Sashe 42
Sarauniyar Kyau Takun Farko Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba É—aya gurin haske ne, na fararen drop light's, tafiya take sanye cikin farar doguwar riga, kanta ba hula dogon gashin kanta ya zubo ta gaba da bayanta.
Daga can nesa ta hango wasu ƙofofi guda biyu, ƙofar farko haske ne da ita kamar yadda wajen yake cike da haske na ban mamaki.
Yayinda ƙofa ta biyu duhu ne da ita sosai. Tsayawa tayi cak ta rasa waca ƙofa zatabi daga ta cikin ƙofa ta biyu mai duhu
Ta hango hannayen mace, da alama taimako take nema, da sauri ta ƙarisa gurin. Domin ta taimakawa matar.
Sai kuma ta tsaya cak a gaban matar tana bin ta da kallon tsoro, fuskar matar ta kalla.
zaro fararen idanunta tayi cike da tsoron ganin ba kowace ke neman taimakon ba, fa ce Haleesat, yayinda daga cikin ƙofar mai duhun gaske wata mata sanye cikin baƙaƙen kaya, ba ka ganin fuskar ta saboda duhun gurin, ta dake sai janyo Haleesat take ciki da ƙarfi.
Yayinda Haleesat taƙi yadda, ita kuma matar taƙi hakura kuka Haleesat take tana miƙo ma ta hannu alamar ta taimaketa, ita kuma saboda tsoro ta kasa komai, da ƙarfi taji wata murya a ta bayanta tana ma ta magana.
A sanyaye ta juya tana kallon matar dake sanye cikin fararen kaya fuskar ta a lulluɓe da mayafi, matar faɗi take "ki taimaki ƴar uwanki, idan ba haka ba waccan azzalumar zata cutar da ita kamar yadda takeso ta cutar dake, ki taimakawa ƴar uwanki, karki baki wancan muguwar matar ta cutar da ita kamar yadda ya cutar dani."
tana gama faɗin haka ta ɓace ɓatt, a firgice ta fara waige waige cikin gurin mai haske amma sama ko ƙasa bataga wannan matar da tayi maganar ba.
Da wata iriyar jarumta ta juya ta fara janyo hannun Haleesat tana ƙoƙarin fitar da ita daga cikin baƙin ɗakin da wannan matar takeso ta shigar ciki.
Amma ta kasa wata kalar jar wuta matar dake a cikin baƙin ɗakin ta jefo ma ta, da sauri ta kauce, wannan kaucewar da tayi shiya ba matar damar tura Haleesat da take kuka kamar ranta zai fita cikin wannan baƙin ɗakin take ƙofar ta rufe ruf matar da Haleesat suna ciki.
A firgice kuma a gigice ta farka daga baccin da ya É—auke ta har tayi wannan mummunar mafarkin, gaba É—aya tabi ta haÉ—a uban zufa, ba abin da take furtawa a bakinta sai, "a'uzu billahi mina shaytanirrajeem."
Saukowa tayi daga saman mattress ɗin agogon bedroom ɗin ta kalla, ƙarfe uku da rabi na dare, hularta ta ɗauka a saman gadon sannan ta shiga bathroom, bakinta ɗauke da addu'a, gaban sink ta tsaya tana sauke haki.
A gaggauce ta ɗauro alwala sannan ta fito, sallaya ta shimfaɗa tayi sallah raka'a huɗu, kana tayi sallama, ta daɗe akan sallayar tana addu'o'i har taka kira sallar asuba, sai da tayi sannan ta miƙe ta ninke sallayar bayan tayi azkhar ta mayar ma'ajiyar ta.
Bathroom ta shiga akalla takai one hour tana wanka sannan ta fito sanye cikin bathrobe, knocking taji daga ƙofa sai da ta saka hijjabi dogo sannan ta nufa ƙofar ta buɗe.
Murmushi tayi ganin Deejarh sanye cikin doguwar rigar atamfa ta saka hijjab blue iya gwiwarta, hanya ta bata ta shigo bedroom É—in, zama tayi saman wata kujera na karatu sannan ta ce.
"Balarabiyar India ta ina kwana kuma da yaushe za'a tafi ne dan na ƙosa sosai sosai?."
