← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 103

Sashe 13

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta juya a fusace zata bar wajen cikin rudani ummah ta riko ta " haba sahura yanzu akan wanannan maganan shine zaki ce haka dan Allah ki rufa mana asiri kiyi hakuri sahura..wallhy na yarda kin mana mutunci kinyi mana adalci fiye da yadda nazo na tarar da garin nan

Nan mah ta dan fashe da kuka, tace bansan ya zanyi bane sahura bazan taba barin yata ta fita cikin irin wayannan mutanen ba ,basu da tarbiya basu da imani gwara ni ayi ta cutar da ni da na kai yata ga halaka,..Allah ya isa tsakani na da duk wanda ya cuce ni...ta dada fashe wa da kuka mai taba zuciya...

"Ni kuma ina chan daki Da shike ana dan taba sanyi Bacci nake yi sosai tun bayan dan hirar da na taya anty sahuran so bana jin komai daga abinda suke fada.

Sahura na shiru tana jin kukan da ummah ta gurfana tana yi, a hankali ta dago ta tace haba wa gambo na san akwai
Dalilin da ya sa kike haka, nifa kika zo kika samu anan garin kuma ma abariki gidan shege da shegiya, ki dube ni da kyau nafi ki sanin halin rayuwa anan

Sai dai ban sha mamaki don kin ki ki gaya min asalin damuwar ki ba dama chan zaman duhu muke kin kasa gaya min komai akanki bare yarki. toh shikenan rike abun ki, gani gaki anan kowa zai gane ma idanun sa..sai dai ki sani duk randa tayi tsami dole zanji,kaiwa nan ta kama hanya ta shige dakin ta.

Anan ummah ta zauna tana jan hawaye,
Tana tuno da yadda cikin kwana kalilan sahura ta karbe su hannu bibbiyu cikin aminci da sauyawar hali,....

amma sam bata da burin tona sirin ta ma wani bare gane take bata yarda da kowa ba yanzun..
kuma gani take kamar in ta tada za'a tsangeme ni ko makamancin haka

Amma ganin yanayin Sahura dazin ya sa tayi tunani" wai shin meyasa ta damu dani haka ? Wai daman akwai masu tausayin mutum har haka ne anan?
Ko dan ni ma mace ce kamar ta ummah tayi tunani cikin nazari mai zurfi..

Bayan nan ta tashi ta shige daki, ta daga ni as usual labarin daya ne babu abunda ya sauya dan abunda ta kalato muka samu muka ci.

Bayan sallahr ishai muna dan hira sa ita mama sai na lura ummah bata cikin hankalin ta kawai jina take ina ta faman surutu, har sai wajen goma saura na kishingide kan tabarma nayi bacci na..

Bayan nan Ummah Waje ta fito,tasan tunda har yanzu akwai haske a dakin sahura to batayi bacci ba kenan tare da sauke ajiyan zuciya ta kama hanyar dakin sahurar....

Wajen shiru sai takun ta tunanin hukuncin data dauka aranta take yi anya abun da zanyi dai dai ne ?wani zuciyan sai yace mata muddin kina so ki cigaba da rayuwar ki dana yarki dole sai kin fuskanci kalubalen ki kin kuma sa wa ranki zaki iya da komai don cimma burin ki ..

Anan ta yi salam bakin kofa kusan minti 2 sannan sahura tace shigo daga ciki....

"Baki bude ummah ke binta da ido ganin yanayin Da ta same ta, bata iya daurewa ba tace
Sahurah? Me nake gani haka? dama kema kina shan wayannan abubuwan ne, tayi nuni da kwalaben codine da totulin akasa an sha guda da alaman zata bude dayan ne..

Sahura na shiru kuma bata sake hada ido da ummah ba, har sai da umma ta zo ta gaban ta suka fuskan ci juna "

kafin umma tace zatayi mata magana kuka ne ya dan subuce ma sahura mai sanyi da ban mamaki...

Cikin rashin fahimta da rudani ummah ,ta zaunar da ita ta shiga rarrashin ta hade da mata wa'azin a nitse cewar bata taba tsammanin Tana shan kayan kwalba ba?
Meye damuwar ta?

Sahura dake jimami ta dau lokaci tana jan shessheka kamar wata sabuwar amarya
,hankalin umma duk ya bi ya tashi ta cigaba da lallabata tana tambayar ta..anan sahura ta dube ummah tace babu komai kawai na tuno da duniya ne....
Cikin damuwa ummah tace habawa sahura, yanzu abunda zaki ce kenan ko dan nima abunda nake fada kenan zaki rama?

Ta ce ko kadan, kawai abubuwan ne dole wata rana zaka ga wasu wayanda zasu tuna maka da naka rayuwar kuma zai maka zafi..

Ummah tace haka ne shiyass nima na zo nan
Dan nagaya miki wacece ni, na yarda da amincin ki sahura kuma na yadda cewa bazan taba iya komai da kaina ba gani ba ilimi ga kauyanci babu kuma wanda na sani anan mai hali nagari na tausayi in ba ke ba

Sahura ta dago a sanyaye ta dube ummah tace ai ciwon ya mace na ya mace ne gambo,kar ki ga wai farkon zuwan ku ban sake muku ba.amma ni tun da na ganki jiki na ya bani kina cikin wani hali bazan boye miki ba ina tausaya miki sosai ,,,

anan ma kukan ya sake kufce mata cikin shessheka ta kuma cewa kuma kinsan Allah a duk sanda na ganku sai na ji kamar kuna tuno min da kaina ne da kuma halin da na shiga ciki a rayuwa adan wani lokaci...

