← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 39

Sashe 27

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

komai yake mata bata ta'baji sonsa ya rago azuciyar taba,saima kullu zuciyar ta k'ara sonsa take,ita kanta tasani itace ke sonsa bashiba, kafinma tasamu ya fara kulata ba k'aramin wahala tashaba, kusan shekara d'aya tana bibiyarsa da soyayyar ta kafin daga baya tasamu ya fara saurararta harya aminci zai aure ta Mahaifinta bai ta'ba sanin itace mai sonsa bashiba,tasani matuk'ar yaji itace ke sonsa komai za ayi bazai ta'ba amincewa ta auresaba,Dan zaicene ba zaikaita gidan da ba ak'aunarta, ganin take tunda har tayin nasarar ya amince zai aure ta komai daran dad'ewa zaizo yafara sonta,haka zataci gaba da hank'uri harzuwa lokacin da zasuyi auran, hawayan nata ta share ta kwanta tajin natsuwa aranta game da wannan tunanin da tayi. (Allah sarki Bashhama harkinban tausayi, son maso wani k'oshin wahala) ___________ Yau tunda Mansura ta tashi take d'aukin Aunty Abida zata koya mata abinda tace, taba Hajo labari kuma tace anan kicin d'inta zasuyi,da tagayawa Rukayya kuwa cewa tayi baza abarta abaya dole tare da ita za ayi,itako Mansura tace ba hakaba saidai itama ta tambayi aunty Abidar idan ta amince shikenan, "naji d'in, nasan dai bazatacemin a'aba" Mansura tace "Wallahi saidai kizama abayana tunda nice na fara tamba ehe" dariya Rukayya tayi tace toke banda abiki ba kicin d'aya zamu zauna ba,kinga kuwa dole atare zamu gani ba maganar cewa gana gaba gana baya" "Kumafa hakane, tashi ma muje muga ko tasawo" ta fad'a tana mik'ewa tsaye, hannun ta Rukayya tajanyo tana cewa "kefa dad'ina dake zumud'i, ki zauna mana idan ta dawo ita dakanta zata nememu tunda tasan tayi alk'awari" zama tayi tace "Wallahi kuwa,kinsan arayuwata inason inga na iya girki kala-kala,ke nifa da Abba zai amince restaurants zan bud'a idan nasamu ilmi akamsa" Rukayya tace "mi zaisa Abba yak'i amincewa idan har kinaso, basai kisa k'wararru acikiba" cikin farin ciki tace "kumafa hakane kin kawo shawara, Allah dai yacikamuna burinkanmu" "Ameen ya Allah" Abida bata dawo daga gidanba sai Karfe 2:37 pm, ruwa kawai ta watsa taci abinci sannnan ta nufo part d'in Hajo, lokacin 3:27 har tayi. Mansura tayi matuk'ar jin dad'i ganin zuwanta,tabbacin bada wasa take mata ba,koda Rukayya ta tambayeta tace ba matsala aisud'in k'annan tane kadasu damu kansu. Kicin suka nufa gaba d'ayansu, Abida ta duba abinda ke akwai kicin d'in,abinda babu tace suje su tambayo Momy ko Ummi idan za samu, dan suncewa Hajo kada ayi girki dare nasu za aci. Sun kuwa samu saura awajan Ummi wasu kuwa awajan Momy, haka suka kawo mata cikin zumud'i. Haka suka natsu suna kallon abinda ake nuna musu suna d'auka acikin janunsu, salla ce kawai ta fiddo su daga cikin kicin d'in,sune basu kammalaba sai 7:3, anan kicin suka barshi bayan Abida ta d'iba wanda zata kaiwa maman ta sai na Ummi da momy wadda Rukayya ta d'auka zata kai musu, sallama tayi musu sannan ta tafi da zumar sai kuma gobe idan Allah ya kaimu. Mansura ba abinda takeyi sai murna domin ganin takeyi ko ayanzu zata iya yinsa idan an barta, duk wahalar da ake kiran yanada ashedai bawata wahalace dashiba, wannan abinci ba komai bane face tuwon dawa da taji miyar kuka sai zuba kanshe yakeyi, sai lemon da tahad'a da kanta na dabino da kwa-kwa da ayaba,ta