← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 99 OF 103

Sashe 99

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tashin hankali bai tsananta ba sai da aka shigar da yazeed dakin hutu inda zasu samu sugan sa.
Gaba daya baya duniya kamar gangan jikin da ne kawai suke gani

Nan Sarah ta nufi toilet sabida laulayin ta ya soma dan nunawa sisai warin ward din yasa ta jin amai sosai sai ta barsu su biyun

Hjy Kwance da jikin yazeed din take hawaye cike da jimami take cewa yanzu ka zabi ka mutu ka barni kenan akan wata?
Yazeed meye ban maka ba a duniya da har bazaka rayu saboda dani ba...
Kasan na damu dakai sosai my child pls get up for me i wll do anything don ka samu abunda kake so..i promise.

tsaye daga bayan ta mahfud yake cike da damuwa da sanyin jiki...
ahankali ya dafa ta cikin dauriya yace mum meyasa zaki boye min?

wani fat taji kirjin ta ya dauke wuta sai ta dago ta dube sa he was not ok kallo daya ya isar maka cewa he's hurting..
Tace what?
Ya dage ifo ya dada kallon cikin idanun ta yace
Mum,kin boye min cewa kunsan matata tun da chan meyaasa?
Ko dan akanta yazeed yake ciwo ne mum...dont i dersev to know all of this,yes sarah matata ce amma yazeed fa dan uwan ne fa?we are family tun kafin nasan sarah na san shi..
So Why did you hide it mum....sai ya sauke mata hawaye

taji wani iri amma son danta ya gama rufe mata ido yanzu mafita kawai take nema don haka bata so ma ta kawo wani tunanin whats right and whats wrong

tasan idan ta rasa yaxeed a wannan hali bazata sake iya duban mahfud a matsayin danta ba bare kuma matar sa da itace silar komai.

Sai ta danne duk wani tunanin ta ta taso tace"
Ashe ma kasani?
Dama kasani kabar min dana acikin wannan halin
Yazeed ya hana ni maganan nan sabida da kai...amma ashe kana sane ka noke sai da kaga zai muyi zaka tuhume ni?
Ai burin ku nee dama ya mutu gashi nan sai ka kira ta ku cinye sa..

Da dan dagon murya Ya ce mum pls stop it,lets talk it out....nima yau nake jin maganan Ashe idan yazeed yayi wautar hakan ke
Bazaki iya nuna masa dai dai ba..?

Nima fa danki ne mumy meyasa bazamu hada kai mu fuskance abunda yake damun mu tare ba
its hurt me mum....
Sai naji kamar baki yarda da ni ba ne, ya za'ayi na so na gansa wannnan halin he's my bro for godsake..

tace prove it.....idan har ka amince muna da muhimmaci arayuwarka ka kawo karshen wannan matsalan right now

yace "its too late mum koda akwai karshen wannan matsalar yanzu dole sai mun jira ya warke asan nayi...

tace noooo,wai bakaji likita yace tunanim matar ka ne yayo masa yawa ba
Ai yazed baida wani warkewan da ya wuce sarah..

Idan har ka yarda ni uwace gare ka kuma yazeed dan uwan ka ne ka damu da shi..

mahfud ka sake ma yazeed sarah yayi rayuwa da ita ...
Ka dauka hakan sadaukarwa ce dan ceto rayuwar dan uwanka..

abun ya doke zuciyan sanda wani rin speed bakin sa har na rawa yace what?!!!!! Na sake matata fa kikace mumy?
akan me?i mean that dosnt make sense me tayi min da zan sake ta..duk dan akan yazeed shikenan sai ma saba ma Allah...?

Tace ohhh ,..dama ai nasani za'ayi hakan..wato ma bakaga me tayi na saki ba da dana yake kwance rai a hannun Allah sabida da ita ko?hmmm tabnn di jam

Shikam Mamakin ta ya gama karya masa gabobin jiki he just cant believe this Yace mum,.. Zan iya komai akanki da yaxeed amma indai akan haka ne gaskiya am sorry bazan iya sakin sarah ba..not in this world and not in another
Allah ma ya sani babu biyayya a sabon sa.
I love my wife babu abunda zaisa na sake ta i promise.

A hatsale ta jiyo ta wanka masa mari..tace yayi... naji"mugu kawai....
Shikenan sai kaje wajen ta daga yau sarah ta dawoo uwarka da uban ka nikuma zan dafa gawar dana na sha useless boy.

Yau Ko a mafarki akace mace zata raba ni da kai mahfud bazan yarda ba dan da na rike amma wai yau shine zai zabi mutuwar dana akan wata ya mace? Sai kaje ai ...ni ka fice min daga gani na Allah ya isar min..

He's really hurting amma bayajin duk wani tashin hankali da fitina zaisa shi har ya sake sarah neva eva yake ayyanawa aransa

yasan damuwa sosai ya rufe ma mum dinsa ido
A yau kuma ta nuna masa boyayyen banbamciin tsakanin sa da yazed a zuciyarta a wajeje dayawa ta inda da baiso ya san da hakan ba

Bayajin dadi ko kadan amma yasan akwai mafitan daya fiiye masa sakin matar sa..

koda yaji kan labarin yaga son kai aciki da kuskure mai tarin yawa..

