← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 96

Sashe 47

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suma dai ajiyesu a gefe tayi, kana ta kuma ciro wani Check na kuÉ—i.

Har rige rigen karɓan Check ɗin ake a hannun Auntie a tsakanin Humaira da Jiddarh.

Humaira ce ta riga karɓa tana dariya ta buɗe. a fili ta ce

"Two Millions Naira fa."

Tayi maganar tana kallon Jiddarh, ai ba tare da wani ɓata lokaci ba, ta rungumo Jiddarh tana faɗin "Congratulations My Dear, Jiddarh a gaskiya keɗin mai sa'a ce a cikin masu nasara a wannan rayuwar."

Sakin Jiddarh tayi sannan ta ɗauki Diamond Wrist Watch ɗin, ta riƙe a hannunta sannan ta kallesu su duka tana faɗar.
"Shin ko kunsan wannan Watch ɗin akalla ba'a kasara ba saiya kai Ten Millions, ga wannan sarƙar da kuma zobe da ƴan kunnaye kuɗaɗensu na badanne fa, dan bazai lissafu ba."

Magana take amma gaba É—aya kamar hankalinta baya a cikin jikinta, saboda tsananin mamaki da kuma farin ciki.

Zama tayi a saman 3sieter sannan ta kalla Jiddarh dake ta faman washe baki kamar gonar auduga saboda tsananin farin ciki tama kasa magana.

Murmushi Humaira tayi sannan kuma mayar da kallonta akan Auntie da ta lula duniyar tunanin.

Zatayi magana tsadaddiyar wayarta dake gefanta tayi ƙara alamar shigowar kira, gaba ɗaya suka sauke ajiyar zuciya na dawowa hayyaci hadda ita.

Ganin bata da niyyar picking call É—in yasa Auntie cewa.

"Ki É—a ga mana ko dai ba kiran ki ake ba, ajiyar zuciya Humaira ta kuma saukewa a karo na bar ka tai sannan ta É—auke kallonta daga kansu ta mayar kan wayarta dake faman sowa.

Murmushi tayi ganin Abokiyar aikinta Hameeda Sagir ce mai kiran nata, da sauri tayi picking sannan ta kara a kunenta bakinta ɗauke da sallama, daga can ɓangaren Hameeda Sagir ta fara magana.

"Ke Komai Naka Girl, aje sallamar nan a gefe kiji abin da zan faÉ—amiki."

"Okay inaji ai."

Humaira ta bata amsa tana saita nutsuwarta, Hameeda Sagir ta ci gaba da cewa.
"Yanzu yanzu ki kunna T.v domin sanin halin da Birnin Kano Najeriya take ciki, dan da alama baki kunna ba, kuma baki sani ba."

Da sauri Humaira ta tambayeta "Menene yake faruwa ne, a garin haka da na ji ki So Anxiety ne?"

Hameeda Sagir ta ce "Kedai kawai ki kunna T.v zaki ga komai." Da faÉ—ar hakan tayi rejected.

Ganin yadda Humaira take bin wayar da kallo batayi magana bane yasa Jiddarh tambayar, "Lafiya kuwa Humaira meke faruwa ne, wacece ta kiraki, kuma mai ta faÉ—a miki."

Kallonta Humaira tayi ta ce "Hameeda Sagir ce Abokiyar aikina ta kirani."

Auntie ta ce "Oho Hameeda dai nan Neighbor É—in mu ko, to menene ta faÉ—a miki.?"

Humaira ta bata amsa da, "Cewa tayi wai na kunna T.v zanga wani abu fa."

Tun kafin ta ƙarisa Jiddarh ta ɗauki Remote Control ta kunna T.v dake a palon gaba ɗaya suka zuba ma T.v ido domin ganin abin da zai faru."

ᴀʙɪɴ ᴅᴀɪ sʜɪ ɴᴇ.
Da farko hoton Asibiti aka fara nunawa sannan kuma aka nuna wannan Shararriyar Æ´ar jaridar da tasan makamar aiki, wato Hameeda Sagir.
Magana take kamar haka.