zuba madara tasaka afirji tace wannan na Dady ne shida Abba,su ta had'ama, saida suka gyara kicin d'in itada Rukayya sannan kuwa ya kama gabansa. Zaune suke afalo Hajo sai santin tuwon takeyi tana sawa Abida albarka na dagewa da tayi harta iya abincinmu na gargajiya,domin kuwa yanzu yaranmu sunfi maida hankalin ga abincin zamaninnan saboda lalacewa, bace kabar wancanba ko wane kimaida gankali da koda kaje gidanka ko wane irin abinci miji ya buk'ace kamasa zaka iya, ta k'arawa musu karfin gwaiwa dasu maida hankali su iya girki kala-kala tasansu sa dagewa akan abu idan sunsashi agaba, sunyi matuk'ar jin dad'i ganin Hajo na yabonsu. Ahaka Mansur ya shigo ya samesu,cikin y'ar gajiyar da yayi yace "Hajjajo Hajo bidirin mi ake badamuba?" dariya tayi tana fad'i "bidirin abinda kafiso mana" Baki yarik'e irin mamakinnan yace "to! baridai inje in watsa ruwa ayi bidirinnan dani yau na makara" Hajo tace "ai kuwadai isauri kar abarka atasha" Rukayya ce tayi saurin gaidasa tana mamakin sa, yau kuma raha akeji dibi kamar bashiba. Amsawa yayi yanayin gaba yana mamakin irin rinin da wacan yarinyar tayi masa,amma zai babbance mata tsakanin fari da bak'i, har zuwa yanzu basan kowaye shiba. Hirarsu sukaci gaba dayi har yayi wanka ya yasamesu anan, "yauwa Hajo gani sai abane koma miye nima idaiji, Rukayya tace ta zuba masa, "tuwon dawane gashinan kuma nasan mutunan kane kai dashi akwai amana" Rukayya da tazuba ta tura masa gabansa sai "Amma nayi farin ciki da ganin wannan tuwon dama an kwana biyu abayisaba, nasan dai Momy ce tayisa dan tasan nayi kewar sa" Hajo tace "to baka cankaba, Abida cedai tazo tayisa sakamakon nacin da Mansura tayi mata tazo ta koyamata" baki ya ta'be yana jan plate agabanta kamar ma baiji abinda ta fad'a ba. Mansura kuwa mik'ewa tayi tana cewa hajo "Hajo bara inje wajansu Abba nasan yanzu sun dawo" Hajo da ta d'aga kai ta kalleta tace "to shikenan" tasan ba komai yasa zata tashi awajanba sai ganin Mansur awajan, addu a takeyi akan Allah ya had'a mata zuri arta,domin tasan Mansura tanada kafuwa. Kicin tashiga ta d'auko musu abinci dake cikin kula tasa acikin madai-daicin basket,ta had'a da lemon da ta had'a musu,da tafito falo kai tsaye hamyar fita ta nufa bata ko kalli wajan da sukeba, tana gaf da fita taji muryarsa yana dad'in "ke! zonan" yi tayi kamar batasan da ita yakeba "Kika sake kika fita acikin falon nan sai na lahira yafiki jin dad'i" sayawa taji bata k'ara koda tako d'aya ba daga inda take, ganin batada niyar yin abinda yace yasashi fad'in "bakiji aninda na fad'a bane ko Yaya?" Idanuwan ta ne suka ciko da hawaye bakinnan ta cinnosa gaba ta juyo ta nufosa, "gani" saida yakai lomar daya d'ebo bakinsa sannnan yace "aini ba makaho bane, aje basket d'innan ki kama gabanki" Da mamaki take kallon sa kafin tace "nafasu Abb... ~mom surayya~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 28 Wani kallon da ya watsa mata batasan lokacin da ta ajiye basket d'in hannun nataba, kafin yace "Wai ke komai sai kin renawa mutane da hankali ne? cewar danai ki ajiye sai kin fad'amin nasu Abba ne ko na tambayeki ko nasu waye? suje matan nasu su girka musu mana" Salatin Hajo ta Sanya tare da fad'in "kanka d'aya kuwa mai sunan Malam? kaji abinda kake fad'a kuwa? iyayen naka kake fad'awa haka" sukuwa Rukayya da Mansura idanuwa suka zuba musu kamar zasu