← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 103

Sashe 12

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anan ne data iso gidan tayi wanka ta kintsa kanta ta biya sallolin ta ta dada kai kukan ta wajen Allah..duk dama zuciyan is full of hatred and bitterness

Sahura da dan aikan ta kuwa ba karamin Mamakin yadda umma ta samo kudi da wuri suka ji ba

Dan haka sahura ta qudiri niyyar sa ma umma ido ko zata san ya take yi jiya jiya ace ta zo kano ,kanon ma bayan gari amma har ta san yadda zatayi shige da fice ta samu kudi mai yawa..

Ranar Ummah ko bacci batayi ba Washe gari da safe
Ta mike ta shirya,
Sallama tayi ma sahura tace ni zanje asibiti..

Sahurah Tace ma ummah insha Allah zata zo itama taga jikin Nawa..
Duk dai ko zata gane wani abu game da ummah amma shiru

Nikuma tun misalim karfe 4 saura na bude ido na warau na ke jina sai dai kananan ciwon ciki da dan jini da nake yi ba sosai ba..

Koda ummah ta ganni a haka ba karamin kuka da godiyan Allah tayi azuciyan ta ba, amma sai ta kasa furta komai sai sannu sannnu take min..

Na dauka duk tausayi na ne amma gaba daya sai na soma gane cewa ummah na fama da wani bakin ciki ma musamman a yau din.

_Share_

*WATTPAD VOTE AND FOLLOW @SURAYYAHMS*

*OFFICIALCATTY🐈*
[2/23, 23:02] ‪+234 802 646 5734‬: *🅱BRILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*
🐈

_PAGE6_

Kallo na bi ummah da shi a nitse tsawon mintinu na 10 amma kamar bata ma sani ba
Duk ta bi tayi tagumi ta bata shiru cikin tunani...

Nace ummah,ummah,
A nan ta dago a dan fakaice tana goge siririn hawayen ta da ta dade tana boye wa bata iya cewa komai ba

Murya na na rawa Nace ummah lpya kuwa ?

Ummah dan Allah kar kisa komai a ranki ki dena zubar min da wannan hawayen naki
..duk da duniya ya juya mana baya bazan rusuna wajen ganin farin ciki a fuskan ki ba..

Ummah nayi alkawari kuma na dauki alwashi duk inda halak yake zan nemo shi don na sa ki farin ciki a duniya
...ummah dan Allah ki dena kuka
Anan nima kukan ya kufce min na kife kai na ina yi.....

Musamman gani danayi maganan dana ke yana dada sa ummah na shiga wani irin halin tsumayi da rudewar tunani....

Ita kam dai tana shiru
A hakan ta daure ta shiga share hawayen ta a hankali ta dawo daf da ni ta kamo hannu na...
Tace"Saratu, kiyi hakuri saratu ki yafe ni...bawai na daga hankali na bane akan rayuwa abubuwan duniya ne kawai suke bani mamaki,rayuwa da ciwo sarahtu .sai dai duk da haka insha Allahu bazan dena kula da ke ba... duka duka ke kadai nake da shi a duniyan nan, kece abun alfahari na...nan tayi ajiyan zuciya tace
Allah ya baki lpya saratu
Kar ki damu dani kinji? Duk zan warware

Cikin sheshheka na dago zan yi magana ta sake min wani murmushi mai tarin nauyin zuciya tace in har farin ciki zaki bani ki daure ki cire komai aran ki saratu, ki dauka wannnan ba yin mu bane ba son ran mu bane,qaddar mu ne. Amma tunda yanzu mun samu kan mu tunanin abunda zamu yi mu tada rayuwar mu kawai zamuyi nan gaba.kinji?

Ba yadda na iya haka Na gyada kai da kyar ina kuka mai dauke da tarin takaici ,shiru ne ya ratsa wajen ummah ta shiga shafa ni gently tana bani karfin gwiwa batare da tace komai ba..

Haka nayi kwana anan gadon asibiti sai da na dan warke sarai sannan aka sallame mu

Ba laifi dukan mu muka soma sawa ranmu ruwan sanyi musamman fannin kau da nadama da koke koke duk muka bada hankali wajen nema makan mu mafita arayuwa ,ummah bata so na kawo wani magana game da komai sai na warke amma kowa da nashi a zuciyan sa kullum sai na saka na warware.

Cikin kwanakin anty sahura ita kadai take zuwa dakin mu wani bin tare da yaron nan daya taimaka ma ummah na.

kamar dai dukan su tausayin mu suke ji sosai duk dama ita bata wani nuna mana akan fuskan ta ..

Har aka sallame mu muka dawo gidan
Anan ne zamantake wa tsakanin mu da anty sahura ya dan fara samun fahimta..

don yanzu har akan gaisa a mutunce wani bin har abinci takan kawo min tace naci
Gashi ta bani rifa da skirt ummah na ta bata zani ya zamto muna sa wanda zamu na sauyawa

Hakan muke zaman mu a bariki zaman fadi tashi, Sai dai yanzu ummah na ke bada matsala

kullum sai naga ta bace shiruuu ta zurma kanta cikin wani irin yanayin kunci da tunani amma ko da na tambaye ta sai tace babu komai...tana lissafin rayuwar mu ne kawai..

