Sashe 39
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
saidai mu rok'i Allah ya kawo mana mafita" "To Allah ya kawo mana mafitar" Hajo da tabiyo bayansu taji duk abinda suka tattauna da juyasu acikin k'wak'walwar ta, minene Mansura tagani takasa fad'a agidan mai sunan Malam? batada mai bata amsa haka yasa ta juya tayi komawar ta dalo tana fad'in "idan tayi tsami maji" haka Mansura tayini cikin damuwa da mamakin abinda ta gane wadda bata ta'ba ganiba tun tashinta, saida kasancewar zaman da tayi a boding yasa tasan abinda wannan abin ke nufi, dan sotari ana kama yara y'an makaranta awannan yanayi harma sunsan dayawa daga cikin su, saidai kasancewar su yarane masu kamun Kai da tarbiya, duk yadda akace bayada tarbiya suna kafa-kafa dashi, kuma duk wadda ya kawo mata wargi zasu tsigesane ba ruwansu, amma yau gashi tagani ganin idonta, Allah kar yakoma nuna mata wannan ranar da zataga wannan abin ko amafarkin ta. To Allah yasa Ummi bataga dowar tasuba sai bata damu ba koda tagansu bayan magriba harda tambayar su Bashhama sukace lafiya k'alau take. Akwana tashi hasarar mai rai kwanakkinmu sai tafiya suke, yau gashi har an canye watanni goma da sati biyu, yau kina in bakwai da auran Abida da Alhaji Kasim tana gidan ta abinta cikin kwanciyar hankali harma daguzirin ciki na wattani hud'u, tarugume marayun 'ya'ya da uwarsu ta rasu ta bari, dukda aciki akwai matashiyar budurwa wadda ak'alla zatayi warinsu Mansura, yaran sunada tarbiya dai-dai gwargwado dan haka takejin dad'in zama agidan, Alhaji Kasim bai ta'ba nuna mata wani abu ya ta'ba samunta, duk da alokacin su Momy sun taka rawa wajan gyara ta yadda zatasumu martaba agidan miji, dan haka ba abinda Abida zatace sai godiyar Allah. Su Mansu y'an makaranta sun maida hankalin sai karatu suke saboda jarabawar dake kusantusu ta gama makaranta, yanzu haka sun sami hutu na sati biyu suna gida sai shan hutunsu suke, kuma har zuwa wannan lokaci tagaza fad'in abinda tagani, tun Rukayya namata naci har tarabu da ita. MAFARIN Yau an waye gari ranar alhamis Mansur ya tashi bayada lafiya ko fitowa ya kasayi, gashi yarasa yadda zaiyi ga yunwa yanaji kuma arayuwar sa Mansur bayacin abincin y'an aiki saboda mugun k'yank'yaminsa, ga Bashhama ma bawani kulata takeba, dan har yanzu da zasu canye kusan shekara da auransu ba abinda ya canza nadaga zaman su, tun Bashhama tana tunanin abin nawasani taga abin ya huce waje, duk da tana samun inda take rage damuwar ta amma har zuwa lokacin bata daina jin abinda takeji gameda Shiba, dan haka itama yau duk da tasan bayada lafiya ta shirya masa wani makircin da baisan ana shirya masaba. Waya ya d'auka yayi kiran Ummi bayan ta d'aga ya gaidata cikin girmamawa kamar yana agabanta, amsawa tayi da tambayar sa lafiya taji muryar sa wani iri? Gaya mata yayi bayada lafiya danshi yakeson atoro masa Rukayya tazo ta zauna anan ko na kwana biyune, da yake Ummi tuni tasan irin zaman da d'an nata keyi da matarsa dan tun auran zuwanta biyu gidan, sai tace ba damuwa amma saidai Mansura tazo ta zauna dan jiya Asma u kimin magana da in tura mata yarannan kafin lokacin hutun nasu ya k'arasa sukama mata wani aiki dan bakomai take iyawaba tunda cikin ta ya ya tsufa, ba damuwa yace ya kashe wayar tasa yana mai kwanciya, yanzu kusan sha biyu da rabi ba inda yaje yana cikin gida kuma ba abinda yaci, yanzune ma da yajin jikin da d'an sauk'i ya tashi watsa ruwa. Lokacin da Ummi ke gayawa Mansura sak'on na Yayan su jin tayi kamar tayi kuka dan cewa tayi Rukayya taje ita zataje gidan Aunty Asma u itako Rukayya tace bata isaba, ita k'aunar zuwa gidanni bata yi saboda tun wancan lokaci bata saki zuwa gidan ba, dole ba yadda zatayi ta shirya direba ya kaita sannan yazo yakai Rukayya. Koda tazo bata tarar da matar gidan ba apaloiba dan haka tasamu waje ta zauna, dan bazata ta'ba sake wannan ganganci da tayi ba. Mansur da baisan da isowar taba saida ya fito zuwa masallaci ya ganta zaune aparlour zaune, gaidasa tayi da yimasa ya jiki tunda taji ance bayada lafiya, amsawa yayi yace "miye kike zama ke kad'ai anan", batace komai ba yasake cewa tashi ki shiga ga d'aki nan kiyi salla kizo ki shiga ga kitchen nan ki girkamin abince" tashi tayi ta shiga d'akin da yake nuna mata. Saida tagama salla sannan tazo ta shiga kitchen ta girka masa abu mai sauk'i, d'auka tayi takai masa d'akin da taga yafito ta tambatar da nasane, saida akabata izini sannan ta tura d'akin ta shiga, d'akin