Sashe 33
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dan gudanar da aikin sa, shi sai ayanzu yake tunanin ya zaiyi da wannan 'yar anacan da zabi ta takurawa rayuwar sa, kuma yasan shidai bazai ta'ba rayuwar aure da itaba komai za ayi, rok'on Allahn da yake Allah kabashi ikon samun abinda yakeso ga mahaifin ta yayi waje room da ita, dandai shi tun ayanzu yafara jinsa atakure, janye tunanin komai yayi yaci gaba da aikin sa har zuwa wani lokaci, yana cikin aikin ya fara jin bugun k'ofa ahankalin, sharewa yayi kamar baijiba yaci gaba da abinda yake, tun ana bugu ahankali har aka fara bugawa da k'arfi, amma dan taikinnan duk bugun da take ko gizo baiyiba bale tatashi har tagaji tabar wurin, saida ya gama abinda zaiyi sannan yaje ya kwanta, shine bai tashiba saida yaji kiran farko akunnuwan sa, tashi yayi yayi alwalla ya fita zuwa masallaci dakenan kusa. Tun Bashhama na zuba idanu zataga Mansur har yafara d'ebe tsanmani, gashi abubuwan da tayi d'irkawa cikin ta sun fara tasiri akanta, wani abu takeji ajikinta kamar ana tsinkarar ta, ba abinda take sai matse-matsan k'afafu da runtsar idanuwa, ganin abin bana k'arewa bane yasa ta sauko daga kan gado ta fita daga d'akin zuwa d'akin nasa, duk bugun duniyar da tayi bai bud'e ba har tagaji ta dawo nan parlour ta kwanta tana juye-juyan ta, awannan daran Bashhama harda kuka tayi ba d'an kad'an ba, domin abubuwane tasha bana wasa ba dan kawai ta burgesa da kuma tushe duk wani abu dazai gane ba shine mutun na farko da zaisanta amatsayin d'iya macce ba, duk da tun dawowar ta Nigeria rabenta da kula wani d'a namiji dande kawai tana gudun watarana ya samu labari yace ya fasa auran ta, duk da bibiyar da ake mata amma ta daure ta shanye dandai kawai ta auri cikar burin ta, har zuwa tayi tasamu doctor na musamman yayi mata d'inki ciki da waje, amma gashi duk wannan zai tashi abanza awofi, kuka tayi babu mai lallashin ta har tagaji ta lalla'ba kanta ta tashi ta koma cikin d'aki ta kwanta, batasan lokacinda baccin wahala ya d'auke taba, itace bata tashiba sai kusan 8:36 am saboda rashin baccin da batayi ba aaran jiya, jiki duk amace ta tashi tashiga ban d'aki tayi wanka ta fito ta shirya, ita sallah ba ama batun yinta kai tsaye d'akin Mansur ta nufa. Tayi sa'ar abud'e take bayan ya dawo masallaci bai rufe ba, ahankali tashiga ta maida k'ofar ta rufe, bacci yakeyi hankalinsa kwaci ba abinda ke damun sa ita yabarta da juye-juyan wahala, fuskar sa take k'arewa kallo wacce ke zagayi da kwantaccan saje wadda batada yawa sosai sai taga ya k'ara mata kyau sosai, jin take kamar ta zauna daga ita saishi aduniyar nan, tana masa son da ita karan kanta batasan adadin saba tana matar su rayu tare su mutu tare, tunanin take miya 'bata masa rai adaran amarcin su wadda ko wane d'an adam ke fatar ganin sa, itadai aganin ta babu wani ango da za akawowa amarya adaran yayi ko oho da ita, tasan duk da itace ke sonta amma yana bata kulawar da ba kuwa bane zai gane bai damu da itaba, wasu sukance halinsa ne ahakan amma irin su idan kaje gidan auran su zaka d'auka ba shibane saboda yadda suke nunawa matan su soyayya, amma ita tun ajiya taga sa'banin haka, hawaye ne