"Assalamu alaikum jama'ar duniya masu kallon mu da sauraron mu, kamar yadda kuka sani sunana Hameeda Sagir ina tare da Abokin aikina mai É—aukar bidiyon abin da ke faruwa, wato Omar Uthman Gaya, yau muna tafe muku da wani rahoto ne, akan wannan dai budurwar Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha, da ta faÉ—i a lokacin da ake tsakiyar gudanar da Gasar SARAUNIYAR KYAU na jahar Kano, ana tsaka da Gasar."

A halin yanzu muna cikin Asibitin da aka kwantar da ita, kamar yadda kuke gani zamuji ta bakin ita wannan budurwar mai suna Juwairiya Jabir Bici.
Domin sanin dalilin da ya sa ta faÉ—i a tsakiyar filin Gasar a sume."

Ƴar jaridar Hameeda Sagir tayi maganar tana nufar cikin Ɗakin da aka kwantar da Juwairiya Jabir Bici yayinda mai ɗaukar bidiyo yake take ma ta baya.

Kyakyawar budurwar tana daga kwance saman Bed irinna na masu jinya jikinta sanye da kayan marasa lafiya ana ma ta ƙarin ruwa.

Zama Hameeda Sagir tayi daga gefanta sannan taba mai É—aukar bidiyon damar mayar da na'urar É—aukar akan Juwairiyar.

Murmushi Hameeda Sagir tayi ma Juwairiya Jabir Bici, ita ma ta mayar ma ta sannan Hameeda ta fara magana.

"Sunana Hameeda Sagir kuma niÉ—in Æ´ar jarida ce, sannan ga Abokin aikina Omar a halin yanzu wannan É—aukar da kikaga anayi ta kai tsaye ne. Don haka Malama Juwairiya Jabir Bici zaki iya faÉ—a mana muda É—umbin mutanen da suke kallo ainihin abin da ya saka kika suma a tsakiyar filin Gasar.?"

Hameeda Sagir tayi ma ta tambayar tana mayar da abin maganar dake hannunta a sai tin fuskar na Juwairiya.

Miƙewa Juwairiya tayi ta zauna da kyau, sannan tayi gyaran murya kana ta fara magana kamar haka.

"Da farko dai,
Sunana Juwairiya Jabir Bici.
Mahaifina Alhaji Jabir cikakken É—an garin Bici ne ta jahar Kano.
Mahaifiyata kuma Asalinta ƴar Nijar ce, a maraɗi, zaman aure ya kawota Najeriya kuma Kano, mu biyar ne a gurin iyayen mu yayyina uku duka maza, sai ƙanwata mace Auta kenan, sai kuma ni.
Tunda na taso a rayuwata burina ɗaya ☝, shine naga wata rana an wayi gari na zama SARAUNIYAR KYAU koda kuwa ta jaha ce.
Ko'a Makaranta ne aka tambaye ni abin da nakeso na zama a rayuwa sai nace burina ɗaya shine na zama SARAUNIYAR KYAU, haka ƴan class ɗin mu zasuyita min dariya, suna cewa tayaya zan zama SARAUNIYAR KYAU bayan kuma ni baƙace?.😭

A lokacin sai dai kawai nayi murmushi nace musu, ai abin ba haka yake ba, zama SARAUNIYAR KYAU, ba dole sai farar fata ba, baƙaƙen fata ma zasu iya zama."👍

Shiru tayi sannan tayi murmushi tana goge siraran hawayen da suka zubo ma ta, ta kalla Hameeda Sagir da tayi shiru tana kallonta, murmushi Juwairiya ta kuma yi sannan ta tambayeta da.

"Kinsan wani abu kuwa?."

Girgiza kai Hameeda tayi alamar a'a.
Juwairiya ta ci gaba da cewa "Akwai wani lokaci, wata rana da bazan taɓa mantawa da ita ba tsawon rayuwata, a lokacin na kammala Secondary School, ina shirin shiga University, a ranar da ta kasance Lahadi kamar yadda yake a al'adata ina zaune a palo ina abin da na saba, wato bincikar yadda ake gudanar da Gasar SARAUNIYAR KYAU. da kuma irin abuwawan da ya kamata wacca ta shiga Gasar tayi.
A Laptop nayi nisa sosai akan abin da nakeyi, najiyo muryar Yayana abin alfarina wanda kaf gidan mu shikaÉ—aine yake bin bayana akan ra'ayina na zama SARAUNIYAR KYAU.

