← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 103

Sashe 81

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adan sakalce shannam Tace granny Bari na sa ma kowa nashi, sai ta mike ta fara kokarin serving din su

Cewar ta tunda yanzu nazo gida ni zan na kulawa da ke little

Kowa yayi dariya...

Sai ta taho daf zata zuba masa a hankali tace and you kitty.

Ya dan harare ta ya maida mata murmushi...

Kau da kai sarahn tayi kadan tana maida dan karamin nishi ciki

Kowa na ci sai granny tace gaskiya abincin yayi dadi..am sooo proud of you my princess.dariyar jin dadi ta mayar ma granny ta dan jingina da ita..

Tace kinga warda ko magana bata yi...

...tun kafin anty warda ta amsa ma joke din
Shbnam Ta dago cike da jin dadi tace ai ba ita kadai bane loook
Tayi nuni da mahfud dake ci a nitse "cikin shauki tace hesso enjoying it...
Kowa yayi murmushi
Shikam Tabe baki yayi ya dago ya dube ta, tace ko ba haka bane? Yayi maka dadi ko kitty.
If u want gobe da safe ma ni zan maka wanda yafishi dadi...

A lokacin Sosai sarah ta dago da kalle ta cikim wani irin yanayi,ita kuwa ko ajikin ta sai wani murmushi take ba kunya

granny tayi murmushi ta kau da kai... .

anty warda ce ta katse ta jokingly tace kai shabnam pls let him eat..

Yayi gyaran murya fuska ba yabo ba fallasa ya tashi ya sha drink dinsa ya ce to nikam ma na koshi...

Ya firta Excuse me...ya tashi yana shirin zamewa daga kan table din

Tace granny wai don nace yaji dadin abincin shine yace ya koshi..ta dan turo baki cikin sakalci....

A cikin ranta Ta tsani tayi magana yaki amsawa ko ya amsa ta half.
Granny ta dube sa abincin yayi dadi mana right ?

Sai ya dube su duka yace
Of cous,
Sai ya sauka ya fita..

Anan sarah ke lura tunda mahfud ya bar nan shabnam ta rage surutu granny ne kawai ke maganan ta ba kamar dazun da mahfud yaje zaune ba..
Tabe baki tayi azuciyan ta tana bin yarinyar da kallo tafara gane wani abu game da ita amma bata so ta kawo insecurities ma zuciyan ta sai ta share..

Ko kafin a tashi anan shabnam ta kasa zama sai tayi excusing dinsu itama tabi bayan sa ba wanda ya lura..

Anan bayan sun gama
Sarah ke ma anty warda hirar jiya cikin nitsuwa suke tadin su..

Granny najin yadda sarahn taje bayyana intrest din ta sosai akan haka..

Bata bayyana ba amma cikin ranta yayi mata dadi..

Anan ta barsu ta haura sama..

...chan sai sukaji noise din rikici da dan surutu

Muryan shabnam ne da granny, tana mata shagwavan mahfud yaki kulata bayan ance ya rika koya mata karatu..

Duk yadda granny tayi da shi sai yace hes busy sai anjima

Far daya anty warda tabsoma lura da chnge of mood a fuskan sarah amma sai ta kaucar mata shi da maganan abubuwan da ta sa agaban ta yanzu...

Haka har suka yi sati guda...

Sarah da shabnam basu taba maganan da ya wuce gaisuwa ba...

Kowa na soo ya gane nufin kowa..

Yadda mahfud ke yawo da idon sa akan sarah kuma yake nuna kula yasa shabnam ta soma dan jin haushin ta...

A kullum sai ta yi maganan ta ma granny duk dama granny ta dauka kishin yarinta ke damun ta..

Ita kuwa shabnam tun daga lokacin sai ta dau alwashi nuna ma sarah akwai wani abu tsakanin ta da mahfud azuciyar ta..

Tunda ta zo sai take Gani kamar hankalin sa na kan sarah..

Sarahn kuwa bata komai yanzu illah bin wayannan cahnnels din tana gyara imanin ta..
She became addicted Wani bin har abincin bata so ta sauko ta ci..

Shi mahfud idan yaga haka sai ya damu sosai yayi ta takurawa akan ta sauko din

Gani yake kamar damuwa ke sata yawan kebe kanta..

Amma azahirin gaskiya zuciyan ta take ginawa da imani da tsoron Allah...

Yanzu har ta kan bata lokacin ta sosai wajen yin chat na tambayoyi da duk abunda ya shige mata duhu da malamai online ana amsa mata su tana fahinta..

In just 2 weeks ta soma yin sallah akan lokacin sa cike da tsoron Allah..

Sometimes idan ta rude sai ta je wajen anty warda su biyun su suyi magana itake kara mata haske akan abubuwa dayawa babu wanda ya san da hakan...

Lokacin da abun ya shige ta sosai idan tayi sallah tunda ga raka atanl fajr zata soma ciko nafilan ta har ishai bata missing..

Sannan within the hours da rana ko da yamma da shike bata taba komai agidan sai take using tana karanta littafn aduoi da hisnul muslim tana koya dakanta...

The same naciya da turjiyan datake yi a da chan baya don career ta shi take applyng dinsa anan ma

Ko ma ace yafi don bangaren rayuwa ne mai muhimmnci wanda tayi nadaman yarda shi sosai.

