← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 96

Sashe 58

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin sauri ta miƙe ta ƙarisa wajen window, sannan ta ya ye labulayen sannan ta buɗe gilashin, tana leƙen farfajiyar gidan.

Hango shi tayi sanye cikin suit Ash and White color wa'danda ba ƙaramin Kyau, suka masa ba.

Karɓar Briefcase ɗin sa ya yi a wajen P-A. Ɗin sa sannan cikin sauri sauri ya shige ciki a dalilin Ruwan sama da ya tsinke kamar da bakin qwarya.

Da sauri ta saki labulen sannan ta mayar da gilashin ta rufe, kana ta dawo gaban madubi tana kallon kanta.

Murmushi tayi sannan ta cire hijjabin jikinta ta a je saman bed saboda ta fita ta tarbe shi.

Tana fita shi kuma a daidai lokacin yasa hannunsa ya buɗe ƙofar Bedroom ɗinsa da key, sannan ya shiga kana ya dawo da ita ya rufe.

Rafi'at tana masa magana amma ko kulata bayyiba, kuma tanada tabbacin ya ganta, tunani ta shiga yi shin taje ta masa knocking ne kuwa?.

Ko kuma ta kira shi a waya ya buɗe ma ta ƙofar?.

Ƙaramin tsaki taja sannan a fili ta ce "Idan ma na kirasa a waya, ko kuma naje na masa knock GIRMA YA FAƊI ke nan sha re shi tayi ita ma, ta wuce bedroom ɗin ta tabi lafiyar gado.

*WASHE GARI*

Amarya Rafi'at bata tashi da wuri ba, sai wuraren ƙarfe bakwai da rabi na safe.

Wanka tayi sannan tayi sallah a gaggauce ko kwalliya batayi tunanin yi ba, da saurin ta ta shirya cikin doguwar rigar atamfa, ta saka hula mai shigen kayan jikinta kana ta fito ƙasa ta sauka palo.

Kai tsaye kitchen ta wuce cikin sauri sauri ta kammala haÉ—a breakfast sannan ta jere a Dining Room kana ta koma Bedroom É—in ta ta kuma yin wanka.
Bayan ta fito ta tsaya ta tsara kwalliya sannan ta shirya cikin shadda milk color mai adon stones coffee color kana ta É—an É—a sa É—aurin ture kaga tsiya.

Tana fitowa daga Bedroom ɗin ta kai tsaye Bedroom ɗin mijinta Abubakar Mai Kyau, ta wuce ta kwankwasa ƙofar Bedroom ɗin dake garƙe.

Ta É—an daÉ—e tana knocking sannan ta ciki taji ance ta shigo.

A hankali tasa hannunta wanda yasha jan lalle, ta tura ƙofar Bedroom ɗin a buɗe ta jita.

Kutsa kai ciki tayi tana mai masa sallama, sai da ta jira ya amsa sannan ta ƙarishe shiga ciki.

Tsaye ta hango shi can gaban madubi yana gyara zaman neck-tie É—in Blue black suit dake jikinsa.

Da sauri ta ƙarisa wurin sa sannan ta karɓa tie ɗin, tana saka masa, sai da ta kammala gyara masa.

Ɗagowa tayi zata masa magana karaf suka haɗa ido, cike da kunya ta ce "Am so sorry Mister Mai Kyau dama kawai saboda naga ka kasa sakawa ne shiyasa, amma ina mai bada haƙuri."

Tayi maganar tana É—an É—agowa domin ganin Reacted É—in sa.

Ga mamakin ta murmushi ya ma ta sannan cikin kamilalliyar Muryar sa yace da ita

''Thank You."

Ɗan murmushin samun nasara tayi, can ƙasan zuciyarta kuwa ta yanke zata biyo masa duk ta yadda ya buƙata, don taga alamar, yanasan mace mai kunya.

A fili kuwa kallon shi ta ɗanyi sannan cikin ƙasa ƙasa da murya ta ce

"Good morning Mister Mai Kyau, da fatan ka tashi lafiya. Dama nazo ne na faÉ—a maka breakfast ya kammala, please idan babu damuwa zamu iya Karin kumallo tare?."

Ga tsananin maÉ—aukakin mamakinta gani tayi ya yi gaba yana faÉ—in.

"It's okay babu damuwa."

Ya yi maganar ne a yayin da ya nufa ƙofar bedroom zai buɗe.

