← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 96

Sashe 89

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Please Ummi yayyanka wa'innan bazan iya ba, sun cika yaji da Yawa."

Karɓa Ummi tayi tana faɗin

"Aikuwa da ganin wannan onions ɗin Yaji zasu yi fah, ae wallahi kina ma ƙoƙari highly."

Murmushi kawai Afeefah tayi wanda ya zaman ma ta jiki koda, yaushe beauty face nata ɗauke take da ƙayataccen murmushi.

Sai dai ba tace komai ba, ita da tabata Albasa saboda karta isheta da surutu, domin kuwa tasan Ummi akwai surutu, sai dai kuma tana Bala'in burgeta ta wasu ɓangarorin domin Ummi nutsatsiyar budurwa ce, akwai ta da hankali sannan kuma bata irin wannan gossip da zaka samu da yawa daga cikin House maid Suke yi ba, ita dai barta da shegen surutu faɗi ba'a tambayeki ba ke nan.😸

Cikin ƙanƙanin lokaci ƙamshin haɗaɗɗun girke girken da suka kammala.
Ya gauraye Gidan gaba ɗaya ciki da waje sannan ya tashi gaba d`aya mutanen Gidan waɗanda basu tashi ba.🥰

Jere gaba ɗaya girke girken suka yi saman dinning tables waɗanda aka ƙara Yawansu saboda baƙin.

Tsayawa tayi tana ƙarewa gaba ɗaya girke girken da suke, jere saman dinning room ɗin kallo, sai faman steaming suke yi ga ƙamshi na musamman da yake tashi mai tayar da yunwa ko ba shiri.🥳

A hankali cike da enjoying Mood da Take ciki. Take kallon duka abincin breakfast É—in gaba É—aya babu abin da babu, komai akwai tun daga kan.

•Meat Balls and potato sauce 😇_____
•Peppered soup with chicken_
•Rolled stuffed moi-moi. 😋__________
•Healthy spinach mix.
•Shredded chicken. 🍲____
•Savoury stuffed Yam balls.
•Fish Ball_&_Gas Meat_&_Special advice.
•Fried Yam with egg special 💢_
•Vegetable Fried Liver_&_Sphagetti salad __
•Mango fruit and pineapple juice 🧃🥤______
•Banana pancakes and potato crush 🥰_________
•Banana and strawberry Juice nd Yoghurt____
•Special gift Tea Wanda sai faman steam Yake ☕.

Da saura ma da ya wa waɗanda wasu ita kanta batasan sunayensu ba, sai dai su Elina da Ummi waɗanda suka ƙirƙiro wannan uban abubuwa Haka.

Kallon Elina da Ummi Tayi cikin murmushi ta ce
"Wannan uban girke girke da ababen shayashaye Haka aiko mutune talatin sunyi kaÉ—an su cinye fa."

Murmushi Ummi Tayi sannan ta ma ta nuni da Deejarh da take faman zaɓan abinci wanda ranta yake so tana sakawa cikin plates da suke saman wani special tray.

Dariya Afeefah tayi tana faÉ—in
"Ke, Deejarth lafiyar ki kuwa?, duk wannan uban abinci ina zaki kai su?."

ÆŠagowa Deejarh tayi tana kallon Afeefah cikin washe fuska ta ce

"Duka ina son su ne, shiyasa zan kwashi rabona naje bedroom ɗina taci, saboda nan akwai baƙi."

Tayi maganar tana ɗaukar tray ɗin da ta cika sa dam shaƙare da abincicika kala kala.

"Amma dai daga nan sai hospital za'ayi dake ko?."

Elina ta tambaya tana kallon ta, Æ´ar dariya Deejarh tayi sannan ta ce
"A'a tas zan cinye kuma na zauna qalau sai ma lafiya da zan ƙara sosai sosai.🥰

Dariyar wautar Deejarh kawai Afeefah take yi girgiza kai, kawai tayi sannan Ta ce

"Gaskiya Yaro Yaro ne, amma banda Abin Deejarh wannan uban abinci kamar wata mai juna huÉ—u haka, tohm Allah ya kyauta."

Tayi maganar a Yayin da ita ma ta ɗauki tray shaƙare da abincicika kala kala da ababen shayashaye ta nufa staircases Wanda Kai tsaye zai sadata da nangaren Maleek.

