← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 103

Sashe 8

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sum sum ya fito gwanin tausayi a Gaban sarki ya hantsala sagir din kamar barawo yace zakayi magana ko sau na ci uban ka...ka fadi kowa yaji...marasa mutunci kawai..

Hankalin kowa ya tashi..ummma ta dada riko hannun na duka muna kukan zuci.

Ban san me naui ma sageer ba amma nasha mamakin Yadda ya hada labarin karya ya bayar akan neman mu.

Baba babaji yace" ka fadi meyake faruwa tsakanin ka da saratu agarin
Sau nawa kuma ena kama ku turmi da ta barya a dakin ka?

Sageer Yayi shiru cahn da dogari suka soma yunkurin zasu daka shi ya dago da kyar yace " ayi hakuri sau dayawa..

wani irin kuka na fashe da shi ina kallon sa cikin razana

"Lahhhh ha ilah ha illahu la hawla wala kuwaata illa billhi

Hau hau hau aka soma tambade de da maganganu ana tabe baki..
wasu suna cewa dama chan sun sani wasu suna cewa tabbass sun sha gani sa tare da ni ashe abunda muke yi kenan?

Sarki ya daga hannu, ya mike tsaye ya ce sagirru " kana nufi kenan cikin jikin saratu naka ne?

Nan ma yayi shiru jikin sa ne ke rawa sosai alaman ba da son ransa yake wannan shariar ba sai da sarki ya daka masa tsawa
Ba bata lokaci ya amsa da i..ina yace"eh kamar nawa ne

Anan ma aka sake kaurewa da salati wato tsabagen iya karuwan cin saratu ba ma da tabbacin waya bata ciki..?

Anan fa Kishiyon ummah na suka soma na su surutun cewa an zubar musu da mutuncin dangin su

Fada ne mummanna ya so ya kaure akayi chaaaaa Ana zagi na ta uwa ta uba sharrin da labarin da ban taba ji ba anan yau sai da aka fade shi kowa sai da tsine min Albarka iya isar ta.

Lokacin ummma ta mike tsaye dani ta bie ni abayan ta daga ni har ita kuka muke yi, babu bakin amsa maganan kowa..

Da kyar sarki yayi controling dattijai da matasa da matan garin da suke wajen

kowa yayi cirko cirko yana nina bacin ransa akan mu.
Musamman ma magana da ya zo da cewa kawai na so ne na bakan ta baba babaji na zubar masa da mutuncin sa.

Aka ce wannan ai cin Zarafi ne dan haka dole adauki mataki mai zafi akan mu ko ayi mana luli zaman garin nan sai ya gagare mu..

Da sarki ya sa aka dan rusuna akayi shiru sautin kuka na kawai ke tashi nan umma na ta daure ta tare numfashin sa ...

'tace ya mai girma Hamma kasani Bani da wani abun cewa anan...
domin kuwa gaskiya kamar hasken rana take idan har ta fito babu wanda ya isa ya sa hannu ya kare ta Allah shi zai isar mana da ni da diyata...

Ina kuma yi muku tuni da Allah bazai barku ba dana fada da ban fada ba zai biye mana haddin mu..kuje da gaskiur ku na rike rashin gaskiya ta da na diyata ayi mana hukunci.

Waje na so ya kaure da sharhi ,sarki yace a dakata masa.

Nan yayi dogon magana mai cike da bacin rai rashin jin dadi da masifa yayi Allah wadar da ni da ummah..

Ya kuma ce zai hukun ta sageer duk dama ba a tabbatar da nashi bane shikan sa kokunto yake.

Anan Aka taru aka bada baba babaji hakuri
Aka bashi baki sosai .aka danne sa kamar da gaske.

Sai sarki ya juya ya kalle mu rai abace yace ke kuma saratu kafin na dawo kanki ki rusuna gaban babanki yanzu anan gaban kowa ki bashi hakuri cin zarafi da bata sunan da kike so kiyi masa.

Jiki na har karkarwa yake yi tsaban kuka da takaici amma haka na shiga yunkurin sabulewa daga jikin ummah zanje gaban baba babaji na bashi hakuri...

Dam dam na ji umma ta riko hannaye ne..

Idanun ta ne suka kuma kafewa Alaman ta bushe zuciyar ta, tace"
Babu wanda zaki bashi hakuri anan saratu..hukunci kawai na roka mana.

mamakin abun da tace yasa aka soma tabe taben baki ana salleme wa.
A umarnin sarkin?
Kai wai me ake jira da gambo ne ba aci uban ta ba..

sarki ya ce adakata...

Gambo?

Umma tace naamm hammayo

"Ki kace bazata ba kowa hakuri ba..

ummah tayi shiru daga bisani tace in har ma kashe mu za'ayi ayi gaggawar yin haka sabida yata dai bazata taba bawa babaji hakuri ba..
kuje da gaskiyar ku Duniya ta ishe kowa riga da wando.

sai tassss umma taji saukar mari afuskan ta daga hannun babban aminin sarki..

yace "Sha shashah kawai ashe baki da hankali gambo?
Allah wadar dake Mu sam bama bukatar irin ku anan garin bakar ashana kawai....

Sarki yace tabbasss , gambo kin nuna mana bamu isa dake ba kuma baza mu iya zama da tsagerun irin ki ba.