Sai ta kaurace ma sauko wa tsakar gidan sosai Besides shabnam takan ruda ko ina da surutu kullum tana sa kanta girki da sauran abubuwa

Damuwar ta shine kowa ya san da gaske take yi akan mahfud

Idan ta takura sai ya mata bitan karatun ta basu karewa sai da fushi amma hakan take nacewa sai dai bata gansa na zaune ba

Sosai take zagewa ta bauta ma granny with the hope that za ace ita ce better macht dinsa...

Shikam damuwar sa bai wuce ya san meya sa sarah ta dan sauya akwana biyun ba...

Amma tafiye tafiye da aiki ya kan sha masa kai sosai sometime wajen ci abinci kawai suke haduwa..

Wasa wasa tsakanin sarah da shabnam sai kallo,maganan tsakanin su sai ya fara rauni sai ayi kwana uku kwana biyu basu tanka ba.

Gwara ma sarahn ta kan mata murmushi normal a wuce

Anan haka wata rana sai granny ta karance su gaba daya ta yanke hukuncin zuba musu gasa a boye...

Saukowar shabnam daga sama,anty warda ce da sarah a bayan ta ana biyo su da trolly

Kusa da granny shabnam ta zo ta zauna tana satan kallon dresing din sarah

Har ranta a duk randa sukayi ido hudu sai ta yaba kyaun ta,ta lura kowani kaya ta sa yana amsar ta ko batayi kwalliya ba tana haskawa amma yanzu haushin abun take ji sosai

Bayan amsa gaisuwar sarahn granny tace har kin fito kenan warda,.anty wardan tace eh mumy...
Nayi latti ma pls ki kula da kanki ta mata light peg..

Ta juyo tace muje sarah..

Charaf shabnam tace anty zakiyi tafiya ne?
Tace eh shab, am going for a week ...

.ta dan tabe baki alaman rashin jin dadi..amma sai ta bi da murmushi ta mike bari nima zan raka ki waje

Tana mikewa ta karbe trolley a hannun mai aiki,granny tace no dear da kinbar sa wont u gett tired..?

Cikin son ta dada zafafa game din ta tace no granny,
I ni nafi dacewa na dauka ma mum kaya ba mai aiki ba right mum?

anty tayi murmushi ta juyo cikin kula ta ce mata to nagode shabnam...
Cike da jin dadi ta shiga ja...

Sarah na shiru tana lura da duk rawan jikin da take yi amma bata ce komai ba

Har suka raka antyn suka dawo,...

Ita ta soma shigowa ta zauna kusa da granny nan inda take ce mata ai warda ta tafi yanzu kam bara mu na ganin ki ba ko sarah?

Tace ahhhh grannny zaki ganni mana im always here for you..

Cahraf shabnam tace ohhh granny why even worry abt that? ko anty warda tana nan ko bata nan ai nikam ina tare dake ko?

Duka suka danyi murmushi

Granny ta shafi kanta tace i trust you my dear.....
Yau ma me zaki dafa mana..

Anan ta mike daga zaune tace"
Yau ina so na dafa matched chicken jollof
Irin na ranar granny baki ga yadda kowa yake so ba...i know mahfud will fall in love with this toooo

Tafada cikin shaukinda jin dadi...

Wanda ya sa granny sake murmushii..

Haka kawai sarahn ta dan daure fuska amma bata tsananta ba ta kau da kai..

Tace Toh Allah ya sa kowa ya zauna aci tare ai yafi dadi ga warda bata nan

Cikin jin dadin Ta kuma cewa ai mum zatayi missing,
Amma anan i will feed you myself grnny. Shima idan yaki saukowa ni dakaina zan jawo sa
Im making this specially for him kinsan fa yana mugun so..cikin rawa jiki ta ke karsawa wanda yake bayyana musu niyyar ta dukan su

Aka bar granny da murmushi ita kuwa sarah sai ta bata shiru abun ta..

Tunanin ta shine wai wannan yarinyar bata da wani magana sai na mahfud? Shes always giggling about him
Ta dan tabe baki a boye ta mike

Tace granny zan koma ciki..

Ita kuwa granny da shike ta shirya plan din ta sai ta dage tana cewa
Ke kenan kinfi son zama ke kadai bazaki zauna da mu ba sarah"
Ga nan sister ki is busy in the kitchen yaushe zaki mana naki muci ne..

That way it wll be lively for all of us ko ya kika ce
Ta karashe da dan karamin dariya mai dauke da optimism

maganan sai ya zo mata wani iri amma da shike grannyn ta kure ta da kallo sai ta daure ta ce
Nima zanyi mana wata rana granny....
I just need to work on somethings now.

Grnny Tace what?work? Babbu masu kula dake ne,why wud thy allow you..
Cikin serious turne ta soma kiran malaika..

"No grannny sunayi ni ce ban tashi da wuri ba dazun shiyasa nace zanje yanzu na kimtsa kan gado na..

Granny tace ohh ok

Tabe baki shabnam tayi cike da burstness" tace hmm nam taKe ta shiga gwada yadda take kula da nata dakin akan lokaci ba sai ta jira mai aiki ba.

Granny sai ta biye mata don tayi teasing din sarahn

sai take ce ma shabnam ai yana da kyau ka rika kula da kanka haka ko da kana da masu tayaka.

Ta haka ne kake dawo mace mai discpline
Im sooo pround of you my princess ..

Dadi ya sa ta dan kwantar da kanta kafan granny tana hararar sarahn kasa ksa
Chapter 81 · 0% Book details