← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 103

Sashe 3

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Akan hanyar sa Dariyar mugun ta yayi sosai har cikin ransa yace " yarinya kenan,ai dama yaro yaro ne,ni babaji bazan taba rainon dan damisa na bar ma na dawa ba wannan karya ne..

Dama chan ena ta farautar sarahtu Amma daga yau ena ga komai ya kare

Wannan ai Sageer ne dan gidan halliru mai nama hmm"dan gidan wanda nake bi bashin filin gona ta daya gina gidan sa ya kasa biya na dan jaraban talauci..kayyah!!!
...ya karashe da wani shu'umin murmushi

Nikuwa Hankali na kwance na zauna a daki,
Sai wajen 8 saura suka kuma shigowa da umma na

A ladabce na sake gaida su
Na kimtsa ma ummah kayan sana'ar ta don dama masa take siyar wa a babban kasuwar kan tudu itake da babban rumfa don ummah na akwai azama da hikima irin na matar karkara.

Hiran su suke yi irin wanda na tsana don sosai kawu babaji yake soka ma umma maganan banza kuma bata isa ta rama ba..

wani bin har yakan ce mata yar bariki goyon farar hula wato karuwa kenan

Umma na bata da hayaniya sabida bata da ilimin komai amma a ladabce take mayar masa da suka in abun ya ishe ta....

abu daya ke bani haushi yadda yake saurin wasa da hankalin ta ta wajen juya magana..

in har yace abu kaza ne bata isa tayi musu da shi ba yafi so ma tabi bayan sa ko kuma tayi shiru kawai

Duk randa ta haura ko akan gaskiyar ta ne sai ya soma dukan ta yana zagin ta ta uwa ta uba,umma na kuwa tunda akayi hakan sau biyu sai ta dena bashi daman haka kwata kwata duk abunda yace yanzu sai dai ta hau kai itama ta dada zuga shi ba don son ranta ba.

Ni kaina nan na sha deban jibga a hannun sa akan samarin dake biyo ni kofar gida

a hakan ma wata rana na san karya yake min amma ban isa na tanka ba haka zasu min lisss
sai dai daga baya umma tabani hakuri

Suna na zaune Wayar sa yayi kara ya dauka

Yace"Wai yaya ne kam zulai?
dan shiru yayi daga bisani ya kwaroro salati
Yace"Hmmmm duniya kenan tabbas anyi mana rashi kai kai kai bari to zan neme ki kawai...

Ai Wannnan maganan ma ku barshi haka zan zo da kaina ma gobe
Yana kaiwa nan ya katse wayar yana jimami,.

Ummah tace "Me gida lpya kuwa...?

bari kawai gambo..ya ya mutsa fuskan kalar jimami yace"ai zama bata kama ki ba Gobe zaki je chan dindima inna wuro ne ta rasu yau din nan da dare.

"Innalihhi wa inna ilaihi rajiun,. Allah ya ji kan innna.. Allah ya sa ta huta amma babaji ciwo tayi ne haka?Sai naga kamar jiya jiyan nan yafendo ta gaya min inna wuro garau take tana ma filin roron gyada.

Ni dai ina daga gefe ta bakin kofa Ina shiru uffan bance ba

"nan baba ya hatsala"Ke da Allah rufe mun baki gambo,da
Cahn mutuwar sai ya zaba wanda zai dauka ne? bana son shashanci da neman tsugudidi fa"

Ummah ta tabe baki tace "ahhhhh toh Allah ya baka hakuri
Mai gida Nace ba?
Goben da su zulai kenan Za muje ko?

"ban sani ba ..ya mike a fusace kamar zai mare ta
wanda hakan ya sani sulalewa chan nesa da bakin kofar kadan na rakube.

Ke kadai nace zaki je, da daban aure ki ba ai su nake turawa..wai nikam rashin kunya zakimin ne gambo?

Uhmm uhmmm..umma tace kamar bata damu ba

Tace Allah ya kaimu goben..daga nan taja bakin ta tayi shiru

Shiru ne ya ratsa wajen ban sake jin motsin su ba..
nima bacci ne yayi nasaran dauka na a gefen bakin kofar ban sani ba

gurnani da sambaton baba babaji ya sa na firgita. cikin sanda da tsananin kunya na mike na kama hanyar soro ba wanda ya sani kamar kullum naje na kwanta kan dakali.

Bayan sallah asubah
Wanke wanke na ke yi ayayin da dai dai kun mutanen gidan mu ke fitowa .

Yanzu kam babu wanda yake kulani sosai a gidan..
su yayu na ma kamar tsine min sukayi ..ai idan mace takai haka a gidan uban ta ba aure to karuwa ce"().

"'yawwwa Gambo ya kamata ki fa hanzarta ki kama hanya maza maza ayi wankan inna dake.
cewar baba babaji.

"toh me gida ummah ta amsa..Nan ta shiga shirin ta tsaf.

Bayan na kammala dumame na rusuna na gaida su" tsaban kallon da baba babaji yake aika min a sace ya sa na kasa cewa komai na daure fuska.

umma duk tana lura da yanayi na amma sam na kasa gaya mata tafiyar tan ne bana so kwata kwata sam hankali na ni bai kwanta ba.

Gashi ya sa ma na ido ko tari umma tayi sai ya amsa"

hakan mukayi rabuwa da kaikayin magana a zucin mu umma ta kama hanyar dindima.

Tun tafiyar ta komai ya sauya Acikin nishadi baba babaji yake, don sosai fuskan sa ya nuna hakan duk dama yana yi yana fuskewa yana shan qamshi..

tunda umma ta tafi ko hutawa banyi ba don tamkar baiwa haka ya maida ni
Yau da safen har wanke masa aswaki da kasar takalmi sai da nayi

"karfe 11 saura ne,sai na dan jinguna kadan ena jiran lokacin makarantar rana yayi,nan naji an kwalla min kira...

gani baba,na shigo na rusuna gaban sa.

je ki bakin kasuwa wajen mai shayi zai baki aika ki kawo min..

