Sashe 22
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wane idanu zata dubesa, wayyo ni Allah ina zansa kaina ni jikanyar mutun hud'u, yaya Mansur ka gama dan... Koyi hank'uri da Jina dakuyi shiru sakamakon rashin waya da nayi,amma in sha zamuci gaba daga yanzu ~MOM SURAYYA~ [2/15, 11:31 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=wwt Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 20 "Sakacin waye ya janyo Mansura? da kikaji abu ya zubomiki ai saikimin bayani insan yadda zai fita ad'akin, yanzu koda fitsarinne kin gwammaci ya ganki ahaka Kenan?" Itadai Mansura takasa cewa komai sai Allah ya isa takewa Mansur azuciyar ta, "bazaki tashi ki gyara jikinkiba ko anan zamu tabbatane?" taji Hajo tana fad'a "to kifita mana" baki Hajo ta kama tare da fad'in "au hakama zakice? to ai sai kibid'i wanda zai maidaki d'aki idan kin gama" baki ta tura gaba batace komaiba, Hajo ta juya domin barin bayin d'in har takama k'ofar taji magana ta "ki mik'omin wasu kayan nawa" juyowa tayi tana harararta tace "sai kibid'i warinki ko y'ar aikinki" tana gama fad'a tayi ficewar ta. Koda ta fito bataga Mansur ad'akin ba dan haka ta tambayi Rukayya "ina yayanku yayi?" Rukayya tace "ohun masa nidai naga yafita yana tsaki" zama tayi akan kujerar d'akin tana jiran tagama kintsawa Kafin ta mik'amata kayan nata. Mansur ne yayi sallama ya shigo cikin d'akin hannunsa rik'e da leda leda bak'a, Sallamar sa Hajo ta amsa tana cewa "Mai sunan malam fita kayi kenan?"yace "eh ga wannan kiba wannan yarinyar" tace "minene aciki?" "Uhu" yace da ita yana fita d'akin, bud'e ledar Hajo tayi taga aidugar matace da k'ananan wanduna guda shedda, ta'be baki tayi tana cewa yaran zamani dai ba kinya. Saida ta kwatanci tagama sannan taje ta d'au hijabi cikin kayan da su Rukayya sukazo mata dashi tare da ledar da Mansur ya batata nufi bayin domin kai mata, Mansura tuni tagama har wanka ma saida tayi tanajiran Hajo ne koma tajita shiru,har ma ta fidda rai da zuwan nata domin tasan halin Hajo sarai, tad'au tawul d'inda ke bayin ta d'aura, tana gudun ta fita ahakan tana tsoron ko wannan mugun nanan,tana cikin wannan tunanin taji knocking k'ofar bayin aranta tace "anyi niya Keenan? kai Hajo rikici" k'ofar ta bud'e amma ba dukaba, Hajo dake atsaye ta mik'amata kayan tare da fad'in "saikace wacce tasan inda kunya tabi ta huce" tana gama fad'i tayi tafiyar ta. Itadai Mansura da ta kar'bi Kayan ledar ta bud'e domin ganin miye aciki, bak'aramin kunya bace taji ta kamata sakamakon abinda tagani, "to ita Hajo ina taga wad'annan Kagan?" Batada mai bata amsa dan taji dad'in Kayan ba kad'an ba dukda batasan inda kayan suka fitoba koma tunanin ta bai bata Mansur ne ya sayaba, da tagama ta zura hijabin ta fito,kai tsaye wajan gadon ta nufa zata zauna amma ta fasa domin ganin abinda tagani, shiru batayi magana ba kuma tak'i hawan gadon, Hajo ce ta dubeta tace "ke lafiyar ki kuwa?" kasa cewa komai tayi taci gaba da tsayuwar ta "waini Mansura badake nakebane, ko tsabar kin gama rainanine? ina miki magana kinyi banza dani". Cikin tura bakinda yazamar mata jiki tace "to a ina zan zauna? baki ganin zanan ya 'bacine" kan gadon Hajo ta maida dubanta domin ganin abinda ya 'bata zanan, itama ganin da tayine yasa tace "amma wallahi Mansura wataran sai abarki, sai kingama shedawa duniya kin girmane ko yaya? sai kace kanki aka fara ne, ai saiki gyara