← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 103

Sashe 44

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai ya zamto Duk dama an sa mata tsaro mai tsanani sai take jin tana so ta kasance da shi a wannan halin daya tsinci kansa..

So washe gari da safe, ta kira su hjya billy wanda suka tabbatar mata da cewa yazeed din is fine hannun sa ne kawai ya gurde amma har ma ya tashi yana magana..

Jin hakan ya sa hankalin ta ya dan kwanta, sai ta shirya tsaf sabida yau babban rana ne, ga media da sauran jounalist duk sun taho domim jin asalin musababbin tashin hankalin..

Mrs ruth da hjy asma a matukar tsorace suke amma sai suke nuna damuwar su fiye da kowa..

Indian team da sauran manyan dake gefe gefe duk an hadu waje daya ana jajan tawa sai dai ba wanda ya kaisu gane gaskiyan sarah a yanzu .

Lokacii guda aka fara inveztigating din gardi da sauran wanda case din ya shafa amma sukan su basu da masaniya akn duk wannan so ba asamu komai ba.

Karfe 9 saura sarahn ta iso asibitin shikan sa sai dayaga tausayin sa boro boro a face din ta duk dama Presnce din safeenah ya hana su sakewa suyi magana

Shi ya bata karfin gwiwar taje suyo shariar ayi hukunci ma mai laifi..

Sannan ta wuce taje, anan aka warware magana tsaff wannan karon da shike akwai media sai abun ya dawo wani gagarumin eventz

Ya kuma zamto tamkar kwaryar qiiira da izinah mai girma ma ire iren su gardi da baba babaji dake kauyuka da birni akan halaye irin nasu..

Ranar ne ranar da rayuwan sarah ta fara hawa wani madaka tan nasarah.

Maimakon ranar ya zamto karshen daukakan ta sai ya zamto wani babban matashin daukakar ta.

Ta samo yabon kwarewa
Da cikakken yarda daga duka manyan officials din wanda ya jawo aka bata rank dai dai dana yazeed..

Abunda bai taba faruwa ba a tarihirin org din.

Don sai da ake warware maganan ake ganewa cewa duk an kulla shirin ne don kar sarah ta samu damar wanzar da adalci ma dije.
Amma kashhh ba asamu criminals din ba

Cece kuce da sa bakin mutane da dama ahakan ya jawo mata wani sabon daraja a idon duniya

cewar babban president na human right and woman affairs na india sarah ta cancanci award of honour bisa ga jajircewa akan wanzar da gaskiya da bin hakkin dan adam.....

Haka aka baza ta a media,news papers da social netwks

Dayawar jama'a ann suke fadin albarkacin bakin su sannan mugayen ayyuka
Sai dada bude su ake ana kawo musu..

Tunda sarah ta gama case din dije succesfully sai ya hankalin ta ya dawo wajen yazeeed baki daya..
Har yanzi tana ji kamar she owed him alot..

Cikin ranta ji take dama ita ce safeenah don ta samu damar biyar sa abubuwan da ya mata ta hanyar kasancewa da shi a wannan time din dayake bukatar kula..

Yau sati guda kenan, amma yana gida bai zuwa office sabida daurin dake hannun sa.

Jifa jifa take kiran sa, a duk safiya ko in ta tashi takan je ta gaishe sa..

Yanzu da shike tana nuna kulawa ta akansa sosai sai abun ya nuna kamar suna matukar kaunar juna a idon safeenah ba wai ba.

Hakan yasa take sa musu ido idan sarah ta zo bata bari suyi hira mai nisa sai ta fara daure fuska tana sa shi baccin dole..

Daga nan bangaren su hajya asma kuma tunda aka kara ma sarah matakalar da tayi musu nisan da zasu tsayar mata yasa suka hakura na lokaci suka zuba ma sarautar Allah ido..

Cewar mrs ruth kamar duk abunda suka yi ma sarah na mugun ta juyawa yake ya zamto mata wani babban alkhairi so tunda sunyi wannan sun sha da kyar su hakura haka su jira wani opputurnity..

Yanzu sarah bata under control din su ,itama kenan zata iya sa'in sa da su tun da matsayin ta dai dai yake da yazeed.

Saukin lamarin ma da yazeed yaki cewa komai,sam sam ya ki nuna cewa ya gane wanda suke bin sarah bare aja case.

Shi dai yanzu target dinsa sarahn ce,game dinsa kawai yake shirin murdawa musamman yanzu dayake da special place a rayuwar ta..

A na cikin wannnan yanayi, komai ya lafa amma yazeed baya daga hannun sa sosai duk da an warware masa bandage din

Yau ake neman cika wata uku da faruwan al'amarin

A bangaren sarah kuwa cikin dan wannan lokaci tauraron ta ya dada hasken da sai da ta zama mace daya da ake kirga ta acikin organisation...

Sai aka dena jin kan su mrs ruth da hjya asma
Shiruuu tamkar basu nan haka suke...

Yanzun bakin cikin su bai wuce yadda Sosai mutane suke yin sarah ba ko wani lungu da sako farin jinin ta ya gauraya zukatan mabukata..

Hankalin ummah a kwance yake sabida haka ta yi dammarah zuwan chan gida mai tsarki don neman cikakken taimako da nuna godiya ma ubangiji da yadda ya cika musu rayuwar su ya kuma dawo da su mutane.

Soyyyar tsakanin ummah da sarah yayi karfin da ko guguwar ajali basu tsammanin zai raba su ta dadi..