Afeefah ta ce "ae tuni na É—auka kin fara hankali, ashe ashe ba haka bane, to yanzu wanne kikeso na amsa miki daga cikin tambayoyin da kike faman antayomin hunm?."
Dariya tayi ta ce "duka nake so ki bani amsar su,"
"ashe dai har yanzu da sauran Deejarh."
Cewar Afeefah tana murmushi, Deejarh ta kuma faÉ—in "amma dai Balarabiyar India yau ba za ki shiga kitchen ba, ko?,"
"Saboda me fa?."
Afeefah ta tambaya, Deejarh ta ce "saboda yau Babbar rana ce....Yauwa baki faɗamin ko ƙarfe nawa za'aje ba."
Afeefah tana dafe goshi alamar gajiya da surutu ta ce "misalin ƙarfe tara zamu tafi, za'a fara ƙarfe goma sannan a kammala karfe sha ɗaya mu dawo gida sha biyu."
Deejarh tana murmushi ta ce "kuma fa wannan tsarin yayi highly highly na miki na Anty Lailash."
Ƙin kulata Afeefah tayi saima closet da ta nufa ta shirya cikin rigar Abaya dark green sannan ta ɗaure igiyar rigar ta baya, mayafin tayi rolling dashi akanta.
Agogon ta kalla ƙarfe takwas dai dai na safe, zaro ido tayi waje ganin lokaci ya tafi.
Deejarth ta ce "idan ma tunanin shiga kitchen kikeyi sai dai kiyi haƙuri, dan tuni mun kammala komai, nida su Auntie Nainarh."
Juyowa Afeefah tayi ta ce "ni banma san lokaci yaja haka ba, wallahi.."
Tayi maganar a yayinda suke fita daga bedroom ɗin, a dining area suka hango duka ƴan gidan, suna karin kumallo ƙarisawa sukayi suka zauna Afeefah ta gaisar da Daddyn da Momy Rafi'at sannan suka fara cin breakfast ɗinsu.
**
Misalin ƙarfe tara dai dai na safiyar ranar litina, gaba ɗaya Ahalin Mai Kyau suna tsaitsaye a parking lot tun daga kan Uban gayyar Abubakar Mai Kyau, da matar tashi Momy Rafi'at Mrs Mai Kyau, Auntie Nainarh, Auntie Nailah, Haleesat, Zaynerb, Afeefah, Lailah sai kuma Deejarh dukansu matan sanye cikin Arabian gown dark green yayinda mayafin su yake fari takalman su ma iri ɗaya fancy ballerina, ko wacce da bag ɗinta na gayu a hannu, hadda Momy Rafi'at sunyi kyau sosai, dama gasu Ahalin Mai Kyau, Daddyn kuma sanye cikin suit blue black.
Kallon Lailah Deejarh tayi sannan ta ce "Auntie Lailah nifa ban gane wani abu ba, zan iya tambaya kuwa, domin anyimin ƙarin bayani?."
Murmushi Lailah tayi ta ce "Menene baki gane ba, mai bakin tambaya?."
"ah kinga laifinta, batta kawai tayi tambayarta, san ranta, domin ma tambayi baya ɓata." cewar Auntie Nainarh.
Deejarh ta kuma cewa "dama tambayar ita ce, naga Balarabiyar India batayi shigar gasar ba, naga ita ma kalar kayan jikin mu shine a jikinta?."
Zaynerb ce ta bata amsa da faÉ—in, "Deejarh kenan to ki bari muje can zakisha mamaki ai ba'a nan zata shirya ba, sai anje can, domin abin akwai tsaruka bawai kara zube akeyi ba."
"ohoo ai sai yanzu na fahimta dama haka ne." cewar Deejarh bakinta a sake cike da ƙauyanci.
Gaba É—ayansu suka nufi motocin suka shiga Auntie Nainarh da Zaynerb da Lailah a mota É—aya, sai kuma Auntie Nailah da Haleesat sai Deejarh a mota É—aya, Mrs Mai Kyau, Mister Mai Kyau, Afeefah a mota É—aya.
Gaba ɗaya motocin sun kama guda uku masu kyau da tsadar gaske na nunawa a B.B.C, tun kafin su ƙarisa bakin gate mai gadi ya wangale musu wagameman gate ɗin gidan suka fita a tare.
