Sashe 21
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
take? zo muje inganta, awane hali take tanzu?" Hajo ce keyin wannan maganar hankalinta duk atashe saikace ance ta mutune, shima dai Mansur hankalinsa tashi yayi amma bazaka ta'ba gani afuskar saba yabar abin azuciya. "Zo muje ki kaimu inda take" yace da ita. Duk kaninsu fitowa sukayi daga cikin office suka nufi cikin asibitin, da sallama suka shiga cikin d'akin,sun tarar da ita ta farka bada jimawa ba su hauwa nata mata sannu, jin sallamar su yasa gaba d'aya suka juyo domin ganin masu shigowa, idanuwanta basu sauka akan kowaba sai akan Hajo dake agaba tanason ganinta, cikin sauri tayi yunk'urin tashi zaune dan ganin Hajon ta,cikin sauri ta dafe cikinta tana fad'in wayyo Allah na c.... ~mom surayya ce~ [2/15, 11:30 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=wwt Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 19 Da sauri Hajo ta k'arasa gunta,kamata tayi tana fad'in "sannu Mansura, ciyon cikine haka?" Kasa maganata tayi sai kwantawa tayi akan cinyar ta hawaye na zubo mata, Jabir shima sannu yayi mata cike da tausayawa, dan dagani taji jiki kodai harda rashin sabon makarantar ne. Mansur kallonta yakeyi duk yaga tarame masa a ido, ciyon d'ai rana, "to minene ke damun ta? " yayi maganar a cikin zuciyar sa, dama ya lafiyar kura,dobi don Allah da zuwan tsohuwa tabi ta langa'be mata, ita kuma sai biye mata takeyi. Mansura duk yadda takeji taji ciyon bai mata yajiki ba, donda basabon abu bane agare sa, dama bai damu da itaba bak'i ta mutuba ya bar ganinta adoron k'asar baki d'aya, haka yak'aramata zubar hawayan nata. Su Asma u da zainab suka shiga gaidasu cikin girmamawa, sunsan koda basu tambayaba y'an gidansu Rukayya ne kodan ganin yadda tsohuwar nan tayi saurin k'arasawa gun Mansura da anbatar sunnantada tayi. Hauwa kuwa tunda taga shigowar sa gaba d'aya ta mutun da kallonsa, domin ita harga Allah idanuwanta shi suka fara gani bama Hajo dake farkon shigowar ba, tadaiga wadda ke bayansa amma bata shi takeyiba ta abin k'aunar ta takeyi, tasan yau zatayi kwanan farin ciki sosai, saboda wadda take mafarkin ganinsa da burin sake ganinsa yau gashi agabanta, ko lokacinda su Zainab ke gaidasu bata samu bakin gaida suba saboda shagala da tayi gunkallon sa. Tun Mansur bai lura sa kallon da ake masaba har yafara ji ajikinsa,dan haka yashiga k'arewa wad'anda ke d'akon kallo, d'ai-d'ai yashiga kallon su har yaga wadda kemai wannan kallon k'urilla, harara ya 'balla mata dan shi arayuwarsa ya tsani kallo marar dalili har agano munin mutun, amma ina batamasan yanayi ba, wani dugun tsaki yaja wadda yasa duk wadda ke d'akin kallon sa, Hajo tace "kai mai sunan Malam mi yafaru kakejan tsaki haka?" "Ke fad'a mata banason kallon da ya huce k'a ida,wallahi zan sa'bawa mutun ba abinda ya daman" gaba d'aya y'an d'akin Hauwa sukabi da kallo ganin ta sunkuyar da kanta k'asa,jin tayi gaba d'aya kunya tagama kamata kamar k'asa ta tsage tashige cikin don kunya, mi na aikata haka ni Hauwa u? wannan abin kunya dami yayi kama?, itafa shat ta sha'afa da basu kad'ai ne ad'akin ba saboda d'aukin ganinsa da tayi. Hajo ganin yanayin da tashiga na kunya yasa tace "haba mai sunan Malam,inbanda abinka Kai ya akayi kagane ana kallon ka? kaida ya kamata kamaida hankali akan y'ar uwarka da batada lafiya amma ka koma wani batun nadaban, kofa sannun banji kawa k'anwar takaba alhalin kaga hali da