← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 103

Sashe 67

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin zasu iya fahimtar wani abu ya sa ta dan ja jiki tare da cewa ta gaji ya shige ciki ta barsu anan....

Mahfud haka kawai Abun ya dame sa ,sai ya juya cike da ladabi yace ma ummahn toh shi zai tafi tunda sarahn ta dawo...

Ummah ne ta ce masa ah a..ya dan tsaya suci abinci ko zai tayata ma saratu magana akan ta rika sanar da ita in har zata dade haka awaje ita tayi har tagaji

Kuma shikan sa yaga yadda hankalin ta ya tashi sosai....

Data fadi hakan sai ta bashi tausayi sosai ummah take kaunar saratu...

Idan ya yaga tana hakan sai yana tuno wahalhalun data sha a da chan baya duk akan yarta...

Take sai yaji ya bata Wani sabon girmamawa a zuciyar sa shikan sa ya san samun mahaifiya kamar ummah yana da matukar wahala.

Haka ya amince suka shigo tare ,ita kuwa sarah quilty consience da tunanin abubuwan da suka faru yau sai ya hanata saukowa

Ummah ta jere abincin ta kira ta ta kira amma shiru sai aikin cewa bata jin yunwa take ,

Ita kuwa ummahn ta so su hadu waje daya dan mahfud yayi maganan amma karshe haka tayi fushi ta koma dakin ta
Ko mahfud din bata saurara ba..

Abun ya bata masa rai sosai...ya rasabya zaiyi da wannan lamarin wai shin meya same sarah take ma ummah cold treatments yau..

Tunanin sa ma a lokcin da ta zo ta same ta cikin tashin hankali zata yi yunkuri saisaita amma sai gashi ita take binta tana borewa..

Har ya sa kai zai fita sai ya tura mata tex yana jiran ta waje
.
Kamar bazata zo ba don ita kadai tasan yadda zuciyan ta ke harbawa da abubuwa da yawa..

Haka ta iso Ta daure fuskan ta shima hakan,bai tsaya wata wata ba ya shiga mata fada,

Mafi akasarin fadan nasa na tuno mata ne akan labarin da ta bashi na wahalar da ummahn ta sha da duk abunda ummahm ta fuskan ta akan ta..

Shi aganin sa ummah bata cancanci ko da miskala zarratin na bacin rai daga gare ta ba

Tun da take da shi bai taba mata masifa mai zafi haka ba, she can tell that yau ransa ya baci da ita sosai...

Amma sai tayi saurin kawowa aranta cewar don ya san sirrin ta yake iya budan baki ya gaya mata magana son ransa..

Shikuma gani yake kamar sarah ta mance da kanta ne dole ya zamto ya mata tuni ko zata shiga hankalin ta akan ummah..

Sai ta sa abun aranta sosai,she just stated regreting again, yanzu da mahfud bai san labari na ba da bazai haura min har haka ba

Ai ga yazeed nan har karya yake hadawa gaban iyayen sa yana sa'insa da su akanta

She just tot that inda shi ne a matsayin mahfud yanzu da bazai tsoma bakin sa akan lamarin ta da ummah ba

Har mahfud yagama masifan sa batace komai ba illah sai da safen da ta amsa ya kama hanya ya wuce gida...

Ya isa kowa na bacci sabida ransu ba adai dai yake ba da faruwan abun da yazeed yayi...

Da shike yayi baci lattti da sassafe ma basu samu damar haduwa kamar yadda suka saba ba suka watse agidan

.....
Ita kuwa sarah har sai da tayi bacci sannan ta soma gane ma kanta sosai
Ba laifi kafin ta fita office din sai ta bada ummahn hakuri akan jiya

Tare da mata alkwarin daga yanzu zata fada mata gaskiya akan komai bazata sake bata mata rai ba..

Gefen yazeed kuwa yau saura kwana uku ne lokacin daya bayar na game of love dinsu ta cika

Ya tara invitations card dinsa masu zafi ya kuma aikawa ma wanda ya shirya su zo masa akan lokaci dai dai da plan din da ya shirya..

Yau ko da sarah take office bata jin dadi sabida sanda taje wajen hajya billy bata hakuri personally kafin ta zo branch din su

Anan take gayawa hapsy komai da yafaru ajiyan don sun mata nauyi sosai..

Musamman da har yanzu ta lura hjiya billy ta sa abun arai
Yanzu ba shakka tana kokuntur tarbiyar ta

Damuwar dake kan fuskan sarahn ya hana hapsy mata fadan data ke shirin yi,don ita sai yanzu ma ta san da dawowar yazeed

Cikin sauke ajiyan zuciya da nema makai nitsuwa ta ce sarah? Kinsan me kike yi kuwa?banyi tsammanin yazeed zai sa
Kina ma ummah karya ba,
And then what?... Na dauka idan kika hadu da shi zaki aikata abun da kika ce zakiyi ne na tambayar sa abun da ke ransa game da ke..me ya kaiki wani kwanciya akan gadon sa ?

Romantics dates ai a gidan sa ya fi dacewa yayi dake idan ya aure ki ba anan ba ..gashi ai ya sake kulla miki wani damuwar..

Ta dago a dan sanyaye ta kalle hapsyn "wato ke baki ganin laifin kowa sai na yazeed ko?yes nasan duka munyi ba dai dai ba da muka kebe har haka
But he defended me,atleast yayi yunkurin nuna ma iyayen sa gaskiyar lamarin..

Cikin kula Hpsy tace and so?

