← Book details Mansura Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 39

Sashe 13

Mansura Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tsaya anan zaki muna kuka? maza kije suna jiranki kar ki 'bata mata lokaci" "To Yaya, amma dan Allah zaka d'aura zuwa Muna ganinka ko?" d'an murmushi yayi wadda iyakacinsa le'bensa yace "idan nasamu lokaci zanzo,komaida hankali ga karatunku matuk'ar kunason mushirya" "In sha Allah Yaya zakayi Al fahari damu" ya kad'akai yace "da kyau,je kutafi suna jira" cikin ransa yana mamakin yadda ta kauda kai garesa kamarma batason ganinsa akan tsana. Fita tayi tana sharar hawaye da gefen hijabinta tana waiwayan Yayan nata,tuni ita Masura tarigada ta fita ta tsaya anan barardar office d'in, koda tafito ba wadda yacewa wani uffan sukabi bayan Hauwa. Koda suka shiga cikin hostel d'in kallon d'alibbai kawai sukeyi,wasu wanki sukeyi wasu kuwa suna kitso saboda acikin wad'annan ranarkun sukeyin irin wad'annan abubuwa,suma wasu binsu sukayi da kallo suna tambatar Hauwa sabbi akasamy?, amsa musi kawai takeyi da eh duk wanda ya tambaya,ba laifi makarantar ta burgesu sosai,sannan duk wadda ka gani cikinta d'an wane da wanene sai kuma wad'anda aka taimakawa. Wani d'aki sukaga ta shiga suna biye da ita abaya,da kallo sukabi d'akin da bayada wani makusa garesa,gado shidda ne acikin d'akin alamar zaman mutun shidda ne a d'akin, gadaje biyu ta nuna musu wadda keda bisa da k'asa,wadda d'aya zai zauna k'asa d'aya kuma asama, tana fad'in "to k'annena wannan shine d'akin da zaku zauna,ku shidda ne zaku zauna acikinsa amma ayanzu ko hud'u ne sai idan ankawo wasu daga baya,duk abinda zaku buk'ata zaku iya yimin magana,kuma duk wadda yayi muku wani abin ko kallon banza kusanar dani,idanma baku gane wani abinba komai magana in sha Allah zan fahintar daku" Ruk'ayya ce tace "in sha Allah Aunty,mun gode k'warai da gaske" murmushi tayi mata tana kallon Mansura da batace mata k"alaba saima zaman da tayi bakin gado tana kauda fuskarta, ta kalli Ruk'ayya tace "nidaikan wannan 'yar uwar taki ko bata magane?,naga tunda na ganta banji tayi magaba" Kallon ta ruk'ayya tayi ganin yadda ta k'ara maida fuskarta gefe tana had'e rannan nata, tace "tana magana mana,wani lokaci haka take da kunsaba zakiga ta sake" "Okay shikenan, bari inje inda Inna Mero domin akwashe muku kaya kar wannan da yakawoku yayi jira" "Okay badamuwa mun gode Aunty" tayi dariya tace "kar kidamu kinji,kud'in ai k'annenane" ta fad'a tana barin d'akin. Harararta Mansura tayi tare da dad'in miye nawani biye mata Kona magana haka harda wani fad'a mata haka nake?" "To miye laifina anan? bakya ganin yadda ta mana k'ok'ari" tace "ai bamu mukasakata ba sata akayi, kinga dole ne tayi tunda ba umarninmu bane" "Hakane, amma ya akayi banga kinwa Yaya sallamaba har kika fito?" "Sallamar mi zam masa tunda dama yagaji da ganinmu, miye zan 'bata lokaci namasa sallama,ba munbasa wajan da muka tare masaba? sai yaje yasha iska" "Kai Mansura,wallahi ki daina wannan rik'o macce kike" "naji mama ta" "Allah yabaki hankuri,ni bani nakai zomon ba,rataya ma ba abaniba" Mansur kuwa yana a office d'in shugaban makarantar zaune yana jiran wadda zatazo kwasar kayan suna d'an magana da shugaban kad'an kad'an,suna cikin hirar ne sukaji sallama, Inna Mero ce ta shigo tare da dur k'usawa tana gaidasu tare da dad'in "gani d'an la'bai" Umarni ya bata taje da sauran su kwashe kayan dake mota, tace "to shikenan wace motar ce?" "A motar wannan kije waje gashinan fitowa yanzu" tashi tayi ta fita domin bin umarnin da