Sashe 18
Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 7 min read
Æangaren Afeefah kuwa tana fita daga É—akin da ta sauke Dije kai tsaye bedroom É—inta ta koma, system É—inta ta É—auka tana karatun exam dayake sun fara ne.
Tana zaune saiga Lailah ta shigo ita ma hannunta riƙe da littafai irinna su na likitoci, zama tayi tana faɗin "a gaskiya na gaji wannan karatun, wallahi karatun likita ba sauƙi saina Allah....kai ina, ni da ma a soke karatu kwata kwata adena a duniya."
kallon Afeefah tayi dake faman aiki da system da alama ma batasan ta shigo ɗakin ba. "Hey miss feefah, duk karatun ne haka ba'asan ma lokacin da na shigo ba." Lailah tayi maganar tana tafa hannunta a fuskar Afeefah ɗin, ɗagowa Afeefah tayi tana kallon Lailah fuskar ta ɗauke da murmushi ta ce "yane likita karatun exam ɗinne, yayi zafi ko?," Aiyar zuciya Lailah ta sauke ta ce "ana fama wallahi, ni fa ko, wani lokacin sai naji kamar nabar wannan karatun likatancin fah." Waro ido waje Afeefah tayi tana ɗan murmushi ta ce "lah lah Lailah aikuwa wannan maganar sai a kunnen daddy, ko dai duk karatun exam ɗinne ya kawo hakan kike saɓa lamba haka."
"Hummm kedai ba zaki gane bane kawai Miss feefah sai dai kawai abar zancen anan," cewar Lailah, "haba zan gane mana idan kika ganar dani Afeefah ita ma ta bawa Lailah amsa tana dariya.ɗaukar littafin karatunta Lailah tayi ba tare da ta ce ma Afeefah ɗin ci kanki ba😂.
**
Sai wajen sha ɗaya na dare, sannan suka kammala karatun nasu wai nanma Lailah ce ta dage bacci takeji shiyasa suka haƙura.
**
Kiran sallah ne da sanyin asuba dake kaɗo curtains ɗin ɗakinne ya tashi Dije daga bacci tashi tayi tana miƙa alamar dai baccin bai isheta ba. Kai tsaye bathroom ta shiga ta ɗauro alwala ta fito ta tada kabbarar sallar asuba bayan ta shimfiɗa sallayar ta da ta zo dashi daga ƙauye.
Tana cikin raka'ar ƙarshe ne aka turo ƙofar ɗakin aka shigo Afeefah ne jikin ta sanye da hijjab fari tas har ƙasa na sallah zama tayi saman bed tana jiran Dije ta idar da sallah.
Juyowa Dije tayi bayan ta idar tana kallon Afeefah ta ce "lah Balarabiyar india kece ashe ina kwana," murmushi Afeefah tayi ta ce "lafiya ƙlau Deejarh ya kike ya baƙunta kuma fatan kina cikin ƙoshin lafiya.
Washe baki Dije tayi ta ce "ae Balarabiyar india ina faɗamiki babu baƙunta don tuni yabi gado, amma wai Balarabiyar india na tambaye ki mana idan babu damuwa?," cewar Dije.
Afeefah ta ce "ina jinki Allah yasa na sani," washe baki Dije ta kuma yi cike da farin ciki wannan kyakyawar Balarabiyar india tana mata magana ta ce, " ah dama Balarabiyar india wannan ɗakin hala na ƙanwar kice?." Dariya Afeefah tayi ta ce "a'a ko ɗaya bana ƙanwa ta bane, amma me kika gani ne?," Dije ta ce "ae naga akwai komai da komai ne, a ciki hadda man wanke gashi fah na gani kala kala a can wajen ta nuna bathroom.
"Okay ae ɗakin baƙi ne idan suka zo sai suke zama anan, kamar dai ace ƴan mata kamar ki, aikin ga ɗakin irinna ƴan mata ne waɗanda basu wuce 15years ba ko," Dije ta ce "E, mana gashi ɗakin mai kyau kuwa, Balarabiyar india wai Menene ma sunan ki na gaskiya sunan akwai daɗi amma kuma sai wahalar faɗa ko miye ma "AFEEF" ne ko "AFFAF" ta tambaya tana kallon Afeefah ɗin.
Yauwa na tuna Afeefah hakane ko?," 'E,' Afeefah ta bata amsa sannan ta ce "follow me muje kitchen Auntie sa'adah na kiran ki zamu haÉ—a breakfast okay," tashi Dije tayi tabi bayan Afeefah bayan ta cire hijjab É—in jikinta ta É—aura É—an kwalin rigar dake a jikinta.
Dije sai faman kallon kitchen ɗin takeyi tana kallon kyau da tsaruwa, muryar gwaggon ta taji suna gaisawa da Afeefah da sauri ta kalla gurin da gwaggon nata take ta ce "lah gwaggona kece wai, to ina kwana ni yasin na manta dake mah," gwaggo ta ce "toh dama tayaya zaki tuna dani kina can kin sama a.c kina kwasar bacci harda minshari.......washe baki Dije tayi tun kafin gwaggonnta ta ƙarisa maganar da takeyi Dijen ta rigata da faɗin, "Yasin kuwa gwaggo bakiji ba kamar karna fito daga ɗakin domin wani irin madarar daɗin bacci ɗakin yake dashi.