Da sauri tabi bayan sa tana kuma murmushin samun nasara.

"Ashe dai wannan Bawan Allah ba shi da wani girman kai, kamar yadda nayi zato. Ashe dai HE IS VERY NORMALCY PERSON.."

gaba ɗaya wannan zancen a can cikin Ranta takeyi 🤓.

A tare suka sauko Downstairs suka ƙarisa Dining table.

Yanzu ma cikin sauri ta ƙarisa tayi saving ɗin sa, duk irin Abin da yake buƙata.
Sannan ita ma ta zauna suka yi karin kumallon a tare.

Bayan sun kammala ta riƙe masa Briefcase ta raka shi har Bakin motarsa dama kuma akwai scarf akanta.

Sallama suka yi sannan ya shiga mota driver yaja, ita kuma ta koma ciki, cike da farin ciki, saman bed É—in ta ta faÉ—a tana sakin ihu a fili ta ce

"Muje zuwa Malam Mai Kyau a tsakanin ni da kai a ga wanda zai sauke girma kai aha."

Haka ma da Rana ta tsara masa Lunch mai rai da motsi, ta zuba a food flask guda biyu sannan kuma ta haɗa lemun kayan marmari na musamman ta zuba a goruna duka ta jeresu a basket, ta haɗa da plate's da kuma cups ƙanana, sannan ta fito farfajiyar gidan ta sama driver ta bashi ya kaima Boss nashi office.

Da marece wuraren ƙarfe Bakwai da rabi ta kammala haɗa dinner, sannan gaba ɗaya ta jere a dining room, kana ta wuce bedroom nata.

Wanka ta fara yi sannan ta tsara kwalliya, kana ta shirya cikin shigar atamfa riga da skirt pencil wa'danda ba ƙaramin kyau shigar tayi ma ta ba.
Ta lura yafi son kalar shigar, to ita kuma ta ɗauki niyyar biyo masa duk ta inda ya buƙata.

https://chat.whatsapp.com/CVLsMqJthIoKIGGGaYlw8j

*💋SARAUNIYAR KYAU💋*
*Takun Farko*

______________________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

🎀🎀ϝιʋҽ ʂƚαɾ'ʂ ɯɾιƚҽɾ'ʂ🎀🎀

ᵀᴴᴱ συɾ σɾԃιɳαɾყ ᴼᴺᴳᴼᴵᴺᴳ ᴮᴼᴼᴷ'ˢ

1:ȥαɳ ʝιɾα ƙα
ɳα
A'isha Alƙali
/ɱɾʂ αყʂιႦ/

2:ιɳ Ⴆα ƙαι
ɳα
Fateemah .M. Kabeer
/συɱ αϝɾҽҽɳ/

3:ɾαʂԋιɳ ʂαɳι
ɳα
Fatahiyya Moh'd Yakasai
/συɱ ყαʂɱҽҽɳ/

4:ʂσɳƙι ɳҽ ƙαԃԃαɾα ƚα
ɳα
Fateemah Abdullahi
/Ⴆαƚσσʅ ƙαɱႦα/

5:ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ
ɳα
Khadeejarth Sabi'u Yahyah
/ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ/

Page *55&56*

Tana fitowa daga bedroom É—in ta kai tsaye bedroom na mijinta Abubakar Mai Kyau ta wuce batare da tayi knocking ba, dan a tunanin ta yanzu kuma shikenan sun haÉ—e.

Tasa hannu ta tura ƙofar a hankali, ta shiga, baya nan a palon bedroom ma hakan.

Can ciki ta wuce a hankali ta tura kanta ciki tana leƙen sa.

Zaune ta hangoshi saman wata doguwar sofa mai mazaunin mutum biyu dake manne da bed ya ba ƙofar yaba, domin kuwa yana kallon bed ne, ga waya manne a kunenshi.

Shiru tayi tana so ta fahimci hanyar da wayar da yake yi ta nufa, duk da cewa a nutse yake yi daɗi da ƙari kuma a hankali yake abin sa.
Amma wannan bai hanata jiyo abin da yake faÉ—a ba.

Abin ya gigita ta sosai, sannan yasa ka dukkanin jikin ta É—aukar rawa kamar mazari

Duk da yanayin tashin hankali da maganar da taji suna fitowa daga bakinsa suka je fata, hakan bai hanata gyara tsayuwar ta ba, tana kuma jin maganar da yake fitarwa waÉ—anda suke nema su saka zuciyarta ta tarwatse, ba tare da ta shirya ba.