akabata,bayan ta fita Mansur yayi masa sallama had'e da godiya,yana k'ara jajjada masa akan dan Allah ya kula daso,kuma duk abinda yaga sukayi ba dai-daiba yayi misu hukunci. "Kar kadamu kanka indan wannan ne,in sha Allah zan kula dasu k'warai da gaske,kuma zansa wad'anda zasu kulamin dasu acikin hostel da makarantar tunda bazaiyi yawo tare dasuba. K'warai Mansur taji dad'in haka kima hankalinsa ya kwanta ayanzu,amma wannan yarinyar na dank'are acikin ransa na yadda tayi masa,amma zata gane batada wayo, fitowa shugaban makarantar yayi domin masa rakkiya, Anan bakin office sukaga Inna Mero tsaye tana jiransu, batare da sunyi mata magana ba sukayi gaba tabi bayasu,dama sauran da zasu kwashe kayan tuni sunje inda sukasan ana aje motoci suna jiran fitowar su,atsaye suka tarar dasu gefe d'aya suna jira,tunda basusan motar ba koma motocin da yawa, suna ganinsu sukayi saurin k'arasowa suna gaidasu, shugaban makarantar kawai ya amsa shi Mansur kayan dake mota ya shiga fiddawa kafin yaje gana baya motar,sukuma suka shiga kwashewa sunayi cikin hostel d'in,dama su ukku ne har Inna Mero su hud'u,saida suka kwashe kayan gaba d'aya sannan Mansur yayi musu ihisani suna ta godiya, nan sukayi sallama da shugaban makarantar yanajin kamar yaje yak'ara ganinsu kafin ya tafi amma bayason ruk'ayya tayi kuka dan yaga itace mai damuwa,dan wacce zuciyarta ta mutu,haka yabar harabar makarantar yana mikewar 'yan k'annan nasa. A'bangar Habib kuwa koda safiya ta waye duk yafita hai yacinsa saboda cizon sauro,idanunnan nasa sunyi zurun-zurun kamar kazar da aka tsame aruwa, kafin gari ya waye harda hawayansa dan shi dama baya da taurin zuciya, haka yake kamar macce,yanaji ana sallah amma ba wannan aransa,da aka kawo masa abin karima anan ya fita batunsa dukda yuwar da yakeji,dan rabonsa da abinci tun wadda yaci kafin suzonan. Sai wajajan sha biyu da yaga ba rawa sai tumami ya d'auka bayan yagma sanyi,kuma sunce idan yana Kai dare idan bai cisaba bazasu bashi waniba sai gobe da safe,dan sunan basu iya almuzaranciba, yaka yakeci yana ruwan hawaye, da yagama ci ya d'au ruwa yasha sai yaji zuciyarsa na tashi kamar zaiyi amai... ~Mom surayya ce~ https://chat.whatsapp.com/HR79LoL1DdlDSXsllPK3fE?mode=ac_t Taping MANSURAS BY; SARATU MOHAMMAD MOM SURAYYA Wannan littafi na kud ine akan 500,shedar biya itace 2729922771 Saratu Mohammad zenith bank, ko kuma kati na MTN ta wannan number 07089530588 Paid book Free page Page 8 Allah ya taimakesa baiyiba ya zauna yana maida numfashi,yana ahaka sai yaga d'ai daga cikin police zai huce,hannu ya d'aga masa alamar yanason yazo, kallon sa yayi yace "inzone?" "Eh dan Allah inason magana dakai" zuwa yayi yada makulli ya bud'e ya shiga, "gani mikakeson cewa?" "Dan Allah zan tambayane ko Dady na yazo?" "Eh yazo jiya kusan sau biyu" "To amma miyasa baizo ya ganninba? har nakwana anan cikin wannan wajan" "Ai bazai ta'ba ganinka anan ba sai anje koto" "K'warai da gaske,dabma kafidda rai da ganin wani naka" "K'aryane wallahi,nasan Dady bazai ta'ba barina har ashiga koto,banyi wulak'antar da harzankai ga haka" "Wannan kuma kai akeji, idanma zaka kwantar dakai ka kwantar ko zaka samu sassauci, kuma ina maibaka shawara idan anje ka kar'bi laifinka ko za adubamaka" "In kar'bi laifi fa kace? ai wannnan ne bazai ta'ba faruwa ba" "Jiki magayi, idan kad'au maganata to, idanma baka d'auka ba kai kajiyo" yana gama fad'a yaja k'ofar ya koma kulle sa yayi gaba abin sa. Acan makaranta kuwa bayan angama kashe kayan Hauwa ce tazo ta tayaso shirya kayansu aka ake komai