suka cika mata idanu har suna gangarowa akan fuskar tata, k'ok'arin maida su tayi duk da sun riga sun zubu ta juya tabar d'akin. Tun lokacin da ta bud'e k'ofar ya farka domin baya da nauyin bacci ko kad'an, abu kad'an ne zai farkar dashi, duk abinda take yana kallon ta har tafita daga d'akin,yaji tausayin ta dan ya tabbatar da Bashhama nasonsa ko irin yadda ta juri wulak'ancin sa, duk abinda yayi saidai ita ta koma basa hank'uri "Bashhama laifin mahaifinki ne ya shafeke da kuma mumunar rayuwar da kikayi, domin bazan ta'ba rayuwa da irin azzalummai maci amana kuma mayaudara, banci haka kuma kin riga da kin 'bata rayuwar ki ta gur 'batacciyar hanya, yanzu haka kallon k'azama nake miki wacce ke iya rayuwa dako wani irin k'azimi, kin zama rijiya dako wane mutun zai d'auko k'azamar gugarsa ya sanya, koma ko ba wannan ba bakida gurbi acikin zuciyar ta domin wacce keda muhalli daban take" afili yayi maganar yana mai lumshe idanun sa, tashi yayi wanka ya shirya cikin d'inkin shadda milk wacce tasha aiki madai-daici,ya d'auko hullar da tadace da shadda ya sanya tare da fesa turarukan da yake amfani dashi sannan ya fita daga d'akin Zaune ya tarar da ita aparlour tana kallo a tv, tana ganin ya fito ta tashi tsaye tace "Beood morning my husband" Morning kawai yace da ita, zama yayi yace "ina breakfast d'inan?" da mamaki take kallon sa ita datake jiran ya tashi abacci ya samar mata abinda zata karya amma yake mata wannan tambayar. "Wai bake nakewa magana bane kika saki baki kina kallo na?" ahankali tace "Breakfast fa kace husband? nifa kasan agida bana komai saidai in tashi in gani kan denning ko in na buk'ata akawomin, ni nan ko indomi ban iya girkawaba, kayi hank'uri kaje gida ka kar'bo mana ko mushier ya muje gidan cin abinci muci acan" ta fad'a tana kallon sa Kallon bakida hankali yayi mata kafin yace "ko d'aya bazanyi ba idan zaki tashi ki girka to, idan kuma bazaki girka ba wannan tarage gareki ba abinda yasha min kai ni kinga tafiyata" ya fad'a yana tashi tsaye "Haba husband yazakace haka! bayan kasan ba iyayi zanyi ba, kuma ma da zuwana ajiya ace yau nashiga kicin, gaskiya ni bazan iya ba" "Dama za'bi na baki idan zaki iya, domin duk abinda kika fad'a ba mai yuwa aciki don iyayena ba bayin ki bane sannan sisina bazaiyi kuka awajan sayan abinci tunda komai na buk'ata akwai akicin" tana k'arasa fad'a yayi tafiyar sa. Hawaye ne suka zubo mata a idanu tana cewa "wannan wane irin miji na aura ne? shi komai yazo masa ba ruwan sa aciki, yanzu ita taya tasan yadda zata sarrafa danyan abinci har ta kuma ninanne, gaskiya da saki dole ne ma tasa a nemo mata mai aiki bare dai ya dawo" dole ba yadda zatayi ta tashi ta shiga kicin ta d'auko ragowar kazar jiya tazo ta zauna taci tunda tanajin yunwa. Mansur yana fita motar sa ya shige yayi mata key mai gadi ya bud'e masa ya fita, kai tsaye gidan nasu ya nufa ransa na mugun 'baci har jijiyoyin kansa suna tashi, le'ben sa na k'asa ya kama ya ciza yana fad'in"lallai yarinyar nan 'yar rinin hankali ce, wato ni zata fad'awa bata iya girka komai ba, zako tagane batada wayo, dan wallahi ba inda zaije ya d'auko mata abinci ko yasanya" Yana shiga cikin gidan