Yana qwalamin kira tun daga waje, da sauri na miƙe tsaye na fita waje gurin shi, ina tambayar shi abin da yake faruwa, a lokacin cike da farin ciki Yayana yake faɗamin abin da na daɗe ina jiran ji a rayuwata.

Cewa an saka sunana acikin jerin Æ´an matan da zasu shiga Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha na shekara.

A lokacin na shiga farin ciki da zaquwa kalar wanda ban taɓa shiga ba, tsayin rayuwata haka zan zauna na dinga qwada kaya kala kala ina neman kalar da zansaka ranar Gasar.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya har akazo saura kwana É—aya a gudanar da Gasar ranar ko bacci na kasa, saboda zaquwa a saman sallaya na sallah na kwana ina jira gari ya waye mutafi wajen Gasar.

Haka ma da gari ya waye ko abinci ban ci ba saboda ƙosawar da nayi.

A TUNANINA idan mutum yana da wani buri nashi, mutanen gidansu sune first waÉ—anda zasu fara qarfafa mishi gwiwa akan burin shi kafin mutanen waje.

Amma ni banyi wannan sa'ar ba, domin kuwa kaf gidan mu ba mai ƙarfafa min gwiwa akan burina, sai Yayana abin alfarina shikaɗaine yake son abin da nakeso.

Babban abin da ya sanyaya min jiki a karo na farko shine.
A Ranar da zamuje Gasar ko mutum É—aya daga cikin Æ´an gidan mu babu wanda yazo domin ganin yadda Gasar zai kasance, sai Yayana shikaÉ—ai.

Haka mukaje wajen Gasar gaba ɗaya jikina a sanyaye, sai dai kuma wani Babban abin da ya ƙara kashemin jiki shine.

A lokacin da akayi Gasar nayi rashin Nasara, domin kuwa koda ta Uku kasa zuwa nayi.
Haka muka koma gida jiki ba qwari, amma ko mutum É—aya a gidanmu an kasa samu wanda zayyimin koda tambayar yadda Gasar ta kasance.

Sai Yayana shikaɗai a kullum yake ƙara ƙarfafamin gwiwa akan nayi hakuri akwai shekara mai zuwa, karna damu kaina domin haka rayuwar take.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya harna shiga University na fara karatu shekara ta zagayo.
Haka wannan shekarar ma Yayana yayi ƙoƙari ya samu aka saka sunana a cikin ƴan matan Gasar.

Haka cike da farin ciki yazo yake faɗamin, sai dai wannan karon na rage zaƙuwar, dan lokacin da ya faɗamin ma ban wani nuna farin ciki na sosai ba, kawai dai cewa nayi Allah ya kaimu lokacin.
Na cigaba da aikin da nakeyi, a lokacin sam Yayana baiji daÉ—in abin da nayi ba, amma bai ce dani komai ba.
Sai washe gari ya sameni yamin nasiha sosai akan yadda da ƙaddara.

A lokacin jikina yayi sanyi sosai kuma na ƙarajin ƙaunar Yayana sosai fiye da baya, sannan fiye da komai a Duniyata gaba ɗaya 💓

Haka rayuwata ta ci gaba da tafiya har akazo ranar Gasar a ranar nida Yayana mun fito harabar gidanmu zamu shiga mota mu tafi, saiga ƙanwata ta ƙariso gurin da gudunta, gaba ɗaya muka juyo muna kallon ta, Yaya ne ya tambaye ta abin da ya sakata gudu, sai cewa tayi tanaso ta rakamu gurin Gasar ne.🙂

Umma bataso Ummanmu ta sani saboda zata hanata🙃.
Duk da jikina yayi sanyi amma haka na daure nace ma ta ta shiga mota mu tafi, haka muka tafi da ita ba tareda Ummanmu ta sani ba, muka tafi wajen Gasar."

Shiru Juwairiya ta kuma yi tana kallon Hameeda Sagir, kamar yadda ita ma Hameedar ta zuba ma ta ido tana kallo cike da tausayi.

Sai da tayi mintuna biyar a haka sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ci gaba cewa.

"Muka ƙarisa gurin Gasa an fara gudanar da Gasar nayi Round ɗina nima cike da gwarin gwiwa irin wanda bantaɓa samun kaina a ciki ba.
Chapter 47 · 0% Book details