💞WOND£RFUL_HALL_ABUJA_CITY💞
Qaton gurin taron ya tsaru sosai, tsaruwa iya tsaruwa yanayin tsarin haɗuwa da zanen gurin dai shine, da farko dai ga wasu kujeru irin na zaman ƴan kallo mutane ne zazzaune akai suna fuskan tar floor ɗin wanda, masu gasa (SHOW) zasu dinga fitowa ta ciki suna tsayawa akai daga sama kuma can gefe Alƙalan gasa ne mata turawa biyu sai kuma baƙaƙen fata biyu suma zazzaune saman kujerun alfarma, daga saman floor na gasar kuwa wata kyakyawar budurwa ce wacca akalla ba zata wuce shekara talatin da biyar ba wato dai mai gabatar wa (Introducing Lady).
Hallau kuma daga can gefe masu É—aukar hoto ne wato (Photographers), gefan su kuwa Æ´an jarida ne maza da mata gaba É—aya sun saita abubuwan É—auka (camera) suna jira lokaci ya cika a fara kafta wasan gasar SARAUNIYAR KYAU (The Fashion Show).
Daga first kujerun gurin na zaman ma ta kuwa su Lailah da Zaynerb da Momy da Haleesat sai Auntie Nainarh, da Auntie Nailah sai kuma Deejarh sune a first chairs na gurin da suke daga ɓangaren hagu, ɓangaren dama kuma maza ne.
Akalla gaba ɗaya mutanen gurin zasu kai su ɗari biyar gaba ɗaya hadda alƙalan gasar da kuma sauran jama'a dake a gurin.
Duk wucewar sakan ɗaya sai Zaynerb ta kalla agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunta, baiwar Allah gaba ɗaya ta ƙosa a fara, haka ma sauran jama'an gurin.
Wata wawiyar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ƙarfe goma ta cika dai dai kuma a dai dai lokacin baturiyar budurwar dake saman floor na gasar take faɗi cikin harshen turanci.
"A halin yanzu lokaci ya cika dan haka ba tare da ɓata lokaci ba za'a fara kafta gasar Allah yaba mai rabo sa'a. Daga ni taku SANDRA nake muku fatan alkhairi kuji daɗin kallon FASHION SHOW, lafiya..!"
Tana gama faɗar hakan ta sauka daga wajen ta koma, saman wata hamshaƙiyar kujera na alfarma ta zauna.
Gaba É—ayan su mutane da Æ´an kallo kowa da kowa na gurin suka mayar da hankulan su a ta saman floor na gurin suna jira suga shahararriyar da zata fara fitowa. Toh nima dai ð‘µð’‚ð’Šð’ð’‚ð’“ð’‰ ð’Œð’… da nake É—auko muku rahoto juyawa nayi aslowly domin naba kyawawan idanunta haƙƙin su😎
Sanu a hankali dogayen labulayen launin jajaye na gurin mai haÉ—e da fari suke yin sama a hankali, tohm kamar yadda curtains É—in suke launin ja da fari haka sauran abubuwan gurin suke ja da fari hatta da tiles na saman gurin shima red color nd White color ne.
In slow motion curtains ɗin sukayi sama a take salon bugun zuciyoyin mutanen gurin ya canza😂
Saboda tsananin kyan kyayawar hallitar da ta bayyana, kyakyawar budurwa ce kyakyawar gaske na bugawa a jarida sanye cikin wasu arnayen kaya na Allah tsine uwar mai ƙarya a kyau, budurwar akalla ba za ta haura shekaru ashirin ba a duniya, cikin taku irinna wacca tasha training na salon tafiya, take taku tana juya jiki abin dai sai an gani, oh Allah wannan budurwa ta haɗu qwarai sai da ƙariso dai dai tsakiyar filin sannan ta juya ta kuma juyowa, taba masu ɗaukar hoto damar ɗaukarta da kyau, aikuwa nan suka shiga yi ma ta ba qaqqautawa bakajin ƙarar komai a gurin sai ƙarar flash flash minti biyar dai dai tayi sannan ta juya ta koma ta wajen da ta shigo bayan wasu sakanni.