Sashe 15
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
motarsu domin samun wadda zai musu sallama dasu,gidane madai-daici tare da filistar sa,amma daganinsa bayada wani girma,fitowa Jabir yayi yayi tsaye bakin motar, babu jimawa saiga wani yaro ya gitta ta wajan, dan haka yayi kiransa tun beyi nisaba, Saida yaron ya kallesa kamar yana shakkar zuwa wajan da yake, ganin haka sai yace "kar kaji tsoro mana,ba asan namiji da tsoroba da jaeunta aka sanshi,nan gidan zaka shiga kace ana kiran Maman Abida" Jin haka yasa yace "to" ya shiga cikin gidan, babu jimawa sai gashi ya fito yace "wai waye?" "Kace mata Mansur ne da Jabir"ya juya ya koma ciki,can saigashi ya koma fitowa yace "tace koshigo daga ciki" dubu d'aya ya janyo daga cikin aljihunsa ya mik'awa yaron yana masa godiya. Cikin tsananin murna yaron ya ansa yana godiya kamar zai masa sujuda har yaba Jabir tausayi,da kaga yaron yana tare da yunwa,har yayi nisa yana tsaye yana kallonsa,saida Mansur yayi masa oda sannan, fitowa yace yayi su shiga ciki, fitowa yayi suka shiga cikin gidan. Da sallama d'auke abakinsu suka shiga cikin gidan,zaune suka tarar dasu akan tabarma 'yar budurwar yarinyar tana kwance an lullu'ba mata wani zane, cikin mutuntawa da matuk'ar jin dad'in ganinasu Maman Abida ta tarbesu game da cewa su zauna akan tabarmar da ta shinfid'a musu tun lokacin da taji sune sukazo, Mansur ne yafara zama gamai da gaidata da tambayar ya mai kiki?,shima Jabir ya gaidata yana tambayar jikin Abidar. "Gatanandai da sauk'i dai za ace,amma har yanzu dai tanajin jiki" Mansur yace "to Allah yak'ara sauk'i,kuma zataji sauk'i in sha Allah" Maman Abida tace "Allah yasa" juyawa yayi gun Abida yana tambayar ta jikinta? amsawa tayi cikin sanyin muryarta "da sauk'i" kallon Maman yayi yace "amma miyasa bako maidata asibiti ba koka zauna agida? kuma idan ban mantaba na baki number ta nace idan kinga wata matsala kiyi gaggawar sanar dani" Hawayene suka zubuwa Maman Abida tasa gefen hannunta na dama ta share hawayan, "kidaina kuka ki fad'a mana abinda ya faru, domin ta hakane kawai zamu samuyin yadda zamu bulluwa al amarin" "Aranar da mukayi maganar dakai ashe akwai d'an lek'en asirinsu yayi mana lek'en yaji abinda muka tattauna, kana fita babu jimawa saiga Alhaji Zakari yashego shida wasu abayansa guda biyu,sai likitan dake kulada Abida shima yana tare dasu, bandaisan abinda suka tattaunawaba a ofishin nasaba ya rubuta takardar sallama ba dukda bawani sauk'i ne tasamuba,nayi mamaki sosai ganin sallamar dasukabamu awanan halin da take,da namasa maganar miyasa ya sallamemu awanan halin sai yacemin natambayi wannan,yana mai nunamin Alhaji Zakari, yanagama gayamin yafita daga d'akin". "Dukda nasan da shigowarsa ad'aki tun shigowar tasa amma sai alokacin nakai dubana garesa nace, miye dalilinka nasawa asallamemu bayan kasan zalincin da d'anka yayi mana,miyasa bakuda tausayine? Miyasa bazaku barmu muji da abinda ke damunba sai kun biyomu har a asibiti,mikukeson kumanane wadda ya huce wadda d'anka ya man... "Ke 'yar talakkawa ki iya bakinki kisan dawa kike anan,idan kuma ba hakaba yanzunan zakisha mamaki" wani daga cikin wad'anda suke bayansa suka katse mata maganar da take. "Wane mamaki kakeson ingani wadda banganba?, sannan da kakecewa nasan dawa nake waye idan ba azzalimaiba maci amana wad'anda suke zaluntar talakkawa saboda alfaharin arzik'in da Allah yabasu" Rufe bakinane kida wuya naji saukar hannu afuskata,koda na d'ago inga waye ke marina sai kace baisan darajjar fuskar