← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 39

Sashe 24

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai bacci,shine bai tashiba saida aka fara kiran la'asar sannan yayi alwalla ya tafi masallaci. Misalin karfe takwas da rabi duk sun hallara afalon Hajo domin cin abincin dare, Hajo ba abinda ad'auke afuskarta sai farin ciki da annashuwa,saboda ganin iyalinta waje d'aya, dukda biyu suna ma'aurinsu, sunci sunsha cikin annashuwa da farin ciki, suma su Mansura fuskokinsu cike su da annashuwa ganinsu acikin 'yan uwa. Yau Litinin kimanin kwanakki biyar da zuwa hutun su Mansura agida, sun sake abinsu har sun fara mantawa da rayuwar makaranta,baje kolinsu kawai suke Inda Hajo, domin kuwa anan part d'in duk suka tare, acewarsu sunfi walawa ba kamar sauran part d'in ba, duk da idan mansur na acikin part d'in Hajo ba komai sukeyi ba har sai ya fita, koma duk wannan kwanakkin Mansura bata ta'ba gaida shiba koda kuwa ta gansa, saidai Rukayya ta gaida shi domin ita tana tsoron dukan sa,watarana ya amsa watarana yayi kamar bai gantaba, koda Hajo ta mata magana tace "wai Mansura miyasa bakya gaida yayanku duk lokacin da kika gansa?" cewa tayi "Akan mi zan gadashi bayan baya sona, ni ba ruwana dashi yayi rayuwar sa inyi tawa, kowa yaji da abinda ya matsesa" "kema wani lokaci bakida kirki, cikinku waye k'arami? sannan mai sunan Malam duk abinda kikaga yanayi yanayi ne domin kulawar sa gareku bawai dan takurawaba, dan haka kimaida hankalinki, banason rashin jituwa yaci gaba da shiga tsakaninku alhalin kuna agida d'... Maneji please ~mom surayya~ [2/15, 11:32 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 23 Hawaye ta fara saikace wacce aka daka tare da fad'in "ai shi dayake d'an gatane agareki baki masa fad'a saini tunda kin daina sona, tsakanin ni dashi waye baya son wani? duk wadda ke gidannan ba wanda yake nunawa k'iyayya kamar ni, bayasona baya k'aunata, duka wane irinne bansha ahannunsaba? amma ba wadda ya damu, duk wannan bai masaba, domin ya daina ganina acikin wannan gida ya cika su Abba da dad'in baki aka kaimu bodin, yanzu haka nasan bak'in cikin wannan hutun da mukasamu yake, baik'i mu dauwama acan ba". Tunda ta fara wannan maganar Hajo ke kallon ta tana mamakinta, ga kuma kukan da take saikace wacce aka kama akawa tsinannan duka, saida takai k'arshan maganar ta tace "a lallai Mansura abin naki ya k'arayi tsamari, yanzu daga wannan maganar zakice ba asonki kara masa sure, sannan we kukan da kike duk namiye?" nifa ina duba miki gabane domin kece da wahala ba waniba" "Ni wallahi bana tare da wata wahala ki daina min fatar tsiya ehe" ya fad'a tana juya mata bayan keya. "Naji uwata" Hajo ta fad'a tare da tashi ta bar masu falon gaba d'aya. Rukayya da tun d'azo bata tsoma musu bakiba sai ayanzu da Hajo ta tafiyar ta, tace "amma gaskiya Mansura baki kyautaba, kema kesan kaf gidannan ba wadda Hajo ke nunawa so da k'auna kamarki, dan haka bai kamata ki fad'a mata hakaba, sannan nafara tunani Yaya ba sonmu ne bayayi, yanasonne ya tsayo akan tarbiyar mune dan Allah ki daina k'aluntar sa" kai ta juya mata tace "ta shiga tanan ta fita anan" ta fad'a tana nuna mata kunnan ta, Rukayya tace "to naji, nama manta ban gaya mikiba Ummi tace murshirya direba ya kaimu inda Aunty Asma u zata aikemu" mutuniyar najin batun yawo ta juyo da sauri tace "da gaske kikeyi?" Dariya Rukayya tayi tace "Allah da gaske nake miki ba karyaba,da safennan take fad'amin, amma kuma.tace sai anyi azzahar sannan,kuma ana la'asar mu dawo gida" Idanu ta fitar "azzahar fa kikace? ai wallahi sai anyi ishsha ma zamu dawo ba magariba ba, yauahe rabon mu da gidan Aunty Asma u, kedai kawai ki kama bakinki muce mata to" da yake kusan halin d'aya ne atake ta yarda da maganar Husainar ta. Bayan sallar azzahar kuwa kamar yadda Ummi tayi musui alk'awari tabasu aikar direba yakaisu. Bak'aramin farin ciki Asma u tayi da ganin 'yan k'annan nata da tayi ba, saboda ba kasafai ake barinsu suna fitaba kuda kuwa gidan yannan nasu ko lokacinda sunana gida, haka suka baje abinsu dan tuni sucewa direba yayi tafiyarsa direban Aunty Asma u zai maidasu idan lokaci yayi, sune suka shiga kicin da kansu suka girka abida sukesu suka ci, domin sunce basasun abinda ta girka, haka suka zauna suna bata labarin makaranta ita kuwa tana biye musu, sune basu tashi awurin ba saida aka kira la'asar, bayan sunyi sallar ne Mansura ta faki idanuwan Aunty Asma u ta d'au wayar ta ta kashe,domin tasan yanzu Ummi zata kirata tace amaidasu tasamu waje ta adana. Aunty Asma u da batasan lokacinda akace sukomaba sai bata kawo komai ba ta d'auka sai bayan magriba, hakan kuma ba k'aramin dad'i yayi mataba, kuma firar da suke ya d'auke mata hankali akan tunanin wayar ta. Ummi kuwa tunda direba yaje yace mata sunce direban Aunty Asma u ne zai maidasu tayi fad'a domin tasan halin yaran nata sarai,kuma Asma u badamuwa zatayiba face biye musu da zatayi, amma tasan abinda zata musu, ana gama sallar la'asar zata kirata tace tasa maidasu, tana gama sallar kuwa bayan tayi azkar ta d'au wayar ta dake kusa da ita ta dubu number Asma u ta kira,saidaimi, kira kusan biyar amma ana fad'a mata akaahe,tasan da saninsu sukayi haka domin kar sudawo ayanzu, har zuwa karfe biyar ba a kunna wayar ba dan haka takira Abdullah,bayan ya d'aga ta tambayesa ko yana kusa? yace baya kusa yana wajan abokin sa kuma yanaganin sai zuwa takwas zasu dawo dan sunje wani wajene. Akalar kirar ta maida ga Mansur, shikan tasamu yace yananan apart d'in Hajo, tace "so nake kaje wajan Asma u ka d'aukomin yarannan kafin Dadyn ku yadawo kasan zaiyi fad'a, sun maida direba dan karsu dawo dawuri kuma ita ta kashe wayar tata dan shirme bansan abinda take nufi da kashe wayar tataba". Ok kawai yace bayan tagama gaya masa,tana kashe wayar ya kama fad'a yana fad'in "ai iskancine da rainin wayo dan sun samu abarsu fitar, to ba gidan uban da zasu koma harsu gama wannan hutun" Hajo dake kallonsa tun fara wayar tasa da gamawar da yayi ya fara fad'an, tace "dan Allah kudaina matsawa yarannan, saidafa sukayi azzahar sannan sukabar gidannan, sannan tunfa zuwan yarannan ba inda suka je, harda inda wannan yarinyar dake mutunci dasu suna shiga inda take baku bare sunjeba, ita kuwa kusan zuwanta biyu, wannan tsananinfa bashi zai hana yara suyi abinda sukaga damaba saidai ayi addu ar Allah ya shiryar dasu". "Naji amma kisani sun jawa kasu, domin ba inda zasu koma har su koma makaranta" yana gama fad'a ya tashi ya fita domin cika umarnin Ummi. Su Mansura hankali kwance sai shar huliyarsu sukeyi sunma manta da cewar zasu koma agida kamar wad'anda zasu kwana anan, su suka shiga kicin suka d'aura mata girkin dare suka gyara