Ranar da zata tafi ma da kyar suka rabu,

Duk dama a lokacin sarahn ta shirya wani karamin shirin wayar da kai da zata je kauyuka kauyuka tana wanzarwa..
Tare da Hadin kai kamfamin lura da cutar kanjamau da tuberculosis..

Bayan ummah ta tafi...

A Ranar da take shirin tafiya sai ga yazeed ya dawo kan aikin sa ..

Bata ma sani ba sai da hapsy ta ce ke"mr yazeed fa ya dawo yau yana office ...

Take zuciyan ta yay mata dadi ta dago Tayi dan karamin murmushi tace wow im glad,yagama
Hutun kenan

Amma ya warke sosai ko..?

Hapsy ta kada kai ta tabe baki tace kaji kamar bake ce mai zuwa duba sa ko wani rana ba..
Ko dai baki kallon sa ne in kinje?..
Suka danyi dariya..

Bari sai anjima zanje nayi masa welcome back

Mmmm yakamata don yanzu naga handbag dinsa tana nan makale da shi...

Uhmmm really,? Chan mata hapsy i just cant get why shes so upset with me... har yau fa in naje bata amsa magana ta har nagaji na denA

Jingina kai da kujera hapsy tayi tace yooo ya zata yi ta amsa bayan ta saki aranta..i mean mr yazeed yana nuna kulawar sa an then kema yanzu kina nuna masa kulawa
Chabbb ai ko nine zan sa ido....tayi dariya

Waje sarah ta budo ido tace kulawa shine me?
Haba hapsy kema zaki fara ko?
I just feel guilty da abunda ya faru, he helped me alot shyasa nake jin yakamata nayi returning favors din sa atleast,
In ba din haka ba to meye...ta dan tabe baki

Hapsy tace "Hmmm toh shikenan dai, nima a haka na dauka but kema sarah sai kiyi a hankali da ita don wallhy ta dau abun har ranta shes too over protective of him.

"Damuwar ta ne wannan haps.. indai namiji ne ina da wanda ya fishi komai da komai agefe na..so"

Dariya sosai hapsyn tayi tace toh an shigo damu filin gwaje gwaje,talking about that,sarah kin same mahfud din kuwa?

Juyowa tayi ta gyada kai alaman a'a

Shiru ne ya dan biyo baya hapsy tace Allah sa lpya dai..
Ni dai jiki na na bani hala wani abu ne ya rike sa

cikin sanyin jiki Sarah tace "Uhmmm haka zai iya kasancewa hakan,
amma duk da haka ni na san waye mahfud,idan bai sake nema na ba nasan duk ni na jawo hakan..he wll not break his promise.
Ko Don darajar dayake bani sosai nasan bazai taba karya alkwarin nan ba
And kinga ranar da muka rabu ni nace kar ya sake nema na,..i was thinking im gonna be fine..
Amma har yau ina mugun jin kewar sa a kowani lungun zuciyata but i just cant do anything about it.
Ba ya social netwkd no phone no messge inaga na tura masa voicemail yafi dari amma no replies

So Why dont ask catherin?ai naji ance tana france
Hapsy tace adan dame.

I did, kawai ce min tayi itama bata sake ganin sa ba...he left
Kuma kinsan ta itama da shegen damuwa she just want me to say yes to his marriege plan gani take kawai karya nake yi ma kaina..

Mikewa daga zaune hapsy tayi ta zuba mata ido tace kamar yafa? Ai kuwa ina ganin kamar lokaci yayi da zaki making wannan decision din sarah.
Kin cika burin ki,and mahfud dint tresspass as u said.. Mu dai shi kawai muke jira ya firo ayi abun nan...

Huhhhhm....kai hapsy! i know duk nasan da haka hapsy,amma ina yake toh.
Ni gani ma nake im kind of not ready again..

Cikin mamaki hapsy tace mene? Not ready kamar ya u kidding me right?

No ,kawai ji nake kamar am still confused.
Tafada a dan dame tana duban hapsyn da serious look

Tabe baki hapsy tayi ta koma kan chair ta jingina ta ce ..,sarah kenan ki nitsu fa, karki kiyi abunda zai sa ki cuci kanki..i dont knw mahfud too well amma i think hes cool.

Sarahn Tayi ajiyan zuciya tace ok fine,ni kam ma abar wannan maganan bari naje na gaishe da yazeed na dawo

Mikewa hapsy tayi tace zata bita sai suka fice tare.

Tun daga bakin stairs take jin bugun zuciya amma sai ta dauke hakan a fuskan ta suna tahowa shiru

Hapsy ce ta soma bude door din offishin,shika dai ne a zaune yana duba file alaman safeenahn ta fice

Kallon sa sarah tayi a sace cikin wani yanayin da zai isar maka ta yaba da shigar nasa

Yau dai dark navy blue long sleeve shirt yasa over a well tucked in black silk cotton material shorts yayi matukar yin kyau ya kuma nuna simpilcityn tsarin halittar kyaun sa.

Theres no daubt that Dan zaman sa a gida yasa ya dada murmurewa ya tohu da sabon sigar kyau mai dauke ido..

Itakan ta hapsy sai da tayi murmushi ganin yadda suke bada juna kallon kallon a boye..

Zama tayi bayan ya amsa sallmr su, tace masa barka dawowa..

Ya amsa da murmushi..
Ya ce musu ya gode da kulawar su..
Chapter 44 · 0% Book details