← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 96

Sashe 69

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuwa ta ɓangaren Amarya Hajarah Babban abin da ya hana ta buɗe fuskar ta a gaban Rafi'at shi ne, ba tasan da wani ido zata kalla Rafi'at ba, sannan kuma ba tasan wani kalar kallo Rafi'at zata ma ta ba, kallon mayaudariya na miki alkhairi kin sakamin da Auren miji?, ko kuwa kallon nagode da kika Aura mijina?.

Tasan dai Auren ta da Abubakar Wanda yake matsayin miji a gareta, wani ikon Allah ne kawai domin kuwa cikin wata biyar komai ya faru tun daga rescue nata da suka yi, da kuma komawar ta Jigawa State wurin su Hajiya Zuwairiya da zaman ta a can.
Dama Auran ta da Abubakar da ya biyo baya komai a cikin watanni biyar kacal ya faru.

Rafi'at mata ga Abubakar Mai Kyau kuma uwar gidan sa, ganin da tayi kowa ya watse an barta, gashi har wuraren goma Abubakar bai shigo gidan ba, to koma ya shigo bata sani ba.

Yasa ta kwashi Yaranta gaba ɗaya da suka yi bacci a nan palon ta shige bedroom ɗinta dasu ta rufe ƙofa.

Washe gari ma tunda ta fito da asuba ta girka ma Yaranta abincin da zasu ci ta kwashe a kula ta koma bedroom ɗin ta, ta kuma rufo ƙofa bata kuma buɗewa ba har wuraren sha biyu na Rana, tana jiyo hayaniyar su Jawaheer sama sama da alama suna shirin komawa Jigawa State ne.

Amma ko fita bata yi ba, har tayi baccin da bata samu tayi ba, a daren jiya, ta tashi taga Yaran gaba É—aya suma baccin wahala suke yi saman bed É—in kusa da ita, amma banda Abdulmaleek da Yake can gefe Yana wasa da Teddy Bear abin shi.

A hankali ta sauko daga saman gadon tana ji cikin ta Yana ma ta ƙugin Yunwa domin kuwa Rabon ta da taci wani abu, tana ganin takai kwana biyu, tana shirin shiga bathroom taji muryar Abdulmaleek Yana kiran sunan ta, juyowa tayi tana kallon sa kana ta ɗaga masa kai alamar "Menene."

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Page *73&74*

Gimtse kyakyawar fuskar sa yaron ya yi sannan yace

"Momy melaca kika kulle mu a bedroom, bayan Daddy ya yi Mana cabuwar Auntie?."🤔.

Cike da maÉ—aukakin mamaki Rafi'at take kallon Yaron nata, tana mamakin kaifin tunani irin nasa.
Ashe duk wannan abin da ake ciki yana kula da komai duk da cewa cikin qwarancin sa na yara ya yi maganar amma ta fahimci komai.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta koma ta zauna a saman bed kana ta masa alama da hannunta naya ƙariso.

A je Teddy ɗin ya yi a gefe sannan ya ƙarisa wurin ta.

Kallon sa tayi kana ta fara magana cikin É—aure fuska

"Buddy Mine, faÉ—a min tsakanin ni da Daddyn ku waye kafi so?."

Da sauri Yaron ya kalleta jin abin da ta ce Duk da cewa shiÉ—in Yaro ne, amma ya fahimci wani abu daga cikin maganar ta, dariya ya yi sannan yace

"Momy ke can ai nafi con Daddyn a kanki." 🤪

ÆŠiif wutar Rafi'at ya É—auke na wani lokaci kana da kyar ta iya furta

"Saboda me kafi son Daddyn ku a kaina?."

Har Yanzu Yaron dariya yake sannan cikin qwaranci yace

"Caboda cima Daddy yana cona kuma baya min faÉ—a idan nayi wani kuch kuye cai dai ya min nasiha kuma ya bani chakuleti da yawa kuma yana kula dani cocai cocai."