Tunda kuwa kin ce sarati bazata bada hakuri ba ai addini ya mana hukunci wanda suka aikata zina sabida haka ranka shi dade tunda saukin da ka musu bai mata ba
Ayi ma yarinyar nan hukuncin ta kawai kowa ya huta

Anan ma aka kusa aka kawo dorina
Aka shimfida ni da karfi da yaji aka kwaso sageer aka mana bulala 100 100 chifff chif

"ni kam Har Sumewa nayi tsaban kuka da azaban da nake ji ajiki na cahn da na kuma farfadowa ummma nagani a kaina tana kukan mai dauke da tashin zuciya...gaba daya ta sauya min kamannin ta kamar ba ita din ba

Worst part awajen in ka dubi fuska kusan kowa babu mai jin tausayin mu sai ma tsana da tirrr dake bayyane a fuskan su karara

Sarki yace toh ke kuma gambo
Daga yau na yanke miki hukuncin barin Garin nan ta kofar yammma, kar na sake ji ko nasake ganin Ki daga nan har yankuna biyar da garin nan
Na haramce ki da kasar nan kiyi nesa damu chan kuje bariki Bakin halin ku shi zai kashe ku..

Guda aka rangada aka shiga tafi ana shewa..

Sarki da mukaraban sa na barin waje aka ma na eeele ni da ummah aka sa mu agaba har hanyar kofar yammma bamu dauki komai namu ba haka muka fice daga garin kurwala.

Ga dare yayi ga bakin ciki ga yunwa ga radadin takaici gashi da kyar ummah ke ja na bulalan da aka min har yanzu na damu na ga danyen ciki ajiki na..

Tafiya kawai muke yi mu biyin mu babu hutawa.
tun muna kukan har muka dena kowa yana ji da abunda ke ransa..

Da kyar muka kai zauren wasu yan uwa fulani..

Matar gidan ita ta taimaka mana da ruwa ganin yadda muka galabaita anan ummah roka mana sarari muka zauna muka huta don kuwa akwai tafiya sosai agaban mu kafin mu kai wani gari....

"sai da na dan huta na dada jin yadda Ciki na ke min ciwo amma bana ma so na ji tsaban yanayin dana tsinci kaina na kuncin rayuwa...

Ummah kam tayi shiru kamar bata tuna komai...
Cahn Tace saratu? Inaga fa zan dan nemi kudi anan yankin saboda kinga yanayin ki baza mu iya jure tafiya da kafa ba gashi bansan ina zamuje ba..

Nace ummah kudi kuma ta yaya zaki samu anan?

Tace "Ke dai bari mana ki gani naga kamar akwai aiki wajen wancan bafulatanin tayi min nuni da shi wani manomi ne sosai ana kan hidiman masa dure a buhuhunan sa ..

Nace to ummah ..nima zan taya ki

Ta girgiza min kai alaman ah a na huta kawai nan ta mike tabisa wajen su..

Cikin hikima da dabara irin nata ta cire kasala da gajiya ta hau aikin ma bafulatnain nan kamar bakar jaka..
shikan sa sai da ya sha mamaki..

Buhuhu na 15 da rabi na sabon gyero umma ta samu ta dura masa kafin nan an aneman goma saura na dare sai layi da haki take idanun ta sunyi jajir dan wahala..

A hakan ma bata daddara ba duk da ma ummah na da saurin sabo amma anan ba wanda ya san meke faruwa da mu tace ma matar gidan insha Allahu washe gari zamu tafi idan aka biya ta..

Anan muka kwana bata mana rowan abinci ba kuwa,muka sauke gajiya cikin daren har da wanka....

Washe gari ban tashi ba tsaban yadda nake ji da tsamin tsamin duka ajiki na ga laulayin ciki da kananun ciwon mara.

Umma kam tuni ta bi layin karbo kudin aiki...
Dubu10 kacal ta samu
A haka ma ji tayi kamar an tsoma ta a Aljanna

Ta zo ta daga ni tace maza ki shirya yanzu zamu tafi kar azo agan mu anan yankin saura mana yanki 2 mubar kurwala....yi da jikin ki saratu..

Nace toh umma na mike adaddafe na shirya ..

Fura mai kyau ummah ta siya dukan mu uka sha harda matan gidan..
Umma ta bata hakura ta bata dari biyar daga kudin aikin ta.
Daga nan muka fece....

Tafiya muke, duk da haka ba Abun hawa
Ciwon ciki na sai dada tsanantawa yake ga waje da nisa gari biyu zamu wuce amma ko rabin daya bamuyi ba ..

Tun ina boye ma ummah abun da nake ji har na soma wash washhh...

Anan ta riko nj niki niki tana mun sannu sannu in mun danyi nisa sai mu zauna bakin inuwa mu huta
Idan naji dama dama sai mu wuce
Har muka fice gari na biyu muka shiga na karshe..

Ido na yayi ja sosai, tsaban azaban danake ji aciki na..umma tace ki daure saratu ba abun hawa ne da sai na daura ki kije tashan mass kki jira ni,
Amma babu kiyi hakuri kinji..?

Anan na dan soma zub da hawaye na sosai..nace babu komai ummah amma cikin nan ne sosai yake murda ni..

Cikin damuwa ummah tace kiyi hakuri saratu nasan dole zaki ji wahala bari muyi sauri mu samu mota sai ki huta...ko zaki ci wani abun ne yanzu?

Na ce mata ah"ah

Nana Ta cigaba da lallabani muka soma tafiya..

tausayin umma ya sanyaya min zuciya ta naga kamar tama mance da kanta a kuncin rayuwa da bakin cikin da aka cusa mata ni kawai take kulawa
Chapter 8 · 0% Book details