Sashe 28
Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tayi falon. Shigarta falon dai-dai da Hajo na k'ok'arin tashi ko ina zataje? oho, ganinta yasa ta koma ta zauna tana fad'in wannan wane irin rasahin mutuncine haka, kinajina amma bazaki iya amsa niba dan mugun hali, kema kinason kizama Mansura ko? wallahi su Amadu basu haifu d'iyaba ko wane da nashi kallar mugun halinsa" dariya Rukayya ta sanya tana fad'in "dakata Hajjajo karki zaganmana iyaye ehe, kufa da kike kirana ina wani abinne, kuma yanzu bagani nazoba" Harararta tayi tace "aikin naki yafi kiran nawa muhimmanci kenan?" "Nifa bakiji abakinaba ehe" "Nidai maza ki gyaramin falo da kuka gama haukatawa haka, tunda kema naga yanzu kin koyi rashin kunya" bata koma cewa komaiba ta shiga gyara wajan dan taga yau itama Hajon fad'a takeji, tana gamawa tayi part d'in Ummi. Mansur yana shiga d'aki basket ya ajiye akan k'aramin daning dake cikin d'akin, ya zauna gefen gado yana dafe kansa, miye haka da nayi ni jikan mutun hud'u? yanzu wannan tsohuwar sai ta fassaramin da wani zance daban, yana cikin wannan tinanin yaji k'arar wayar sa, sai yamaida hankali ga wayar, ganin mikira yaja k'aramin tsaki yana mai janyo laptop ya bud'e danyin wani aiki, ganin bazata daina kiran nasa ba sai ya cirewa wayar tasa k'ara tak'arashi kiran nasa ta hank'ura, ya maida hankalinsa ga aikin da yakeyi. Bashhama ta shiga damuwa ganin kusan 10 missed call bai d'aba, amma dunda haka sai tace baya kusa da wayar dan babu ta yadda zaiga wannan kiran ya k'yaleta,dan haka ta yanke hukuncin tura masa da message kawai. Washe gari Mansur yana dawowa amasallaci bayan yayi azkar d'in da zaiyi ya d'au basket d'innan najiya ya shiga d'akin Hajo, akan sallaya ya tarar da ita alamun bata gama azkar d'in nataba, bayan tagama ya gaida ita ta amsa, sannan yace "Hajo dan Allah ga wanna tuwon ad'umamin shi incishi kafin na fita, dama tun jiya yana gama aikin nasa na fama ya d'au lemon ya Sanya acikin firjin' kallon sa Hajo tayi sama da k'asa kafin tace "Wazai maka d'umame anan? kaje ka kaiwa matar taka mana ta maka" kallon nata yayi yace "haba Hajo miya kawo wannan maganar kuma anan dan Allah? nidai dan Allah gashinan amin inason kumawa bacci kuma inason koda nake tashi anyi ci d'ai zanyi na huce" "To sannu mijina ko kuma nace ubana ba" "Mijin dai dan Allah karki kaine inda banjeba,dama kinada wani mijinne bayan nine?" "Cewa tayi koma miye kabid'i wacce zatama amma nidai bazanyi ba" "To shikenan tunda bazakiyi ba, ai inada wacce na isa da ita zansa tamin" "Oho dai, kasan da itane kake kwaso gwamammin k'afafuwan naka kazo guna" baice mata komai ba ya d'au wayar tasa yana kira, bayan an d'aga ya gaida ita da kwana sannan yace dan Allah Ummi Rukayya tazo ta d'au fa tuwo nan falon Hajo ta d'umamamin shi" amsawa Ummi tayi da shikenan yanzu zatazo, ya yanke wayar yana mik'ewa tsaye tare da d'aukar basket d'in ya ajiye afalon, "saidai can, dan nasan Rukayya ce kawai zakasa tayi maka akwashe lafiya, da na d'auka Mansura zakasa" cewar Hajo, shidai baice mata komai ba yayi ficewar sa. Koda ya tashi kuwa Rukayya tazo ta masa ta d'ura masa akan daning,dan haka yaje ya d'auko lemon dake firjin'yayi karinsa mai rai da lafiya, sannan yayi ficewar sa office. Aiki fa yasamu Abida dan kusan kullun sai tazo ta koyawa su Mansura wani kalar abinci