Shiru Rafi'at tayi tana kallon Yaron a kullum kaifin basirar sa ƙara nin kuwa yake Yaron brain ɗin sa tana ja sosai.

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa sannan ta ce
"Saboda haka ne kawai kafi son Daddyn ku a kaina ko?."

Girgiza ma ta kai ya yi alamar "Eh," murmushin mugunta tayi kana tana faÉ—in

"Yanzu idan ni ma na dena maka faÉ—a, sai dai nasiha kuma ina kula da kai sosai, ina baka chakuleti cikin basket da komai da komai zaka soni fi ye da Daddyn ku, kuma zaka dinga jin magana ta?."

Abun ka da ƙaramin Yaro yaji maganar chakuleti cikin basket, Aikuwa da sauri ya shiga girgiza ma ta kai alamar "Eh, ya amince.
Murmushi tayi nan dai ta ci gaba da janshi da fira, tuni ta manta da wata Yunwa.

**
Wuraren ƙarfe Takwas na Daren Ranar Rafi'at tana zaune a palon dake ɓangaren ta Yaranta zagaye da ita suna ma ta qwaran cin su na Yara tana biye musu.

Abubakar Ya yi sallama yana shiga ciki, da kyar ta iya amsa masa sallamar dan ma kawai tasan matsayin ta ne a Addini shiyasa.

Ƙarisa shigowa ya yi sannan ya sama wuri ya zauna kusa da ita, aikuwa da ganin sa Yaran gaba ɗaya suka dawo wurin sa cike da farin cikin ganin sa, shima dai nan ya shiga nuna musu Kalar ƙaunar da yake musu.

Sai faman satar kallon sa Rafi'at take yi ta ƙasan ido. Ƴan kwanakin da tayi bata gansa ba, sai taga kamar anƙara masa wani kyau na musamman fi ye da Wanda ta sansa dashi a baya.

Ajiyar zuciya ta sauke tana danne kishinta a kansa tuno wai a halin Yanzu ba ita kaɗai bace matar sa akwai wata a gefe.🤨

"Matar Mai Kyau ina ga da kin dena satar kallona, domin ni ɗin gaba ɗaya naki ne, gwara ki fito fili ki kalleni san ranki, dan bamai hanaki kinji tawan."😅

Duk wannan maganar Abubakar Mai Kyau ne yake antayo ma Rafi'at a lokacin da ya juyo da kallon sa a kanta.

Ɗan murmushi tayi ko banza taji daɗin abin da ya faɗa wato hakan na nufin ke nan mijinta har yanzu yana ƙaunar ta duk da bai taɓa fitowa fili ya faɗa ma ta ba, ta fahimci Abubakar shiɗin na musamman ne a cikin mutane, domin kuwa baya bayyana abu da baki sai dai ya yi shi a aikace.

"Kodai matar Mai Kyau tana azumin magana da mijin nata ne. Yana ta magana babu amsa."

Abubakar ya kuma faÉ—a cike da Zoyala, murmushi tayi kana ta ce

"A'a kawai dai matar Mai Kyau tayi kewar My Lawful É—in ta ne obaaa."

"To gashi ya dawo sai matar mai kyau ta kwantar da hankalin ta domin kuwa Lawful ba inda zai ƙara tafiya Yabar matar mai kyau ita kaɗai."

Wannan karon murmushin da ya bayyana fararen haƙoranta tayi, wato dai su maza a kullum sun san takan mace ko. 😡

Ganin Yaran gaba ɗaya sunyi bacci ne, yasa ta miƙe ta ɗauka Nainarh tana faɗin

"Please My lawful taimaka min da Buddy ya cika nauyi wasu lokutan."

Tayi maganar a lokacin da take ƙoƙarin ɗaukar Nailah ita ma, da sauri Abubakar ya miƙe tsaye kana ya karɓa Nailah daga hannunta Yana faɗin

"Kudai mata akwai ku da kasa da. Yanzu idan kika yar da ita Nainarh wajen É—aukar Nailah fa, wato saboda qwiuya zaki haÉ—asu duka, salon ki yarda É—aya ko?."