"Haba dai, ya zaki dinga faÉ—ar hakan bayan kin san cewa baku haÉ—a iyaye da ita ba, kodai bakya sona ne?."

ÆŠan shiru ya yi domin ya sama damar jin abin da zata ce.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan cikin ƙara ƙasa da murya ya kira sunan ta

"Haleesat Rashid Rayyan..!'

Bai jira ta amsa ba ya ci gaba da cewa "Muddun kin yarda da ƙaunar da nake miki, kuma kema ɗin kina sona.! To kawai ki bari na turo magabata na nanda five months, nasan zuwa lokacin na gama duka wasu shirya shiryen da suka kamata sannan idan ma bakya so ku zauna a gida ɗaya da 'Rafi'at, wannan ba damuwa bane zan iya a je ki a ɗayan gidana."

Shiru ya kuma yi sannan ya ciro wayar daga kunen shi yana dubawa.
"Ta kashe wayar da gaske fa. Katse min kira tayi fa."

Ya faɗa a fili kuma yana sauke hucin ɓacin rai.

Ganin yana shirin juyowa ne yasa Rafi'at da tayi suman tsaye, tun a lokacin da taji ya kira sunan 'Haleesat Rashid Rayyan'.
Saurin rufe ƙofar tayi ta juya da sauri sauri tabar bedroom ɗin.

Tana fita daga bedroom ɗin a maimakon tayi hanyar bedroom ɗin ta, bin hanyar ɗan ƙaramin kitchen ɗin dake anan upstairs ɗin tayi, ta shiga ciki.
Zama tayi a d`aya daga cikin kujerun dining dake kitchen a maimakon taji hawaye sun zubo mata kamar yadda tayi tsammani.
Neman su tayi ta rasa ashe dai hawaye ma rahama ne a wasu lokutan, domin ita gashi yau tana neman su ruwa a jallo amma ta rasa.

A kalla takai mintuna goma a haka bata sani ba, ta riga da ta faÉ—a a duniyar tunanin yadda zata yiwa tufkar hanci.

Ajiyar zuciya ta sauke tana sakin murmushin nan dai nata mara tabbas.

Ganin zama a wurin babu abin da zai ƙara ma ta illa ciwon kai, yasa ta miƙe ta fito daga kitchen ɗin.

Bedroom na mijinta Abubakar mai kyau Abin ƙaunar ta a kullum ta kuma komawa sai dai wannan karon tsayawa tayi cak a bakin ƙofar sannan ta saka hannun daman ta tayi knocking, kusan sau uku sannan yazo ya buɗe ma ta, murmushi tayi sannan cikin tsananin girmamawa da ƙanƙan da kai ta ce.

''Good evening Mister, dama cewa zanyi ne Dinner ya kammala a Dining room…"

Shiru tayi bayanta faÉ—an haka tana jira taji abin da zai ce.

"It's okay je ki ina zuwa."

Ya bata amsa a yayin da yake komawa ciki.

Rafi'at ji tayi tamkar ya watsa ma ta ruwan zafi a duka jikin ta, amma sai ta daure ta shanye kamar yadda ta sha alwashi.

Murmushin takaici ta saki a fili cikin ƙasa da murya ta ce

"Zaka shigo hannu ne, duk ranar da ka sake ka shigo hannuna. Ni Rafi'atu Rafiq Rayyan. Na Rantse da Allah mai girma zaka É—anÉ—ani kuÉ—ar ka..."

Ta kumayin dariyar bosawa Like a zararriya, sannan tayi gaba Downstairs ta sauko ta ƙarisa Dining room ta ja kujera ta zauna, kana tayi saving kanta duk abin da zata buƙata shima tasa masa abin da ta fahimci yana so.

Komawa tayi ta zauna sannan ta É—auki fork tana caccakar pounded Yam dake gabanta tamkar ta sama Haleesat Rashid Rayyan take gani.

Ta ɗauki tsawon mintuna biyar a haka, sannan ta jiyo sassayan ƙamshin turaren sa yana hallartar duka ƙofofin hancinta.

Kana daga baya mamallakin wannan sassayan ƙamshi mai haskaka zuciya ya bayyana cikin kyakyawar shiga.
Chapter 58 · 0% Book details