← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 103

Sashe 26

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma yau komai ya wuce tunda ta sanar da shi mafi munin labarin ta amanan ta qaddarar ta da raunin ta...

Dama shi kam bai boye mata komai game da nashi rayuwan ba duk dama babu dadin ji, amma ta nuna masa iya amanan ta da tausayin ta, ta bashi karfin gwaiwa..he knew he have to do the same now dan ita ma ta bude masa nata..

Toh me ya rage in ba ya gaya mata yana kaunar tan ba,?kallo ya sake bin ta da shi, cikin ransa ya titse yana rokon Allah ya sa sarah ta amince da shi yace" insha Allahu ni zan aure ki i will wipe away all ur sorrows sarah...im here . Ya karashe ahankali yana dada duban kyakywanr fuskan ta.

Sake saken kauna amana da tausayi zuciyan sa ke kan sakawa ayayin da ya gyara mata kwanciyar nata ya rufe ta da soft duvet comforter sa Ya juya ya shiga bayi..

Wanka yayi shima ya sauke nauyin dake dawainiya da zuciyan sa...
Kafin nan biyar ya buga ana shirye shiryen kiran sallahr asubah.

Sai ya dakata yayi sallahn sa sannan ya kishin gide gefe da ita atake wani gajiyayyen bacci yayi awon gaba da shi..

Bacci mai cike da yanayin ajiyan zuciya suje kwasa dukan su biyu musamman ita sarah da shike yanzu ne giyan ke asalin fita a jikin ta.....juyi take son ranta tana neman juye nauyin zuciyan ta akan baccin.

Sai wajen 7.56am ta bude idanun ta gani tayi haske ya dan fara dokar windown sa da shike upstairs ne kuma windown glassses ne..

Shiru tayi na dan lokaci daga kwancen kamar bata gane inda kanta yake ba tukuna..don sosai kanta ke warwarewa lokaci guda ta soma tunanin abuwan da suka faru jiya...

Bit by bit komai yake dawowa mata wani mummuanan tsoro da fargaba ne ya ziyar ce ta take ganin kamar a mafarki komai ya faru...

daga cikin bargon sai tayi juyi a hankali tana feeling naked bodyn ta dga cikin towel din dake neman karkacewa da kansa anan ta dafe kai cikin rudani ta juyo a dan sace "don ta tabbatar makanta ba tare da namiji yau ta kwana ba ...

But where is he? Don ita kadai ce yanzu akan gadon ba kowa

Ko da taga yanayin kwanciyar sun a shatin bedding din She has to closed her eyes tsam tsam sabida wani azabbaben kunyar da ya rufe ta,nan ta daure dai ta shiga duba ko ina da kwayan idanun ta anan ne take ganin alaman kamar wani abu ne ya faru wanda bai kama ta ba..

Har ta fara Kawo tunanin sai kuma rudewan tunanin hade da tashin hankalin tuno da abubuwan da tayi jiyan ya sa ta mike a kan gadon da sauri kamar mai ciwon hauka ...

Zuciyan ta har na sama da kasa tsaban ta rikice
MAHFUD!!!!!ta kwalla masa kira amma shiru babu shi,

Da sauri ta Ja curtain din dake jikin window tana duba saba t inda ya saba tsayawa bata gansa...

Cikin rudani ta juyo nan idon ta ya ci karo da wasikar sa akan madubi..

Da dark blur pen ya rubuta"
Zama tayi gefen gado bayan ta dauko
Tafara karantawa a hankali"

_"forgive me..da na jira har sai kin tashi a bacci na fada miki but im helpless.. heroien, nasan zaki iya wannan don kin riga da kinci gasar_
_u won the battle of your destiny, and for this you must win too.. becos your confidence is still with you,abinda ya faru jiya ki dauka ba komai ba ne illah wani qaddarar da_ _rayuwar mu ya zo mana da shi tare dake..idan kin tashi ki shirya kije ki karasa abun da kika fara.i will neva let you back down from this.. A yanzu ne kike da bukatar ki zama abunda kike so a rayuwan ki..yau nasan idan har akwai digon yarda dani azuciyan ki zaki fahimci me nake gaya miki yanzu wanda bazan iya fuskantar ki na fada miki ba_

_go sarah lokaci yayi da zaki zama macen da kike buri,today i feel like im not ur role model but ure my role model._
_Zan jira ki anan sama idan kin karbo abun da ya kasance naki ne ki taho ki same ni,i have a confession to make_ .

_yours Mahfud lingard_

Sauke ajiyan zuciya tayi tayi zugum cikin radadin tunanin yadda ta zubda kan ta ajiyan gaban sa,komai ma cunkushe mata yake dada yi a zuciyan ta da kyar ta lallaba ta shiga bath ta kimtsa kanta sananan ta dauro alwala tayi sallah..

Duk jikin ta a muce yake..musamman idan ta tuno da abubuwan da ummah ta dade tana mata tsoro game da bayyanar siiririn su a wajen wani"musamman namiji," wa iya zubillah me ya kaini shan giya'tafada makanta cikin zazzafan nadama.

Hawaye ne suka wanke fuskan ta tuntuni ta ma arasa wani tunani daya zata bada hankalin ta kai..

Amanan su da ummhan ta data ci wajen bude sirrin ta jiya ma mahfud.

Ko nadaman shan giyar data yi ta bata kimar ta a idon Sa..

"Koko zata rufe ido ne kawai ta fuskance aBunda mahfud din yake gayawa mata a wasikar sa..

Sam ta kasa sa hankalin ta waje daya..