Ya yi maganar ne shima Yana saɓa Nailah a kafaɗa sannan kuma ya ɗauki Abdulmaleek ya haɗa su ya nufa bedroom dasu.🤭.

Baki sake ta bisa da kallo tana murmushi, wato ya ma ta faɗa akan ɗaukar Yara biyu a haɗe, shikuma ya ɗauka ko?.🤓

Girgiza Kai tayi cike da nishaɗi kana tabi bayan sa ita ma kafaɗarta saɓe da Nainarh.

Shimfiɗe Yaran su kayi, Abdulmaleek bed nasa daban, haka su Nainarh da Nailah da suke ƙanana aka haɗasu a bed ɗaya da yake gadon Babba ne.

Lulluɓa musu blanket tayi gaba ɗaya kana ta rage gudun Air condition sannan ta juya zata bar bedroom ɗin, harta kai ƙofa taji yo muryar sa yana kiran sunanta.

ÆŠan dakata wa tayi amma kuma bata juyo ba.

Murmushi ya yi daga inda yake tsaye kana Yace

"Please matar mai kyau, ki a je komai a gefe kizo ɓangarena akwai maganar da nakeso na muku da Ƴar uwar zaman ki H..."
Ya yi maganar ne domin a tunanin sa zuwa yanzu Rafi'at tasan wacece Abokiyar zaman da ya ƙara ma ta. 🤭🏃

Bata Jira ya kuma cewa komai ba, ta fice daga bedroom É—in, kai tsaye bedroom nata ta wuce, zuciyarta tunani fall, wato dai farkon sunanta 'H', ne tunda taji ya faÉ—a hakan, da shigar ta É—akin kasa zaune tayi bare tsaye, sai faman safa da marwa take yi, ta rasa mai zatayi tunani take akan taje ko kuwa karta je komai zai faru ya daÉ—e bai faru ba.

Ajiyar zuciya ta sauke abin da zuciyarta ta raya ma ta, shi zata aikata saboda haka ta yanke shawarar zuwa tayi.

Da sauri ta ƙarisa jikin Dressing mirror tana kallon kanta, murmushi tayi kana a fili ta ce

"Dan Allah dube ni Like a SARAUNIYAR KYAU, amma Abubakar ya rasa mai zai min sai kishi..."

Kasa ƙarisawa tayi saboda girman kalmar a wurin ta.

Mayafi ta É—auka milk color shigen Arabian gown dake a jikinta, kana tayi rolling kanta dashi, sannan ta fito daga bedroom É—in, kai tsaye part É—in sa ta nufa zuciyarta na har bawa na Rashin dalili.

A hankali takai hannunta na dama ta tura ƙofar sannan ta shiga ciki bakinta ɗauke da sallama, sai dai kuma ba kowa a palon, dan haka ƙarisa shiga ciki tayi, sannan ta sama wuri ta zauna a saman 3sieter ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana karkaɗawa tana jiran ƙarisowar Ango da Amaryar sa.

Ta ɗan daɗe zaune a haka, sai kuma can taji alamar shigowar mutane wurin, bugun zuciyarta ne ya ƙaru a lokacin da suke ƙara matsowa wurin da take, da yake ta basu baya shiya sa har suka ƙariso wurin suka zauna fuskar Amaryar kamar yadda ta saba ganin ta lulluɓe da mayafi.

Taɓe baki tayi ƙasa ƙasa yadda ita kaɗai zataji ta ce
"Wannan kodai munafuka ce ita sai haka, idan ba tsaban munafunci ba, ta Aure min miji shi ne hadda wani rufe fuska?."

Taja tsaki ƙasa ƙasa ta gyara zamanta tana binsu da kallo.

Buɗe Taron Abubakar ya yi da addu'a sannan ya fara musu nasiha a kan zaman lafiya da sauran su, yana ta yi dai kuma har zuwa lokacin Amarya bata buɗe fuskar ta ba, a domin uwar gida ta gani.😏
Chapter 69 · 0% Book details