← Book details Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 103

Sashe 39

Samarin Shaho Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kuma duk report sai ya zo wajen ta ta duba kafin ayi aproving.

Lokaci guda wajen ya dawo sooo busy..

Ga clients da al'umma sai dada samun wayewar kai suke ta dalilin sabbin tsarin da ta kawo musu masu jan hankali da amfani ga rayuwa

Suna bada taimako sosai don organisation din is well registerd with sharia law and judiciaries

Akwai kwarrarun hukuma dake bin cike sosai sabida haka kowa yake
Daukar abun da muhimmnci

sannan Yanzu ana tattaunawa a gidajen redio da talabijin ana yada sakon bada taimako ma duk wanda yake halin ha'ulin rayuwa da zalunci makamancin irin wanda ta fuskanta a baya da ma wanda suka fi su akan su garzayo za a taimake su anan whra office Sannan an bada numbobi da adreshi a ko yaushe domin samon su akan kari.

Yanzu sarah ta zama zakara,tauraruwa duk da presence din su hajya asma da mrs ruth din amma hakan bai cika damun ta ba

Ita dai gani take suna tsoron su mata wani abu yazeed na nan zai tona musu asiri

Har yau da ake shirin kaiwa Wata uku da samun nasaran ta ba wanda ya sake gaya mata maganan banza ko yayi accusing dinta da yin wani abu

Sosai take jin abun aranta a duk lokacin da ta ga kanta sai ta tuno da yazeed ne ne ya sama mata wannnan matsayin kwanciyar hankalin.

Gashi tana rayuwar taimakon jamar ta peacefully kamar yadda ita da ummahn ta sukayi buri

Shikuwa tun ranar da abun ya faru sai ya dauke kafar sa baki daya batare da ya sanar da kowa ba.

A bakin farida sectaryn sa take jin ai tun ranar yayi tafiya yaje paris hutu.

Anan Sai da ya shafi wata biyu masu kyau kafin ya dawo aiki

A kullum inta zauna Haka kawai take jin missing dinsa, his oderz his smiles his smartness and oll taht sai dai ba wanda ya lura da Hakan

Ranar da ya dawo ta so ta boye jin dadin hakan amma she cudnt

Ko da suka hadu sai da ta bashi impresion din she's glad that he's back
Duk dama bata furta masa boro boro ba

Sosai ya gane ta sake da shi kuma zuciyan ta ya aminta da shi yanzu..

He just knew that yana bukatar wanzar da hakan da kyau a zuciyan ta yana bukatar ta fara kaunar sa da kanta Ba sai ya furta mata ba.

Tunda ya lura da yanzu bata daga masa kai ko bai mata smile ba zata mayar masa..

Sai ya shiga jan jiki yana basarwa cikin hikiman sa.

Ko ajikin ta don har ila yau ita gani take maybe baya son ya sake da ita ne sabida da chan din ma sabida aiki yasa suke yawan samun acquintances..

Hankalin sa a kwance yake, yana kuma watching move dinta sai dai shima har yanzu yana yabawa da kamun kanta

yasan dai yana cikin zuciyar ta amma sai yake imagining da ace wata ya mace she wud have been loose ta kowa ni hanya don ta nuna Masa abun
dake ranta

amma sarah is trying to keep thing low and casual duk dama yasan abun ya fi karfin haka aranta..

Yasan mata kala kala a duniya so he can tell the difference,"sarah daban ce."

Yau ta kama juma'a yau din ne aka kawo case mai zafi wanda ya kuma yafii la'akari da irin rayuwar ta baya..

Sunan yariyanr dijeh, sai dai ita cikin nata har ya girma yakai wata uku ajikin ta

Tare da kanwar mahaifiyar ta suka zo neman taimako wajen sarah

Da matar ta gama bata testimonyn abunda ya faru da su,,..Hankalin ta ya tashi kam ba wai bai tashi ba amma a duk sanda ta fara shiga wani halin tuno da kanta sai ta tino da maganganun mahfud da duk abunda ya gaya mata a baya na cewa zata iya..

Karfin gwiwaar ta kenan
Kuma words dinsan Ke bata daman jin zata iya daukar case din duk dama zaluncin da akai ma dije ya kusan fin nata..

A cewar kanwar maman dije har yan kauyen su sarki,da mijin mahaifiyar dije sun sa wuta an kona mahaifiyar dije da rai bisa sharrin kazafin maita da aka daura mata
Mai tsanani

Sun dai tabbatar da cewa sun samu sun fitar da ita daga wutar amma yanzu haka tana yashe a wani gida rabin jikn ta ya riga ya kone sosai sai kakarin nishin mutuwa da azaba take yi cikin wani hali
Sunje asibiti anki karban su

Dije dake kunshe da bakin ciki ta kuma tabbatar ma sarahn da hakan duk shiri ne a zahirin gaskiya mahaifiyar ta bata maita,
Tace "sharri ne kawai. shigen irin yadda a kayi ma ummahn ta kazafin karuwanci da safaran miyagun kwayoyi.

Sosai ta fahimce su sabida itama tabi ta wannan hanyar amma su basu sani ba.

Lokaci guda tausayin su ya girgiza zuciyan kowa dake wajen sarahn Sai ta bada oder a rike su anan ana kula da su ita zata taje dakanta wajen mahaifiyar dije tare da ambulance don akaita asibiti.

Fitar ta ke da wuya sai ga motar hajiya asma da safeenah tare da wasu baki..