mata falo, itako bakinsu tayasu wasu 'yan ayunka, da yake acan makarantar duk ranar Friday bayan la'asar suke Zuwa wajan koyon girki kala-kala, sai shidda na yamma suke tasuwa, duk wadda ke ra'ayi yake zuwa kuma anan cikin makarantar take, Yaya Mansur ne yasakasu duk tsadar ta, ganin haka suma Zainab da Asma u suma sukayi magana asasu lokacinda akazo musu bistin. Sun maida hankali su gaba d'aya akan girkin da suke,domin sunce sai sun bata mamaki, ta yadda da Baban Ammar yaci girkinsu sai yaga I ba ita tayisaba saboda tsabar dad'in sa, itako tace zata gani, dan bataga ta yadda zasu fita iya girkiba, watakir ma bazai iyaciba saboda tsabar kwa'ba, ta fad'a tana dariya, dande itama k'anshi sai cikamata hanci yake, suma dariya suk sumayi suna fad'in "zaki gani kuwa, k'ilama idan yaci bazai k'aracin nakiba sai yazo yana lalla'bamu muzo gidansa muna masa", "kunga kuwa da nasamu 'yan aiki, bakina inci in kwanta abina". Suna cikin wannan gaddamar sukaji sallama kamar afalo dan.haka Rukayya ta fita domin ganin ko waye ke sallama, koda ta fito taga mai yowa Aunty Asma u wankine, anan yake gayamata ga oga can awaje yace su fito Kuma kar su 'bata masa lokaci, hankalin Rukayya ya tashi domin sun san wadda suke kira da oga, tayi saurin shiga kicin dan gayawa Mansura. Lokacin da Mansura taji labari itama hankalinta ya tashi dukda bata nunaba azahiri, Dan Allah yasani bata k'aunar duka, shi Kuma babu abinda yafi k'warewa akansa irin dukan cin zalin, itama Aunty Asma u tace suyi sauri su shirya dan idan yakai ga shigowa nan falon itama ranta zai 'baci, duk da kuwa basan ainahin karfe nawa akace su dawoba, sauri-sauri suka shirya suka fito harabar gidan, motar sace dai tabbacin shine yazo ba waniba, sauri Rukayya tayi ta bud'e gidan baya ta shiga dan batasin ma su had'a idanuwa fan tasan kwanan zancan, dole Mansura badan rai yasuba ta shiga gidan gaba, suna gama shiga yaja motar da sauri ya fita dukda yaga Asma u abayansu alamar wajansa zatazo su gaisa, baki ta ta'be Allah ya d'aukemin wannan jarabar taka, tayi juyawar ta ta shige ciki. Banda gudu ba abinda Mansur yake kwararawa,gundun da sukeji har cikin zuciyar su saboda sunsan laifin su, yana kaiwa gida aka bud'e masa get ya shiga, yana gama dai-daita zaman motar yace ko biyoni part d'ina, atare suji zuciyar su su buga saboda tsabar ts... ~Mom surayya~ [2/15, 11:32 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE Typing MANSURA BY:SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 24 Mansura ganin saura kad'an ya shige part d'in nasa batare da ya juyoba tayi sauri zata shige part d'in Hajo, abazata taji yace "kina shiga sai na canza Miki akamanni da sai ankasa tattance kamannin waye" tsayawa tayi kamar wadda aka kafe, tana mamakin wannan bawan Allah mai gani har hanji, taya ya gane zata gudu shida ba waigowa yayiba? batada mai bata amsa san tuni Rukayya tabi bayansa,dole badan rai yasoba ta nufi part d'in nasa zuciyar ta na rawa bama jikin taba, domin tasan ko taje inda Hajo bazai hana yaje ya karya mata k'asusuwa ba,hakan yasa tabawa kanta lafiya. Shi kuwa Mansur sanin halin nata da yayi yasa saura kad'an ya shige ya juyo da fuskar sa, ta yadda ba kuwama zai luraba,ai kuwa yaga abinda take shirin yi,dan haka yayi saurin kwa'bar ta. Anan falo ta tarar da Rukayya sai rawar
Chapter 24 · 0% Book details