daban, kuma sai ta fahinci sun gane sannan take tafiya, hakan ba k'aramin dad'i yake musuba hakan yasa suke maida hankalin su sosai agare ta, ahakan suka canye hutunsu na makaranta yanzu haka saura kwanakki ukku su koma makarantar tasu. Yaune Bashhama zatazo gaida su Hajo,domin kusan sati d'aya kenan da take rok'on sa da tanason tazo ta gaida iyayansa amma yak'i bata damar zuwa,sai jiya da taramesa harda kukan ta akan kodai bayason tazo taga iyayansa da 'yan uwan sa, domin ta sansu su santa ko dan watarana, yace mata zaiyi tunani amma tai tarok'on sa dan Allah ya barta tazo yau tunda juma'a ne, to shine fa yace tazo. Da safennan da ya tashi yake gayawa Hajo, Hajo tace shikenan Allah ya kawota lafiya, sannan ya fita domin sanar dasu Ummi. Mansura dake cikin d'aki takejin maganar su tace "ashe yau akwai abu agidannan dan wallahi sai ta rama wulak'ancin da yake mata agidannan,badai zai kawo budurwarsa agidannan, wazai takali kunama abanza akwashe lafiya, itakad'ai tasan abubuwan da zatayi ayau d'inan. Misalin 3:06 wata mota tasanyo kanta cikin gidan bayan mai gadi ya bud'e mata. tunda dama ansanar masa za ayi bak'uwa, parking tayi adaidai ma ajiyar motoci, fitowa tayi cikin wata shigeyar matsatsar riga da takama dukan ilahirin jikin ta, sai kace idan tayi wani k'wakk'waran mutsi zata rabe gida biyu, kannan nata yaci uban k'arin gashi ga wasu takalma da tasanya masu uban tsini sai kace ba wacce tazo gaida surukkai ba, ba abinda ta sanya akan nata sai wani k'aramin gyale wadda koda d'an shekara goma bazaiyi amfani dashi ba, wai ahakanma dan za agaida surukaine amma da ahakan za afita. Duk ma aikatan gidan binta sukayi da kallo da tambayar wannan kuma daga Ina? basuda mai basu amsa dan haka suka kama bakunnansu, gidan takebi da kallo tana tunanin ta ina zata fara, tunda dai kusan part hud'u ne agidan, rasa inda zata shiga yasa tawa wani hannu cikin ma aikatan gidan, tambayarsa tayi akan inane part d'in Hajo, ta fad'i hakane domin yawanjin sunanta abinsa da takeji, da hannu ya nuna mata shi dan haka kai tsaye can ya nufa. Tunda motar tashigo Mansura da ta fito part d'in Ummi tabi motar da kallo ganin ko wanene da addu ar Allah kasa budurwar Yaya Mansur ce, tananan atsaye taga ta fito tana dube-dube har lokacin da ta tambaya aka nuna mata part d'in takuma nufi can yasa taja tsaki tace ko Ina kuma Hajo ta kwaso wannan jikar inyamurai, domin dai daga ganin wannan shigar bata Malam bahaushe bace, dan haka ta nufi part d'in Momy. Bashhama kuwa na kaiwa bakin k'ofar falon shiga da sallama, Hajo dake zaune acikin falon kan kujera ta d'ago kanta tana amsa sallamar, ganin tayi tsaye bata k'arasuba yasa tace "bismila k'araso mana ki zauna, Bashhama ta k'arasa kan kujera ta zauna tare da gaidata anan zaune kan kujerar, amsawa tayi tare da fad'in 'yan mata daga ina? domin ban wayeki ba" K'asa Bashhama tayi dakai tace "nice wacce Mansur zai aura" fad'in wannan maganar dai-dai akunnan Mansura dake son shigowa yanzu tace "kan ubannan, dama wannan inyamurar zai aura? lallai Yaya Mansur an fad'i ba nauyi tad'i" kallon takallmin dake bakin k'ofar ya tabbatar mata da natane ta duka ta d'auke ware d'aya tayi can cikin fulawoyin gidan dashi ta 'buye sannan ta jiyo ta dawo. Itakon Hajo mamakine ya k'ameta azaunan da take har takasa magana,cikin ranta take fad'in "oni Hajo, yanzu sabida Allah mai sunan Malam ya rasa wacce zai aura sai wannan abin" dak'yar tasamu ta fisgo magana tace "to,to dama ya fad'a mana zakizo ya iyayan naki?" amsawa tayi da "lafiya" dai-dai man Mansura ke sallama tana shigowa, Hajo tace "yauwa Mansura je ki gayawa iyayan ki ga 'yarsu nan ta k'araso" baki ta tura gaba "kai Hajo da shigowata" tana gama fad'a sai ga Rukayya ma tana shigowa tace "bari inje in sanar dasu Hajo" dayake taji komai "yauwa 'yar albarka jeki" zama Mansura tayi kan kujera bata ma kalli inda Bashhama takeba bale tasamu arzik'in gaida ita, Hajo dai batace komaiba tunda dai bak'uwa akusa bai kamata asaida hali ba sai cewa da tayi "kawo mata ruwa sai kuma ki kawo mata abin ta'bawa" "Kai Hajo badai zaki barni in hutaba sai kinsani aiki" hakadai ta tafi tana k'ananan mitoci, dai-dai nan su Ummi ke shigowa falon, suma dai da mamaki suke kallon ta matsayin matar da d'an nasu zai aura, dak'yar suka samu amsa gaisuwar da take masu,sumadai kamar Hajo akan kujerar ta gaidasu,zama dukaninsu kayi da tambayar 'yan gidansu ta ansa da suna lafiya, Mansura ta ajiye tiran da ta d'auko bayan ta gama k'eta aciki, ruwan gorane saida ta tsaya ta 'bude ta zagga musu gishiri kayan ma da ta d'auko saida tabi d'aya bayan d'aya ta zuba gishiri tayadda ba abinda zaiciyo, acewar ta kayan gidansu na masu mutuncine ba irin wa d'annan ba, ruwan ta bud'e ta zuba mata cikin k"aramin kofi ta mik'a mata itako ta kar'ba cikin yanga, sannan duk suka mata ganin anyi abin kwar'e harda duk'awa yayin bata ruwan. Ai cikin sauri Bashhama ta zubar da ruwanda tafara sha sakamakon tsabagen gishin da taji ruwan dashi har tana k'ok'arin yin amai, Da sauri duk suka nufi kanta suna tambayar l.... ~Mom surayya ce~ [2/15, 11:34 AM] mom surayya: https://whatsapp.com/channel/0029Vb6oSrvFnSz2KP83hw32 https://chat.whatsapp.com/JzfdWiIDtVECfU4ZXj6S9F Typing MANSURA BY: SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Page 29 Idanuwanta da har sukayi ja ta d'ago tace "k'warewace nayi" sannu duk sukayi mata tana d'aga kai, ba abinda Mansura keyi sai wani makirin murmushi wadda saida Bashhama ta lura daita, lallai zata koyawa wannan yarinyar hankali domin ta lura yarinyar batada kunya kuma ta fahinci tsaf da gangan ta aikata mata wannan abin, amma tajira zata shigo gidan. Abincin sukace taci amma tace alhamdulillah, hira suka dan soma can sukaji Mansura tace "Ummi dan Allah ki aramana wayarki muyi hoto da matar Yayanmu domin naga tanada kirki sannan kuma tanada kyau" dariya sukayi su dukansu banda Hajo da Rukayya,dan sarai sunga lokacinda take mirmushin wadda ke nuna dukkan alamu na k'etane, "Ummi ce tace "Kai d'iyata bakida dama zo gata kuyi kuma abani abata,nasan idan ba hakaba sunan katina na ciki sorry" dariya Mansura tayi dan tasan gaskiya Ummi ta fad'a, duk ranar da tabasu wayar ta ko suka faki idanunta suka d'aika tofa ranar zasuyi bidiren su da ita sai sunga kona flashing babu sannan fa za amaida mata wayar. Tashi tayi tace "Rukayya zo muyi kar tarehi yazo babu ke" tasuwa Rukayya tayi sukasata atsakkiya, da farko kamar abin arzik'i sun d'auka kusan ukku zuwa hud'u sannan ta danna video ba tare da saninnin suba tace "to aunty ki cire mayafin kinfi kyau ahakan" kafinma tasamu damar cewa wani abin ta janye mata mayafin gashin dokinnan ya bayyana dukda ana