← Book details Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 96

Sashe 37

Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read

"aikuwa sai dai aniyar ki ta biki domin Haleesat tafi ƙarfin ki nesa ba kusa ba, domin 'she was very £xtraordinary lady' ita ba kalarki bace, ko zuwa Night Club da takeyi jarab tane kuma kema kinsani Haleesat batayi kalar mata masu yawon ta zubar ba."

Shiru tayi domin kuwa a yanzu bata da amsar da zata bani, ganin haka naja tsaki ina faɗin "idiot kawai kina mace bakisan ciwon kanki ba, wai kuma a haka kike yarinya a gurin babban malami shahararre, andaiji kunya ƴar malam taƙi halin malam.

Duk sunaji na amma daga ita har Feenah dake kwance saman bed, sun kasa tankamin, na kuma jan tsaki sannan na nufi wardrobe na ciro kayan da zan saka.
Harna kammala shiri suna É—akin sunyi gum kamar ruwa ya shanye su.

Dare misalin ƙarfe goma saura a lokacin wayata tayi full charge, ina zaune saman doguwar kujerar ɗakin, ina sipping coffee, na lalubo lambar ki na kira duk a zato na, sunyi bacci shine fa, kina ɗagawa Feenah ta ƙure volume na speakers, ke kuma daga wajen ki bakyaji sosai, na miƙe da niyyar fita waje, nan wani jiri ya kwashe ni mug dake hannuna ya tarwatse a ƙasa, daga nan nima na bishi bansan tayaya kuma meya faru ba.

Kawai dai da safe na farka ne na ganni a saman bed, ɗakin ba kowa alamar dai ba'a anan suka kwana ba, a lokacin kasa tashi nayi saboda kaina dake matuƙar sarawa haka kuma ga jikina ba qwari.

Nafi ƙarfin two hours a haka sai daga baya na samu na tashi da kyar na shiga bathroom nayi wanka na fito, har lokacin ba ɗayarsu da ta dawo a gurguje na shirya cikin sauri sauri.

Bayan na shirya ne fa, wuraren ƙarfe biyu na rana har lokacin dai ba wacca ta dawo, zuwa lokacin hankalina ya fara tashi ina nan zaune, saiga ƙanwar Zuree ta shigo ɗakin wai tazo gurin Zuree yayarta, kuma tarema suke da babban yayansu.

Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba, ma ta bayanin abin da ke faruwa tun daga farko har ƙarshe.
Ita kuma tanajin haka ba ɓoye ɓoye taje ta faɗama babban yayansu dake waje cikin mota yana jira, shima dai kamar ƙanwar yasha mamaki, amma sayya dake ya ciro phone ɗinshi a trouser pocket ɗinshi ya lalubo lambar Zuree, ya danna kira amma waya a kashe ya kira yakai sau goma amma dai abu ɗaya waya a kashe.

TASHIN S£NS£!

Muna tsaye a bakin gate munyi cirko cirko muna jiran tsammani, saiga wata arniyar mota black color ƙirar R.R. ROLLS ROYC£.
Tayi parking a can gefen mu saiga ƙanwar Feenah, wato Fannah ta fito daga ciki da sauri ta ƙariso gurin da muke tana tambaya na ko lafiya, sannan kuma Feenah tanan sun kawo ma ta ziyara ne.

A lokacin duk da bani ce nayi laifin ba, amma wallah saida naji wani fitsarin tsoro ya cika marata.

Da kyar na samu na ce ma ta "Feenah bata nan," zatayi magana saiga Dadynsu da kuma Momyn su matar da Feenah take a hannunta, da kuma wani saurayi da alama yayansu ne sun ƙariso gurin.

Hannu yayansu Feenah yaba Babban yayansu Zuree sukayi misa baha, sannan suma suke tambaya ko lafiya suka ganmu cirko cirko dayake na É—an saba da Æ´an gidansu Feenah ba laifi.

