← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 96

Sashe 46

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ƙarfi Humaira ta qwace hannunta daga cikin na Auntie, ta buɗe mota a fusace ta shiga ciki.
Ajiyar zuciya kawai Auntie take saukewa cike da tsaban tsoro, kamo hannunta Jiddarh tayi idanunta sun cicciko tab da qwalla ta ce "Dan Allah Auntie karki saka wannan abun a ranki, saboda ke mahaifiyarta ce kinsan dai ba halinta bane raini, bata cikin hayyacinta ne shiyasa.

Ɗan murmushi Auntie tayi sannan ta ce "Ba komai Jiddarh na sani gaskiyarta ne duka laifina ne, da banyi wannan maganar ba, da ranta bai ɓaci ba, har waɗannan mutanen su leƙo kuma a fusace."

Magana Auntie takeyi tana leƙen motar da Jumaira take ciki.

Hakan da tayi da kuma maganar da tayi duka ba ƙaramin dariya taso ta ba Jiddarh ba. Amma ta danne ta ce "Auntie wai ina su Sister Ni'ima ne suzo mutafi gida, lokaci yana ƙurewa fa, naji da wannan ɗaukar Video da hotunan da ake min."

Murmushi Auntie tayi ta ce "Su Ni'ima akwai gurin da zasu biya, ki shiga mota kawai mu tafi gida zamu haÉ—u dasu acan.

"To" Jiddarh ta ce sannan ta nufa motar da Humaira take ciki. Da sauri Auntie ta ce "A'a Jiddarh inaga kizo wannan motar da nake mu tafi tare naga kamar mutanen basu koma ba."

Qumshe dariya Jiddarh tayi tana rufe baki ta ce "A'a Auntie barni na shiga wannan kawai, ai sun sanni Abokai nane, babh abin da zasumin fa domin mun saba."

Tayi maganar tana buÉ—e motar zata shiga, Auntie ta ce

"Ni dai ba ruwa na, Jiddarh tunda kince wannan motar zaki shiga su waɗannan mutanen ba ruwan su da wata Abota ko ƴan uwan taka uban mutum zasuci da gayya." 😝

Dariya Jiddarh tayi sannan ta shige motar ta zauna gefan Humaira dake waya abin ta. Daga ɓangaren hannun hagu ta zauna sannan driver yaja suka fita daga gate ɗin gurin motocin nasu guda huɗu rass, sannan suka ɗauki hanyar gida ɗoɗar.

A hanya Jiddarh ta ɗan kalla Humaira sai kuma da sauri ta kauda kanta tana karanto duk addu'ar da tazo bakinta, ƙara kallon Humaira tayi a zuciyarta ta ce "Wata ƙila sun koma."

Ɗan taɓo kafaɗun Humaira tayi cike da tsoro, wani irin juyowa Humaira tayi gaba ɗayanta tana kallon Jiddarh da idanunta waɗanda suka canza kala izuwa dark maroon.

Wani irin fitsarin tsoro ne yazo ma Jiddarh amma ta maƙale shi tana zare ido, so take tayi ihu koda driver zaiji ya tsayar da Motar kota samu ta tsere, amma ta kasa daga ta buɗe baki sai taji kamar an mayar dashi da ƙarfi an rufe. Ba abin da takeyi sai zufa ƙoƙari take tayi hawaye koda zasuji tausayinta. amma mandaƙas idanunta suke ko ɗan qwalla babu.

Matsawa jikin murfin mota take yayinda Humaira take biyota kamar wata 😘.

Wata dabara ce ya faÉ—o ma ta da sauri ta lalubo wayarta, a cikin jakarta dake a hannunta, cikin rawar hannu ta lalubo lambar Humaira ta danna kira.

Kai tsaye kiran ya shigo wayar Humaira dake saman cinyarta sautin zazzaƙar muryar Ahmad Sulaiman yana karanto suratul Ma'ida ya karaɗe motar.

Firgigit Humaira ta dawo hayyacinta, wata wawiyar ajiyar zuciya Jiddarh ta sauke sannan tayi rejected kiran, kallon Humaira tayi tana murmushin yaƙe ta ce "Uhm sannu Humaira kin farka daga baccin kenan.?"

Ya mutsa fuska Humaira tayi tana faɗin "Wai ya akayi ma na ganni a mota ba'a tsaye muke ba munajiran ƙarisowar Ni'ima.?"