macceba,koda yake ina zai sani yana tare da marassa tausayi, d'aya ne wadda tun shigowarsu baiyi maganaba shine da wannan aiki Shima Alhaji Zakari da sai yanzu yakeyin magana ya dubeta yace "ko ayanzu kinsan ko wanene ni,koma kin gane ba sa ar yinkibane ni, sannan kuskuran da zakiyi nasake magana anan kamar kina wasa da rayuwar 'yarki ne,yanzuma ba wani abubane ya kawoni wannan k'azamar asibiti ba,saidan inyimiki kashedi indan har kinason rayuwar wannan yarinyar taki, kibar jin dad'in ganin wannan tsageran yaron nason ya tsaya miki har kinajin wani k'warin gwaiwa,inason kibani number da yabaki domin kiransa kuma kiyi nesa damu banason k'ara ganin ko mai kama daku,zan nema muku gidan hayar da zaku zauna na shekara biyu daganan kusan tayi, kisani wallahi akan d'ana zan iyayin komai ciki kuwa harda kaudaku adoron duniya" "Nan dai yayi maganar da yake so kafi yasa likita yabamu takardar sallama yasa yaransa suka kawomu nan unguwar ko bari basuyi muka kwason kayanmuba,Malam ma saida dare yazo tare da kayanmu ba wadda mukawa sallama" Saidai abinda basu saniba alokacinda yake duk wannan maganar Allah yabani inkon yin d'auka ta recording awannan k'aramar wayar tawa" ta fad'a tana mik'a musu wayar tata. Mansur ne ya kar'bi wayar yana wani murmushin da yatsaya iya la'bansa, yace "Maman Abida bak'aramar dubara kikayiba na d'aukar wanan recording kikayi ba,wannan ma ya ishemu shedun da zai tabbatarmana da Habib shine wadda ya aikata wannan laifin" Jabir yace "k'warai d'anla'be wannan ma babbar shaidace garemu,yanzu abinda ya rage mana mud'auki Abida mukaita asibiti dan ayanzu shine abinda tafi buk'ata, kuma ayanzu dolene mu had'asu da amintaccan ma aikacinmu wadda zai zauna dasu a asibitin,dan nasan ayanzu komai zai iya sake faruwa dan nasan bazasu daina bibiyarsu ba" Zama Mansur ya gyara kafin yace "tunani mai kyau Jabir, saidai aganinka waya kama musa wadda zai zauna dasu,kasan shima Alhaji Zari shegen kansane?" Tunani Jabir ya d'anyi na wasu mintuna sannan yace mizai hana asa Kausar domin na yarda da ita kuma na yaba da hankalinta" "Idan har ka amince da ita shikenan,amma ka garfad'eta sosai gudun samun matsala, domin idan har nasamu wani kuskure gareta ta kuka da kanta" "In sha Allah bazama asamuba domin tasan aikinta sosai kuma dashi ta dogara batason rayi wani kuskure da har zaisa ta rasa aikinta" Juyawa yayi ya kalli Maman Abida yace "ki shiryata yanzu za amaidata asibiti, domin inason kafin a shiga koto taji dama". Godiya tashiga yi masa sosai hawaye na zubomata tace "tabbas daza ace dukkannin 'yan sada haka soke da baza asami lalacewar k'asaba,da talakkawa basu zubar hawayansuba akan zalincin da ake musu, mutane ire-iranmu da dama hakan na faruwa da yaransu, amma haka zasu hank'ura saboda kosunkai k'arawa 'yan sada da anbasu cin hanci haka zasu korasu da kiran kar su koma ganin ko mai kama dasu saboda daud'ar duniya,haka zasuci kuka su gaji subarwa Allah,nima Allah ne ya dubemu da idanun rahama ya had'amu dakai, nagode-nagode Allah yasaka da alkairi, sannan tabbas Alhaji Zari akullun cikin bibiyar mu suke,acikin satinnan nema Yaran sa sukabar zama alayinnan,domin atunaninsu zaka nememu dukda sun kar'bi number da zan iya samun ka da ita, amma kuma nayi makikin da har kukasan wurinnan kukazo" Jabir ne yace "karki damu akan sanin wannan munayin aikinmune kawai, kitashi ki gyara Abida muje" "To shikenan,amma mahaifita ma akwance yake ba lafiya,idan mukaje ba kuwa wadda zai kula dashi" "Yana inane?" Cewar Jabir "yana