Nanfa babban yayansu Zuree ya gyara tsayuwarshi, yaba su labari kamar yadda na bashi.

Nanfa naga ɓacin rai kalar wanda ban taɓa gani ba, dan kuwa yayansu Feenah yafi Babban yayansu Zuree nuna tsantsar ɓac
cin ranshi akan abin da yaji su Feenah sun aikata ko ince suke akan aikatawa.

Cikin tsananin ɓacin rai yake faɗin "yaushe kuma ta yaya Safeenah, dama haka sunan Feenah yake na gaskiya.

Ta zama haka, kuma mu muna ina, a wannan lokacin da ƙarfi ya damɗe hannun shi yana futar da huci, shikuwa Dadynsu Feenah tsananin mamaki ya hanashi faɗin komai, haka dai munkai kusan minti talatin muna tsaye a gurin kowa da abin da yake saƙawa aranshi.

Can saiga Motar Zuree ta nufo gate É—in bamu sani ba, sun hago mutane ne a gurin ko miye ya faru, da sauri dai mukaga motar tayi reverse zata bar gurin.

Ai a three sixty 360 yayansu Feenah shida Babban yayansu Zuree suka bi motar wata kalar super Babban yayansu Zuree yayi yasha gaban motar, yayinda yayansu Feenah ya fasa glass ɗin motar da hannun shi, bai damu da jinin da hannun shi yake ba, ya finciko Feenah waje bai tsaya komai ba, ya dingi ball da ita yana marinta ta ko'ina dukanta yakeyi, don koda yaga ta suma ruwan roba ya ɗauko a mota ya kwara ma ta, ba shiri ta farfaɗo shi kuma ya ci gaba daga inda ya tsaya, ganin zayyi kisane yasa ƙanwar Feenah, Fannah ta ruga da gudu tana kare Feenah tana bashi haƙuri, amma ina kamar ma cewa take ya ci gaba, aikuwa ya haɗa da ita yana jibga baya ma gajiya ga mutane har an fara taruwa ƴan kallon qwaqwaf hadda masu ɗaukar video.

Ganin zai kashesu su duka ne yasa Momyn su ta tafi da sauri ta shiga tsakani, sannan fa ya dakata, shikuwa Dadynsu yana gani yaƙi magana sai ma mota daya koma abinshi.

Shikuma Babban yayansu Zuree tun lokacin da ya kamota wani farin gam yasa ya rufe mata baki dashi, sannan ya ɗauko igiya ya ɗaure m ata hannu da ƙafafu duka biyu sannan fa yahau dukanta yana kwallo da ita haɗe da marinta, fuskar nan nata da tasha bleaching tayi wani irin jajir kamar kamar me.
Bai dena dukanta ba sai da yaga bata motsi sannan ya ciciɓeta a haka ya jefa a mota kamar kayan wanki sannan ya dawo wajen yayansu Feenah suka sakeyin misabaha, ya min godiya sannan ya shiga mota ita ma ƙanwar Zuree ta shiga yajasu suka bar gurin.
Shima yayansu Feenah kaÉ—asu yayi suka shiga mota suka bar gurin suma daga nan kuma kowa yayi gaba, nima haka jiki ba gwari na koma ciki.

Ajiyar zuciya Jenny ta sauke da ta kawo nan sannan ta kalla Haleesat da tunda ta fara maganar ta zuba ma ta ido, murmushi tayi ta ce "in taƙaice miki dai Zuree a ranar mahaifinta ya aurar da ita sadaka ga wani almajirinshi, sannan kuma yace karatun ma an barshi ba ita ba ƙara zuwa school forever...ita kuwa Feenah taci wuya amma dai ita ba'a katse ma ta karatu ba saboda Dadynsu cikaken ɗan boko ne, gaba da baya amma dai yanzu bata kwana a hostel sai dai ana tashi driver yazo ya ɗauketa su tafi gida thats is all.

