← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 39

Sashe 34

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

k'awata maka ita, zandai fi yadda idan kace zakayi d'an dubarun ku na zamani wanda zai hana samuwar ciki, dan dai ne harga Allah banason had'a zuri a da wannan talikin" Yasan ayanzu duk abinda zai gaya mata ba kalle ta yarda ba, bayan haka bazai iya duguwar magana da ita irin wannan ba duk da kuwa kqkace ita, dan haka yace "to shikenan zan bincika in sha Allah" "Yauwa ko kaifa, yanzu daga nan ina zakaje? dan dai nasan ba aiki zakaje ba sainan da sati biyu" Ba inda zanje yanzu zan shige part d'ina in kwanta kafin zuwa ajima in d'an zagaya, yanzu dai zanje na gaida su Momy sannan" Hajo tace "haba mai sunan Malam kasan dai bazai yuba kabar 'yar mutane ita kad'ai agida ba tunda ba sabawa tayi ba" Tashi yayi tare da fad'in "sai naga ita ai ba k'aramar yarinya ceba da zan zauna da ita cikin gida ina bata tsaro" yana fad'a yayi ficewar sa don gaida iyayan nasa Part d'in Momy ya fara shiga kasancewar itace farko kafin Ummi "lale marhabin da zuwan d'ana kuma ango" Momy ta fad'a lokacin da takejin sallamar tasa, amsawa yayi yana fad'in "antashi lafiya Momy" ya fad'a yana kaiwa zaune kan kujera, "Iafiya k'alau Mansur ya d'iyar tawa fatar tana lafiya?" "Lafiya k'alau take Momy tamace agaida ku" ya fad'a yana sunne kai k'asa alamar waishi kunya Momy tace ina kuwa amsa kwarai da gaske, kaga kuwa tun d'azo na had'a breakfast gashinan akan daninng tun d'azu nake tunanin wazai Kai muku, yanzu nake tunanin fita na tambaye direba ko yasan gidan" Ba damuwa Momy nariga da na karya itama ta karya tacema afad'a muku karma kuce zaku wahalar da kanku zata iya girkawa" Kai ta girgiza tace "baza ayi hakaba itama zata samu ta huta ko na sati d'aya ne" cikin son matar k'anan mahaifin nasa da irin k'aunar da yake mata kamar itace ta haisa ba Ummi ba saboda tarin kulawar ta akan sa yace "Allah Momy da kun batshi tace zata iya, kuma Kinga wurin da d'an jayawa" "Hakane kuma! amma sai nake ganin kamar ba akyaut mataba ta farayin girki tun yanzu" bai tsaya mata amsa ba dan kawai ashare wacce magana yace "ina Abba ko ya fotane?" Dukda ta fahinci dan baison maganar ne shiyasa ya d'auko wata daban sai tabasa amsa da cewa "yananan yashiga wanka ne shine ma nake k'ok'arin had'a masa breakfast, kaima nasan zakaci tunda mutuniyar kace waina tun d'azu ma na aikawa Hajo da tata" kafin yabata amsa saiga Abba yafito cikin shirinsa na manya kaya da alamar fita zaiyi "Ina kwana Abba" y fad'a lokacin da yake k'arasowa gun su "lafiya k'alau son ya amarya" Yace "lafiyarta k'alau Abba" "Masha Allah haka akeso" Abba ya fad'a yana zama kan kujerar dake dinning "Abba ina zakaje da safennan?, tunda yau badai aiki kamata yayi ku zauna agida yau ku huta kafin zuwa gobe gashi jiya kunsha zirga-zirga" Abba yayi 'yar dariya kafin yace "in banda abinka son sukuma bak'in da suka rage basu komaba muyi yaya dasu? dole dai sai munje munyi musu godiya da kuma sallama dasu, kagama tun d'azu Yaya ke kirana ni kad'ai yake jira" ya fad'a yana nuna masa kiran Dady da yake masa kafin ya daga yace masa gashinan fitowa zai karyane. Mansur yace "to Abba bari naje mu gaida kafin ya fito" to