← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 103

Sashe 53

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anan ma dai dai ku ne basu hallara ba kamar irim su baba babaji sabida ya saba da tsanwagwama kuma riga am haramce mishi shiga cikin mutane.

Agents din ta na gefe,ta tsaya ganan kowa cikin jawabin ta ,ta musu nasihan akan mummunan abunda suke aika ta ma kansu na jahilci da cin zarafin nakasa da su.

Sai ta hada da abunda suka mata ita da ummah cikim hikima Tas tasss ta wanke su sai da jikin kowa yayi sanyi,
sannan ta dawo Tana ganin yadda yayun ta suka dawo tsoffi karfi da yaji ga yara gaban su rututu sai ido suke fitarwa tsaban takauci da wahala.

Ta so ta sanar da su itace saratu sai ta tuna da ba ita kadai bace anan da mutane ta zo.
Its her personal life that she wont like to publicise it

So bayan ta gama bayanin ta sanar da sarkii ci cewar nan da wata guda zata sa a zo a dauko duk wanda ta sa sunan su,har da baba babaji..

Da har kamar zata shige mota kawai sai ta fasa tare da ce musu tana zuwa.

Gidan mahaifin ta ta wuce direct, ta same su nan tsakiyar gida ana ta san barka Da ita.

Sun sha mamakim ganin ta amma ji take bazata iya barin garin batare da ta sanar da wani nata cewa ita bace..

Nan suka mata fadan ci
Zuciyar ta kamar zai fidda ruwan hawayen da yake zuba

Amma haka ta daure ta sa aka taro mata kan yan uwan ta da yayun ta a tsakar gida su ya sun su.

Duk sun tsorata sun dauka ko wani sukayi ma musamman

Sai da ta bari kowa ya nitsu sannan ta soma gaya musu asalin itace saratun su..

Kanwar su, yar su.wanda suka tsangwama Suka kora anan kurwala

Cewar ta ya zama dole
Ta sanar da su ita waye tunda jini daya gare su,mahaifin su daya sannan duk da sun guje ta ita tasan duk inda kaje ka dawo hannun ka bazai rube ka cire ka yar ba
.

Cikin tsananin tashin hankli da mamaki kowa ke jin ta har sai da ta gamsar da su eh ita din ce,Masu suma sun suma masu fashe wa da kuka sun fara, a hakama mafi akasarin su sun tsorata matuka

Don haka kowa ya rusuna gaban ta yana neman gafara ta cikin nadamam rayuwa..
Ba a jin na wani.

Da kyar ta lallaba su
Wasu sai boye fuskan su suke ,yau su yaya mati da yaya hamza ke kuka sharbe sharbe agaban ta
Anan suka shiga tambayar ta labarin ummah

Inda ta sanar da su rayuwar su mai shake da cigaba,kwanciyar hankali da jin dadin rayuwa..

Kowa sai da yaji ragowar imanin sa ya motsa
Tabbas wannan alhakin ne ya gauraya musu zaman lpyar sa da kwanciyar hankalin su..

Gashi Allah ya saka ma gambo ya kuma daga saratu,
Sannan ya kaskantar da dukkan wanda suka zalunce su..

Kowa sai da ya bata labarin sa,jikin jimamin nadama
Inna wuro kam tuni Allah ya mata rasuwa

Ganin zata bata lokaci ya sa ta rubuce cheque mai kauri ta bada babban yayan su yaya mati ta kuma masa bayanin yadda zai ciro su ,akan ya raba ma kowa da kowa kudin isasshe tare da musu albishirin ta yafe musu haka ma umman ta.

Anan Duk suka hada baki cikin jin kunya suka ki amsar kudin data rubuce musu,kowa na fadar kaicon sa akan irin bakar wulkanci da tozarcin da suka jefa rayuwar ta aciki

Sosai ta zage tayi kuka sabida bata taba tsammanin nadaman su ya kai haka ba,

Ko a mafarki basu yi tsammanin zasu sake ganin ta ba bare kuma
Har a wannan yanayi

Da kyar da nasiha ta sa suka amince

Bakin cikin su daya shine da suka ga alaman kamar ta yafe sun me amma bazata sake haka zuria da su ba..

Basu so ace ga nasu nan Allah ya daukaka amma
kuma baya tare da su ba..

Amma ganin girman abunda suka mata da kuma saurin yafe musu da daraja su da tayi yasa
Suka mata uzurin haka..

Tsakanin su sa ita sai dai a sunan yan uwan taka but no family attachment.

Sannan ta roki alfarman cewa kar su fada ma kowa itace saratu muddin sun san ba zai rufe bakin sa ba..

Domin bata son hakan yayi sanadiyar kasa samun daman ta zo ta taimake su akan kari..

Tace "Idan da jama'ar gari zasu gane ita ce, nadaman da koke koken zai jawo mata koma baya wajen mance da abubuwan da suka riga suka shude

Haka kowa yayi mata alkwarin,har suka rabu cikin amana da jimamin juna..

A lokacin sai taji wani sanyi na ratsa ta fiye da na koyaushe

Ko da ba ace komai ba yau tayi magana da wanda ya dasa mata bakin ciki a duniyan ta
Yau Dakan sa agaban ta ya fada mata nadaman sa
Ta ga sakayyar Allah kiri kiri atattare da shi..

