Sashe 7
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
amen ya Allah nandai suka dad e suna tattaunawa saida sukaga lokacin sallar azzahar ya gabato sannan sukayi sallama kowa ya shiga motar sa. Baton makarantar su Mansura dai ya tabbata,domin kuwa su Dady sun tsayar da makarantar da za akaisu anan cikin Kano,sai ba makarantar gwannatin za akaisuba kamar yadda shi Mansur yaso Dady yace ba tsaro, badan ransa yasoba aka samar musu CRESCENT INTERNATIONAL SCHOOL , lokacinda su Abba suka buk aci ganinta itada Ruk ayya afalon Ummi, gabanta sai fad uwa yakeyi dukda Batasan mi kiran ke nufiba, ta tararda Ruk ayya zaune kusa da Dady hakan yasa itama tasamu waje kusada da Ruk ayya ta zauna tana gaidashi, amsawa yayi yana mai gyara zaman sa kafin yace ba komaine yasa nace inason ganinkuba saidan in shaida muku kufara shiri in sha Allah acikin k arshan watannan zaku koma makaranta da zama gaba d aya abisa shawaran da muka yanke, munriga da munyi komai lokacin fara zuwa kawai ya rage, dan haka kufad I duk abinda kuke buk ata zanba yayanku ya saya mukushi tunda Dady yafara maganar makaranta jikin Mansura ke rawa ga hawaye nason su zubomata alamar sonyin kuka, dan haka yana gama magana tayi saurin cewa amma Dady naji kana kiran mukuma makaranta da zama kamar ba day bace kenan? aramar dariya Dady yayi dan dama yasan za ayi daru da ita sannan yace inbanda abinki Mansura, ai tunda kikaji nace kukoma da zama kinsan ba day bace bording ce, mun yake shawarar nanne abisa wani dalili dan haka kiyi hankuri kuje tunda keda yar uwarkice ba abinda zai faru, duk abinda nasan zaku iya buk ata muntadanar muku dashi sai abinda kuka fad a za ak ara samar muku kukan da take k arin rik ewane ya kucce mata tareda fad in ni Allah Dady banason bording school amayar damu day kawai,nasan wannan duk Yayane yasa kukaimu saboda baya k aunata, agidannan bawadda yayi bording saimu dan ba asonmu, bayan naji ance anaba mutane wahala sosai hatta ruwa d iba akeyi tak arasa fad a hawaye nak ara zubomata, janyota jikinsa yayi yana lallashinta yace ba abinda zai faru sai alheri, sannan kingaba jss zakuba ss1 ne zaku shiga in sha Allah bam ai wahalar min da ya kinji ki daina kuka, nima baa son raina bane dolene yasa bisa wani dalili namu, sannan kidaina fad in Yayanku bayasonku soyayyar da yake mukuce tasa yace akaiku acan dan kusami kwanciyar hankali da natsuwar yin karatu, kar ink arajin haka kinji? Kai tad aga alamar taji yace to share hawayan naki daina kuka ba abinda zai faru, dakin saba zakiji dad inta sosai nanma kai tad aga tana share hawayan da gefen hijabinta, nasiha yayi musu sosai kafin yace su tashi sutafi, tashi sukayi jiki ba karfi sukayi cikin d akin har Mansura. Awannan yinin bak aramin kuka Mansura tashaba dan kuka tayi sosai har idanunta suka rikid a, jin take bazata ta ba yafema Yaya Mansur ba hart agama makaranta,jin tsanarsa take har cikin zuciyarta ko sunansa batasonji, anyi lallashi har suka kyaleta har zuwa lokacinda taga damar bari, Hajo ma saidai tazuba mata idanu tunda taga abin nata bana k arewane nan kusaba, itadai Ruk aya tayi daga baya tayi shiru tunda taga dai dole wannan tafiyar ba fashi, to