar mijinta Abubakar ɗakin.

Jin shiru bashi ba labarin sa yasa ta miƙe sannan ɗauki lab-coat ɗinta da kuma jakar ta dama tuni ta yafa mayafin ta.

Fitowa tayi kai tsaye ta wuce bedroom ɗin sa tura ƙofar tayi bakinta ɗauke da sallama daga can ta hango sa tsaye sanye cikin shigar alfarma na manyan kaya.

ÆŠan dafe kanta tayi ita ta manta Yau Laraba wacca ta kasance first October babu aiki sam.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ƙarisa shiga ciki tana faɗin

"Oh amma a gaisheni, gaba ɗaya na manta da cewa Yau ɗin a Free muke Ranar zagayowar Ƴan cin ƙasarmu abin alfaharin mu."

Tayi maganar tana dariya.
"Karki damu kinji kin kusa samun Abokiyar zama kinga saita dinga tayaki wasu ayyukan inaga idan kika sama Abokiyar zaman zaki rage samun tention da yawa ko kuwa?.."

Tunda Abubakar ya fara maganar Rafi'at take faman antaya masa harara.

Lura da hakan da ya yi ne ya shi canza topic ɗin ba shiri.🤣

Murmushi Abubakar Mai Kyau Ya yi sannan Yace

"Okay to ai babu damuwa a haka ma Yadda kike zaki iya Rakani izuwa unguwa tare da Yara."

"Unguwa kuma to wurin wa."

Rafi'at ta tambaya cikin suɓutar baki.

"Kedai kawai ki shirya zaki gani ai."

Abubakar ya bata amsa, bata kuma cewa komai ba ta miƙe tana kallon sa sannan ta ce

"Ka bani mintuna biyar Yanzunnan zan shirya shaf-shaf."

Tayi maganar tana nufar ƙofa ta buɗe sannan fita.

Tana fita bedroom É—in ta ta wuce tana shirya wa tana tauna maganganun Abubakar wato Abokiyar zama, kuma ita hmmm, murmushin Takaici tayi a fili ta ce

"Rafi'at Rafiq Rayyan tafi ƙarfin ayi ma ta kishiya har duniya ta naɗe forever Wallahi."

Tsaf ta gama shirinta sannan ta ɗauki jakar ta da mayafinta ta fito waje har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba domin kuwa har wani zazzaɓine taji Yana shirin kamata jin maganar kishiya, wai danma da wasa ya yi ma ta maganar, imagine take yi to da'ace da gaske Abubakar Yake wannan maganar ya zatayi ke nan."

A fili ta ce "Sai dai idan bani a duniyar."

Downstairs ta sauko daga can saman kujeru ta hango mijinta Abubakar ga Yaranta suma a shirye cikin shigar alfarma suna fira da mahaifinsu Abin gunin ban sha'awa.

Murmushi kawai take yi tuni ta manta da maganar wata banza kishiya, hango mijinta da tayi da Yaranta cikin farin ciki.

Sai ita ma ta tsinci kanta a cikin matsanancin Farin ciki taji gaba ɗaya baƙin cikin da Abubakar ya ƙunsa ma ta na maganar kishiya ya gudu.

Qarisowa wurin tayi fuska ɗauke da ƙayataccen murmushi tana faɗin

"Oh My Lawful ayi haƙuri dani na ɓata muku lokaci daya wa ko?."

Tayi maganar cike da ƙissa, murmushi Yayi Yace

"Oh no Yaranki sun qwace ki saboda sun zagaye mahaifin su suna masa tatsuniya."

Tana dariya ta ce "Ai haka ake so."

Abdulmaleek Yaron da bazai wuce shekaru huÉ—u da watanni ba a lokacin ya kalla mahaifiyar sa kana ya mayar da kallon sa akan mahaifin nasa dariya ya yi cikin qwaranci irin na sa Yace

"Daddy! Mommy!!."