Sannan maganan da yan uwan ta ya sa ta dada jin sauyin yanayi, a yau ko ma yaya ne tasan mahaifin ta zai yi alfahari sa ita tunda bata watsar da zuriar su ba..

Haka suka kama hanyar airpot

Tana gani jerin yan uwan ta ne agaba wajen mata
Hannu, sai da naciki ma ciki

Sai gani ake suna share kwalla amma ba wanda ya lura da make faruwa
Har si sarahn suka bace

Abun ya matukar girgiza familyn ta don kusan sati gida suka dauka suna jimamin abun

amma Haka suka rike amanar ta ba su fada ma kowa saratu bace sarahn
Haka suka raba kudin tsakanin su cike da sama ta albarka..

A chan abuja kowa rayuwar ta da yazeed ba wani canji yadda suke haka yake tafiya

Tana dai kan missiom din ta na sa shi dole ya baiyana mata sirrin abunda ke tsakanin sa da ita..

Bayan sati biyu a washe garin Ranar talata,

Wani abu ya hada baba babaji da sageer achan bayan gari inda yake nomar sam.

Yunwa ta hana baba babaji zama don haka ya fito yana bin jeji ko zai samu ya dan dauki ko da masara ne a gona ya gasa ya ci

Anan ne sageer din ke masa tijara da zage zage, kamar bai san shi ba.

Har sai da ya tara masa jama'a makil akan sa yana tsine masa

Da kyar yaya hamza ya shiga tsakain rigimar ya kora kowa ya barsu anan su uki

Anan ya shiga musu fada, cewar sa ya lura tun da sarahtu ta bar garin wani mummuman Tashin hankali ke wanzuwa a tsakanin su
Har yau absu shirya ba

Cikin taurin zuciya da bacin rai sageer yace"
Yo ai tsakanin na da wannan bakin azzAlumi sai gaban Allah..

Anan ya shiga sake tonu maganan yadda ya wulakanta sa da uban sa akan filin gida duk akan haka yasa shi ya ma sarahtu sharri ranar ba don san ransa ba..

Sai sa ya sake tuno masa cewa shiyasa mahaifin sa ya yi karya akan saratu duk dama yasan burinsa ne ya aure ta.

Sageer sosai ya rike abun aransa yasan yayinma sarah butulci kuma ya cuce kansa matuka

Tuno da sarahn ya sa baba babaji sake shiga wani hali ga yunwa na mugun cin sa a lokacin..

Haka yaya hamza ya zaunar da su...

Yayi musu dogon nasiha mai shiga rai..

Daga bisani ya sanar da su maganganun sarah
Da dada bayyana musu cewa Sarahn da suje fada akai ma da ta zo

yace matar nam fa saratu ne da suka sani ba wata...

Rike rike aka soma yi da baba babaji zai fada kasa cikin tashin hankali cewarsa a kyale sa zai je wajen ta neman gafara ko Allah zai jikan sa .. Ya sassauta masa daga bakar rayuwar da yake ciki

Da kyar da wahala suka yi convincing dinsa ...

Amma inabSai da ya turje anan suka bashi goyon bayan akan cewa zaije birni ya nemi gafarar saratu tunsa yanzu yasan inda take..

Gani yake idan ta yafe shi shikenan zaiji sauki

Sageer ma yace toh zai bisah sai suje tare.

Yaya hamza kuwa dama so yake su sassauta makan su yafe ma juna gaban shekaru da suke rike ma kansu.

Hakan Kuwa ya faru,yanzun kawai so suke suma su fuskance ta su fadi abun da ke ransu su huta..

Babu wanda ya san da maganan
Baba babaji da sageer suka yi shirin tafiyar lagos

Kwana biyu suka rafka a mota sannan suka iso garin lagos..
#surayyahmz

*Writers note*
_godiya ta musamman ma masoyan surayyahms a duk inda kuke ...Acikin shafukan whatsap mafi akasari naji ana cewa this is the most anoying storyline surayyhams has writen sarah tana bada kowa haushi,well yes gaskiya nima zuciyata na min zafi da takaicin musamman ni da nasan kan labarin gaba daya" amma let me make it clear to you dearies...sometimes we must face the bitter truth to learn the most important lessons in life,this story has already happen in reality arond 2012,..99.9% of our girls are going throu so much in hands of this cassinovas,heartgamblers,deceivers,sai nake ganin wanda yawancin suke korafin sakarcin sarah inda da qaddarar ta zai sauka akan wata sai taga tayi abunda yafi nata sabida samarin shaho fa sunyi kama ne amma ba dai dai yake da mayaudari ba,shi baiya aikin sa da garaje dole sai ya gina foundation dinsa mai karfi a zuciyar mace inda bazata taba gane kalar sa ba,most of the men appear so smart and perfect yadda komin ilimi, tarbiya,wayewa ,iko da kyaun mace da kyar take fita a tarkon su"so i urge my beautiful followers and readers to forget about who is right or wrong in this story my main motive is to let you know,so take the lessons analyse them into ur daily lives if possible.. daganan sai ka san yadda zaka sa kafan ka idan irin haka ta fado maka.........writers note continued in next page27_

Ofical cat
[2/24, 07:17] ‪+234 802 646 5734‬: *🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

27
Chapter 53 · 0% Book details