← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 96

Sashe 67

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda yake tsaye daga tsakiyar staircases sanye cikin kayan shan iska ya ɗaura hannu a waist yana kallon Yaran su cike da Nishaɗi, sannan a hankali ya ƙarisa saukowa daga saman Floor ɗin kana ya ƙariso wurin ta yana sakar ma ta ƙayataccen murmushi Wanda yasa sai da gabanta ya faɗi.

Zama ya yi a 3sieter gefanta ke nan Yana kallonta kamar yadda ita ma ta zuba masa ido tana kallo Like a ta sama TV.

"Matar Mai Kyau Yane ya da wannan kallo haka?."

Abubakar ya yi ma ta tambayar yana dariya.
Murmushi tayi tana faɗin "Mijina Mister Mai Kyau ina son ka, ina ƙaunarka fi ye da Rayuwa ta."

Tsura ma ta ido ya yi yana kallo ya fahimci maganar dake fitowa daga bakinta, ba iya fatar bakinta ya tsaya ba, a'a tunda ga ƙasan zuciyarta take masa maganar, Ajiyar zuciya ya sauke tunani yake anya kuwa ya faɗa ma ta maganar dake a bakin sa kuwa, ko ya fasa sai gaba?.

Kai ina gwara kawai ya faɗa a yau kuma yanzu saboda a kullum lokaci ƙara ja yake yi obaa.

Gyara zamansa ya yi a kujerar yana kuma matsawa kusa da ita, sannan ya kamo hannunta duka biyun kana ya kira sunan ta da wata murya wacca Alƙalamin Nainarh Kd ya yi kaɗan wajen rubuta sufar ta.😘

Amsa wa tayi ita ma cikin faÉ—uwar gaba maras dalili, ci gaba da cewa ya yi

"Ina so zamuyi wata magana mai muhimmanci dake, shin zamu tsaya anan ne ko kuwa?."

Ya yi maganar idonsa a kanta, murmushin ƙarfin hali ta masa kana ta janye hannunta daga cikin nashi, ta ƙarisa wajen center table ta ɗauko juice a glass cup ta dawo ta zauna ta miƙa masa tana faɗin

"Oh Allah My Lawful ke nan yi maganar ka kai tsaye kawai ba tare da wani shakka ba, kaji nawan."

Ƙin amsar juice ɗin da take miƙa masa ya yi saima cewa da ya yi

"Ina ga ke yafi kamata ki sha wannan Ruwan Ƴaƴan ita cen ba ni ba, ni dai kawai hankalin ki nake buƙata a tare dani."

Wannan karon gyara zama ita ma tayi sai da ta kurɓa juice ɗin hannunta sannan cike da ƙissa da kisisina tana kashe murya ta ce

"Okay My Lawful ina jin ka."

Tayi maganar tana riƙe glass cup na hannunta da kyau.

"Rafi'at Aure zan ƙara nanda sati uku shi ne dama maganar da nakeso muyi dake..."

Ya yi maganar yana zuba ma ta kyakyawan idanunsa kamar mai tsoron ta, bawai fargaba yake ba, a'a kawai Yana tsoron Halin wasu matan....🌚

"Damn All wai Rafi'at Aure zan ƙara nanda sati uku shi ne dama maganar da nakeso muyi dake..."

Ta maimaita wannan maganar a cikin zuciyarta Yafi sau dubu a cikin sakanni uku kacal.

"Damn it..."

Da ƙarfin gaske ta damƙe glass cup ɗin dake a hannunta har sai da glass cup ɗin ya tarwatse aikuwa nan hannunta yahau zubar jini kamar an bude famfo, amma ita ko a jikinta maimaita maganar ƙarin Aure kawai take cikin ranta. "Kaico Wallahi, kaico da Halin wasu mazan,"

To wai ma dakata tambaya ɗaya take dashi wai shin Menene bata yiwa wannan Bawan Allah da zai saka ma ta da maganar ƙarin Aure idan fanin kula dashi a bed ne, tasan tana iyakar bakin ƙoƙarin ta kuma ta tabbata ita ɗin ba raguwa bace, idan kuma a kace ta fannin mutunta shi ne, ko kuma mutunta dangin shi da duk waɗanda suke a Ahalin sa, tasan dole a bata kyautar oscar ta wannan ɓangaren, idan kuma a kace ta ɓangaren kula da Gida da kuma Yarane, wannan ma ajin farko take.