miye nawahalar dakai tazo tajama kanta ciyo daga baya. Har dare Mansura na kuka ga kanta tanajin kamar ya rabe biyu saboda tsabar ciyo ko abinci tak I taci, bayadda Hajo tayi da ita taci ko kad anne inyaso taci gaba da kukan tunda shi takeso amma tayi mata banza dole tarabu da ita, karfe tara da kusan rabi Mansur yashigo gidan, saida yaje yagaida iyayansa sannan yazonan bangaran Hajo dan yasan nan dole Hajo zatajashi da fira, shigowa yayi da sallama yasameta zaune itakad ai ta zuba uban tagomi, dandai ita harga Allah dan bayadda zatayine ta hana zuwa wannan makarantar ne, dan kukan da Mansura takeyi jinsa take har cikin ranta gashi tunda taji batun zuwan wannan makarantar tunda safe tak i cin abinci har zuwa yanzu sai kukan da take. Hajo lafiya kika zuba tagomi haka wani abinne ya faru? sai alokacin Hajo tasan da shigowarsa ta d aga kai tana kallonsa tace yaushe ka shigo mai sunan Malam banji shigowarkaba? zama yayi kusa da ita akan kujerar da take mai zaman mutun biyu sannan yace yanzunan nashigo kuma natarar da kinzuba uban tagomi haka alamar kina cikin damuwa, kuma yanzu na fito daga cikin gida amma baga wani alamon wani abu marar dad I ya faruba, gayamin mike damunki kodai kin tuno da tsohun mijin kine inji? kanada abin dariya mai sunan Malam ai tunoda mijina wannan wajibine tunda acikin ko wace sallah ina masa addu a, niba wannan ne abinda ke damunaba Mansura ce tunda taji Dadyn ku yagaya mata batun makaranta take kuka tunda safe kuma tak icin komai, gudun danakeyi kar taje tajawowa kanta wani ciyo daban, tunda dai bataso abarta asata wacce takeso kar aje ashiga hak inta ajiyar zuciya ya sauke jin abinda yake damunta kenan ba wani abinba yanzu dan Allah shine kike zama kisa ranki adamuwa, idan tak ici cikin waye ba nataba? Yunwarce bata damaitaba da bakisani lokacinda zataci o o mai sunan Malam kar muje mushiga hak inta, nidan idan har akwai yadda za ayi acanza mata kawai mik ewa yayi yace ina zuwa bari inje in watsa ruwa inajin jikina naming naiyi kaallonsa tayi ganin har yanaso tafiya tace ya inama magana zaka tafi, kodan bakad au maganar tawa da muhimmanciba? yadda kakeda iko akanta kasan nima inada nawa ikon ko? Nasani amam ba kamar nawaba yafad a yana mai hucewa gaba d aya karma tasamu jefomasa wata maganar. Kai tsaye d akinta ya huce dan ya kula rainin yarinyarnan yawane dashi, dolene sai anyi mata abinda takesone, kenan ita bazata iya yin abinda akace tayiba sai abinda takeso. Kwance yasameta akan gado ta rufe har kanta tana sheshekar kuka, dan kanta ke mata ciyo sosai har batason d aga kanta, jin muryarsa tayi alamar cikin fushi yake yana fad waike kowa nunawa kike bakida kunya, kan ance miki zaki makaranta zakibi ki tayarwa kowa hankali da kukanki na banza harda k incin abinci, to bari kiji ko mutuwa kikayi ba wanda yayi hasara dan bake kad aice agidanba, kuma kuka in na jinni zaki kiyi kigama makaranta kingama zuwanta ki mutu kafin gobe inga k in rashin makaranta yana gama fad a yayi juyawarsa ya fita. Wani irin bak in cikine ya tokare mata wuya amma ba halinyin magana saboda yadda takejin kanta, kuma tana gudun ya wanka mata wannan marin nasa maisa mutun ya rud e dan