Zata fara taka steps na farko ke nan, ta hango fitowar Mah'fuz da Yasir suna saukowa suma daga ɓangaren Maleek ɗin, da yake su acan suka sauko, ko dama can Haka Abin Yake, a ɓangaren Maleek suke sauko indai aka zo Taro ko Wani Abu Cikin Gidan, da yake duka suda Maleek ɗin duk sa'annin junane watanni ne tsakanin su domin kuwa bae kae shekaru ba.

Washe baki Afeefah tayi tana faÉ—in "YaYa mah'fuz and YaYa Yasir, Good morning to you All, Fatan kun Tashi lafiya a cikin Gidan mu?."

Murmushi suka yi a tare sannan kuma a dai dai lokacin da suka ƙariso wurin da take rsaye riƙe da tray.

A Tare suka kuma faÉ—in
"Feefah Mai Kyau toya Garin SARAUNIYAR KYAU ta madinatul Abuja muna miƙo gaisuwa fah."

Har Lokacin fuskar Afeefah a washe take da ƙayataccen murmushi Ta ce

"Oh YaYa Yasir and YaYa Mah'fuz har Yanzu dai kuna nan da wannan Abu naku Tamkar wasu twin's, hmmm ae koda Yake idan mutum bae sani ba zai iya kiran ku da twin's É—in, domin kuwa komai naku É—aya ne, hatta magana idan zaku yi a tare ne."

"Ae dama twin's É—in ne tun tuni sai dai kuma Hassan Yana Kano ne shi kuma Hussein Yana a Borno State."

cewar Yasir a taƙaice sannan kuma cikin murmushi.

"Okay.. 👌

Toh mai zai Hana ɗaya daga ciki ya koma State ɗin da ɗaya Yake ba, ae kunga daga nan kuma ba Mai ƙara tantama akan cewar kuɗin ba twin's bane."

Cewar Afeefah a lokacin da tayi gaba ta fara taka steps na staircases É—in.

Murmushi kawai suka yi a tare sannan suka nufi Dining domin bawa ciki haƙƙinsa.😋

Hango mutum tafe ne tasa Ummi tayi, off na Wayar dake hannunta sannan ta mayar cikin apron pocket dake jikinta.

Kallon su tayi Bayan sun zazzauna sannan cikin muryarta ta ce "Good morning everyone's please which kind of food did you needed for?."

Kallon juna suka yi a tare sannan kuma suka mayar da kallon su a kanta kana Yasir ya faɗa kalar wanda yake so yaci da sha, sannan tayi saving nashi bayan ta kammala ta ƙara kallon Mah'fuz sannan ta ce

"Yallaɓai uhum?."

Kallon ta mah'fuz Ya yi shima sannan Yace
"Menene kuma uhum?. Menene kalmar uhm take Nufi?."

Gyara tsayuwarta tayi ta ce
"Ina nufin wani kalar Abinci kakeso daga cikin nan domin nayi saving naka?."

Lumshe kyawawan idanun sa Ya yi sannan yana faÉ—in
"Okay, wato dai yanzu wannan kalma ɗayan ce duk take nufin duk wannan bayanan da kika jeromin ko shikenan, amma fah Hakan Ya yi.👌

Murmushi tayi sannan ta ce "Yeah yanzu dai Yallaɓai zaɓa abin da kakeso domin na saka maka."

Shima murmushin ya saki kana Yace

"£verything, All."

Zaro ido Ummi tayi waje, As Austere ta ce
"Menene amma dai wasa kake yi dai ko?."

"A'a da gaske nake duka gaba É—aya zakiyi saving nawa, domin kuwa duka nakejin ci."

Ummi ta ce
"A'a please Boss ka taimaka ka zaɓa wasu daga ciki domin kuwa bazaka iya cinye wa duka ba."

"Ah gwada mana a gani, ae sai an gwada akan san na qwarai ko?."

Shima mah'fuz ya faÉ—a, ae nan fa suka shiga compromise tsakanin su. Ita Ummi cewa take ya daure ya faÉ—a kalar nau'in abinci da yake so, domin tayi saving nashi.
Yayin da shi kuma mah'fuz ya dage kai da fata sai tayi saving nashi duka abincin wurin.🤣

Yasir da gaba É—aya surutun nasu ya hanashi sukuni, da yake shiÉ—in ba, person ne mai son hayaniya highly ba ne.

