← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 103

Sashe 55

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya dade yana kawo tots daga bisani yace ma su baba babaji,
Kar su daga hnkalin su,
Shi yasan yadda zai yi suga sarah amma su daure su bashi zuwa gobe,
Godiya sukayi ta masa sai dai hankalin sa bai ya wajen su,
Tunanin kawai yake yi kala kala akan sirrin rayuwar saratu daya dan ji yqnzu...
Now he knows where her abject inspiration to help the needy is coming from.

Babu shakkka jajircewar saratu ya samo asali ne daga ciwon qaddarar ta dake makale a zuciyan ta..

But this is not the end yana so yaji ya akayi ta cimma burin ta har tayi,ilimi da kudi haka..

according to baba babaji cewa yayi da ya fara nadama ya shiga neman su a da chan ance masa sun tafi birni a motar kano.

Kenan a kano saratu da ummah suka yi kudi?a kauyan cin nasu??,damn but they r oll women...thy r suppose to be weak,inma ba haka ba ai zai yi wuya ace mace ta shiga wannan halin sannan ta mance da shi so easily har ta tashi ta daga rayuwar ta..

Sai ya sa aransa dole sai yaji sauran kwaf kwaf din sannan ya samu nitsuwa

A daren daya koma gida sai ya tura makudan kudi ma wani mai suna zulkhi cewar sa ya hau jirgi ya taho su hadu gobe a gidan sa.

Anan su baba babaji suka kwana,

Washe gari da sassafe yazeed ya kawo wani agents dinsa ya hada su tare yace akai su ga saratu..

Daga nan shi kuma ya wuce wajen zulkhi bai bari ma sarah ta san da shi ba..

Anan ta karbe su ba yabo ba fallsa ta kaisu wani wajen daban suka samu zama.

Kamar a mafarki suke ganin realityn su,ita kuwa bata boye musu ba ta fada musu itace din,..

Duk dama ta sha mamakin ganin su amma sai bata nuna ba,..

Anan duk suka dada warware mata duk munafurcin Da suka mata cike da nadama da neman yafiya
Suka roke ta don ta yafe musu..

Dukan su kuka suke yi har da ita don Tasan za'ayi hakan ya sa ta sa suka bar office din gaba daya suka je wani waje.

Bayan sun fahince juna ta kaisu gida har wajen ummah,anan ma suka nemi gafarar ta.

Dan itakam ummah addini yanzu ya shige ta sosai halayen ta ko da ba ace ba kasan imani ya ratsa zuciyan ta ya mamaye shi..

Duk da bata iya hade baqi ba,takan zauna ta kunna karatun qur'ani tana ji yana mata dadi sosai.

Tsaban naci har ta haddace wasu surorin cikin sauki ta haka.

Kuma zata iya daukar fiye da awa 4 tana kallon wa'azin malaman nan bata gaji ba.

Gashi dama da saratu ta samu cin gaban rayuwa sai ta rage mata zuwa aikin ta, yanzu haka managers din ta ke lura mata da gidan gonan ta da gidan kajin ta.

Su baba babaji A duk yadda suke ganin saratu tayi musu karamci bai kai yadda suka ga ni wajen ummah ba,don sosai ta mance da komai sai ma nasiha mai shiga rai data yi musu..

Haduwan su da ummah ya dada zafafa zafin nadaman da baba babaji keji aran sa....lallai ya kasance hasararre ya kaskatar da rayuwar gambo amma Allah ya nuna masa cewa gambo ce mai nasara tun a duniya.

Kwana biyu suka yi anan gidan su saratu cike da goma na alheri suka koma gida...

Sarah ke tabbatar masa da cewa idan sati biyun ya cika zata sa a dawo da su a fara masa jinya...

Tsaban dadin yanayin da suka samu yafiya cikin sauki ya sa suka mance da yazeed don haka basu ko fada ma sarah cewar sun hadu da shi ba har aka rabu

Ita kam dama yanan nade a zuciyan ta amma kwana biyu data ga kamar ya share ta ya sa ta dan bada hankalin ta wajen ayyukan dake gaban ta

Amma yau da su baba babaji suka tafi

Tana Dawowa sai ta wuce straight offishin sa ko zata lallaba sa taji meye matsalan ,

Amma da mamakin ta sai ta ga offishin sa a
kulle
Ta sake kiran layin sa shiru shi ba off ba shi ba ringing ba.

Ko da ta tambaye farida secteryn sa ce mata akayi
Kwana biyu sukan su ba su gansa ba kuma basu san inda yake ba.

*Writers coments continued*
_samarin shaho is also to ladies that have everything in life but give less important to their god,sarah na daya daga cikin wanda suka mance da wani muhimmin bangare na rayuwa...misali, Ku dubi yadda sarah take mance da yin sallah akan lokaci idan suna tare da yazeed,ku fada min meyasa hakan bazai faru da ita ba?...yan mata ku tsaya ku kalle rayuwar sarah nan gaba... its very important...."kenan dan wani mummunan qaddara ya faru da kai arayuwa sai ka sa burinsa agaban ka fiye da komai har kula da ubangijn ka?toh wa zai taimake ka akan mugayen maza kamar samarin shaho?wayon ka ko ilimin ka?..,Kuma ina kira da kar kuyi ma labarin hanzari ku dan sassauta min i want to give more pages,nasan labarin baida dadi sosai amma sakon dake ciki is kind of more realistic than fictional#relax fans im also with you on this#sakallahu khairan,wah saka biljannat awaiting ur heartouching coments always😍_

*Official cat*
[2/24, 08:55] ‪+234 802 646 5734‬: *🅱RILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

_28.._

Abun bai daga mata hankali sosai ba, sabida tasan maybe yar fushin nan Ne daya saba idan bata bashi attention dinsa ba,..