ba imanine da shiba. Haka tayi ta fama zuwa wani lokaci jikinta har cira yakeyi. Hajo ganin Mansur yad au lokaci bai dawoba yasa ta nufi d akin Mansura,dandai ita rashin cin abincin nata ya dameta, ace mutun tun Karin safe bai kuma cin wani abuba har zuwa yanzu karfe gama saura. Da sauri tak arasa tana kiran inna lillahi wa inna ilaihim raji un ganin yadda take dafe da kanta tana kiran wayyo kaina, kaina zai cire wayyo Abbana Momy kizo zan mutu tallabota tayi tana rungometa jikinta zau zafi kingani ko? Dama nasan wannan kukan da kikeyi dolene kijawa kanki ciyo, kinji jikinki da ya gashe da zafi kuwa? kwantar da ita tayi tace bari ina zuwa fita tayi daga d akin kai tsaye d akin Mansur ta nufa. Samunsa tayi ya fito daga wanka ya shirya cikin kayan bacci, dogon wando ne sai rigarsa marar nauyi yana zaune akan kujera yana aikinsa na fama wato dannar laptop, jin turo k ufar kuma batare da iziniba yasa ya d ago kansa dukda yasan bamai masa haka sai mutun d aya, ganin wace d in yake zatoce kuma kamar ad an rikice yace miyafaru kuma? Mai sunan Malam dan Allah ka kira mana likintan da zai duba yarinyarnan, gashican sai kuka take tana kiran kanta zai fashe zata mutu, kar wani abu yaje yasami yarinyar nan . o my god, kinada matsala tsohuwar nan wallahi, wai miye nadamun kanki tunda ba wani abu aka mataba, ko miye bai ta tajanyowa kantaba? Kije ki kwanta abinki ki kwantar da hankalin ki da mamaki take kallonsa tace ayya kanka d aya mai sunan Malam? In kwantar da hankalina fa kace? Sai mubar yarinya acikin wannan hali? To idan bazaka kiraba bari inje inkira wad anda na isa dasu suyimin abinda nake buk tafad a tana mai juyawa zatabar d akin. Kansa ya dafe yana fad Hajo rigima kuma yasanta sare zata fita yanzunnan ta tayarwa su Abba da hankali ne kawai, kuma shi baisan wadda zai tayar awannan lokacinba akan abinda baicai ya kawoba, dan haka yayi saurin tsaidata dan har takai bakin kofar tsaya ina zuwa tajisa amma bata tsaya tayi tafiyar ta dan taji haushinsa, saida ya tsaya ya d au Panadol dan yasan tajisa sarai kyalesa kawai tayi, bayanta yabi shima, Rungome yasameta da ita dan yanzu ko kukan takasa yi sai juya kai da takeyi, kauda kansa yayi gefe kamar ciyon nata bai damaisaba, sai sannu Hajo ke zuba mata tanajin kamar ta maida ciyon jikin ta, ruwan tea yace ma Hajo ta samar masa dan dolene kafin tasha magani sai tasawa cikinta wani abin, ba musu Hajo ta maidata kan gado ta tashi ta fita. Da kanta ta had a ruwan tea mai kauri tazo ta kawo masa,kar ba yayi ya nufi kusa da ita adake yace bi nan kisha jin yadda yayi maganar ba alamar wasa aciki yasa adaddafe ta tashi zaune Hajo ta taimakamata ta zauna daidai, Hajo ce ta kar bi kofin hannunsa ganin takasa kar ba dan jikinta yar rawa yakeyi, bata tashigayi tana mata saunu, ahankali take shansa dan tsayen da yayi akanta tasan ba wasa acikinsa kuma harga Allah tanajin yunwar fitinace dai irin tata, saida tagama shanye tea d in gaba d aya sannan ya balla maganin ya bata, arayuwar ta magani na d ai daga cikin abinda ta tsana dan haka ta duk ar da kanta tak I kar ba, zan sa ba miki idan baki kar bi maganinnan kinshaba, kinbi kin ishe mutane da koke kokenki