Ajiyar zuciya Haleesat ta sauke, sai da ta nisa sannan ta ce "duk da abin da suka min banji daÉ—in hukuncin da aka yankewa Zuree ba, aure bashi zaisa ta nutsu ba, nasan halin Zuree gaba da baya."

Da tsananin mamaki Jenny take kallon Haleesat ta ce "ae na ɗauka zanga kina farin ciki ne, a lokacin da nake baki labari,..sai kuma kika bani mamaki...a gaskiya Haleesat bazan ɓoye miki ba, kina burgeni sosai fa over, sannan kuma zuciyarki mai kyau ce, ina alfahari dake a matsayin ƙawata, am so very proud of you, ashe akwai mutane irin ki a duniya lallai ne, yau na yadda da kalmar na 'INDA RANKA KA SHA KALLO.'

Ɗan murmushi Haleesat tayi aiƙaice sannan ta ce "Jenny kenan akwai ki da sonyin karin magana, gashi baki wani iya ba," ta ƙarishe maganar tana kuma sakin murmushi, Jenny ta ce.

"saura kuma abu É—aya, da ban faÉ—amiki ba,"

"Menene shi?,"

Haleesat ta tambaya, Jenny ta ce "na sama Admission a Beijing China, acan zan É—aura master's É—ina."

Ta faɗa cike da farin ciki, washe baki Haleesat tayi sannan ta miƙawa Jenny hannu tana faɗin.
"congratulations Dear, yanzu shikenan zaki tafi, ki barmu da kewar ki ko?."
Jenny tana dariya ta ce, "toya za'ayi duk acikin neman ilimi ne.."

Dariya sukayi a tare Haleesat ta ce "kuma fa kinyi gaskiya," tashi sukayi a tare Haleesat ta nufi motar ta shiga taja, ita ma Jenny ta nufa nata ta shiga.

HAL££SAT

Tana driving amma gabaÉ—aya hankalinta baya jikinta, ta faÉ—a duniyar tunanin hali irin na mutane zaka haÉ—u da mutane kala kala a Rayuwar ka sannan kuma zakaga kowa da kalar halinshi.

Horn tayi a ƙofar gate ɗin gidansu bayan ta iso, wangale ma ta gate ɗin mai gadi yayi, sannan ta shiga da motar ciki.

Saida ta daidai ta parking a wajen da aka tanadar domin yi sannan ta fito, back seat ta buÉ—e ta ciro handbag É—inta da wasu files, sannan ta nufa ciki, gabaÉ—aya jikinta a sanyaye.

Wasu lambobi ta danna a jikin glass door ɗin nan take ƙofar ta buɗe da kanta saida tsaya a bakin ƙofar ta canza takalman kafafunta izuwa slippers na shiga, sannan ta shiga ciki bakinta ɗauke da sallama.

Gaba ɗaya mutanen dake zaune a palon suka amsa ma ta Zaynerb tana daga saman doguwar kujera tana kallon wani indian drama 'THOLI PREMA' na varun tej da Raashi Khanna, yayinda Nainarh takeyi ma jaririn Nailah wasa. Ita kuma Nailah tana baje a tsakiyar palon tana duba wasu takardu, ƙarisa shiga ciki tayi.
Zaynerb ta ce "yau baki dawo da wuri ba, fatan komai Normalcy?,"
Kallon Zaynerb dake magana Haleesat tayi sannan tana murmushi ta ce "komai lafiya sister, kawai dai yanayin garinne,"
Zaynerb ta ce "haka akeso komai ya kasance lafiya a kullum kuma a ko yaushe,"

Haleesat tayi dariya Zaynerb akwai ta da barkwanci wani lokacin bedroom É—inta ta wuce bayan tama su Auntie Nainarh barka.

Tana shiga ta aje handbag É—inta da sauran files É—in dake hannunta a saman glass center table, sannan ta fara kici kicin rage kayan jikinta, bayanta gama É—aura towel tayi sannan ta shiga bathroom, wanka tayi da brush dayake bata da tsarki.
Chapter 37 · 0% Book details