zubo k'asa saboda tsabar namakin maganar sa. shi kuwa gogan ko ajikinsa kamar bashi bane yayi maganar, saima cewar da yayi "Allah ko Hajo? aini bangansu anan bane ko suna acikin d'akin kene in sani, ko karya na fad'a basuda matan da zasu girka musune?" ya maida dubansa ga Mansura "maza ki 'bacemin anan da kikamin tsaye sai kace wata sak'ago" ai cikin sauri tabar wajan kar abinda ke kansa su fatattakata, eh mana dan ita aganinta bakansa d'aya ba su Abba zai fad'awa wannan maganar? Rukayya ma da ba akai ga korar tataba taja yan matan kafafunta tayi gaba. Kai Hajo ke kad'awa tareda fad'in "lallai abinka azimun ne mai sunan Malam! anya kanka d'aya kuwa?" "A a biyu ne" yabata amsa yana maici gaba dacin abincinsa kamar bashi ba "nasan arina, domin duk mai kai irin na mutane da hankali bazai aikata wannan abinba" d'ago kai yayi ya dubeta jin maganar da ta fad'a, ganin itama kallon nasa take yasa yace " ni kan aljannune dani" yana gama fad'a ya d'auki basket d'inda Mansura ta had'awa su Abba yayi d'akinsa, "ka dawo ka karasa shi wannan da kabari waka barma?" cewar Hajo "d'auki ki cika gurbin da bai cikaba" yana gama fad'a yayi shigewarsa cikin d'aki, itako Hajo ta d'aga murya tayadda zaijita tace "rufeni da k'anzo Malam,wadda ya hana akaiwa iyayansa toni asuwa kare da gudun layya da za abarmin rage kuma inci" murya ta d'aga tana kiran Rukayya domin tazo ta gyara wajan. Rukayya dake cikin d'aki suna gulmar Yaya Mansur, Rukayya tace "wai yau miyasamu Yaya ne?" da yake duk maganar dasuke akunnuwansu take, Mansura tace "koma miye akannasa shi yajiyo, dande wallahi ban yafe wahalar da nayi wajan had'a wannan lemon da sunan su Abba ba, haka kawai in 'bata lokaci da zumar samun lada amma wani k'ato abanza ayofi ya karfe ya hana in kai" da mamaki Rukayya ta kalle ta kafin tace "Mansura Yayan ne wani k'ato?" itama kallon nata tayi tace "au haushi kikaji kenan? itama ta maida mata da tambayar "karfa ki manta Yaya Mansur yayanki ne ba wani abokin wasanki neba dako wace irin magana tazo miki fad'ar ta kike, sannan koda baki sansaba bakisan inda ya fito ba kinsan ashekaru ya girmiki nesa ba kusaba" ha'ba Mansura ta rek'e "to fad'a min ciki d'aya kuka fito basai kin tsayamin dogon sharhiba" Idanuwan Rukayya ne suka ciko da hawaye jin abinda Mansura ta gaya mata "au haka ma zakici?, nice na cancanci wannan maganar take? ba komai" hawaye na saukar mata a idanuwan ta, jikin Mansura ne yayi sanyi ganin hawaye a idanuwan ta, matsota tayi tace kece da wani zance naki, miye na wani kare shi basai ki goyamin bayaba, amma sai kika nunamin abayan nasa kike shiyasa na fad'i wannan maganar, amma kiyi hankuri" cikin haka sukaji muryar Hajo na kiran Rukayya, yun kurin tashi tayi amma Mansura ta hanata tashi sakamakon rik'e mata hannuwan da tayi, kallon ta tayi mai nuni da miye haka? "taya zan barki alhalin banji kince kin hank'ura ba" hawayen nata ta share taci "naji komai ya huce, amma dan Allah karki saki fad'a min wannan maganar ba zanji dad'i ba" tace "in sha Allah hakan bazai sake faruwaba" "Allah yasa indai kece nafasan halin naki,yanzu dai ba wannan ba tashi muje kinji Hajo sai kwalan kira take sai kace tabani ajiya" sakin hannuwan nata tayi tace "jeki kedai kida take kira amma ni ba inda zanje" kallon ta tayi tace " to shikenan" tana gama fad'a
Chapter 27 · 0% Book details