"Kai kai! No.! No! Way..!!

Bazai yiwu ba, bazai taɓa yiwuwa ba Wallahi..."

Ta faɗa da kuwwa a can ƙasan zuciyarta Yayin da idanunta suka yi jajir na ɓacin rai, tana ji Abubakar ya tashi da sauri can ya dawo da first aid box a hannun sa ya shiga bata treatment a hannunta da ya fashe amma ko motsi ta kasa.

Har ya kammala ya mayar first aid box ma'ajiyar shi sannan ya dawo ya zauna kusa da ita Yana kallonta kamar yadda ita ma É—in shi take kallo, buÉ—e baki ya yi zai ma ta magana.

Katse sa tayi da sauri

"Abubakar please ina buƙatar na kasance ni ɗaya ko zan iya samun wannan damar?."

Tayi maganar tana kallon yadda ya saki baki da hanci yana kallonta jin abin da take faɗi iya kar sannin shi da ita bata taɓa kiran ainihin sunan shi ba, sai yau

"Lallai kuwa an ta ɓota obaaaaa..."

Ya faɗa a ƙasan ranshi yana jin jina kai.

Ganin ya mayar da ita tamkar hoto ne yana kallo yasa taja mugun tsaki sannan ta miƙe da gudu ta haye staircases tana ji Yana kwala ma ta kira amma taƙi tsayawa, domin ji take idan ta ci gaba da kallon sa sai ta kai masa mari bata sani ba.

Ita kanta tasan tana da bad temper obaaaaa, shi yasa take kiyaye wa daga abin da zai ɓata ma ta rai, domin tasan ƙarshen bazai yi kyau ba, gashi a yau mijinta Abubakar yana so ya tayar ma ta da hawan Ruwa.🙆

Wani wawan bugu ta kaima ƙofar bedroom nata, aikuwa ba shiri ƙofa ta buɗe dama babu key a jiki, shiga bedroom ɗin tayi sannan ta mayar da ƙofar ta rufe hadda murza key.

Dafe kanta dake faman sara mata Tamkar zai rabe gida Biyar tayi, tana huci da gudu ta ƙarisa wurin Dress Mirror ta ɗauki wani kwalbar turare iya ƙarfinta ta jefa wa Mirror ɗi wannan kwalbar aikuwa nan take Mirror ya tarwatse, hakan ma bai ishe ta ba, nan ta shiga watsi da kayan bedroom ɗin faɗi take

"Wallahi Abubakar baka isa ba, kayi kaÉ—an, ba macen da ta isa ta aure ka muddun ni Rafi'at Rafiq Rayyan mata ga Abubakar Mai Kyau, ina Raye a doron duniya wallahi babu macen da takai wannan matsayin..."

Ihu take tana surutai tana watsi da kayan bedroom É—in.

Ta É—auki tsawon lokaci tana haka sai da ta tarwatsa komai na É—akin bata bar komai ba, sannan ta dakata dan kanta.

Komawa gefe tayi ta zauna tana faman haki tanaji Abubakar yana buga ƙofar amma taƙi ta buɗe, duk da magiyar da yake ma ta tana ji taƙi buɗe wa, can kuma taji shiru da alama ya gaji ya koma inda ya fito.🤨

Dogon tsaki taja sannan ta duba a gogon bangon ɗakin ƙarfe Takwas na dare wani tsakin ta kuma ja sannan ta ce a fili

"Ashe ma lokaci ya tafi haka, tashi tayi ta haye saman bed da yake bata da tsarki shiyasa bata damu ba.

Duk yadda taso bacci ya ɗauketa a wannan daren ƙin zuwa ya yi to, ta ya ya ma zai zo bayan taji abin da duk duniya tafi tsana maganar kishiya.

