← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 103

Sashe 46

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan Allah ki fahimce ni ,lets end all this i dint come her for anything,kar ki dau abun da wani manufa..pls safeenah

Safeenah kuwa ko jin ta bata yi Hannu ta sa zata ture ta daga gefen ta,yazeed ya yi saurin bugewa Wanda hakan yasa shi sake sake wani uban kara..

A take Duka suka yo kansa a tare amma tuno da abunda ya ke faruwa yanzun yasa sarah ta dakata ta bari ma safeenahn ta riko shi

Baiji dadin hakan ba sai ya buge hannun nata cikin fushi,cikin ransa yace duk ke kika jawo u just ruin my peace here,
Suna dagiwa
"Sarah ta ce enough,dan Allah ku bari lets make things clear now

Dago safeenah tayi, tayi mata nuni da jacket din jikin sa sannan ta bata labarin komai da yafaru tsakani da Allah har aka kawo wannan lokaci.

Tace Kiyi hakuri thats not what i mean with him wallhy bazan taba shiga tsakanin ki da shi ba.
I told many times babu wannan tsakani na da shi i swear..

Safeenah na shiru kamar wanda take jin abun amma zuciyar ta wani abu daban yake aiyanawa

So yazeed ya kwana daki daya da sarah ranar shine yayi shiru bai fada ma kowa ba har ita?

Wani fushi mai tattare da bakar kishin ya sa ta fincike hannun ta daga jikin sarah..ta juya mata baya alaman bata yarda da ita ba..

Sarah dake cikin wani yanayin har zata sake bin ta tayi magana yazeed yace stop sarah ya isah haka nd please can you just leave us alone for now?
ta juyo ta kalle sa cikin mamakin jin maganan sa.
Amma sai ta gyada kai tace ok ..
Cikin sanyin jiki ta dauki bag din ta ta wuce ta basu waje..

Fada ne sosai ya tashi tsakanin su.

Musamman da safeenah ta haura masa akan boye mata da yayi cewa ranar sun kwana daki guda da sarah ...

Shima sai ya kasa hakuri duk dama thats what he really want har cikin ransa yana so ya fara playing game dinsa da sarah
So baya son abunda zai shigo tsakanin su
Sai ya haura shima ba wanda yake sauraran juna...on top of thier voices

A ranar suka yanke hukuncin rabuwa da juna
Cikin fushi...
Kowa yayi hanyar sa.

Sarah kuwa ta damu matuka wanda har ya so ya nuna akan fuskan ta

Amma da shike kauyen da suka je babu netwk sai ta hakura da shaukin son ta kira sa taji ya ake ciki

Nan dai Ta hakura tayi concentrating kawai akan aikin ta..

Kwana uku ya dauke ta anan suna zaga kauyukan dake gefe da kauyen su.

Sai dai abun mamakin shine har yanzu bata samu mutum daya daya gane ta ba..

Duk dama ta gane mutane dayawa Sosai
Musamman mahaifin sageer..

Sai gashi kuma Allah ya daura musu kaunar ta
Kowa na haba haba da ita

Ita kuwa Sosai take tausaya ma yadda rayuwan su ya dawo duk dama bata shiga asalin kurwalan ba.

Amma Da ga ganin dai daidai kunsu kasan suna cikin wani irn iftilain rayuwa..
Abun a tausaya,a cewar tsohuwar dake gefen ta
Ai yawancin wahalar su ya fara ne daga lokacin da mutanen kauyen kurwala suka soma hijra suna shigowa sauran yanki sabida yawan gobara ,iska da zinace zinace da ya addabe alumann ya kuma zamo koma bayar arzikin su da zaman lpyar su.

Sarah Tasha mamakin jin hakan,amma sai taji bata ma bukatar ta san meya jawo musabbain shigar su wannan hali..

Haka ma bata ko kwatanta tambayar ya rayuwar yan uwanta da bangaren ubanta yake ba bare kuma baba babaji..

Ko da ta cika kwana hudu anan sai ta bayyana ma sauran agents cewa bazata je kauyen kurwala ba,sai dai suje su dawo
Amma bata fada ma kowa dalilin hakan ba

Haka kuwa sauran agents din suka je,
Gashi yan kurwala sun saka aransu zasu ga sarahn da suke jin labari a redio da talabijin ido da ido

Da shike suna cikin ha'ula'in matsi da neman taimako fiye da kowa ni yanki sai suka sa aransu idan ta zo dole zata tausaya ta kawo karshen wahalar su..

Amma ina,sai akayi rashin sa'a da sannun ta taki sam ko taka wajen batayi ba.

Haka kuwa aka gama da yankin kurwala babu wanda yaga idonun ta..

Kwana biyar kenan tayi anan kafin suka shiga shirin dawowa

Itakam Dama Allah Allah take ta shigo gari ko dan ta ji labarin abubuwa dayawa data tafi ta bari

Musamman tsakanin yazeed da safeenah.
Gani take kamar bata kyauta ba..

Amm her hrt was pure ita dai tasan tana jin ta kyautata masa amma sam bata da niyyarsa wata alakan so tsakanin ta da shi...

Sai dai duk da hakan amma Wani lokacin idan ta ganshi sai taji bata gane komai..

A bangaren sa kuwa har ya sauya takon sa,yanzu safeenah da shi suna matsayin rabuwa so rayuwar sa kawai yake playing yadda yake so..