Gaba É—aya suka juyo suna kallon shi Yace
"Momy Daddy Yafi ki kyau cocai cocai."🤣

Dariya suka yi baki É—aya kana Rafi'at ta ce

"Aha ai kowa ma haka ake cewa harni ma na sani saboda shiÉ—in kyakyawane a cikin kyawawa."

Tayi maganar cike da nishaɗi, miƙewa suka yi ita ta riƙe Nailah Yayin da Abubakar Ya ɗauki Nainarh sannan Ya riƙe hannun Abdulmaleek suka fita waje, motar sa suka shiga baki ɗaya sannan ya tayar da Motar, gate man ya wangale masa gate ya fita sai unguwa🚗..../This is the happiness family/....🚗

***

Cak murmushin dake akan kyakyawar fuskar ta ya gushe fuskarta ta koma Tamkar bata taɓa murmushi ba, saboda tsaban mamakin wurin da taka mijinta Abubakar ya dawo dasu "this is unbelievable."

Wato shiyasa taka jiya da dare ya fita bai dawo ba sai wuraren sha ɗaya Abin da bai taɓa ma ta ba.

Kallon sa tayi dai dai lokacin da shima ya juyo da kallon shi akanta, cike da tsaban takaici ta ce

"Haba My lawful yana ga ka dawo damu wannan emergency kodai wani ne aka kwantar ban sani ba?."

Tayi maganar cike da sa ran ya bata amsa ba kalar wanda take tunani ba.

Gimtse kyakyawar fuskar sa ya yi alamar ba wasa kana ya ce

"Wurin Ƴar uwanki muka zo domin tafiya da ita gida."

Ya mutsa fuska tayi cike da alamar tambaya take kallon sa sannan ta ce

"Wacca Ƴar uwata kuma Sailuba ba ko wa?."

Girgiza ma ta kai ya yi alamar a'a kana Yace

"Fito mu shiga zakiga ko wacece ai."

Babu musu ta buɗe motar ta fito shima bayan ya fito suka riƙe Yaran sannan suka nufa ciki Yayin da wasu Nurses ma ta ke bin bayan su da kulolin abincin da suka zo dasu.

Ita dai Rafi'at tafiya take kawai amma gaba É—aya hankalin ta baya a jikin ta tunani take shin ko wurin waye haka Abubakar ya kawo su, ita ko kaÉ—an bata kawo wannan budurwa da suka taimakawa jiya a tunanin ta.

To akan me ma zatayi tunanin ko ita ce bayan cewa taimakon ta kawai suka yi bawai zasu kasance da ita bane.

Har suka ƙariso Ward ɗin bata ankara ba, har sai da taga waɗanan Nurses dake gabansu sun shiga wani Room kana ta fahimci nanne Room ɗin da wacca suka zo wurinta take.

Tura ƙofar Room ɗin Abubakar ya yi ya shiga Bakin sa ɗauke da sallama yayin da ita ma Rafi'at ta take masa baya.

Zaune take a saman gadon marasa lafiya jikinta sanye da kayan asibiti gaban ta kuma tufa ne take ci a hankali, kanta a duƙe tana kallon ƙasa, sai da ta cinye Wanda yake a bakinta sannan ta amsa sallamar da taji anayi a daidai lokacin da ta ɗago da kanta tana kallon mutanen dake shigowa ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallon Rashin sani.

Wani irin bugawa ƙirjin Rafi'at Ya yi ganin kyakyawar fuskar budurwar dake a ɗakin zaune saman bed.

It's unbelievable menene kuma haka me yasa Abubakar ya dawo dasu wurin wannan to su mata Mene?.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sama wuri ta zauna a saman wata farar kujera kusa da mijinta Abubakar da shima ya zauna.

"Sannun ku fa please Mister and Mrs kune kuka taimake ni. In Yesterday?."
Chapter 64 · 0% Book details