Dakata wa Ya yi da kai loma Bakin sa sannan ya kalla Ummi Yana cewa

"Please Miss saka masa duka abin da kikaga dama, wannan bashi da ragadi ki dena Biye masa domin kuwa sai ku kwana anan kuna compromise tsakanin ku."

Murmushi Ummi tayi sannan ta ce "Nagode Yallaɓai domin kuwa duk surutuna naga alama so yake ya ƙure ni fa."

Tayi maganar tana ƙoƙarin saving na Mah'fuz ɗin.

"Kar ki sake kiyi saving nawa muddun ba, duka abincin bane kinji ko?."

Da sauri gaba ɗaya daga Ummi har Yasir da kuma Lailah wacca take shirin ƙari sawa Dining ɗin, taji maganar sa na ƙarshe a sama. Duk suka juya suna kallon sa.

Cike da tsananin mamaki Yasir ya tambaya.

"Saboda me ke nan?."

Kai tsaye mah'fuz ya basa amsa da cewa

"Saboda Haka nakeso kuma na zaɓa. Idan kuma ba Haka ba sai dai mu kwana anan."

Kallon Ummi wacca tayi raurau da ido tamkar zata fashe da kuka Yasir Ya yi sannan Yace

"Kinji Miss ki Rabu dashi, wannan ya zare fa da alama."

Cike da takaicin su duka Ummi ta kalla Yasir sannan ta ce dashi

"Sunana Ummu Sulaym, amma anfi kirana da Ummi, bawai Miss nake ba ehe. Menene Wani Miss sai kace kana kiran mage?."

Murmushi Lailah tayi a lokacin da ta zauna ta fahimci hau shin da mah'fuz ya cusa ma ta take zubarwa kan Yasir.

"Wata ƙila Ita ma Ummyn Yaya mah'fuz ɗin Ya yi ma ta kwarjinin da yake yi ma sauran girlfriend's ne, shiya sa ta kasa masa masifa ta ƙare akan Yasir."

Haka kawai Lailah take ayyana wa cikin zuciyarta tana dariyar wannan drama da Yaya mah'fuz ya tattara.
Ta fahimci komai sai dai zatayi shiru da bakinta domin ci gaba da ganin wannan sweet drama.

Sallama ɗauke saman laɓɓanta ta ƙarisa shiga cikin Katafaren Palon wanda Yasha kayan Mo re Rayuwar duniya daular duniya ke nan.

Can saman Royal sofa ta sangosa zaune ga System gabansa yana sarrafawa, yana sanye cikin t-shirt black color and trouser short black color.

Qari sawa tayi sannan ta É—aura tray dake hanunta saman glass center table dake palon.
Sannan ta zauna a saman royal sofa 1sieter tana kallon Yayan nata cike da farin ciki. Yanzu dai daga ƙarshen ƙarshe ga YaYa Maleek nata ya dawo Gida.
zata ci gaba da kawo masa abinci kullum kamar dai baya.

Murmushi tayi sannan ta ce
"Yaya Maleek Good morning, Fatan dai kana Lafiya?." Tayi maganar cikin washe fuska.

A hankali ya É—ago da sexy eyes nasa yana kallonta kamar sakanni biyu sannan ya amsa da faÉ—in

"Bana Lafiya. Sai Yanzu kikaga damar zuwa ganina ko?, gaba É—aya jiya inata saka ran shigowar ki, amma ba ki zo ganin Yaya Maleek naki ba, kowa Yazo banda ke hatta Nainarh da take fushi dani tazo munsha fira."

Kama Baki Afeefah tayi cikin dariya ta riƙe ear nata duka biyun sannan ta ce
"Please Yaya Maleek nawa afuwan wai dama fa, na bari ka huta ne zuwa ya fah."

Qayataccen murmushi Maleek ya saki sannan ya amsa ma ta da
"Afeefah ta ni ma da wasa nake yi, sauri ki saki kunen ki saboda kar suyi ciwo kinji ta gidana?."

Murmushi ita ma tayi tana faÉ—in

"Godiya nake Yayana."

Miƙewa tayi sannan ta ƙarisa wurin center table ta fara saving nasa, suna taɓa fira tsakanin su biyun.

Konawa tayi ta zauna bayan ta kammala saving nasa ta ce
Chapter 89 · 0% Book details