gadon dannidai ba boyarki bace uwar ubanki ce ehe". Rukayya ce ganin Hajo ta zak'alk'ale tasa ta tashi ta nufi kan gadon, zanan gadon ta janye gaba d'aya danma ba wani mai yawa bane sosai, saima idan ka maida hankali zaka gani, fita tayi daga d'akin dashi babu Jimawa ta dawo hannunta rik'e da wani zanan, shinfid'awa tayi sannan tace mata ta hau ta kwanta, hawa kuwa Mansura tayi tareda kwanciya tana fadin Allah sarki d'an uwa mai dad'i,harda y'ar wak'arta ta idan wani yak'ika wani zai soka. Hojo tace "Allah sarki inji 'barawo zuma,kwana nawa anji kanku idan kece,ke kuma bari kikeyi kinsan ko wacece" itadai Rukayya dariya kawai tayi, matukar fa aka had'u tsakanin Hajo da Mansura sai sunyi wannan rikicin sai idande basu had'u ba. Bacci sosai Mansura tayi dan sai wajan karfe biyu ta farka, saida ta tashine takejin an sallamesu ko komai taji dad'i dan ita harga Allah ba k'aunar zaman asibitin takeyiba,tuni su Hajo sun gama had'a komai tashinta kawai suke jira. Rukayya ce ta d'au kayan tunda ba wani yawane dasuba suka fito, motar Mansur suka nufa suka shiga,yana gaba Jabir na agefensa,saida suka gama shiga ya tayar da motar ya nufi hanyar fita, ganin hanyar hoster ya nufaba ya d'au wata hanyar daban mamaki ya kama Rukayya da Mansura amma suka had'iye abinsu, Hajo cedai takasa saida ta maganta "Wai mai sunan Malam ina muka nufane? naga ka kauda hanyar da zamuje kosal ko minene kudai kikasani ,kuma banga kabi hanyar fitaba bale ince gida zamuje". "Wajan masu fillar kai zan kaiku" ya kuma fuske kamar bashine yayi maganar ba, "wakeda hasara inba uwayan kaba Indan ma kake ka huce inda za afille manakai kakaimu inda za aturbud'emu da ranmu" ta fad'a tare da hararaesa. Ida gidajan malammai suke su Rukayya sukaga ya nufa sannan suka gane inda suka nufa,suna k'arasawa ya ciro waya yayi kira,ana d'agawa yace "gamu munk'araso" ba musan mi aka fad'a masaba ya yace ok tare da yanke kiran. Mintuna basu huce biyu zuwa uku ba saiga shugaban makaranta yana fitowa awani gidan tare da k'arasowa wajansu, bud'e murfin motar yayi shima ya fita,gaisawa sukayi shima Jabir da yafito ya basa hannu suka gaisa, motar Mansur ya bud'e ta gefen Hajo tafito har k'asa shugaban makaranta ya duk'a ya gaida Hajo, itama ta amsa cikin sakin fuska, Rukayya suma da suka fito ta dayan k'ofar suka duka suna gaidashi, amsawa yayi da tambayar Mansura ya jiki? "da sauk'i" ta amsa masa "to Allah yak'ara sauk'i, kozo muk'arasa daga ciki mana". "A a basai mun shigaba yanzu zamu tafi inason k'arasa wash ayunkane agida, Mansura ce da kace akawota anan takwana biyu idan taji dama ta koma kan karatunta" "ok badamuwa, amma na d'auka zaku tsaya kuci abincine tunda tun zuwanku bakuci komai ba" "A a alhamdulillah amma ban saniba ko Hajo da Jabir zasuci" Hajo tace "nikan alhamdullah ak'oshe nake naci abincin da yarannan suka dafa" Jabir shima dai yace bazaiciba. "To shikenan tunda bakuci ba,amma kusani duk ranar da Allah yakaini inda kuke ko ruwa bazan shaba" y'ar dariya Mansur yayi yace "zakaci in sha Allah, ai muma watarana zamucine" "Allah yasa" yace "amin" anan sukayi sallama sukabar Mansura da Rukayya dukda basuji dad'i aransuba, bayan sun hucene yayi musu jagora har cikin gida, sunsami matarsa mai mutunci da karrama mutane ga kuma fara a, ruwa da abinci ta fara gabatar musu dashi anan cikin falon ta,basajin yunwa amma haka sukaci kad'an saboda