Da sauri cikin sarƙewar murya Jieddarh ta ce "E, e mana kwarai, ai a tsaye muke sai kikace muzo mu tafi gida bacci kikeji, wannan ne abin da ya faru fa."

Qura ma ta ido Humaira tayi tana kallonta sannan ta ce "Ya naga kina inda inda kodai ƙishi kikeji ne.?"

Da sauri Jiddarh ta fara tari kamar da gaske tana faÉ—in "Ruwa, a bani ruwa please, dai dai lokacin da driver ya shiga da motar gidan.

Fitowa tayi daga motar tana riƙe baki kamar mai jin ƙishin da gaske da sauri Auntie ta ƙariso gurin tana tambayar ba'asi.

Cike da damuwa Humaira ta ce "Wai ƙishi takeji shiyasa take tari fa."

Kallon Jiddarh Auntie tayi zatayi magana Jiddarh ta kashe ma ta ido É—aya, tuni Auntie ta ramfo abin da take nufi. Dan haka kallon Humaira tayi ta ce "mu shiga ciki ko."

Da gudu Jiddarh ta taye sama bayan sun shiga palon saboda sauri in twin's take taka staircases É—in hannunta na rawa tasa key ta buÉ—e Bedroom É—in ta.

Da ido Auntie da Humaira suka bita da kallo Sannan Auntie ta dawo da kallonta kan Humaira cike da tuhuma ta ce "Menene ya faru a mota naga kamar bata cikin nutsuwar ta.?"

Fuskarta da alamar Rashin jindaɗi Humaira ta ce "Nima dai bansan abin da ya faru ba, farkawa kawai nayi na tsinci kaina a cikin mota driver yana tuƙi ga Jiddarh a gefena, shi ne na tambaye ta abin da ya faru tahau inda inda, bayan na tambaye ta ko qishi takeji sai ta hau tari ba ƙaƙƙautawa."
Humaira tayi maganar tana zama a two sieter.

"To Allah ya kyauta gaba."

Cewar Auntie a lokacin da tayi picking call É—in da ya shigo wayarta, sannan tayi hanyar kitchen tana magana.
Da ido Humaira ta bita sai kuma ta taɓe baki tana gyara kwanciyar a saman kujerar da take akai.

Jiddarh kuwa tana shiga haÉ—aÉ—É—en palon ta wanda ya gaji da haÉ—uwa, jifa tayi da handbag É—inta saman kujera sannan ta É—auki ruwan roba a fridge tasha, kana ta dawo ta zauna akan kujera tana kici kicin rage kayan jikinta.

Sai da ta kammala cire doguwar gown ɗin jikinta sannan ta miƙe ta shige Bedroom a saman bed ta aje gown ɗin sannan ta shiga bathroom.
Sai da ta kwashe mintuna Ashirin tana wanka kana ta fito É—aure da towel White color a chest É—inta.

Gaban Dress Mirror ta tsaya tana kallon kanta tayi murmushi afili ta ce "Saini Jiddarth ɗiyar Ahalin Komai Naga, yau na cinye Gasar SARAUNIYAR KYAU matakin jaha saura na ƙasa, ina fatan kamar yadda na lashe wannan shima na lashe shi." 😎

Sai tayi shiru da sauri ta ɗauki red jam baki ta buɗe, sannan ta zizara a saman jajayen laɓɓanta kana ta mayar da jam bakin saman Dress Mirror.

Kallon kanta ta kuma a madubi washe baki tayi a fili ta kuma cewa "Amazing Masha Allah sai ni Jiddarh kuma fa wallahi ina da kyau sosai. Ya Allah wannan baiwar ta ka Jiddarh tana godiya da wannan hallitar da aka ma ta bada wayonta ko dabara ba."
Kwance Ribbons É—in da ta É—aure dogon gashin kanta tayi aikuwa gashin ya zubo ta gabanta da bayanta duk yabi ya rufe ma ta fuska.

Gefe ta matsa da gashin da ya rufe ma ta fuska, kallon kanta ta kumayi a madubi ta ce "Wash sai ni Jiddarh SARAUNIYAR KYAU a garin kano, wannan kyau haka aiko Larabawa da Turawa saina cinyesu a Gasa bansani ba."