Haka ta kwana bedroom É—in a hargitse idanunta a buÉ—e tana kallon ceiling, kiran sallan farko a kunenta a kayi amma ta kasa tashi saboda gajiya sai lokacin ta fara jin gajiyar haukar da tayima ÆŠakin.

Ba ita ta tashi daga saman bed ɗin nan ba, sai wuraren ƙarfe bakwai da rabi, sannan ta sauko daga saman mattress ɗin kai tsaye bathroom ta shige tayi wanka bata damu da yanayin bedroom ɗin ba, ta shirya cikin ƙananan kaya bayan ta fito daga bathroom ɗin.

Fitowa tayi daga bedroom ɗin kai tsaye bedroom na Yara ta wuce, sai Yanzu kwakwalwar kanta ta fara dawowa kan sai ti tunani take shin ko a wani hali mijinta da Yaranta suka kwana Ooho.😏

Buɗe bedroom ɗin tayi ta shiga wayam babu kowa, du ba du be ta fara, amma ba Yara ba Sanadin su, hankali a ɗan tashe ta fito waje tana du ba ko'ina, amma ba Yara ba ubansu har bedroom nasa ta duba ba kowa tuni ta fara da ta sanin rufe ƙofar da tayi.

Da sauri ta nufi staircases ta fara taka wa saboda tsananin tashin hankalin da take ciki yasa da bibbiyu take taka benen saukowa Downstairs tayi, ta fara dubawa amma wayam kamar ance ta mayar da kallon ta a ɓangaren da Dining room, aikuwa ta hangosu Zaune gaba ɗaya Yaran da uban suna Karin kumallo.

Da sauri ta nufi wurin har tana tun tuɓe amma bata damu ba, ta ƙarisa wurin tana haki ta ja kujera ta zauna, aikuwa da ganin ta ƙananan Yaran suka fara miƙo ma ta hannu suna dariya.

Ajiyar zuciya ta sauke tana binsu da murmushi, ɗan satar kallon mijin nata tayi, aikuwa tayi kyakyawar gani fuskar nan a Tamke ya haɗe girar sama da ta ƙasa.

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa sannan da kyar ta iya haÉ—iye lomar abincin da takai bakinta kallon ÆŠanta Abdulmaleek Tayi ta ce

"Yane Buddy baka ganni bane naga baka min magana ba?."

Kallon mahaifiyar tashi Yaron ya yi yana ɓa ta fuska sannan cikin qwarancin sa Yace

"Momyn ina fici da ke, jiya kin sha Daddy a fyacin lai cocai cocai, kuma a bedroom naca muka kwaya, nida su Nailah kuma ya yi mana wanka Nainarh sai kuka take yi, wai taya emanki, kuma fa Nailah bata futa ba cabulu ya ciga mata idooo..."

Tunda Yaron ya fara magana Rafi'at ta saki baki tana kallon shi cike da tsananin mamaki ashe haka Yara suke da kula tsaf.
Har sai da yakai aya sannan ta sama zarafin yin magana.

"Am so sorry My Buddy jiya Momyn bata da lafiya shiyasa bata kula daku ba, amma ba zata ƙara ba, kaji?."

Tayi maganar tana kama kunne, a maimakon taga Yaron ya sausauto, a'a sai ma ƙara Tamke fuska ya yi kamar yadda ubansa ya yi sannan yace

"Toh melaca aki gayawa Daddy ba ya siyo miki agani?."

Wannan karon baki sake take kallon sa a zuciyarta kuwa ayyana irin zuciya na wannan ÆŠa nata take yi

"Aikuwa akwai Babban aiki a gaba na."

Ta faÉ—a a hankali sannan ta ce

"Toh ai Daddy yana fushi dani shiyasa..."

"A'ina ki kaga ina fushi dake?, ni bana fushi dake, to akan me zanyi fushi dake, bayan ma ni na kar zomon?."

Taji muryar mijinta Abubakar yana faÉ—in maganar kuma har lokacin bai juyo ya kalleta ba.
Chapter 67 · 0% Book details