shikenan nima ganinan zuwa, amma da katsaya muci wainar mana?" "A,a Abba naci gun Hajo sannan nayonan" "To shikenan" ya tashi yanawa Momy sai anjima sannan ya fita. Zaune ya tarar dasu afalo suna fira baidai san maganar da sukeyi ba, samun wuri yayi ya zauna yana gaishesu, amsawa duk sukayi tare da tambayar iyalin na, ya amsa musu da lafiya k'alau, Amina ce wacce ke bima Rukayya ta fito daga cikin d'akin su, ganin Yayan nasu tayi sauri zata juya ta koma cikin d'akin amma sai taji yace "ke zonan!" dole ba yadda zatayi ta jiyo jikin ta na k'yarma tazo ta zuk'unna "gani Yaya Ina kwana?" harararta yayi yace "Rik'e gaisuwar take, da bankirakiba bazakizo ba kennan gaida ni?" Ahankali tace "kayi hank'uri Yaya" "Mi yahanaki zuwa makaranta yau?" ya jefo mata tambaya da taso hargitsata dun cikin 'yar tsawa yai mata tambayar, shiru takasa magana saida ya koma daka mata tsawar da saida dady yace "imata ahankali mana Mansur, haka ai sai yasa takasa baka amsar" "Ummi tace "kyalesu Dadyn su ya horar dasu, ba yadda banyi da yarannan su tashi suje makaranta amma sukace sun gaji ba inda zasuje sai gobe tunda karfe 03:30 darabi zasu dawo, kaga yanzu sai su fad'a masa tunda ni sun rainani?" Tuni hawaye har su sami muhalli akan fuskar Amina, Allah da tasan zaizo yau da bata biyewa Khadija ba,yanzu gashinan ita tana baccin ta hankali kwance ita ko tsautsayi ya fidda i... Maganar sa ce ta katse mata tunanin da ta fad'a yana fad'in "minti biyar na bako maza kozo direba ya kaiku inba hakaba jikinkune zai fad'a muku" Aima kafin yakai ga karasawa tuni ta mik'e tayi hanyar d'aki dunbin umarni da ya bata, bayan ta shigene Dady yace "kazanka binsu ahankali Mansur ko zasu rage tsoronka, kasan akwai gajiyar biki ajikin su dole su buk'aci su huta ko na d'ai ranane" kafin Mansur yakai ga magana wayar Dady tayi k'ara, ganin wadda ke kira ya mik'e yace "to nidai na tafi sai nadawo" adawo lafiya suka masa. Amina ce itada Khadija suka fito ko wane sanye da tufafin makarantar islamiya ba wanda yasamu arzik'i wanka acikinsu tunda minti biyar ne ya basu, Khadija ma alamun bacci ne a idanuwan nata dan tana cikin sa Amina ta ta data, dole tayi saurin mik'ewa dunji daga inda umarnin yake, harararsu yayi yace " uwar mi kike jira bazaku jeba" cikin hanzari suka kama hanyar fita, tashi yayi yawa Ummi sallama yabi bayan nasu. Saida ya gargad'i direban cewa duk ranar dasukace bazasu makaranta ba ya kirashi ya fad'a masa, idan ba haka zai 'bata masa da rai, dole sunaji suna gani suka shiga motar direba yaja suka tafi shi kuma ya koma part d'in Hajo ya kwanta Shine bai tashiba saida aka kira sallar azzahar sannan yaje yayi wanka tunda akwai kayansa da yawa wadda baikai can gidan ba acewar sa akwai ranar buk'atar su, sallama yayiwa Hajo yace daga can sai bayan isha zai dawo ya fofito zuwa masallaci. Saida yayi sallah sannan ya kira Jabir yace gashinan zuwa. Tunda Jabir yaga fitowar Mansur amota ya fara da tsokanar sa da fad'in "ango-ango, ango kasha- ango kash... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 36 "Kaifa banza ne wani lokaci wallahi, basha naiba canyewa nayi' dariya Jabir yayi tare da fad'in "haba nawa yada haka kuma? kaida nake tunanin kafin asaka a idanu sainan da sati biyun da kad'auka saboda cin amarcin" Hararar sa yayi yace "wai miyasa kake kamar bakasan komai ba ne! kai kasan yadda aurannan ya kasance, amma kake min wata magana daban, kai kasan ko mata sun K'are ba abinda zanyi da wanan k'azamar da ko wane banza yasani" "Allah yabaka hank'uri muk'arasa daga ciki zaifi" bai ce masa komai ba yayi gaba abinsa, shi kuwa Jabir ba abinda yake sai dariya ta shak'iyanci yana bin bayan sa dashi tuni har ya shige falon. Koda ya shiga ya tarar da Mansur agaban Momy suna gaisawa tana tambayar iyalin nasa shi kuwa yana amsawa da lafiya k'alau, samun wuri yayi ya zauna gefen da yake zaune shima har yanzu da dariya abakin sa, "Kai kuma lafiyar ka kake wasar baki haka sai kace wadda akama al bishin wani abu?" Momy ta tambaye sa tana kallo Jabir d'in "Rabo dashi Momy kinsa halin wanan sai abarsa" Mansur ya fad'a yana hararar Jabir d'in "Kyalesa Mansur ai kai kayi kyau kai tunda kai kayi auran ka huta kafita daga layin gwarraye, shi ya tsayawa mutane yawo da hankali, anason masa gata yana gujewa, ana nuna masa gabas yana kauda kansa" Mansur cikin son tunzara abokin nasa yace "ai Momy kamata yayi anuna masa isa saidai yaga amarya ta tare ba atsaya na binsa yadda yake so" ya fad'a yana murmushin k'asan le'be. "Hakama za ayi Mansur ka kawo shawara mai kyau, idan yaso ranar da akakaita ya maido mana da ita sannan zamu tabbatar da lallai bayason auran" ta fad'a alamar har k'asan ranta take maganar "Haba Momy yazaki biyewa ta wannan, kamata yayi nima atsaya abi ra ayina" Jabir ya fad'a yana kallon Mansur, kallon dake nuna burinka yacika kaji dad'i na zuga Momy da kayi "Allah yabaka hank'uri nifa shawara kawai na bada, amma Momy tunda abokina bayason akyalesa har yaga tsofewa awaje" Ganin abin nasa harda renin wayo aciki yasa ya tashi cikin d'an fushi yayi d'akin sa, dariya duk sukayi suna bin bayansa da kallo, Momy tace raboda shi kawai zai dawo kan hanyane koma wallahi wannan maganar taka ayau tasani atunanin dole haka za ayi" "Allah nifa Momy da wasa nakeyi karkisa abokin nawa ya k'ullaceni, kabari yasamu wacce yakeson ya aura kar azo yarinyar tak'ijin dad'in zama dashi tunda bayaso Kinga ita za afi cutarwa dan Allah Momy " alamar rok'o "Naji zanyi tunani" tace dashi kawai badan zata janye da k'udirin taba "Godiya nake Momy, bari inje in lallashin katana dan nasan na konnashi yau" yana gama fad'a ya tashi yanabin bayan nasa. Bakin gado yasamesa azaune yayi tagomi, duk da yaji shigowar tasa amma ko d'agowa baiyi ba alamar zuciyar maza akusa take, sanin halin abinsa da yayi yasa yayi murmushi yana k'arasawa kosa gare sa yana dafa kansa tare da fad'in "angon nan kusa yane?" hannunsa dake akansa ya janye tare da cewa "mi yakawoka wajeba kuma? kaje ka k'ara kitsa mata mana, ka kyauta babu komai" "Haba abokina yada hasala haka? nifa gata nakeson maka kayi aurannan naka bako sisinka" "Bana buk'ata ka rik'e gatan naka" k'aramar dariya yayi tare da dafa kafad'ar sa yana rera 'yar guntuwar waka "ABOTA MUKEE, SON JUNA MUKE BA FA'DAA.... kafinma ya k'arasa Jabir ya katse sa da fad'in "yaushe ka koma mawak'i banida labari?" "Ranar da kafara fushi dani mana, ai dakabari in k'arasa wak'ar zatafi armashi
Chapter 34 · 0% Book details