kar taji ba dad'i, bayan sun gama ta zauna acikinsu suna fira,anan sukejin sunanta Hajara itama ta tambaye sunayensu suka fad'a mata, basu tashiba saida aka kira sallar la'asar sannan ta nuna musu d'akin da zata zauna. Bayan Rukayya tayi salla ita kuwa Mansura ta sakeyin wanka dan akwai mugun kyankyami gare ta, batada wasu kayan da zata canza dan haka tamaida rigar jikinta hakanan kafin akawo mata wasu kayan,sake gyara jikin ta kawai tayi, Zama tayi gefen Rukayya tace "Allah ni naso ace gida zanje kuma nasan wannan mugun ne ya hana, ya wanisa inzo nan duk da naga matar tanada mutunci batada matsala" Rukayya tace "ya zakiyi sai hank'uri tunda suka riga suka yanke hukunci ba yadda zakiyi" "Allah ni ba abinda nakeji ayanzu sai abinda ba arasaba,dama hostel d'in sukabari na koma zaifimin" "Ai dan yazomiki da matsalane shi yasa, danni kinga lokacin da nayi nawa ba wani ciyon marar danayi saida kawai da nagani" cewar Rukayya, da yake ita tun awacan watan ta fara har Asma u na tsokanarsu Mansura da Zainab sune kawai da saura basu faraba,to gadai Mansura an shiga layi saura Zainab. Rukayya batabar gidanba sai kusan biyar da rabi na yamma sannan tayi musu sallama acewar ta sai zuwa gobe idan Allah yakaimu, "lallai ma yarinyar nan, mikike nufi da sai gobe? wazai kawomin kayan da zansa? Ko kina nufin da wad'annan zan zauna ko yaya?" "Zan bayar akawomiki, idan kuma su Asma u zasuzo mybee muzo tare" "Ok shikenan, amma wallahi ba dad'i nikad'ai anan,waima bazakizo nan mukwanba ne?" Rukayya ta zaro idanu tace "dan Allah Mansura kirufamin asiri,kima san abinda bazai yibane, nikinga tafiya ta sai n... ~MOM SURAYYA CE~ [2/15, 11:31 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=wwt Typing MANSURA BY:SARATU 3 MOM SURAYYA Assalamu alaikum warahamatullahi ta Allah, ina bawa masu karanta wannan littafin na Mansura hank'uri, abisa tsaikon da ake samu, nima ba ason raina haka ke faruwaba domin nima inason in kammala,amma bisa ga wasu dalillai da kuma rashin lafiyar da nake fama da ita hakan ke faruwa, amma dan Allah kusani cikin addu o'inku, in sha Allah zanyi kokari inyi typing duk lokacin da nasamu Kafin in walwale gaba d'aya. Page 21 "Shikenan sai kunzo,amma dan Allah kar kibarni da zuba idon ganinki" dariya Rukayya tayi Kafin tace "in sha Allah zamuzo karki damu". Falo ta rakata tayiwa Aunty Hajara sallama sannan,abakin k'ofar fita sukayi sallama ta dawo tana mai kewar 'yar uwar ta kuma Hasanar ta. Kusan sati tayi Kafin ta koma hoster taci gaba da karatunta, tun awashe gari Rukayya tazo tare dasu Asma u da Aunty Hauwa,sukazo dubata tare da sauran d'alibban da suke hukunci, acikin wannan satin d'aya da tayi ba laifi taji dad'in zama da aunty Hajara,domin duk rashinson magana irin na Mansura haka zatasa ta fito falo tana janta da hira,musamman ma idan taga tashige cikin d'aki kuma ba bacci takeyiba, Aunty Hajara batada yaro ko d'aya,tadai ta'ba gayamata ta haifi 'ya macce bata rufa shekaraba ta rasu,yanzu kusan shekaru hud'u da rabi kenan,suna fatar Allah yabasu wasu masu albarka, hakama ta fannin PC makarantar tasu ba laifi, agaskiya ba abinda zatace sai son barka, koda tayi wanka amatuk'ar takure takejin kanta, saboda Mansura akwai mugun k'yank'yami,ajima-ajima taje tayi wanka har zuwa looacin da tasamu tagama sai sannan tajita sakayo, aranta take fad'ar mata na takura kafin su sami tsarki. Mansur