Ta fahimta sosai officials ne na humanatarian na kasa...
Mace da namiji ne da wata tsohuwar hamshakiyar mace.

She can recall that suma manya ne daga dayan agency amma su sunfi aikin su achan kasar india..

But yanzun Thy wll be staying here for some months as well.

Fargaban ta bai wuce su mrs ruth da hajiya asma ba amma duk da haka yanzun bawai ya dame ta sosai bane,itace WHRA president kuma tasan akwai mai tsaya mata sannan bakar aniyar su akan ta shine babban madakata tsakanin su yanzu.

Tana daga kan hanyar fitowa tare da medical agents a sace take duban su suna ta tattaunawa safeenah na gefen su.....

Ko da ba fada ba tasan sun san juna sosai tunda aikin su duk iri daya,

Kafin su shiga mota sai ta dakata, tace ma team din med agents din sufara gaba

nan ta taho ta iske su tsaye jikin mutane ganin yadda dafeenahn ke binta da wani irin kallo yasa dukan su suka dan hankara,

I bet shes the current whra president... tsohuwar tafada sarahn naji,

Murmushi ta dan yi ta ce yes maam you are higly welcome...
Ta gaishe su cikin ladabi da biyayya,

Mr abdlrasheed rani ya dube ta yace she's young,..amma maganan san yana refering ma yan uwan sa en irin su duba ashe dasgke karamar yarinya ce aka bata wannan damar..

Hajiya asma ta so ta kara nata amma sai ta tuno da idan maganan yayi nisa za ce ai safeenah ma kusan sa'ar sarah ce..

Ita kam sarah bata damu ba Anan ta ke sanar da su zata tafi da medicals emrgency humanatarian case..

Lokaci guda suka hau kai kowa yana so yaji, batayi kasa agwaiwa ba ta gaya musu sam sama abun da ke faruwa.

Sannan suka dada bata karfin gwiwar cigaba anan ta wuce ta barsu.

Sam abun baiyi ma hjy asma ba,don bata son wayannan ma su ce zasu bi bayan sarah..
So take ta samu memebrs wanda zasu takura rayuwar ta anan har su samu mafita ma yarta..

So suna shiga office kowa ya kama aikin gaban sa

Duk dama su ukun nan waje daya suke zaune ana yi ana kawo musu sun supervising

Bayan awa uku da rabi hajya asma ta fito ita da mrs ruth Daf da hanyar da zai kaita office din bakin nasu sai ga wasu mutane

Wani gardi ne da abokin sa da agents..

Sai suka tsaya cikin mamaki suka Ce ina zakuje haka?

Gardin da shike dattijon bakauye ne sai ya fara musu bayanin shine wanda ake zargin sa,... yaji ance dije ta kawo karar sa nan shi yasa ya zo ya shawo kan ta ko zasu sasan ta kar ayi masa hukunci..

Kallon kallon su mrs ruth suka bada juna su,daga bisani tace kenan tsoron hukunci ya kawo ka ba nadaman abunda kayimata ba.?

Yayi shiru abunsa yana tsuru tsuru da ido..

Nan sukayi dan kuskus cikin harshen turanci mrs ruth take cewa yanzu ne dai dai lokacin da zamu fara bata wahala, its time for us to do something ai idan tasan wata bata san wata

Wannan case din babba ne kuma kinga team din india sun soma sa mata baki,muma nan Ya kamata mu nuna musu gazawar ta na cewa sarahn tayi karama ma responsiblityn da take dauka

Inyaso mu zamu nemo a namu jinin Ko assistant a laka mata yadda zamu samu daman wargaza ta lokaci guda..

Beside idan muka nuna boro boro cewa macen da bata yi aure ba ta ina zata san ciwon zamantake war aure za a fara yarda damu....
Its too obvious.

Hjya asma ta dan jinjina kai tayi ajiyan zuciya tace ai dole ma a yarda, sabida ba komai bane zaka karanta a littafi ko ka koya a makaranta kace za kayi aiki akai you need to have some physical challenges and constructive demonstrations

Mrs ruth tace to ya za muyi da shi?

Hjya asma tayi murmushi tace relax mu bar na wajen tukun..

Kai Malam biyo ni... tafada tana kallon su duka

Nan suka juya offishin su shikuwa na biye da su a baya..

OFFICIALL Catty
[2/24, 06:28] ‪+234 802 646 5734‬: *🅱RILLlANT WRITERS ASSO🖊*
{ _pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_ }
™\jan\2019
🍒🍒
*SAMARIN SHAHO*
_The scorned_
🍒🍒
*#lovestory:#destiny@fault#purefic#thriller:#romance,any resembelance of life or story shud be considered as a coincedence i give no permission for copy or comparison#copycat*
_A true sensational story_
*VOTE STORY AND FOLLOW WATTPAD@ SURAYYAHMS*

_PAGE19_

Daga shigar su office suka shiga kulla ma gardin nan maganganu cewa ya nace akan karya ya kuma jajirce dacewa shine da gaskiya akan lamarin su zasu taimake sa..

Gani suke idan har ya taimake su sarah ta fadi a wannan case din gaban wayannan bakin,ba za sake daukar ta da wani daraja ba daga haka zasu fara karya mata mulki har sai sun cimma burin su..

A bangaren sarah kuwa abun ya bata mamaki ganin Kafin ta iso yazeed ne akan case din a asibitin har yasa an fara ma mahaifiyar dije aiki..
Chapter 39 · 0% Book details