Dariya Afeefah tayi ta ce "to malama deejarh mai ɗaki, ga wannan juyo in ɗaura miki, kallon abinda Afeefah take miƙo mata Dije tayi ta ce "laha'ila wannan kuma Menene wai ku nan birni idan za'ayi girki sai an saga wannan abunne?."
Afeefah ta ce "E, mana ta yadda bazai ɓata kayan ki ba" Dije ta kuma washe baki ta ce "to Balarabiyar india! au Adda Afeefah miye sunan wannan ɗin shi kuma muji idan akwai daɗi.
Saida Afeefah ta gama É—aura mata sannan ta ce "cikin murmushi sunan shi apron.
Dije ta ce "aikuwa daga yau na riƙe sunan shi don fita kunya, apron ko kika ce ae,"
Gyaɗa mata kai Afeefah tayi Sannan ta bata kayan vegetables ta ce "ina fatan dai kin iya yankawa ƙanana ƙanwata?," Dije ta ce "E, mana Balarabiyar india sosai ma, na iya a ƙauye.
"Okay to yanka mu gani tunda kince kin iya," É—auka Dije Tayi ta fara yankawa iya qwarewarta, Afeefah tana lura da'ita tana mamakin yadda yarinyar ta iya aikin highly, don ita da farko ma tayi tunanin yarinyar ba za ta iya aikin komai ba, sai kuma gashi yanzu yarinyar ta bata mamaki.
Kallon Auntie sa'adah Afeefah tayi Sannan ta ce "Auntie jiya naji kamar kince zaki faÉ—amin wani abu koh, É—an juyowa Auntie sa'adah tayi tana kallon Dije sannan ta nuna ma Afeefah, Dije É—in ta ce.
"Ita wannan sunan ta khadijatu kuma ɗiyar YaYa na da muke uwa ɗaya uba ɗaya dashi ne, mahaifiyarta ta rasu tun tana da shekaru biyu a Duniya, a lokacin naso YaYa na wato mahaifin ta ya bani ita na ci gaba da rainonta tunda kamar yadda aka sani ne ban taɓa haihuwa ba amma Allah bai nufa ba.
A hannun kishiyar uwanta ta taso, matar ba ƙaramin wahalar da'ita tayi ba, don da kyarma aka samu ta bari aka sakata makaranta na arabic da na boko, to haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Dije tana hannun kishiyar mahaifiyarta har ta kawo wannan lokacin sati ɗaya baya, daya wuce ne wai su isu isu ƴan matan ƙauyen wai suka haɗa gasa wai suna gasar SARAUNIYAR KYAU ? sannan tsarin gasar shine, duk wacca tafi kyau to zasu haɗa kuɗin da ƴan kallon gasar suka haɗa, su ba wacca tayi nasara, to ana haka shine fah, ita ma Dijen ƴar ƙaniya da ita, ta shiga kuma taci shine da aka bata kuɗinta a matsayin wacca taci nasarar, ita kuma ba ta ba Ladidi ba, ta yi harkar gabanta dasu, Ladidi wato matar babanta da take riƙonta, shine ita kuma Ladidi taji haushin hakan wanda dalilin kenan da yasa ta kamata ta ɗaure a ɗaki ta mata dukan mutuwa kuma taƙi ta kwanceta abinci ma taƙi bata saida YaYa na wato mahaifinta ya dawo gidan yaga halin da take ciki, a lokacin ranshi ba ƙaramin ɓaci yayi ba, nan dai ya kwanceta ya kawota gurina shine ni kuma na yanke shawarar na kawota nan aikatau saboda na kusa Aure nanda sati ɗaya ne InshaAllah shiyasa jiya kika ganmu da dare, Auntie sa'adah ta ƙarishe maganar tana sauke ajiyar zuciya, duk da cewa yankan kaɗan daga cikin tarihin rayuwar Dije tayi ta ba Afeefah a taƙaice kuma a gajarce don ba duka bane, hasali ma iya labarin da ta ba Afeefah kaɗanne ko na ce kamar talla ne daga cikin labarin rayuwar Dije.
Ita ma Afeefah ajiyar zuciyar ta sauke tana bin Dije da kallon tausayi sannan ta mayar hankalinta kan Auntie sa'adah ta ce "to amma dai hukuma ta hukunta matar ko, dubi yadda duk jikin ta yake a farfashe fa. Tayi maganar tana kuma kallon yadda wasu gurare ajikin Dije suke duk wounds ne.
Hucin takaici Auntie sa'adah ta sauke tana faÉ—in, "wani hukunci ae ba abinda aka mata hasali ma, shi YaYan nawa da kanshi, ya kasa ko mata kallon banza balle azo maganar hukunci.
Da tsananin mamaki a wannan taƙin Afeefah take kallon Auntie sa'adah ta ce "kamar yaya bayyi mata komai ba kenan kinaso kice min babu abinda aka mata, aka barta ta ci gaba da rayuwa a haka. "E' haka nake nufi" cewar Auntie sa'adah.