Ta dan jima a haka daga bisani ta tashi ta shirya ta fuce zuwa masaukin ta..

Da shike bata taba kwana wani waje ba ya sa yau take ji daban da tambayoyin da sauran team mates din ta ke mata..

Amma bata cikin yanayin da zata amsa ma kowa maganan sa musamman cath da ke shakkun abunda ta aikata mata ajiyan.

Shiri tayi mai kyau ta kama hanyar Fara aiwatar da shawarar da ta yanke na karshe aranta..

After 6 hours misalin karfe 4.30 na yamma
Devh singania imperial college cike take dam da mutane da manyan officials don tabbatar da sakamakon fafatawar..

Ana daf za'a fara sarah ta samu damar isowa...

Duk dama Tayi duk abubuwan data ga ya dace amm Still zuciyan ta bai kwanta ba da taga babu mahfud anan din..

Anyi speech masu ilmantarwa cike da tunatar musu da su wanene a idon jama'a..

Duba da su mutane dayawa afadin Duniya musamman kaskantatu marasa galihu zasu na kallo a field din aikin su yanzu
Yasa Board members na humanatarin activist da human right suka bada gargadi mai tsauri akan su jajirce wajen kare nasu tarbiyan su kafin suce zasu karbe ma wani dan adam nashi hakkin...

A cewar su Bazai yiyu marar mutunci da kima ya yi ikirarin zai kare hakkin dan adam ba..

Darajah, tausayi,mutunci da jajircewa wajen basiran zama da al'ummah Shi ake fi bukata don kare suna da martaban organisation din Gaba daya na duniya

Don haka ba bata lokaci

Aka sanar da sakamakon gasar,
Sai dai wannan karon daban ne..sabida yarda kowa ya nuna zakowar sa ma wayannan jajirtaccun dalaibai

A cewar su kowa yayi kokari amma team din da suka basu daman shiga org sunfi kowa nuna tausayin su da kulawar su..uwa uba jajircewa da gskiya.

Sarah bukar ita ta jagiranci award din da kuma licenced din sa aka bada kowane memebr team din ta..

Murmushi mai dauke da Kuka ne ya dan kufce mata amma ta kasa bari ya sauke mata da hawaye...

Shikenan burin ta ya cika..

Mahfud is always right gashi ta sake tashi
Ta bada mahaifiyar vashika karfin gwiwa a yayin da nata ma ya dawo mara..

Taga mutane kam ba adadi,
Musamman ma Memebers din sabon office din da zata fara aiki da su na human right

Tun daga nan suka fara dada cusa mata ra'ayin kara zage damtse wajen daukar aikin ta da muhimmanci ....

Sosai abun yayi tasiri a zuciyan ta..musamman da yazo a yanayin da take ciki na wani nl rauni da rashin Sanin Me zatayi nan gaba..

Bayan waje ya lafa kowa ya dan watse hutun sati biyu da aka bata take so ta koma gida gaba daya nigeria tun da yamma ya rufa sai ta sa aranta Haduwar su sa mahfud anan sama sai da dare

Dama abubuwa da yawa na damun Ta game da haduwar nasu

Kunyar sa take ji yanzu, sannan zuciyan ta na matukar bugawa musamman idan ta tuno da yanzun yasan sirrin ta da duk abunda take ciki a rayuwa

Hakan ya sa ta nitsu sosai ta shiga kundun tunani

bayan ta gama shirin ta tsaf misalin karfe 10 saura na dare ta taho rai walia hotel..

Ta dan kwan kwasa door din Shiru
Hakan ya tabbatar mata da cewa yana chan saman kenan ba bata lokaci ta bishi..

Anan yaje ya bada kofa baya yana kallon bakin titi daga saman verandar benen daya zauna kamar yadda suka saba..

Durus ta tsaya tana bin kyakkwar hallitar sa da ido duk dama yasan ita din ce ta zo amma bai juyo ba tukun..

Shiru ne ya ratsa wajen na dan mintoci

Bugun zuciyar su na dada karuwa..
Gani take kamar bashi ba..

Haka shima ya dade da shiga wani yanayin da bazai iya fassara shi ba..

Har ta iso daff da shi, hasken bakin suman kansa sa da ya dada haska fatar sa dake shekin kyau ke dada dauke mata ido..

A sanyaye ta dan dafa kafadar sa wanda ya sashi lumshe idanun sa yana zugar iskan daya zo da sabuwar kaunar ta da tausayin ta aranshi...

Hero,I did it..
Tace cikin sanyin murya mai dadi da ke sarkafewa har yana cracking cikin kunnen sa

Tana jin yadda yake gode ma Allah duk dama bai fada da karfi ba..

Hannun da ta dafa shi ya kamo a hankali ya juyo ya kure ta sassanyar idanun sa..

Sun dade a haka suna kallon kallo kowa da kalar abunda yake ganowa .

Sai dai a lokacin Bayan Tsantsar so da kaunar Har da tsoro da fargaba na gauraye da nunfashin su..

A karo na biyu data yi yunkurin sauke idanun ta daga nashi,don sosai zuciyan ke ke naman rikita ta ta rasa sukuni..

Gashi ra riga ta yanke shawarar ma rayuwan ta..

Cikin sanyin jiki ta juya zata tafi bata hankara ba ya jawo ta kusa da shi...
cikin wani irin kallo mai tatarre da yanayin da ita kadai ta ke fahimtar sa yace" mata congratulations heroine..dama nasan nakii ne..u did it..
Chapter 26 · 0% Book details