Toh yanzu ya zakiyi kenan,yazeed din ne yanzu ko mahfud..?

kin ga sarah da wannan abun da ya faru jiya
i still think mahfud is a better option for you..

atklleast bazaki aure sa wani a dangin sa ko iyayen sa suna miki kallon marar tarbiya ba

Ke da kanki kin ce hajiy billy is on it....Allah kadai yasan ko baban nashi ma hakan ya kulla aransa amma yayi shiru

Tayi shiru tana jin hapsy..

Mikewa tsaye tayi zuwa jikin window ta dauki mintuna 30 tana kallon waje

Har hapsyn ta ja kujera ta yi shiru tana binta da ido..

Chan data gaji ta tashi ta dafa ta cikin sanyin murya tace lpya kuwa sarah? Nayi magana baki ce komai ba.

Hawayen da ta ke boye wa ne suka sauko"

Da kyar hapsyn ta jawo ta suka zauna cikin lallami ta shiga bata shawaran ta nitsu akan abu daya lokaci yazo da zata san asalin wanda ya dace da ita..

Anan sarahn ta daure ta share hawayen ta da cewa"
Na riga na yanke hukun cin haka hapsy..

Amma na tambaye ki mana?

Hapsyn tace ina jinki..

tace dan karamin labari zan baki sai ki bani amsa sa acikin sa

Hapsyn tace uhum"

Cikin nitsuwa tace" a mazan zamanin nan namu wani saurayi ne wabda da wuya kikaga kuskuren sa tsaban nagartar sa,

Sai ya hadu da yar wata barauniyar mafa marar tarbiya,har maita tayi,..

Amma ba wanda ya san ba da son ransu suke haka ba,uwar tayi ma yarta ne don ta rayu..

Ki dauka duk wannan ya faru ne a idon saurayin nan yaga sirrin su yasan me suke ciki da bakar qaddarar su, da yagama fahimtar rayuwar su
Sai yace zai aure yar matan nan.

A dayan bangaren kuma akwai wani shima kamar wancan saurayin ne, sai dai shi bai san komai akan su ba amma yana iya yin komai dan farin cikin su, sannan ya yarda da su..mind you bai san sirrin su ba..
Sai ya fito da cewa zai aure yar matan nan..

Toh acikin wayannan biyun
" wanne kiga yafi rufin asiri yar ta aura

shin wanda yake da hankali amma yasan sirrin su?
Ko wanda ya Ke da hankali amma baisan sirrin su ba?

Hawaye ne ya sauko mata sai ta share ta kalle hapsyn alaman tana jiran amsa

Shiru hapsy tayi tana lailaya gajeren labarin,ace mahaifiyar ki mayya barauniya marar tarbiya,?

Kai Tsakanin harshe da hakuri ma akwai sabani
Kaiiiiii anya wata rana bazai zama abun gori ba?what if aka zo aka samu misunderstanding? Soyayyar zai iya sauyawa ya zamto kiyayya kenan..

Nan hapsy ta dago tace inaga mai hankali wanda bai san sirrin su ba ya fi cancanta..don kazantar da ba ka gani ba ma tsaftace.

Sannan shi mutum tara yake bai cika goma ba..

Duka kansu da zasu dace da ita sabida dayan shi yasan ita wacece amma yana da hankali...future kawai ake tunani akan sa

Amma wannan kuma bai sani ba,zai iya yuwa kafin ya zo ya sani ansamu kyakywar fahimtar juna agaba.

Da kyar sarah tayi ajiyan zuciya tace nagode hapsy

Ashe hukuncin da na yanke na kan hanya kema kin fada..

cikin rashin fahinta hapsy tace kamar yafa? Ni kwata kwata ban gane me kike cewa ba.
Whats all this sarah?

Tace babu komai barinje gida wajen ummah na i will have to talk to you later pls ki kira min catherine itama zan mata magana anjima..

Batare da ta jira ba ta dauki jakar ta ta wuce gida.

Bangaren mahfud kuwa alhj nafiu ne ya dauke sa suka je humanataran service a wata kauye su biyu da sauran officials din su

Hankalin su gaba daya na chan ana ta hidiman jama'a is like alhj nafiu yana so yayi retire ne ya dawo politics abunsa.

Ita kuwa hajiya billy sam sai bata jin dadin zancen auren yazeed da sarah ba,
Yanzu ne take kawo wa ita dama safeenah ce,

Don hankalin ta zai fi kwanciya ta kowani fanni idan hakan ta faru.

Ai bata taba samin safeenah da boyauyen hali ba, gashi iyayen ta ma sannanu ne anan waje ta bata da fargaba akan su..

Abun ya dan dame ta sosai amma tasan dole su ma yazeed abunda yake so..

Isowar sarah gida ta ajiye motar ta ta hauro ciiki ta samu ummah ta idar da sallah kenan tana adduoi

Shiru tayi daga gefe tana tuno da wayar da sukayi da yazeed na cewa zata fada ma ummahn ta maganan auren su shima ya tabbatar mata da yana jiran amsar ta ko a gobe ne sai adaura musu auren domin su dada toshe kofan zargin tabewar tarbiya da iyayen sa suka fara nuna mata
Jiyan.

Cikin mamaki ummahn ta dube ta, tace lpya dai saratu ya naga kin dawo da tsakar rana haka?

Tayi shiri cahn anjima ta sauke ajiyan zuciya ta taho gaban ummah ta rusuna

Hawayen ta ne suka soma sauka ta bi ta sunkuyar da kai kamar me neman gafarar wani mummunan laifi

Lokaci guda ummah ta daga hankali tana tambayar ta meya faru?
Chapter 67 · 0% Book details