Har sarahn ta dawo office akayi report akayi komai cikin nasarah amma basu samu damar tattaunawa da shi ba..

Sai da ranar hapsy ta bata labarin cewa ai safeenah ta bar nigeria sabida taji mrs asma tana habaicin an raba ta da yazeed..

News din sai da ya doki zuciyan ta lokaci guda ta shiga shock tana bin hapsy da ido..
Kar dai sabida ni suka rabu?
Ta kawo aranta ita kadai tana tunani..

Sam abun sai bai mata dadi ba,gashi too late for her ance safeenah ta riga ta tafi, ya za'ayi ta shiga maganan har su sasanta?

Sai ta shiga halin rashin jin dadi da tunani, at the same time tana lura da mood din sa

Wanda yake nuna mata babu komai besides yanzu kam ma ya dada dawowa normal da aikin sa kamar yadda ta san shi ada chan

Da shike matsayin su daya ne so kusan kowani time suna haduwa suna tattaunawa sai ta lura kamar yana kaucewa baiya son ta tambaye shi
Komi game sa last haduwan su kafin ta ke kauyuka.

Ranar da yamma bayan ta gama duk abunda zata yi ta tattaro file din zata kawo masa kamar yadda ta saba
Daga bakin kofar take jin shi da abokin sa

Suna tattaunawa akan rabuwar su da safeenah..

Anan yake bayyanawa frend dinsa cewa eh lallai kowa yayi hanyar sa sabida safeenah taki kwantar da hankalin ta ta yarda da shi har yanzu..

Sai ta lura a yadda yake maganan kamar aransa yana kaunar safeenah amma he did secrifice the love for the sake of peace...
Dan hankalin kowa ya kwanta

Lokaci guda taji zuciyan ta ya kamu da tausayin sa, hakan ya sa bata shigo ba ta juya abun ta

dan hutun weknd din da zasu shiga take tunanin yadda zata tsara shi inda zata samu damar gaya ma yazeed abubuwan dake ranta

Sosai ta qudirah zata warware masa intention din ta akansa idan ba haka ba bazata dena jin nauyin cewa ita take kawo silar faruwar abubuwa dayawa a rayuwar sa ba..

Hakan ya sa ta shiga tsara ranar date da kuma maganganin da zata gaya masa ko da zata samu sauki aranta..

Bayn sunje gida a daren yana kwance sai ga shigowar tex din ta,

Ta sa masa venue da time amma bata fadi musababbin haduwar nasu ba,

Baiyi kasa agwiwa ba ya amsa gayyatar nata a ransa batare da ya nuna mata yama ga tex din ba..

Haka itama bata sake neman sa taji ko ya gani ba ,

Har ranar lahadi da misalin karfe 5.00 na yamma sai ta shirya cikin simple atamfar ta dark blue da fari,
She looks difernt sabida aikin ta baiya barii ta sa su akai akai..

Wajen wani cool down ta zauna wanda akayi shi domin zaman mutane biyu anan ita kadai tana jiran isowar sa

Sai gashi Minti 5 da lokacin data bada ya iso cikin sigar kananan kaya tshirt red da jean kafar sa ya sha tsadadiyar sneakers mai dauke idanu,

amma sai bai bari ta gansa ba har sai da ya gama daukar 20minutes yana kare ma halitttar ta kallo, yana yaba tsantsar kyaun ta aransa.

Lura da batayi odering komai ba yasa ya je ya dauko coool ice ream packs guda biyu fari da pink ya taho dashi,

Bata hankara ba kawai sai taji mutum ,
Yana zama kuwa ya sauke mata wani irin lallausan murmushi ya mika mata nata pink,..

Yace im late ko?

Ta dan sauke ajiyan zuciyan bayan kare masa kallon datayi tace,thanks for coming....

Yace babu komai, ..dan shiru ne ya ratsa wajen duk sai ta kasa tabuka komai ta shiga wasa da spoon din ice cream din batare da takai bakin ta ba..

Yana lura da ita shima sai yayi shiru,..amma shi yana zukar abunsa daga bisani, ya dago yace sarah, lpya kuwa?

Ta dago a hankali suka hade ido, ta sauke ajiyan zuciya ta dube sa
..cikin sanyin murya tace
Hakuri na zo na baka yazeed..
Nasan na shiga rayuwar ka and im not happy about the way things are turning out..

Dan Allah ka yafe min,har cikin zuciya ta bana nufin ka da sharri sai alheri...ta dan marairace,kirjin ta ne ya shiga budu a hankali

Sai yadan jinjina Ya dan kalle serious face dinta, yace hakan kike tunani?
Amma ai ni bance kin min komai ba,sabida baki min ba..whats all this for?

Tace,hala hakan zai iya zamo wa gaskiya a wajen ka amma nikam im feeling guilty about many things
Idan kuma ban fada maka na baka hakuri ba i wont be at ease..

Yace kamar me kenan?
I think we are good belive me bani da wani matsala dake..
U did notthing wrong sarah

Look, my life is normal kamar yadda nake yinsa a da ,so dont stress urself with worrying abt anything..

Cikin daurewa ta cije ta kalle sa eyeball to eyeball tace no ure not saying the truth,
Ur life is not normal now.

It cant be normal witout safeenah, evrything is not ok witou love,and im feeling quilty about that

Zaiyo magana tace naji duk abunda ya faru yazeed pls dont deny it.

Fata na kabani dama na gyara abunda na bata.can you pls get back with her?
Chapter 46 · 0% Book details