yayi parking motar ya fito, part d'in Hajo ya nufa domin yasan dai yanzu tana falo tunda dai shine wajan zamanta kullu yaumi, idan har kaga tashiga d'aki taje salla ne ko bacci amma tafison zaman ta afalo. Zaune kuwa ya tarar da ita tana rik'e da azkar tana karan tawa, azkarul saba walmasa take karan tawa afili da guda-guda tana gamewa, sallama yayi ta d'ago kanta tana fad'in "wa nake gani kamar ango da farar safiyar nan?" Dariya Mansur yayi yace "haba Hajo yanzu fa karfe 10:15am amma kike kiran safiya sai kace wanda yazo karfe bakwai, mi aka dafa agidannan ne? wallahi yunwa nakeji kamar amin satar hanji" "Da alamar dai wannan amarya batasan kanta ba, wacce amarya ce zatabar angon ta ya fito daga gida yanajin yunwa" "Inbada abinki Hajo ba kobane zako kai mata tunda bak'uwa ce ita, amma kuka kyale ba wanda ya tuna damu" baki ta ta'be tace "wane marar aikine zai d'au abinci yakai muku ita tananan tana bacci" Baice mata uffan ba ya janyo abinci yafara ci, waina ce da miya domin ita yau Momy tayi abinda zabayi breakfast da ita. "Ayi dai mugane idan tusa zata hura huta, kuma duk wadda yasai rariya yasan zatayi zubar ruwa... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 35 Mansur dake cin wainar ya d'ago kai yana kallon ta da mamaki "mi kike nufi da wannan maganar Hajo?" ya fad'a yana k'ara kai wainar bakinsa "Abinda nake nufi da itamana! kace mana ka aure tane danyin aiki da ita wanda ka d'au shekaru biyar kanayisa, shin tayaya ita dake gidanka zata maka aiki akan mahaifin ta? sannan haka zaka dinga kai kawo tsakanin can danan doncin abinci? shin kana ganin baka janyowa kanka aiki babba ba?" Plate d'in gaban sa na wainar ya janje ya jiyo yana fuskantar ta tare da gyara zaman sa "tabbas zanyi amfani da ita ta yadda ita kanta batasan amfani zanyi da itaba, zan jefe tsuntsu biyu da dutsi d'aya, tunda na tabbatar da wad'anna ta kaddu suna ahannunsa zansa ta d'auko minsu duk da inada cikakkiyar hujjar da zaisa agurfanar dasu gaban koto amma inada buk'atar wata shedar, kinsani Hajo tunda kikaga na canza tsari akan burina na zama doctor da nataso dashi tun yarinta nazama acikin aikin da ko amafarki ban ta'ba kawosa araina ba domin d'aukar fansa, nasan Allah zai shiga wannan lamarin in sha Allah, nidai abinda nake rok'on ki akai kici gaba damin addu arnan da kika saba" "To mai sunan Malam ai addu a akullun cikin ta kake kuma bazan fasa yimakaba sai ranar da nabar numfashi adoron duniyar nan, nidai rok'o na dan Allah kar kabari muhad'a zuri a dashi da zaisa har ana alakantamu dasu" Kai tsaye ya fahinci ida maganar tata ta dusa dan haka yayi k'aramar dariya wacce sai in yaso yakeyin ta "ki kwantar da hankalin ki Hajjajo in sha Allah hakan bazai ta'ba faruwa na, dan gujewa haka yasa tun jiya na za'bi kwana d'aki daban itama ta kwana adaban" Kallon amma bakada hankali take masa sannan tace "haba mai sunan Malam bazaka iyaba?" "Miyasa kikace haka?" "Saboda nasan abinda bazai yubane, ka kwana da macce agida d'aya sannan kace ba abinda zai shiga tsakanin ku alhalin kana mutun lafiyayye, macce ma wacce kasan ta halatta agarika tunda an d'aura muku aure da ita, bayan haka shaid'an zaiyi ta