Dariya tayi sannan ta É—auki kwalli ta kuma zizarawa a dara daran kyawawan idanunta, bayan ta gama haka ta ci gaba da yaba kanta da kanta har sai da gaji dan kanta sannan ta hakura dan kanta.

https://chat.whatsapp.com/LUPynCNbwwKFbvnBmQ504P

*💋💋𝑆𝐴𝑅𝐴𝑈𝑁𝐼𝑌𝐴𝑅 𝐾𝑌𝐴𝑈💋💋*

*👑𝑇ℎ𝑒 𝐺𝑙𝑎𝑚 𝑄𝑢𝑒𝑒𝑛👑*

*𝑊𝑟𝑖𝑡𝑖𝑛𝑔 & 𝑆𝑡𝑜𝑟𝑦 𝐵𝑦*

*𝐾ℎ𝑎𝑑𝑒𝑒𝑗𝑎𝑟𝑡ℎ 𝑆𝑎𝑏𝑖`𝑢 𝑌𝑎ℎ𝑦𝑎ℎ*

{♥︎𝑇ℎ𝑒 𝑁𝑎𝑖𝑛𝑎𝑟ℎ 𝑘𝑑♥︎}

*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.}``` ✏️

𝐓𝐡𝐢𝐬 𝐒𝐭𝐨𝐫𝐲

_In dedication to my dear Classmate Science G.S.S.S BELE ROAD._

Page *41&42*

Shiryawa tayi cikin kayan shan iska wando jeans black color, sai riga Top mai gajeren hannu milk, sannan ta saka Ribbons milk da black ta kamo doguwar sumarta kanta ta tufke da kyar, hular bat saka akanta black color.

Palo ta fito ta ɗauki handbag ɗin ta a saman kujera sannan ta saka flat shoes black color fitowa tayi daga Bedroom ɗin, sannan ta fara taka staircases tana saukowa ƙasa.

Downstairs ta sauko can saman 2sieter ta hango Humaira tana kallon wani Nigerian Drama 'The Best Friend In The World.'

Qarisawa tayi ta zauna a saman 3sieter ita ma tana mayar da kallonta akan Tv.
Shiru sukayi gaba ɗaya suna kallon, can sai ga Auntie ta sauko Downstairs ɗin cikin shigar alfarma sai baza ƙamshi take, zama tayi a 2sieter tana kallon su gaba ɗaya da alama ba wacca tasan lokacin da ta ƙariso gurin.

Remote ta É—auka sannan ta danna pause, gaba É—aya su biyun suka juya suna kallonta a firgice.

Dariya Jiddarh tayi sannan ta ce "lah Auntie yaushe kika ƙariso nan bamu sani ba?."
Harara Auntie ta galla ma ta tana faÉ—in "To dama yaushe zakusan nazo gaba É—aya hankulanku yana akan Tv."

Jiddarh ta ce "Allah Drama É—in akwai kyau ne shiyasa,"

"Uhm ba wani nan, yanzu ina kyautar naki yake mugani." cewar Auntie fuska washe.

Dariya Jiddarh tayi sannan ta miƙawa Auntie jakarta tana cewa "Box ɗin yana ciki du ba mana muga abin da ke ciki."

Karɓar jakar Auntie tayi sannan ta zuge zip ɗin ta ciro ɗan box ciki.

"Wannan box É—in da gani ba wani abun kirki bane a ciki, to wai dama haka akeyi gurin Gasar idan anyi Nasara a bada secret box?." Humaira ta tambaya.

Jiddarh ta ce "Ni ma dai bansani ba, amma wata ƙila su wannan ne salon su, sai dai hakan ya ƙayatar dani matuƙa."

Tayi maganar tana kallon box ɗin da Auntie take warware igiyoyin da aka ɗaure dashi, Humaira ta kuma cewa "Ni fa gaba ɗaya na ƙosa a buɗe domin ganin ko menene a ciki, so samu ace wannan buɗewar a gaban su Abba da Yaya Heesham dasu Ni'ima za'ayi da zaifi armashi over."

Jiddarh ta amsa da faÉ—in "Barsu kawai gaba É—ayansu nayi fushi dasu, har Abban sai da yaga ranar Gasar shine ya gudu Spain, shima Yaya Heesham ya bishi ko, zasu dawo su gamu dani ae." Jiddarh tayi maganar ne tsakaninta Allah tana É—aure fuska, alamar rashin jin daÉ—i.

Humaira tayi dariya zatayi magana ne, amma cak maganar ta tsaya a bakinta ganin danƙareran Diamond Wrist Watch da Auntie ta ciro daga cikin box ɗin.

Ajiye shi Auntie tayi a gefe sannan ta kuma ciro wasu haÉ—aÉ—É—un Diamond Chain and Earings da kuma Diamond Ring.
Chapter 46 · 0% Book details