Hakan ya sa ta koma bakin aikin ta tana yi tana gwada layin sa amma babu wani sauyi,

Haka har ta tashi daga aiki ta koma gida bata ji shi ba.

A chan bangaren yazeed kowa haduwar su da zulkhi ya sa ya tambaye sa yadda za'ayi su samu tarihin sarah da mahaifiyar ta a garin kano shekaru da suka wuce.

Ya nuna masa hotunan sarah da na ummahn ta,

Sannan ya bashi dan detail din da ya samo daga binciken sa akan ummah da shekarun da ummah ta zo lagos.

Toh shi zulkhi shiya binciko musu cewa ai gidan kaji da gidan gonan da umma ta mallaka na shahararren Mai kudin nan ne alhaji abdul azeez shayal...

Daga nan yazeed ya sha dammara suka wuce kano ba bu wanda ya sani,suka shiga neman diddigin labarin ummah dana saratu..

Da kyar da wahala suke samun bayani daya sabida rayuwar su sunyi shi ne a cikin sirri wanda akalla sahura ce kawai ta san komai..

Amma da shike abubuwan mamaki da yawa sun faru, a ko yaushe idan wani sirrin ya fito sai ya dada sa ma yazeed din son yaji karshen bayanin..

Yanzu haka har kudi ya biya ana nema masa inda zaiji gaskiyan lamarin rayuwar su.

Anan kuma lagos sarah day by day tana shiga tashin hankalin rashin samun yazeed

Tunani dayawa ta kawo aranta nacewa ina zai je wanda har iyayen sa basa zu sani ba

Don ta tambayi kowa har gidan sa taje amma shiru babu shi ba labarin sa

Gashi yau ya cika wata guda chasss bai dawo ba.

Shikuwa da sannin sa yake yin haka ,so yake ya kwaba mata lissafi
Don shika dai yasan me ya ke shirya mata one big time...

Haka ta lalace da tunanin sa, bata iya cin abinci sosai bare bacci,

Saukin abun ma shine yanzu hapsy ta dawo nan branch din ta..

Ita kanta hapsy tausayin sarahn ke damun ta
A ko taushe da duba wayar ta sai taga dialled calls din yazeed yafi a kirga

Har ta gaji ta sa ta gaba tace,sarah dan Allah ki sassauta makan ki mana,
Ai inda ya damu dake bazai bace miki rana guda kiyi ta neman sa baki same sa ba..

Please this is getting too much baki ganin yadda kika dawo ko?

Abun na damun ta sosai duk dama kullum idan hapsy ta kawo magana bata tankawa yau kam sai taji dole ta sawwake ma zuciyan ta ko zata samu saukin zafin da yake mata.

Tace hapsy wallhy na kasa ne,kaina ya daure
I just cant hepl it na shaku da shi sosai...sai ta dan fara sauke hawaye..

Hapsy na shiru itama din tunani take yi,chan ta taso ta zo kusa da ita ta dafa ta
Sarah"?
Dago ki kalle ni,

A hankali ta dago.

Tace kina son yazeed ko?

Wasu hawayen ne suka taro mata lokaci guda tace eh hapsat ,ena son shi..kuma nasan shima yana so na
But we dint make it official

Hapsat tace ohhh crab .. now thats your problem,ya za'ayi ku rinka azabtar da kanku haka? Wai shin baku aminta da son dakuke ma wa juna bane ko yaudarar kanku kuke da bazaku furta shi ba?

Idan dukan baku bar wannan wasan banzan ba fa zaku yi illah ma zuciyoyin ku.

Cikin kuka ta ce to ni ya zanyi hapsy,nice zan ce ina son shi ya aure ni,ko shi zai fara fada min haka.?

I just dont get him...kinsan kuwa ranar da na vata masa rai ma haka nayi ta neman sa ban same sa sai daga baya ya zo yana gaya min wai bazai iya jure rashina kusa da shi ba ne"

I think don ban samu time dinsa sosai kwana biyun nan ba yasa ya tafi ya barni,this is tooo much for me
Yau kusan wata kenan Ban sake ganin sa..
Im feeling the pain i love him sooo much..

Kuka ta keyi sosai har da kife kanta akan teber gwanin tausayi..

Itakan ta hapsy yanzu tana cikin rudani

To wannan wani irin salon soyayya ne sarah ta dauka makanta..

Nan dai ta shiga rarrashin sarahn tana bata baki har ta nitsu tare da bata karfin gwiwar cewa tabbas akwai babban dalilin da yasa yazeeed yayi haka

Idan kuma ta yadda da yana son ta tayi hakuri ta bashi dama.

A cewar hapsyn maybe yana cahn yana shirya rayuwar su ne yadda idan ya dawo sai taga komai ya wuce..

da haka ta samu gwarun gwiwa
Chapter 55 · 0% Book details