Bayan wata guda lokacin har na mike tarwal jiki na ya dada bayyana wani sirrin girma kadan sabida abubuwan da suka faru dani har nonowa da kugu na suka dan taso sosai ba yabo ba fallasa ban rame ba..
Hasken fata na ne kawai ya rago.

Babban damuwa ko ince baban matsalar mu baki daya da ni da anty sahura shine ummah..

don kuwa sosai abun umman ta keyin gaba gaba shiru shirun umma ya soma daga mana hankali..

Gashi kullum a buga buga take neman kudi bata zama amma ko da ta tafi a kullum in banda zallan wulakanci da takaici babu abunda take karba wajen mutane

Munyi fama da Rashin sa'a kamar wanda aka mana mumumman baki Cikin kwanaki da abubuwa suka tsanan ta har anty sahura ta yafe mana biyan kudin dakin da muke ciki"
Tace kawai mu zauna anan din batare da wani fargaba ba sai dai dakin namu babu ko wutar lantarki,dama daga tabarma ne sai dan tsumman kayan mu da baifi kala biyu ba

Ni kaina da na fara tunanin ko tsaban yadda ummah take cin karo da mummuman rashin sa'a da takaicin mutanen birni ya ke sa ta wani yanayi amma sam abun yaki zama sosai araina..

Nasan Dole akwai babban abunda ke cinta a rai amma taki sam ta fada mana daga ni har anty sahura..

Ana cikin wannan yanayin matsin wata
Ranar da yamma bayan ummah ta fita nima mana abun sawa a baki, Sahura ne zaune akan dakalin kofar dakin ta tana gyaran farcen ta sai ga umman ta dawo

Fuska ba yabo ba fallasa Tace sannu da dawowa gambo,

Ummah ta sauke murmushin gajiya da tunani tace yawwa mutan gidan ne a tsakar gida
Nan Ta karaso ta dan zauna kusa da ita..

Murmushi suka maida ma juna as usual sahuran ta ce yau kuma me aka samo?

Tare da sauke ajiyan zuciya ummah tace ,hmmm bari kawai ni abun ma ya soma isana akwai wahala anan sannan har yanzu ba abunda na tara na azo agani...ace kai kenan sai dai ka samu na cin yau na gobe sai ka sake fita? Kai ni dai kullum ina fada rayuwar birni babu abun gani aciki sai tarin wahala..a gajiye take maganan kamar ba ita ba

Sahura Ta tabe tace ai ke ki kaga dama gambo, na sha gaya miki ki kyale yarinyar nan taje ta nema muku wani abun ko dan aikatau din na bazata rasa ba ,gata da kyaun fuska da kuruciya ba mai ki ya bata aiki,amma kina nan tsofe tsofe kin nace saam kin sa wahala ma kanki ga yarinya tana so ta taimake ki amma kinki...

Jin sahura ta fadi hakan yasa sai da taji wani iri aranta
'Hmmmm ummah ta sauke ajiyan zuciya.. abubuwan dayawa ke dawo mata arai

Tace sahura kenan,duk abunda nake gujewa kenan amma baki gani,wallhy bazan taba yarda yata ta fice cikin gari nan ba kam sai dai nayi ta wahalan har duniya ta nade..
Allah ya kiyaye ...uhm uhm

"Nan ran sahura ya dan soma baci she juzt wonder how adamant one can be bayan ga uban wahalar data ke sha,

Tace ni fa ban ma gane miki ba ne kwata kwata gambo,ke kince baki tare da mijin ki, to na yarkin fa? Ko shima baya tare da ita ne?...to wai mijin yarkin ne kike tsoron sa da baki so taje ta nemi na kanta ta rufa muku asiri ke ki dan huta,? Shi din ina yake da zai dau nauyi ba ya barki da wahala wai shin wani rin rabuwa suka yi ne? Wannan wani irin rayuwar wahal dakai ne kike yi ne gambo?

Ummah tayi shiru tana mamakin ta yadda anty sahura ta dau abun da zafi

bisa ga dukkan alamu Sun gaji ne da damuwa da yadda take wahalar dakantan ba dare ba rana ni kuma ina zaune a gidan bana komai..

Ummah ta dan murmusa tace haba haj sahura, miyayi zafi haka?

Ke dai ki bar wannan maganan ni na daukar ma kaina hakan kuma zan cigaba da nema har na dace,maganan yata kuma wannan ai rayuwar mu ce ke dai ki ci gaba da taya mu da addu'a kamar yadda aka saba..

A fusace sahura ta mike tsaye tace bazan taya ba, haba ke kuwa baiwar Allah
Ke yanzu a kwana biyun nan da muke zama daku wani irin yarda ne ban gwada miki ba? Ko ce miki akayi a irin halin da na tsince ku akwai wanda zai bari ku zauna masa agida ne baisan ku bai san asalin ku ba amma wai har ina baki shawara kina ki?

Toh wallhy in har irin wannan zaman da zakiyi dani kenan ki tattara ina ki inaki ki bar mani gida...

Anan hankalin ummah ya tashi don bata dauki abun yayi tsamari har haka ba ga sahura sai dada hawan diri take ta shake fuskan ta sosai..

Ummahh zatayi magana sahura tace, kinga baiwar Allah ki tafi kawai ni nafasa zama da ku kuje chan na fasa karban ko sisin ku ma na yafe kuje kawai ..
Chapter 12 · 0% Book details