bayada wata hayaniya daga gado sai wardrobe sai sofa guda d'aya inda yawancin duk kayan aikinsane abisa, saida tasake gaidasa tare da ajiye tiran dake hannunta, bai ce komaiba sai d'aga hannun da yayi, arayuwar ta ta tsani ta gaida mutun ya amsa mata da hannu, haka ta tashi ta fita daga d'akin tana maijin takaicin zama agidan har na tsawon kwana biyu. Parlour ta koma tayi zaman ta tanajinta duk babu dad'i an takurawa rayuwar ta, tana nan azaune Bashhama ta fito daga d'akin ta, da mamaki take kallon ta tana tambar kanta "ita wannan kuma yaushe tazo?" Kallon ta Mansura tayi ta watsar tayi da d'ai kamar bataga mutun agidan ba taci gaba da kallon da takeyi, duk da Bashhama taji haushin abinda wannan y'ar rinin hankali tayi mata amma sai bata nunaba ta shiga kitchen taga ko mai aiki tayi girki yau, dan duk da banan take kwana ba amma kullun sai tazo bayan la'asar ta koma, girki da tagani sai k'anshi yake ta tambata ba mai aiki tayi saba, "kenan yau bata zoba kenan?" Batada mai bata amsa dan haka bata k'etaci kantaba ta d'iba anan kitchen ta zauna taci abinci, yau Jancy batazo gidan ba dan ta gayamata bai fitaba da alamar bayada lafiya, saida ta k'oshin sannan ta fito tayi komawar ta d'aki, kallo Mansu tabita dashi tana mai fad'i aran ta "aikin banza" sannan itama ta shige d'akin da ya nuna mata d'azu dan zaman ya isheta. Bashhama ganin har dare yarinyar nanan dan haka ta tabbatar anan zata kwana, haka yasa tace aikin nata zai tafi dai-dai, dan haka ta tashi domin fara shirin ta, sannu da tayi shi mutunan komai dare dole sai yasha furansa ta k'a Ida yasa taje tajik'a wata k'waya ta zuba acikin furan ta gwauraye sannan ta maida acikin firjin tayi komawar ta d'aki ta abinta hankali kwance, dole ne ta shafa musu bak'in feti arayuwar su idan tak'amar su girmai Kai, ta tabbatar da komai taurin kansa yau sai ya zubar dashi dan ba hank'uri zai iya yoba saboda k'arfin k'wayar, kwanciyar ta tayi hankali kwance tana mai jiran lokaci. Misalin sha d'aya da rabi Mansur yazo ya d'au furar sa dakesawa kullun afijin yaje d 'aki ya sha, sannan ya d'au laptop d'insa ta fama ya fara gudanar da aikin sa, bai dad'e da fara aikin ba ya fara jin wani iri ajikin sa, tun yana d'aukar kamar yanayin da yake yawanjine yake daure wa amma sai yaga wannan wa wuce tunanin sa, tun yana daurewa yana aiki har yakasa fahimtar komai dole ya ture laptop d'in gefe, tunda yake aduniyar nan bai ta'ba jin yanayi na buk'atuwa irin wanan, eh tabbas yasan shi mutunan da Allah yawa lafiya da zai zauna da kowace irin macce dan lolaci-lokaci yanayin na mutsa masa saidai ya kan yawaita azumin alhamis da litani, da yawan shan ruwan lemon tsami sai in abin ya gazane yake bid'ar magani yasha, amma sai yau yakejin idan har baiyi abinda yakejin zai samar masa lafiya zai iya mutuwa ayadda yakeji, tun yana tunanin zai iya daurewa har yagafa wankin hulla zaikaisa dare, adaddafe ya tashi ya fita daga d'akin ya nufi d'akin Bashhama, yasan haka shine kawai samuwar lafiyar sa. K'wank'wasa k'ofar ya fara ahankali yanajiran ta bud'e, kusan mintuna goma yana bugu amma take bud'ewa dak'yar ya juya zai koma d'aki amma k'afafunsa suka kasa d'aukar sa anan cikin parlour ya zube har wani kakarin amai yake na wahala. Tun lokacin daya fara bugun k'ofar Bashhama akan kunnan Mansura da takasa bacci saboda rashin sabo, jin ta daina bugu saima kamar kakarin aman da takejini yasa tayi saurin fitowa daga d'akin ta dan ganin ko lafiya. Yanayin da tagansane yasa tayi saurin k'arasawa gunsa tana kiran sunan sa tana kama hannun da taga yana rik'e cikin sa tana tambayar lafiya?" Shi kuwa yanajin mutun ajikin sa tuni ya k'arasa rikicewa ya k'ara hautsinewa, nan take ya juyar da ita cikin wani salo yana bid'ar cire mata riga. Tsoro ne yakama Mansura ganin abinda yake bid'ar yimata, turesa tashiga yi da k'arfin da Allah yabata amma ko gizo baiyi ba, bata zataba taji hannun sa akan .... Anan littafi na d'aya ya kare sai Allah mai kowa mai komai ya kaimu bayan sallah zamu cigaba da na biyu in sha Allah, wadda zai kasance na kud'i. Ya Allah ka kar'bi ibadunmu albarkacin wannan watan Ramadan da zamu shiga indan Allah ya kaddari munada rabon ganinsa, ya Allah ya yafe mana zunubban mu da kurakuranmu baki d'aya. Sai bayan sallah idan Allah yakaimu ~Mom surayya ce~ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office Normal Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ fc6cd503d20749f6ad922984d76f7f58