Nace toh azuciya naa ina tunani"Tabbb yanzu fa ya ci dumame jibgi guda ko mai zaiyi da aikan mai shayi oho"

Nan na mike ina kokarin ficewa .

Ya dada hade rai Yace saura kuma nazo na kama ki a inda kika saba lafewa kina iskan ci da yan iskan nan marasa tarbiya irin ki,..

madallah ma kinsan yanzu nine aka bar min ke agidan na ko?to ki kiyaye kan ki da ni saratu.

A ladabce nace to ,sai ya juya kansa ya ce
Kuma layin mai goro zakii bi kar ki sake kibi bakin titi kinji na gaya miki kenan.

Gyada kai kawai nayi
Bance uffan ba na sabule nayi waje na kama hanyar kasuwa...

Ina fita Ihu ya sake ya soma rawa yana kirari makan sa adakin shi kadai
" Kiriiiiiii baram bam bam bam bam kaii kai,..sai ni babaji dan gidan goggoji sara dai a hankali.... dawa sai maza,, .. duk wanda yayi jiran tasha dani da shi zamuyi kwanan mota.

Yiiihuhu sai ni babajii dan goggoji yau ango kake tartil babu hafsin.

Kikiki ya fashe da dariyar kuruciyan zuci Mai shake da jahilci da tsananin mugun ta.

hahahaha yarinya yau naki taka kare kwanan ki sai agadon babaji dama chan nagaji da cin durin uwaki...

Ya koma kan gado ya kwanta galala cikin tunani yace"Ga nan rabi bazaura na jira na alayi kwana nan zan yaga ku na auri ta na huta.. Na gaji.

Haba,itama tabi duk ta hanani sakat babu dama nace zan ci nata durin agaban gambo dan nasan munafurcin mata sarai.

Cikin shakekken nishadi yake maganan sa'yanzu duk sai sun gane kuran su.

Ya koma ya dada juyi cikin maganan zuci wanda zai tabbatar maka da ya kullace ummahn ya ke cewa"hnmmmmm Kina wasa dani ne gambo,yo ni me zanyi da saiwar jikin ki da yaya bukar ya gama shanye wa?dama chan dan kuruciyar ki na gani.

dukan ku ai akan tarko na kuke lokacin ku ne yayi,kinga kafin ki dawo daga gaisuwan mutuwar karyan dana miki.

Lokacin har wannan shashashar yar nakin ta san ni waye,

itama da sannu zata haura kan qayar dana daura mata shi yanzu....

kai bari ma na fita saboda naji dadin ganin komai ya tafi min dai dai idan kuwa sageer yamin kuskure nasu ya kare agarin nan.

dariya ce akan fuskan sa ya dau hular sa ya fice hanyar kasuwa.

_FIRST CHAPTER REVIEWS I NEED SOME MOTIVATION_ 🙄🙄, _yana ji na gaji ne_ 🥺

*Follow Wattpad@ SURAYYAHMS*
[2/23, 22:35] ‪+234 802 646 5734‬: .*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }

™/SAT5/ 2019🔞
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒

_A TRUE SENSATIONAL STORY_

~_Story written by_~
*SURAYYAHMS*🔥
*OFFICIALCATTY🐈*

*_WATTPAD_ @SURAYYAHMS_*
@ IG:Surriem-sule_

*#Lovestory2018/19*
*#romance#purefiction*
*#Destiny at fault..*
*Any resemblence of life style or story should be considered as a coencidence"i give no permission for any comparison All my stories are strickly mine,beware copycats!.*

*hmm It seems like the universe has given me soo many special maryams THIS PAGE IS also for this exceptionaly special maryam watoh"MARYAM SANEE(mamuhgee)GOD will bless you for me#ride or die with us#die hard is uz🥰*

*SURATUL HUJURAT*

*2."Wa La Yagtab":* Do not backbite each other. Its a major sin equivalent to eating your dead brother's flesh

_PAGE2_

Umma na da kafa take takowa zuwa tasha don haka ta dau Lokaci sosai don sai wajen karfe 10 na safe ma ta kai kan titi.

anan ma zaman diris tayi tana jiran motan haya koda kuwa akori kura ne ya kaita cikin yankin su inna wuro amma shiru babu wanda ya wulga...

"nikuwa tun da na foce a gidan Tafiya nake sanye da hijabin uniform dina bana kallon kowa.

Gashi dama hankali na ba a kwance yake ba sabida yanayin lungun da baba babaji yace na bi.

wajen shiruuu ne babu mutane sosai,ni kaina Allah Allah nake na samu na fice..

Sai da na kai Daf da bakin gargada naji wani kara kamar an fasa tayar mota sai da na dan razana ,ko samun daman juyi banyi ba naji an shakuro ni ta baya an matse min baki da karfi...

Firgici na shigayi cikin tsainnanen tashin hankali da tsoro ganin sageerr ne a kaina yana faman kokuwa da ni...

Ka sake ni..ka sake ni nace..nan na shiga tsala ihu neman ceto.

Shikam Baice uffan ba ya jawo ni da karfin mallaka yayi wani hanya dani daga nan ban sake sanin meyafaru ba..

Daga bangaren ummah kuwa har yanzu bata yi dacen mota ba, har tagaji da bata lokacin da zaman jira, chan da azahar sai ta tashi ta soma daukar niyyar takawa da kafa kadan kadan zuwa kauyen su inna wuron.
Chapter 3 · 0% Book details