To maiyasaa bazasu hakura yazeed ya dan ji sauki su yi facing case son ta hanyar da yadace ba sai ace ya sake matar sa?

Koda ta kore sa daga dakin baice komai ba ya fice abun sa
Yasan bazai iya ya bar ta a halin da suke ciki ba

Amma yana da yaqinin bazai taba sakin matar sa ba duk rintsi duk tsiya sabida yasan kuskure ne mafi muni idan ya shagala ya aikata.

🐈VOTEs
[2/24, 10:37] SURAYYAHMS🐈: *🅱RILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

_for all Members of SURAYYAHMS NOVELS_

_51_

Nan sarah har ta tafito bata gansa ba ko da ta tanbaya wani hararar da hjiy billy ta rakata da shi yasa ta sha jinin jikin ta ta sulale tabar wajen..

Zaune yake a dan corridor ya dafe kansa, tasan baijin dadi sabida ba fuskan sa ba har jikin sa ya nuna hakan.

Zama tayi kusa da shi ta dafa sa 'cikin lallami da kulaawa ta soma bashi hakuri mai dauke da nasihan da sansanyar kalamai masu sa zuciya sanyi...

Shiru kawai yayi yana jin ta amma shikn sa baisan me zaiyi nan gaba ba..

Haka suka kasance bai isa yaje kusa da inda yazeed yake ba zata kora sa da mummunan kalamai...

Har yamma yayi sosai lokacin sai sarah ta taho gida ta barsa

Gashi dama har anty warda ta ce zata taho sabida ta duba jikin yazeed din shiyasa sarahn tayi zaman jiran calls din ta a tunanin ta ko yau zata samu isowa..

Ganin har 8 na dare yayi anty warda bata kira ba yasa sarahn ta higa mota ta kama hnyr asibiti.

Anan kuma tun bayan ishai jikin yazeed ya taso gadan gadan kamar wanda zai sheka yanzu
His E Line is droping at speed

Likitoci duk an taru akan sa ana danna masa life shocking ko zai samu yayi stabilising amma abu sai gaba gaba yake.

Mahfud tun daga waje yajiwo ihun ta anan ya ta shi ya taho yana rike da ita dukan su suna hawaye .....
Its too obvious that yazeed dagaske mutuwa zaiyi komai ya rikice ya sukurkuce..

Ganin abun na dada razana su duka ya sa ya jawo ta suka koma daga gefe...

Sun kai awa 1 da rabi a tsaye Da kyar aka samu aka stabilising yazeed tare da basu cikakken bayanin idan har ba a sama masa mafita ba nan da awa 18 zai mutu wato gobe da safe kenan.

Hjy blky Har muryan ta ya dishe wajen kuka da ihun sunan danta...
ta rasa meke mata dadi
Anan ta hatsala ta soma kai ma mahfud duka tana haukacewa akan lallai shiya jawo hakan ma rayuwar danta..

Tace shikenan yazeed mutuwa zaiyi sabida kai da matar ka mahffud..?
Yau Da na san zan rike wanda zai girma ya dauke min farinciki na da na mutu tun a dakin haihuwa.

Bai iya magana ba sabida kukan shima yake yi duk abunda take yi na masa zafi sosai....Yana kokarin riko ta ko zata dena maganganun ta yi shiru amma sai dada hawa take..

tace ma mahfud yau na san meyasa Allah ya sa uwarka data haifeka bata san darajar ka ba..da sai na ce idan kasan daraja ta ka sake sarah da na ya rayu..

Butulu mugu kawai azzalumi..
Ka cuce ni da ka jefa dana a wannan halin mahfud...
Duk akan mace? Dame sarahn tafini..me take maka wanda banyi ba Kai bakaji kunya ba,i raise you fed you protect you like my own son meyayi saurah?gindi?...
Kwana da nine kawai ya rage maka kayi ko shi ma na maka ne kafin kasan daraja ta?..

Kirjin sa bakaramin bugawa yayi ba ya dago ya kalle ta araunane ...

lokaci guda ta yaye mayafin ta ta watsar kasa afusace...tace toh gashi na baka kaina idan na dawo dai dai da sarah a zuciyar ka sai ka daraja ni nima..

jikin sa har na rawa yayi saurin sulalewa ya dauko mayafin nata da ga kasa ya rufe mata jikin ta da shi...

nan sarahn ta iso daga gefe tana jin duk abunda yake afkuwa bata motsa ba

Bata fasa ba tace"na amince mahfud ... kayi duk yadda kake so dani fansar rayuwar da na baka a matsayin da na da duk favours din dana maka arayuwa...yau inaso ka biya ni wahalan da nayi da kai da rayuwar dana yazeed go on do it now..ta dada hatsala

He was so terrified amma haka ya daure ya fito da cracking voice dinsa cikin sanyin jiki yace"
ure right...Amma dan Allah Kiyi hakuri mumy....hala kina da gaskiyar ki yau na kasa ganin abunda kike ji akan dan ki...

maybe son kaina da mugun hali na yayi yawa har ya rufe mun ido.. hala ma shiyasa uwata ta kasa sanin daraja ta tun farko ban sani ba.

Im wrong always..im bad in seeing things the way thy shud be...Bantaba daukar ke ba uwa bace awaje na sai awajen yazeed shikadai..im hurting mum, im deeply hurt by evrything
Chapter 99 · 0% Book details