take ciki" Jin tanason k'ashemasa tanadi yasa ya kauda kanta gefe yayi kamar bai gantaba, da wannan damar Hauwa tasamu tabar d'akin ko sallama bata musuba, su Zainab binta sukayi da kallon tausayi dan basuji dad'in abinda wannan yayan nasu Mansura yamataba, duk da itama baikamata ta d'aura kallonsa tunda ba kowabane mai son kallo ba arayuwarsa, maganar Hajo ce ta katse musu tunaninda suka fad'a, inda take tambayar Rukayya "ke mike damuta? mi likitoci sukace yake damun ta?" Rukayya ganin yayan nasu takasa fad'a ma Hajo abinda ke daminta, dan tarasa yadda zata fad'a mata, sumadai Su Asma u noce kansu sukayi k'asa, dande da kunya gaskiya su fad'a mata bayan ga maza ad'akin. Mansur ganin abin nasu naraine hankaline yasa ya bugawa Rukayya tsawar da harda Mansura dake kwance tanajinsu ta zabura, "waike dan ubanki ba tambayar ki akeyi bane kigayi banza da mutane?" Raku'bewa tayi bayan Hajo gudun kar yakaimata mazzaga tace "ni basu fad'a mana abinda ke damuntaba kaje ka tambayesu" shine dan renin wayo kikayi banza da mutane" "Kabita ahankali mana mai sunan Malam" tsoki yaja yana barin d'akin gaba d'aya, bayansa Jabir yabi yana mamakin abokimsa, irin wannan fad'an haka?. Yana faita kai tsaye d'akin likita yasa aka nuna masa baima lura da Jabir na bisa abayaba saida zai shiga d'akin sannan ya lura dashi, "ina zakaje Malam?" yace yana duban Jabir. "ALLAH yabaka hankuri ranka ya dad'e" yace yana ja da baya, acikin zuciyar sa yana fad'in "mike damun boss yaune koma yace yanzu? duk yabi ya tada hankalinsa muma yanason tayar mana da namu, Allah dai ya kyauta ya kuma sa lafiya" Saida yayi knocking k'ofar Kafin abasa izinin Shiga, da sallamar sa yashiga cikin office d'in, macece ya yatarar a cikin office d'in, gaisawa sukayi Kafin tabasa wajan zama. Saida tagama rubuce-rubucan da takeyi atakaddun dake kan teburin sannan ta d'ago kanta tace dashi "Kayi hank'uri nak'arasa wani uzirine,make tafe Dalai?" "Ba damuwa,nazone domin inje abinda ke damun sister nane, wace aka kawo adaran jiya" Agaskiya bazan iya gane wadda kake nufiba,domin kuwa kusan mutun hud'u zuwa biyar ne aka kawo adaran jiya, amma zaka iya fad'an sunnanta sai abincika" "Sunanta Mansura Ahmad" yace da ita, waya ta d'auka tayi kira tace aduba mata fale d'in Mansura Ahmad, babu Jimawa d'ai daga cikin nouse d'in asibintin tayi sallama rik'e da fale ahannunta, duk'awa tayi ta gaidasu tare da mik'amata fale d'in, bayan ta kar'bane ta bata izinin tafiya,fale d'in tashiga dubawa Kafin ta d'ago kanta tace dashi "ok bawani abin damuwa bane girma ne zai kamata, zai iya zomata ako wane irin lokaci" Cikin d'an rashin fahinta yace "girma Kuma, wane irin girma kuma?" cikin mamaki ta dubesa azuciyarta tana Gurmarsa "dubesa a ido sai kace wayayye,taya zaice baisan abinda take nufiba" amma afili sai tace "girma dai wadda kasan ko wace d'iya mace zatakai ga zuwansa" shi harga Allah sai yanzu yafahinta, cigaba tayi da fad'in "amma in sha Allah zuwa ajima zamu bata sallama tunda taji sauk'i in sha Allah, saidai dan Allah tarage shan abu mai zak'i da mai Maik'o sosai,dakumacin abu mai taji,kaima da duk wani abu da akasan zai iya cutar da ita" "Ok badamuwa in sha Allah za akiyaye,nan sukayi sallama yafito, yana fitowa yaga Jabir a inda ya barshi baiko zaunaba,damamaki yake cewa "wai kai dama har yanzu kananan atsaye?" K'aramar dariya yayi tare da fad'in "ba doleba tunda an hanani in shiga, Kaga kuwa