Wannan abun shi yasa na kan sha wannan abun don na samu sauki arai na..

Ummah tace Allah sarki, sahura har akwai damuwar da tafi nawa kenan wanda har zai sa ki cutar da kanki ?

nifa a inda na fito wallhy shan kayan kwalba tamkar zunubi ne babba...
kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki komai na duniya mai wuce wa ne..
Baga shi yanzu kina zaman ki asiri a rufe ba

Anan ajiyan zuciya sahura tayi tace haka ne,
Don dai baki san wacece ni bane gambo, ko kina ganin akwai kwanciyar hankali ga wance ke zaune da tsinuwar iyayen ta ne?

Wani rasss ummah taji...sahura tace
Ni din na ma da kike gani daga kauye na fito, kuma ba wani karatu nayi ba,ina aji na uku a secndry aka min Auren dole bayan fyaden gangami da wasu yan shaye shaye suka min wajen tallar abinci da umma na ke daura min a tashan garin mu kowani yamma ..

Naki auren nan amma sam suka turje sai na aure shi, cewar su ai babban mutum ne ga shi da dukiya da rufin asiri.. yaya na harda min wa'azi akan na amince Ni dama Sam sam banyi karatun allon nan ba haka na amince da su..

"Gambo, nayi hakuri na zauna da miji na ..sabida ba yadda bai nuna amanan sa wa iyayen mu ba ,amma daga bisa ni kadai nasan azaban da na sha hannun sa...

Nan Ta bude ma ummah gadon Bayan ta wanda ke dauke da layi layi bakake da wasu patches suma sun dishe sunyi manyan tabo tace har yau bazan manta yadda mijina ke duka na ba, ya zage ni ya ci mutunci na,kuma yayi min gorin cewar sa ai ya sayi bakin iyaye na sun bada ni a banza...

Cikin tsananin mamaki da magiya ummah tace shine baki kai karar sa ba kin ga jikin ki kuwa sahura?

Cikin kuka tace,wani kara kuwa gambo? Ai gaskiyan shi ne basu ganin laifin sa don yana basu kudi yana musu alheri yana nuna musu ina zaman lpya da kishiyoyi na...

shiyasa kuma kullum idan na kai magana sabanin haka a gida ake ci min mutunci sosai wata rana ma har a korana ni da duka..haka nayi ta zaman kunci gashi yana da mata har biyu nice na uku

Ke Ban tashi ganin zan mutu a hannun sa ba sai da Allah ya bani ciki,miji na yayii bakin ciki sosai da na gaya maza, kuma nasha duka wajen sa har sai da na kasa tashi..

fitar sa yaje ya karbo min maganin zubda ciki ban ma san da ga ina ya samo ba kina gani kinsan ba mai kyau bane..ya jika a ruwa yace maza na shanye tasss a gaban sa ko ya kashe ni...
Wallhy baida imani gambo, haka na sha nayi ta ruwan jini anan kasa a daki na tsawon lokaci sai dai ya zo ya wuce ya barni rai na a hannun Allah,gashi matan sa basu isa su zo kusa dani ba ya hana kowa motsawa..

Washe gari Ban tashi ganin kaina ba sai akan gadon Asibiti kawata ce aminiya ta ita batayi aure ba ma itace ta kaini asibitin anan na kwana ana duba ni ..

"dana farfado da danyen jiki na na lallaba na taso na wuce gidan mu,Ko da naje da maganan nan mijina ya gama kulle nashi,kuma bayan sa suka bi sosai suka kuma tsane ni.

Ko magana ba abari nayi ba aka shiga min fada babu wanda yake so ya saurare ni ,kawu na har da min dan banzan duka cewar sa na tona musu asiri...

Duk na lura da su kowa na fadan ne da son zuciyan sa,su baba su kawu duk dan abunda suke ci ne a karkashin miji na na arziki basu so ya rabu da ni

Dana tabbatar da hakan Nima sai nayi zuciya nace bana son aure na tada bori na haukace har sai da na tunzira miji na ya sake ni a gaban kowa da kowa

Su ummah da su baba Haka Suka taru akaina suka ce na bada hakuri a sasan ta nace sam sam na kuma turje nayi zuciyan maza..

..wannan kuskukern ya sa uwata da ubana suka yi Allah ya tsine dani ..

Nayi nadama gambo amma raina ne ya baci ina ji ina gani da kuruciya ta amma zuciya ta ta soma kangare wa da rashin imani...

nasan idan na koma aure na miji na kashe ni zaiyi kuma bazai dame su ba don ba su san wani hali nake ciki ba.

tun daga ranar kowa ni abu marar kyau ya same shi sai ya laka min alhaki

Bakar Tsangwama da mummunan tsana daga iyaye da dangi ya sa na bi shawaran zuciya na na fito duniya har kika ganni anan...

Yau shekara na kusan 15 kenan Da barin gida kuma nasan ba mai sake karba na ko da na koma
Chapter 13 · 0% Book details