cikin d'aki" ta basa amsa, kallon Mansur yayi yana jiran umarnin sa, karki damu Mama shima ashiryashi yana buk'atar gsnin likita" Ai kuwa kamar ta masa sujuda gun masa godiya,shidai tashi yayi ya fita, Jabir yabi bayansa yace idan kin fama kimana magana muna jiranki a mota, to ta amsa dashi ta tashi domin gyara Abida. Bata wani 'bata lokaciba ta fito tana sheda musu tagama,sune suka taimakawa Malam Ilya suka sashi amota,itako ta kama Abida ahankali saboda bata takawa dai-dai har zuwa yanzu duk da irin kular da mahaifitar ta ta ke mata, abayan muta duka suka zauna Jabir yaja motar Mansur na abayansa... ~mom surayya ce~ [2/15, 11:29 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=ac_t Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 12 Asibiti suka nufa mai zaman kanta wadda takasance ta wani aminin Jabir ce,taimakon gaggawa aka shiga basu lokacin tuni Jabir ya kira Kausar tana kan hanyar zuwa, sun duba Abida sun bata taimakon da yadace su bata harma tasamu bacci, dan ma d'unkin jikinta da yasamu matsala sun koma gyara matashi. Hakama Malam sun dubasa shima sai bacci yake abinsa,dama damuwace tamasa yawa har takai da jininsa ya hau sosai har yakai ga kwanciya, Manan Abida sai godiya take musu da fatan gamawa da duniya lafiya,tana ganin Kausar ta k'araso ta lalla'ba taje taga mijinta, hankalinta ya k'wanta ganin likaci k'ank'ane sun dawo haitacinsu. Ba k'aramin jan kunne Jabir yawa Kausar ba, ya fad'a mata takiyaye domin wanan aiki banasabane na oga ne, tace "in sha Allah zan kiyaye baza asamu matsala agareniba,kuma duk abinda nagani ba dai-daiba zanyi saurin sanar daku" "Yayi kyau,shiyasa naga bawanda zansa wanan aikin saike nasan bazakibani kunnyaba,ni yanzu zamu huce sai gobe in sha Allah zamu dawo, ga Abida nan ki kula da ita dan Allah,dan inaganin ke kad'aice zaki kwana tare da ita, Maman nata zata zauna da mahaifita shima ba lafiya, sannan zan turo muku da Anas shima ya zauna anan gudun matsala dan ke Macce ce" "Ok sir, zanyi duk abinda kace" nan yayi mata salama ya fita yaje ya tarar da Mansur dake jiransa,zuwa sukayi sukawa Maman Abida sallama suna cewa sai gobe zasuzo ta kula dashi, godiya ta k'ara yimusu suka fito suna maijin tausayinsu, mota suka tayar suka fita daga harabar asibitin. Rayuwar su Mansura amakaranta ba laifi sun fara sabawa,basuda damuwar komai sai takewar iyaye da 'yan uwa,basusan wata wahala ta 'yan makarantaba domin Hauwa ta rik'e musu kan maciji suna wasa da bindinsa,ruwan wanka gashi sa take akawo musu har ban d'aki,wanki basayi sun zama 'yan gatan Hauwa, duk rashin sabon Mansura yanzu bakaji sai Aunty Hauwa,hakama su Asma u sunyi sabo dasu kamar sun dad'e da sanin juna, dan haka wasu daga ciki suka farajin haushinsu musamman wad'anda Hauwa ke basu kulawa kafin zuwansu, dan haka idan suka gansu sai sufara yad'a bak'ar magana, kala su Mansura basu gane da suke sukeba har takai suka fahimta, Mansura mai bid'a ga duhu balantana an haska masa, dan aranar sun gane waye Mansura domin rashin mutunci ta zuba aranar harda d'aga hannu ta wankama d'aya daga cikin su mari, aiko wanan fad'an har agaban shugaban makaranta. Koda ya tambayi mafara akagaya masa take yabawa wad'ancan rashin gaskiya kuma ya gargad'esu akan kar yaga haka tasake faruwa, hakan bakaramin k'ona musu rai yayiba ganin shima shugaban makarantar ya goya musu baya,rai 'bace sukabar waurin . Tun awannan lokacin basu sake shiga cikin sha aninsuba, bamai ga maciji atsakaninsu gashi harsun kwan goma sha biyar amakarantar,kuma