ai dolene in tsaya gadi, ina fatar ba wani abin damuwa bane?" "Eh kawai yace dashi yanayi cikin dak'in da aka kwantar da Mansura, kai kawai Jabir ya gir-girza tare dacewa "halinka sai mai hank'uri ke iya zama dakai oga, idan miskilawan na kusa haka zai d'aura wa mutane magana Kamar wadda kawai dole,bai bisa cikin d'akin ba yasamu kujera ya zauna. Kuda yashiga baice komaiba,saidai agefen ido yake kallon ta,aransa fad'in yake "yanzu dan Allah wannan tarinyar ce ta isa wannan abin,duka-dukafa har yanzu bata gama cika shekaru goma sha biyar ba,yanzu wannan yama zatayi ta kula da kanta,yarinyar da ko natsuwa bata gama isartaba,ai kuwa Kafin agama za aga shirme da shiririta awajanta" (Amma agaskiya yaya Mansur kaci Mansurar mu data sabida Allah yazakace hankali bai gama isartaba, Koda yake bakina da taba idan tajika,kota kukace fans) Hajoce tagaji da zaman kuramen da akeyi tace "mai sunan Malam kaga likitan ne? mi sukace yana damunta?" Kafin takai ga bata amsa Mansura ta katseta da fad'in "Hajo fitsari nakeji" "To,to bari in kamaki ki shiga bayin" itakonan wani abune taji yazubomata mai d'an d'umi,to ita awotarta fitsarine ya matseta har yakai da zubo mata, Kamata Hajo tayi ta mik'ar da ita tsaye, bayi ta nufa da ita a hankali, amatuka'ar bazata idanuwan Mansur suka sauka akan duguwar rigar dake jikin Mansura, saurin runtse idanuwansa yayi ganin abinda suka ganar masa, aransa yace dad'afa abu yakai ga mata,kuwama sai yagama gani, yanzu dan Allah da Jabir ya biyosa shima haka zai ganta, kai Allah dai ya kyauta. Tashi yayi da zumar fita idanunsa suka sake kyakkyawan gani akan gado, dudda ba wani mai yawa bane amma ransa ya d'an 'baci, yanzu dan Allah zatace batasan ya zubo mataba har ya 'bata gado, ko saboda tsabar k'azantace,tsaki yayi ya fita daga d'akin gaba d'aya. Da idanuwa Rukayya ta bisa ganin yaja wani uban tsaki ya fita daga d'akin, ganin ya fita afili tace "shi kuma wannan dawa yake?" batada mai bata amsa,dan haka ta maida dubanta akan littafin da take kan dubawa tun d'azu. Acan cikin bayin kuwa saida suka isa sannan ta lura da jikin Mansura, ha'ba ta kama Kafin tace "ke Mansura kice girmane ya kamaki shine musabbabin ciyon naki" damamaki ta jiyo ta kalleta Kafin tace "girma kuma Hajo? to wane irin girma kike nufa?" Yaran zamani Kodai sai abarku,yanzu sabi da Allah ke bake lura da halinda kike acikiba,to duba rigarki ki gani" Duba rigar tara tayi amma bataga komaiba,cikin d'an turo baki tace "waini mikike binyamin? nifa banga komai ba" bayan rigar tata Hajo ta kama ta nuna mata tace "duba kigani minene wannan?" Ganin abinda take nuna mata taji wata matsanan ciyar kuya ta kamata,saurin duk'ewa tayi tare da noce kanta ak'afafuwanta, Hajo tace "yar kwal uba,dama kinsan wani abu waishi kunya dama,yaushe kika fara ban saniba?" ni Allah ban ta'ba yiba Hajo,wannan d'inma bansan dashiba,ni saima da kika binyamin nagani" "Innalillahi, Allah yakaimu zamani ni Hadizatu,yanzu dan Allah Mansura abu har yakai ga 'bata miki jiki amma baki saniba,yanzu koda ahanyane haka zakiyi ta yawo hankalinki kwance" Cikin d'an tura baki tace "to nida naji abu ya zubomin ai an na d'auka fitsarine, shine nacemiki inajin fitsari" "Aiko kinga shikenan mai sunan malam yagama ganin komai tunda yana ad'akin"wata kunyace takumajin ta kamata,saima taji ayanzuma Kamar agabansa take,sai kawai Hawaye taji suna zubo mata afuska,shikenan yagama da ita,yanzu da