amuhallinsa,sunayi tanajansu da hira harsuka kammala, duk dayake yawancin firar tsakanin Hauwa ne da ruk'ayya,dan Mansura kamar ma bata wajan, Hauwa ta lura da wannan yarinyar miskilar gaske ce,amma duk yadda take zata bisu domin samun abinda takeso, dan agaskeya takamu da soyayyar sa, koma da yadar Allah zatayi duk yadda zatayi domin ta samesa. Mik'ewa tayi gani sun gama tace kuje kuk'ara hutawa,akwai abokan zaman naku zasu shigu sun fitane,amma nasan duk inda suke zasu shigo yanzu,nasan zakuji dad'in zama dasu dan basuda matsala" "Okay shikenan mun gode k'warai Aunty,kinada kirki sosai" "Bakomai ruk'ayya,ai yiwa kaine,kuma kun riga da kunzama k'annena" "Hakane Aunty" nan tayi musu sallama ta fita,sukaci gaba dazaman shiru,dandai Mansura ba wata firar arzik'i takeyiba. Sunnan shiru dan ita Mansura har bacci yafara d'aukarta, sai ga wasu matasan 'yan mata sun shigo da sallama kyawawa dasu,da mamaki suke kallon su ruk'ayya, d'aya daga cikinsu tayi saurin k'arasowa tace "ashe mun samu 'yan uwa bamuda labari" ta fad'a tana kaiwa zaune kusa da Ruk'ayya. Dariya Ruk'ayya tayi tace "eh muzo tun d'azu" "Masha Allah, gsky naji dad'i sosai" d'ayar ma tazo ta zauna kusa dasu tana nunajin dad'in ta,sai ta kalli Mansura dake kwance tace "wannan lafiya take kwance?" "Lafiya k'alau bacci ne kawai" "okay, ni sunana Zainab Ibrahim, wannan kuwa Asma u Aliyu" ta fad'a tana dafa wacce ta fara magana acikinsu, "fatar zaku bamu had'in kai mu zauna lafiya?" "In sha Allah idai wannan ne kar kidamu zamu zauna lafiya dani har 'yar uwar tawa" Wadda aka kira da Asma u Aliyu tace " ni gobe indan Allah yakaimu zan cika sati d'aya da zuwa,ina j,s,s1a, Zainab kuwa yau take kwana uku da zuwa, kar injaki da dungun surutu ahankali zamu fahinci juna" Ruk'ayya ta girgiza kai hankalinta na kwanciya da wad'anda Allah ya had'asu awajan zama. "Kinji namu suna sauran ki fad'a mana naku" cewar Zainab tana kallon Ruk'ayya Ruk'ayya tayi murmushi sannan tace sunana Ruk'ayya Idris, sister na kuwa, Mansura Ahmad, mud'in family ne domin iyayanmu wane da k'ane" "Masha Allah,to Allah yabamu hank'urin zama" nan suka ci gaba da hirar su kamar sun dad'e da sanin juna,dama haka Ruk'ayya take batada wuyar sabo,daka zauna tare da ita dandanan kun saba,yarinyace mai faran-faran,dan yawancin k'awayansu duk sanadin Ruk'ayya ne, Mansura itace mai wuyar sabo,dan kafin kusaba sai an kwana biyu. Duk yawancin firar da sukeyi akunnan Mansura dan baccin nata bamai nisa bane,kuma batada nauyin bacci,amma hakan baisa ta tashiba saida taji fitsarin da takeji ya matsa mata sannan, tashi tayi zaine tana mai zuro k'afafuwanta k'asa daga gadon da take zaune, kallon ta Asma u tayi tace "sister kin tashi?" Kai ta d'aga mata alamar eh,sauka tayi daga kan gadon tace ma Ruk'ayya "anyi salla ne?" "Bansaniba gaskiya" Asma u tace "anyi sallah,muma itace mukazoyi amma ganinki yasa mun muce" 'yar dariya Mansura tayi yace ko yashi kuje kuyi tun lokaci bai k'oreba,dan idan kuka biyewa surutun wanna bazakuyi sallar ba" tafad'a tana nuna Ruk'ayya. "Mikike nufi da idan suka biyemin? wato gani suda sarkin surutu ko! duk surutuna nakaiki?". Itadai bata kulataba kar lukacin sallah ya huce,ta shige bayi ta barsunan. Tana fitowa suka shiga da d'ai-d'ai sukayi arwalla suka tada salla. Mansur koda ya isa gida ruwa kawai ya watsa ya kwanta bacci,domin yau lahadi ba office kuma baiyi bacci da wuriba sai kusan uku da rabi, saida kiran sallar azzahar ya tayar dashi sannan yaje yayi sallah,da yadawo 'bangaran Hajo ya
Chapter 13 · 0% Book details